Showing 3001 words to 6000 words out of 100561 words

Chapter 2 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

453

ya wuce ya fice da ga cikin gidan..ta na jin har lokacin da aka mayar da gate aka zuge amma ko motsi ta gagara yi in banda hawaye ba abunda ya ke shatata a kan kyakkywar cute face d’inta.

Ta jima a wajen ta na kuka sosai zuciyarta ta na wani kalar k’una da suka…ji ta ke kamar ta dauwwama a wajen kawai dan inda ta nufa shine waje mafi k’untata a gareta!
Ko zancen sunan gidansu sam ba ta so ta ji an yi a rayuwarta domin kuwa memories na d’aci da k’uncin da ta shak’a a gidan nan ba na wasa bane, tsaf suke sake tarwatsa mata duk wata ragowar nutsuwa tata…


A wajen ta yi sallah, tukunna ta nufi gate zuciyarta kamar za ta burtso waje.
Dama ita mai gadin ya ke jira dan haka ta na ficewa ya mayar da k’ofar ya rufe ta shima ya wuce dan wani ne daban zai zo ya zauna a gidan su kam shi da ragowar masu yiwa gidan hidima sai in mai gidan na su ya dawo tukunnna suma za su dawo.


Ba ta damu ta hau abun hawa ba saboda a ganinta azabar tafiya za ta iya rage mata zafin da zuciyarta ta ke ciki sannan ta gwammaci tafiyar akan ta yi saurin k’arasawa gidansu, shiyasanya ta zab’i ta tafi a k’afa…

Tafe ta ke iskar la’asar d’in da ta taso a sakamokon Hadarin da ya yi gangami ta na kad’ata amma gaba d’aya zafi da k’uncin da zuciyarta su ke a ciki sun k’i su barta ta shak’i sanyi ko da guda d’aya ne…
Wani irin zafi k’ofofin hanci da kuma fatarta su ke zuk’ar mata zuwa cikin jikinta….memories d’inta ita da shi ne kawai su ke dawo mata
Tabbas a yau d’innan ta yarda ta kuma sake tabbatar da masifaffiyar k’aunar da ta ke yiwa mutumin da ta tsana fiye da kowa a rayuwarta a da, womanizer, mutumin da ya tarwatsa rayuwar y’ar uwarta, mashayi kuma matsafi, mutumin da bata tab’a tunanin za ta so shi ba, mutumin da a baya ta ke tunanin za ta iya halaka shi muddin babu zunubi sabida tsananin tsoro da tsanar da ta ke yi masa…

Akwai d’an tazara tsakanin gidan nasu da inda ta baro dan haka sai gab da Magriba tukunna ta k’arasa unguwar tasu (mariri).

Tun a k’ofar gida ta tarar da dandazon mutane dan haka ta sadda kanta k’asa kawai ta shige ciki ta na mamaki…
Nan cikin gidan ma mata ne sosai mak’il wannan dalili ya sanya tsoro ya fara game ta.

K’ofar d’akin Annen ta su ya fi jama’a dan haka a take k’afafuwanta su ka d’auki karkarwa, saboda zullumin jin mai ya faru…
Furucinsa na k’arshe ya shiga dawo mata…. A take kwakwalwarta ta dilmiyar da ita chan wata duniya mafi ban tsoro……
Kamar a mafarki ta ji an dafa ta dan haka ta shak’i wani numfashi mai sauti a take hankalinta ya dawo cikin gidan.
Ta na juyawa su ka yi ido biyu da Adda dan haka ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a lokaci guda kuma ta na tambayarta “mai ya faru?”
Cikin tsantsar damuwa Adda ta ce “kina fita Aliya ta sauk’a (ta haihu)
Sai dai ita ta yi doguwar suma d’an nata shi kuma ya koma
dan har an tabbatar mana duk sun rasu ne ma da farko sakamokon yadda ta yi saboda hatta Likitocin suma duk sun d’auka ta Mutu ne, sai da aka zo gida ana fara yi mata wanka ta farfad’o yanzu haka ana ciki ana sake dubata da kuma rarrashinta dan kwata-kwata ta k’i ta yarda ta bada d’an a yi masa sutura….”

A hankali ta sunkuyar da kanta k’asa kamar ba za ta ce komai ba, sai kuma ta ce “Allah ya ji k’ansa…”
Daga haka ta fara k’ok’arin juyawa da niyyar nufar d’akin Adda dan so ta ke yi ta bar wajen…
Da sauri Adda ta ruk’o hannunta sannan ta ce “Amal, sam hakan ba halinki bane ba, yayarki ce fa, kar ki yi haka dan Allah ki shiga ki taya ta alhini ki bata hope da kulawa…”
Juyowar da Amal d’in ta yi ta na mai kafe ta da idanuwanta ne ya sanya ta yin shiru…
Kafin chan kuma a hankali Addan ta ce “ko ba za ta kula ki ba ki je ki yi mata gaisuwa Amal….ko meye a tsakaninku ki manta da shi for now kin ji y’ar albarka…
Anne itama tun lokacin da gawar Aliya ta shak’i numfashi ta bud’e ido ta sume har yanzu ba ta farfad’o ba, ki shiga ki ganta ko?“
Kamar ba za ta ce komai ba yanzun ma sai kuma ta shak’i numfashi ta fesar kamar d’azu kafin ta ce “Allah ya sa mai ceto ne…”
Daga haka ta fara k’ok’arin barin wajen kawai su ka ga Anne ta fito daga cikin d’akinta a haukace..tun lokacin da gawar Aliya ta yi motsi ta sume sai yanzun ne ta dawo dai-dai.

A hankali matan da su ke cikin gidan suka hau watsewa dan su kam abun kunya ne a wajensu a ce sun zo gaisuwa fad’a ya kaure a gidan dan haka gara su tafi dan kakaf d’insù sun san babu mai iya controlling Anne sun riga sun sani…

Dan haka suka fara ficewa one by one…bai fi mutum uku bane su ka yi saura.


BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*02*

Ko bi ta kan su Adda Anne ba ta yi ba ta nufi k’ofar d’akin Sajida a zuciye.
Adda ta san me ta ke shirin yi dan haka ta yi saurin bin ta a baya ta na kiran sunanta da niyyar tsaida ita tun kafin ta janyo musu bala’in da za a b’atar da su gaba d’ayansu.

A rufe su ka tarar da k’ofar d’akin nata dan haka Anne ta juya ta nufi k’ofar band’akinsu ta rarumo manjagarar da idanunta suka sauk’a a kai ta nufo su ba tare da ta saurari Adda wadda ta ke cewa “A’a fa! A’a!! Haba Anne kamar ba rasuwa aka yi mana ba!?”
Dai-dai nan Sajida ta bud’e k’ofar Allah ya taimaketa Anne ba ta kai ga sauk’e manjagaran nata ba.
Da sauri Sajidar ta d’an jaa baya dama hayaniyar ce ta farkar da ita daga b’arawon barcin da ya kwasheta yanzunnan, har ta kaita ga fitowa.
Cikin tsantsar mamaki ta ce “Subahanallah, Anne lafiya ki ke kuwa? Mai ya faru?”
Ta yi tambayar ta na mamakin dalilin da zai kawota k’ofar d’akinta a hakan.
Cike da tsana da bak’in cikin da yau ya gagara b’oyuwa ta ce “kar in sake ji kin ce mini Anne, kira ni da Nuratu kawai tunda ni ba uwarki ba ce ba…”

Sosai Sajida ta ji haushin abun amma sai ta shanye fuskarta na nuna alamun rashin jin dad’i ta ce “Anne yau kuma? Har mai ya yi zafi haka? Mai ya faru ne kwana biyu wani abun na yi wanda ban sani ba?
Inda kara kam ae kema uwata ce ko?….”
Ta yi tambayar cikin kissa da rainin wayo dan sarai zuwa yanzu ta san mai ya kawo Annen, dama kuma wannan ranar ta ke jira,
yayinda a chan k’asan zuciyarta kuma ta ke yi wa Annen dariyar mugunta na ganin ta ci galaba a kanta yau gashi ta karya lagonta ta fito da fuskarta ta asali..

“Tabbas kin yi komai ma Sajida”
Anne ta furta ranta na k’arasa b’aci tsanar Sajidar ta na dad’a samun matsugunni a cikin zuciyarta, sannan ta d’aura da cewa “kuma wallahi kin ji dae na rantse miki ko za ki mutu sai kin bar gidan d’ana a yau ba gobe ba tunda na lura ba ki da wani amfani a cikin rayuwarmu, mun gama zama da Muguwa marar imani, d’an dae ya rasu ya bar miki duniyar dan haka kamar yadda ya bar duniya kema sai kin bar rayuwarmu bari na har gaban abada…”
Dai-dai nan Amal ta girgiza kai kawai ta juya ta shige cikin d’akin Adda yayinda Sajida ta saki wani murmushin takaici sannan ta ce “Da farko dai Anne kin san cewa ba ni na yiwa Aliya ciki ba ballantana in d’auki nauyin cikin da haihuwarsa ko?.”
Kafin ta d’aura da cewa
“Tabbas Anne kin tabbata butulu! Saboda a ganina na yi mata bakin k’ok’arina….sannan
kuma yau na sake gasgata zargina a kanki! Wato auroni ku ka yi in zame muku atm machine kenan ko? To wallahi k’aryanki! Dan ba alfarma ku ke yi mini ta hanyar aurena da d’anki ya yi ba ballantana in yi tunanin zan siye ku da kud’i, ki godewa Ubangiji ma da na yarda na zo nan d’in na zauna a D’aki d’aya tak da d’an naki! D’akin da ko store d’in b’angarena bai kai ba a cikin gidan ubana…”
Cikin fushi Anne ta ce “to
ae kuwa a yau sai kin tattara kin bar gidan d’ana kin koma gidan uban na ki……a yau sai kin bar masa gidansa wallahi…”
“Abeg shut up!” Sajida ta daka mata tsawa sannan ta d’aura da cewa “kin bi kin ishi mutane da wani gidan d’anki!! Gidan d’ankki!!! D’aki dae! Ina gidan ya ke? Ki ce mini in bar d’akin d’anki kurkukun da soyayya ta rufe mini ido na shigo shi ban shirya ba…a haka za ki k’are wallahi cikin bak’in ciki, da na sani da kuma tarin failures tunda ke dai you can’t build a paradise for yourself sai aukin yunk’urin sace pleasure d’in wasu ki ka iya…
Allah ya yi miki ni’ima ya baki roof over your head amma saboda rashin gode masa sam ba kya gani sai aukin hangen na gaba da ke…kuma ke ba ki iya nema ba ba ki da zuciya da wayon nema amma kin nace sai kin yi rayuwar d’agawa wanda hakan ya sanya ba za ki tab’a samun jin dad’i a rayuwarki ba tunda ba kya ganin ni’imar da Allah ya yi miki…
Inda ace ma kinada zuciya mai kyau ne to da watak’ila Allah ya dubeki da idon rahama ya bud’a miki yadda ki ke so
Amma mutane kalar ku a cikin al’umma kad’an d’inku ne su ke yin walwala dan yadda zuciyoyinku su ke da muni haka mafiya akasariinku rayuwarku itama take kasancewa mai muni da k’unci…
There is nothing good about you Anne!
Komai naki marar kyau ne.
Ba ki da Hali ko guda d’aya tak mai kyau in akwai shi kuma dan Allah wani ya fad’a mini a cikinku Ina sauraro…”
Ta yi maganar ta na kallon Adda da matan da su ke tsaye a wajen waenda su ka yi shiruu
su ka tsaya jin gulma, dan zuwa yanzu d’ayar ma ta tafi saura mutum biyu, d’aki kuma daga Yadukko sai wata mata.

Yayinda itama Annen kawai ta yi shiru ta na kallonta ta na mamakinta wato dae ita da Sajida ta na mata kallon biri ne ita kuma ta na yi mata kallon ayaba….a tunaninta in ta kashe mata auren Amir za ta ji zafin abun amma a yadda ta fahimta yanzu kam ta san ba za ta ji komai ba, dan haka a take zuciyarta ta k’untata saboda ta so ta guma mata ne yau d’in kamar yadda itama ta saka ta a k’unci.
Amma ba komai za ta san yadda za ta rama ne,but first a yadda ta zaman nan ta sake tabbatar da Yarinyar ba za ta moru ba dan haka dole ta k’ara mata mai….
Jin duk an yi shiru ya sanya Sajida ta d’aura da cewa
“Ko shaid’an na tabbata in ya ganki guduwa yake yi saboda ya san za ki gudanar da duk wani aikin da zai yi.
Y’ay’anki da Mijinki da y’ar uwan Mijinki hatta da y’an Unguwa duk kuka su ke yi da ke!
Ko zaman minti goma zuwa ashirin mutum in ya yi da ke to tabbas sai kin cucesa…ki gaya mini dan Allah ta yaya za ki ga dai-dai?”
Marin da ta deb’o za ta zube mata ne ya sanya ta ta yi shiru ta na bin ta da irin kallon tab’a ni ki ga ikon Allah d’innan…..
Da sauri Adda wadda ta rik’e mata hannun ta ce “Anne mu je D’aki….
Mutuwar d’an Aliya has nothing to do with Sajida k’addara ce kar ki ga laifinta…”
Cikin fushi Sajida ta ce “ae da kin barta ta tab’ani yau da ta san ita ba kowan kowa bace ba wallahi! A yau da sai ta tabbatar da cewa ita d’in k’ask’antacciya ce ba ta da gatan uwar komai, wahalalliya asararriya kawai butulu….”
Cikin d’an b’acin rai Adda ta juyo ta kalleta sannan ta ce “Haba mana Sajida, ya kamar kina jira dama? Rasuwa fa aka yi sannan ga marar lafiya chan a kwance amma ko a jikinki? Meye haka ki ke yi kamar ba a gidan surukan ki ba?”

“Rabu da la’ananniya, shegiya!
Bari ki ga yanzunnan Ina sheme ta sai in ga ta bakin tsiwar…”
Yadikko wadda fitowarta kenan daga inda Aliya ke kwance ta fad’a tana mai d’aga sandarta da k’ok’arin ganin ta saita inda ta ke jiyo muryar Sajidar tun d’azu anata hayagaga da ita domin ita Yadikkon ba ta gani…makaho da basira kuwa tsaf ta saitota tana shirin sauk’e mata sandar Sajida ta ingijeta ita da sandar tata su ka tafi yuuu sandar ta yi gefe itama ta fad’i a gefe warwas dama a buge ta ke ta yi mak’il, ga jiri ta na yi shiyasa tunda ta fad’i ba ta motsa ba, a wajen ta yi kamar matacciya …
Dai-dai da shigowar Baba da Ya Amir waenda hayaniyar su Annen ta fita har wajen da ake zaman makoki dan haka aka ce ‘su shigo su duba mai ya ke faruwa a gidan…’

Kan Yadikko Baba Ya nufa ya shiga duddubata sai da ya ga ta na numfashi da d’an alamun motsi tukunna hankalinsa ya kwanta yayinda Ya Amir ya tsaya yana kallon Sajida tana huci
wadda ko ba a fad’a masa ba ya san ita ce ta aikata wannan b’arna da aika-aikar, gaba d’aya kwana biyun nan ta zama azzaluma
ta zamto marar kunya wata aba daban da bai sani ba…wanda da farko iyaka shi kad’ai ta fara yi mawa a D’aki yanzu kuwa gashi ya ga abun nata ya fara fitowa fili…gaba d’ayanta ta chanja kamar ba Sajidarsa ba…

Ita kuwa Sajida zuwa yanzu ta fahimci Annen ne sarai, da yadda aka yi ta auri Amir d’in ba a haiyyacinta ba ma, shiyasa ta ke kallonsu rass..kuma ba ta shayin yi musu koma meye tunda ta fahimci suma ba su san Allah ba.

Dukda haushin Ya Amir d’in ta ke ji shima sai ta d’an ji tausayinsa, dan yadda ta ga ya kafeta da idanuwa yanayinsa ya nuna he is very broken kamar mai shirin fashewa da kuka..ba k’aramin kalar tausayin ya zama ba.
Wata zuciyar ce ta ce mata ‘har da shi dae aka yi miki asiri ki ka shigo cikin wannan bak’in
Talaucin saboda son kai irin nasu…’
Dan haka a take ta ji tsanarsa ta maye gurbin komai, cikin tsantsar rashin mutunci ta ce “uwarka ta ce ka sake ni…”

A hankali ya sunkuyar da kansa k’asa kamar wani k’aramin Yaro sai ga hawaye….
Da sauri Adda ta ce “ya isa haka. Baba dan Allah ku taimaka min mu kama Yadikko mu kaita asibiti ko d’akinta a samu ta farfad’o, Amir wuce ka je d’akinka ke kuma Sajida ki bar komai for now….”
Cikin tarar numfashinta Anne ta ce “to sannu uwarsa! Wadda ta yi mini nak’udarsa da laulayinsa…”
Kamar Adda za ta rushe da kuka ta ce “Shin ba kya ganin halin da shi gudan jinin naki ya ke a ciki ne?
Ki sarara mana haba Anne, ki bari za a yi maganar wata rana…”
Dai-dai Baba wanda ya duk’a zai d’auki Yadikko ya cewa Ya Amir “zo mu je kama mini ita…”
Da sauri kuwa ya nufi Baban dama neman abunda zai rabasa da wajen ya ke, sai dai kuma bai kai ga barin wajen ba ya ji an ruk’o hannunsa, kasancewar jikinsa a mugun sanyaye ya ke gashi har karkarwa jikin nasa ya ke yi ya sanya Annen ta yi nasarar fincikosa ta dawo da shi baya.
Cikin b’acin rai ta ce “Sannu solob’iyo! To wallahi ba ka isa ba dan ni jarumi na haifa…maza sake ta a yanzu a ta ke! Dan ba ta da wani amfani a cikin gidan nan! Ka saketa Allah zai kawo maka wata…
Ba ta isa ta rafka rashin kunya kuma ta ci gaba da zama da aurenka rangad’ad’au a ka ba wallahi, k’aryanta….”
ta yi maganar ta na kallon Sajida ta na huci, wadda itama Sajidar ita ta ke bi da wani matsiyacin kallo
Ita Anne lokacin da ta ke nacin auren a tunaninta ma za a bawa Sajidar gida ne ta yadda za ta tare ita da y’ay’anta sai gashi ashe uban Yarinyar ya fi su wayo…
‘Gara ta tafi kawai duk wata kissa da asiri an yi amma ta ki moruwa…’
Annen ta aiyyana hakan a cikin ranta, Allah Allah kawai ta ke yi a sallami Sajidar ta san na yi da Ya Amir dan shekaru tafiya su ke yi ba ta da lokaci…

Cikin sanyin murya Baba wanda ya gaji da b’acin ran Anne kwarai ya kalleta sannan ya ce “amma dae kin san ba ki da hurumin sakawa a yi sakin nan ko? Infact auren ma kansa ba ki da hurumin shiga amma ki ka shiga ki ka yi kane-kane ki ka tilasata komai sannan yanzu kuma ki zo da wannan zancen? To bari ki ji ba ki isa ba…!”
Ya k’arashe da d’an zafi…

Tab’e Baki ta yi sannan ta ce “Ina son in ji kana cewa ban Isa ba d’innan saboda ni kuma a lokacin ne nake nuna maka tabbas na isa!”
Cikin juya akalar maganar tata ga Ya Amir ta ce “auren dole na yi maka?”
Kamar ruwa ya cinyesa a wajen haka ya yi, dan a sanda aka yi auren ba ya son Sajida amma yanzu kam sonta ya ke yi kamar hauka…
“Ina fa! Ae ke da shi kun san me ku ka yi har na yarda na auresa…”
Sajida ta fad’a cikin karb’e zancen sannan ta kalli Ya Amir yau kam ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login