Showing 24001 words to 27000 words out of 100561 words
na duniya ba lalle ka gama iya nema mata yafiya ba har ka mutu.."
Sai kuma ta yi shiruuuu, kafin cikin
sauƙe numfashi kawai ta basar da maganar sannan ta ce “faɗa mini sunan asibitin da take, zan zo…"
Saboda kwata-kwata ta kasa daure ci gaba da shaƙar iska ɗaya ita da shi so ta ke yi kawai ya fita....wallahi ko muryarsa ba ta ƙaunar ji.
Ya so su tafi tare amma ta ce da shi ya tafi kawai ba ta gama shawara da zuciyarta ba tukunna….
Bayan tafiyar sa da kamar mintuna arba’in ta shirya tsaf itama ta bi bayansa dan sai da ya wuce tukunna ta tuna tabbas akwai kalar bankwanan da ya kamata ta yi ita da Nuratu (Anne).
Tsohuwa ce sosai amma har yanzu kanta bai juye ba dan da kanta ta kai kanta har asibitin murtala...
Ta ci sa’a kuwa dan tun a waje ta haɗu da Kaka Nura wanda ya fake da zuwa sallah ya yashe mutanen da su ka je siyayya kasuwar wajen..dan haka direct su ka wuce ward ɗin da Anne ta ke a cikin wani waje a keɓance da polisawa su na tsaronta.
Su kaɗai ne a ta wajejen sannan an ɗan ja labule an sake keɓance wajen ga police a tsaye ya na gadi shi da wani soja tun a waje, bincike sosai aka yi musu har da Kaka Nuran bayan ya tabbatar musu Uwani ce ta haifi Nuratu, sannan aka barsu su ka shige cikin labulen..
A kwance ta ke hatta idonta da mugun kyar ta ke iya buɗewa amma an haɗa hannunta da ƙarfen jikin gadon an datsawa ankwa saboda gudun kar ta gudu!
Sannan ga sojoji nan har guda biyu su na tsaronta sosai bayan wanda ke a waje a tsaye tare da police.
Fitowarta kenan daga inda aka yi mata theater ba a daɗe ba inda aka yanke ƙafafunta duka biyun daga saman guiwa zuwa ƙasa sakamokon ɗiwar da su ka fara yi su na wari.
Likitoci har biyu ne a kanta su na ta faman sake dubata su na ƴan maganganunsu...
Dan haka Uwani da Kaka wanda ya yi matuƙar jin zuwan nata su ka ja gefe su ka tsaya idanun Uwani a kanta ta na sake jaddada ikon Allah yayinda Kaka Nura ya ke tsaye ya na kallon ƴar tasa ya na kuka sosai kamar wani ƙaramin Yaro!
Wallahi wallahi in sha Allah sai ya tarwatsa rayuwar Amal tunda dai ya san ko mai zai yiwa Baba yanzu kam ba zai ji zafi ba tunda dama mutuwa zai yi amma ya san a yadda Baban ya ke ji da Amal in ya taɓa ta sai ya girgiza kwarai, sannan ya na fatan ko da ace Baban ya na lahira ne ya zamana a duk lokacin da ya azabtar da Amal za a tashesa a nuna masa.
Ya gama bada amannar cewa Baba ne silar duk wani halinda Annen ta ke ciki a yanzu, saboda ya yi revenge…. ya rama duk wani abunda su ka yi musu kafin ya mutu, shiyasa ya fara ta kanta tunda dama tun usul kowa ya shaida Baba ya tsani Anne kamar mutuwarsa…
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*11*
Likitocin sun jima a kanta su na gwaje-gwaje kafin finally suka sake ɗaukar sample na jininta da ɗiwar da ke fita a ƙirjinta, Likitan ya na mai cewa "bara a yi test na jinin a dawo"
dan wanchan bai gama yarda da shi ba ba komai aka yi ba, Emergency ne shiyasa kawai ya bari
aka shiga da ita amma in za a koma da ita cire nonuwan nata dole za a buƙaci jini saboda babu a jikinta sosai…".
wanda zuwa wannan lokacin itama Anne ta farka dan sun ga ma ta na motsi..
Alluran da su ka siya duk sun ƙare an gama yi mata dan haka su ka juya su ka kalli
Kaka Nura ɗayan ya ce masa "ka nemo kuɗi a ƙaro allurar rage raɗaɗi a yi
mata if not za ta sha wahala sosai gaskiya sai kuma ka je ka biya kuɗin wannan aikin da za a sake shiga a yi mata.."
Ya yi maganar ya na miƙo masa wasu takardu sannan ya ɗaura da cewa
"bara a yi wannan test ɗin za mu dawo nan ba da jimawa ba in sha Allahu…"
Daga haka su ka sa kai su ka fita Likitan ya na sake jadda ikon Ubangiji...
Ya san Anne sosai ta na yawan zuwa private hospital ɗ’insa
Matar da a ko da yaushe ya ke yaba kyawu da kyan surar jikinta dan ko kaɗan in ka ganta ba za ka ce ta na da ƴaƴa manya ba ma wae yau ita ce a haka...tashi ɗaya Ubangiji ya mayar da ita haka…
Su na fita soja ɗaya ya fita ya bar ɗaya wanda ya koma chan gefe ya tsaya ya ci gaba da ƙamewa ba tare da ya sake kallonsu ba.
Su na kammala fita Kaka Nura ya sake rushewa da wani sabon kuka dan ya fahimci zuwa yanzu ta tabbata ƙirjin nata ma yankewa za a yi kenan...yayinda Uwani ta juyo a hankali kawai
ta na kallonsa ta na mamakin ashe in ya ga wani nasa a haka zai ji zafi dan ta na tuna lokacin da su ka saka
Mutan masu yawa a kwatankwacin shigen irin wannan halin…
Girgiza kanta kawai ta yi sannan ta ce masa “ka daina wani kuka fa abunda ku ka shuka ne ku ke girba”
Daga haka ta wuce cikin tafiyarta ta tsoffi ta ƙarasa inda Annen ta ke a kwance…yayinda shi kuma ya ɗago ya na kallonta da mamaki tsantsa a kan fuskarsa ya na tunanin tunda ta fara furta irin haka Anya kuwa za ta yafewa Nuratu?
zai yi magana ya ga ta ƙurawa Anne ido sannan ta soma yi mata magana….
AFRA…
Ta na kammala waya da su ta rushe da wani kalar rikitaccen kuka, yayinda kishi ya ke azalzalar zuciyarta, Sam! Kwata-kwata lissafinta bai bata cewa ae saboda su Anne da kowa Asad ya koma ba kawai lissafinta bata ya ke yi sabida Afra ne ya barta a nan ita kaɗai ya juya ya koma gashi har yanzu bai dawo ba wanda ta na da tabbacin in ba da kyar ba ya na chan tare da Amal ne.
Tunda gashi duk sun ce mata ya dawo yau kusan kwana biyar kenan ita kuma ba ta saka shi ko a idanunta ba.
Ya barta a nan cake ne kawai ta tarar a fridge daga shi ba komai sai ruwan da ta ke ta sha ta fanfo..Sai fruit ɗin da ta ke fita ta tsinka(inibì) bayan shi babu komai a gidan gashi gaba ɗaya tsoro ya lulluɓeta dan wani kalar motsi-motsi ta ke ji a cikin gidan kullum dare kuma in ta duba ba ta ganin komai, apart from that ma gaba ɗaya gidan tsoronsa ta ke ji saboda ya yi girma sosai.
Wanne kalar Ango ne zai bar Amaryarsa ba tare da ya zo gareta ba na tsawon kusan mako ɗaya fisabilillahi!
Sannan babu waya ba komai! Bai kirata ba kuma ya ga baƙuwar number amma bai ɗaga ba shi da ya san ya bar mace ita kaɗai ae in ya ga number ƙasar ya kamata a ce ya ɗauka ko ya biyo amma sam ya ƙi responding, messages ma ba ya respondin ƙarshe ma ya kashe wayar gaba ɗaya..ita kam kunya ma ta ke ji ace Asad ɗin da ta ke haukar so ya yi mata hakan shiyasa ta gagara sanarwa su Ya Amir halinda ta ke ciki.
Tabbas ita kanta dama ta san gangar jikinsa ta aura amma ba ta yi tunanin wulaƙanci daga garesa ba, wulaƙancin ma since from day 1..
Ta yi tunanin za ta shawo kansa cikin sauƙi..
Ko numberta fa Mijinta na aure bashi da, tashi ma ita ta bi ta kuma nema.
Ba shiri ta ke yi da mahaifiyarsa wadda ta tsaneta kamar mutuwarta ba ballanta ta nemeshi ta hanyar ta, Akram kuwa shi da ita mahaifiyartasa duk tafiyarsu ɗaya bakinsu ɗaya...
Ubansa kuwa ɗan Akuya kwata-kwata ba ta ƙaunar abunda zai haɗata da shi ballanta ta je ta samu Matsala da Ya Asad ɗinta ta sanadiyyar hakan….
Wani kalar tafarfasa zuciyarta ta ke yi yayinda kishin ƴaruwarta aba mafi soyuwa a gareta a da ya ke dabaibayi a cikin zuciyarta ya na sake addabarta ta na wani kalar kuka...
Tabbas yanzu aka fara game ɗin!
Dan wallahi bayan ta kwace Asad daga wajen Amal completely sai ta juya mata rayuwa zuwa masifa da bala’i sai dai in ba sunanta Afra ba, ƙiri-ƙiri sannan baki da baki Amal ɗin ta ce mata ta haƙura ita tun usul dama ba ta son Asad ashe munafukar masifar muguntar da ta shirya mata kenan...
Ta ci burin amarcinta ta ci burin kasancewa tare da masoyinta amma Amal ta lalata mata komai da komai….
Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ta durƙushe a wajen ga wani azababben ciwon ciki da uban zazzaɓin da suka rufar mata a ta sanadiyyar ciwon marar da ya ke addabar rayuwarta dan Anne ba ta yi sanya ba wajen dura mata magungunan mata masu masifar ƙarfi ba na wasa ba…
A wajen ta zube ta na nishi yunwa da wahala suka sanya ta yi wani kalar wahalallen barci wanda za a fi iya kiransa da suma…
Wani kalar azababben ƙarni ne ya farkar da ita
wanda ya sanya ta tashi ta zauna da sauri ta na mai dafe kanta sakamokon nauyin da ya yi mata, da kyar ta iya tashi tsaye ta na jin kamar za ta zube yayinda ƙarnin ya yi mata yawa matuƙa zuwa yanzu dan the more ta ke sake wartsakewa the more ƙarnin ya ke sake yin yawa..dan haka kamar ana janta haka nan ta ke bin ƙarnin har ta fito daga bedroom ɗin da take ta nufi inda hancinta ya ke janta zuwa ga ƙarnin...
Ta na mai mamakin masifaffen ƙarnin wanda kamar ba na lafiya ba!
Dan kamar an haɗa har da na asiri duba da yanayin ƙarfin ƙarnin sannan da yadda ya taso ta daga barci Ashe ma a hakan wae ba a kusa da ita yake ba..
Kusan a tare za a ce su ka farka ita da Asad wanda shima ƙarnin ne ya farkar da shi…
Da kuma tsantsar faɗuwar gaba kamar dae itan shima da mugun ciwon kai ya farka har ya na buɗe idanunsa da kyar sai kuma ya yi firgigit ya tashi zaune ya buɗe idanunsa tangargar sakamokon jinsa da ya yi shane-shane cikin wani abu mai kama da ruwa sai dai ya fi ruwan danƙo.
Tabbas ba a nan ɗakin ya kwanta ba to amma ya aka yi ya zo nan ɗin?...
Ya na wannan lissafin idanunsa su ka sauƙa akan wata calender shi da ya ajjiye
a saman drawer ɗakin mai amfani da electricity kullum ta na chanja kwanan wata da rana har ma da lokaci in ya motsa da yanayin whether komai dai in ya sauya itama ta na sauyawa ta nuna maka halinda ake ciki...wadda yanayin figure nata ya kasance sak figure na duniya mai kyau da sheƙi....
Zabura ya yi domin kuwa in dai har yau Wednesday ne kamar yadda calender ta nuna masa to kuwa ya shafe kwanaki huɗu kenan chur ba tare da ya san inda kansa ya ke ba!
Miƙewa ya yi da masifar sauri gaba ɗayansa ya gigice! Da niyyar ya ƙarasa wajen ya ga ko dai calendar ta ɓaci ne ko kuma wuta ya daina kai mata
Kawai ya zame ya yi wani kalar mahaukacin faɗuwar ruf da ciki sakamokon santsin da ya kwashesa
sai da ya kai ƙasa ya yi ninƙaya a cikin abunda ya ji ɗazun tukunna ya tuna ɗazu fa ya ji sa cikin Abu kaca-kaca dan haka ya buɗe idanunsa waenda ya
runtse tun sanda ya bugu a ƙasa ya sauƙesu a kan floor ɗin...
A take zuciyarsa ta wani kalar mahaukacin bugawa sannan ya sake buɗe idanun nasa tarrr da kyau ya na so ya tabbatar da shin abunda ya ke gani gaskiya ne
Dai-dai nan ya ji motsi a bakin k’ofar d’akin alamun za a shigo.
…………
Tun lokacin da Yagwalgwal ta ji batun abunda ya samu gidansu Baba ta ke yiwa Baban naci Akan maganarsu dan ta ce a ganinta suma ɗin yanzu kam ba su da wani security da kariya ko mutunci dan haka basu da banbanci da ita…dan gashi mai Unguwa ya soma shirin korarsu.
Tun ta na yi masa magana har ta zo ta fara binsa da masifa jiya kuwa threatning ɗinsa ta yi dan haka ya yanke shawarar zuwa yau ya samu Amal dukda kuwa ya san hakan ba dai-dai bane ba, sam! Ba a yiwa Yarinyar adalci ba amma ba shi da yadda zai yi!
Tunda ya ke a rayuwarsa bai taɓa tsintar kansa cikin jin matsanancin tausayin wani ba kamar
Amal Yarinyace mai hankali kawaici da haƙuri zagaye da munanan ƙaddarori mabambanta.
Ya na wannan tunanin ya ƙarasa ƙofar ɗakin Adda ya ɗan yi knocking ya tsaya.
Sai da ta leƙo ta ga shine ta ce ya shigo tukunna ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.
A kwance ya sameta (Amal) a kan kafet ta na barci ta na sauƙe ajiyar zuciya.
Kuka suka gama ci yanzun daga ita har Addan Akan lamarin ya Abba dan sama ko ƙasa sun nemi taimako sun rasa wasu sun ma ƙi su kulasu...
Ko an kulasu ɗin ma daga an ji waye da case ɗin duk sai su ja baya, gashi duk alƙawarin da ta ɗauka a kan Ya Asad ta sauƙo dan tun shekaran jiya ta ke ta faman kiransa amma ba ya ɗaga wayar….Afra itama ta daina amsa hatta kiran Ya Amir...
Ita babban tashin hankalinta ma shine a barta ta san halinda Ya Abba ya ke ciki, Allah ya sa ba a wani cel mai tarin macizai ko ma uƙubar da ta fi nan ɗin Ya Asad ya je ya saka shi ciki ba...yayinda Adda ta ke fargaba sosai da tsoro tunda shi Asad d’in ga abubuwan da ake zarginsa da shi kar ta je ta rasa d’anta tilo har Abada ........ko hutuwa ba a barshi ya yi ba daga azabar cel ɗinnan da su kansu har gobe dukda an basu kuma ana kan bata kulawa ta musamman ba ta barsu ba...
Cikin tsantsar mutuwar jiki Baba ya nemi waje ya zauna idanunsa a kanta dan gaba ɗaya ƴan gidan sun koma kamar wasu waenda aka yiwa wahayin ƙunci haka nan su ke kowa jiki a saluɓe…
Ba tare da ɓata lokaci ba ya cewa Adda "ɗan tada mini ita za mu yi magana" bayan sun gaisa.
Kamar Addan za ta ce masa yanzun naan fa ta samu barcin dan kwanakinta uku yau curr bata ko rintsa ba sai kuma ta ga kamar ya na da buƙatar maganar da gaggawa ne dan haka ta ɗan saka hannu a hankali cikin nutsuwa ta shiga kiran sunan "Amal" ɗin ta na ɗan tattaɓata….
Ba ta jima ta na yi mata hakan ba ta farka da salati ɗauke a bakinta ta na mai kallonta kafin kuma ta mayar da dubanta zuwa ga Baba!
Sannan ta miƙe ta zauna a hankali cikin nutsuwarta ta na mai gaidashi.
Da kyar ya amsa ba tare da ya iya kallonta ido cikin ido ba dan haka nan duk sai ya ji nauyi da kunyar Yarinyar masu haɗe da tausayinta sun baibayeshi.
Kame-kame ya fara yi kafin ya tattaro courage ya shigar sanar mata komai game da yadda suka yi shi da Yagwalgwal wanda tun lokacin da Allah ya bashi ikon ambato sunan Yagwalgwal ɗin fuskar Amal ta jiƙe sharkaf da hawaye!
Ta shiga nanata kalmar
"Innalillahi wa inna ilaihirrajiun" ta na mai roƙon Ubangiji da ya zare ranta a take a lokacin ko ta samu sa’idar wannan masifar da ta tunkaro kai.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*12*
ANNE..
Kwance ta ke cikin tsantsar mawuyacin Hali azabar acid ɗin da aka watsa mata da kuma zafin ƙafafunta biyu waenda aka yanke su na neman zautar da ita…
Hatta magana ba iya jiyota ta ke yi sosai ba dan ko iyayenta da su ke a ɗakin tare da ita sama-sama ta ke iya jiyosu sakamokon wani Abu mai nauyi da ya ke shirin sake fisgarta kamar yadda ya fisgeta ta sume ɗazun…
Tabbas ta san ta sha miya kwarai da gaske domin kuwa a halin yanzu shekarunta sun haura arba’in da biyu sannan ta hayayyafa sai dai kuma ita kanta ba ta yi tunanin za ta ji azabar bakin cikin halinda ta ke ciki ba a yanzu da aka ce an yanke mata ƙafafuwa sannan fuskarta ta raunata ga ƙirjinta da ta ji Likita ya na iƙirarin acid ɗ’in da aka watsa mata ya taba kuma ba a yi magani da wuri ba, dan haka ya tado da jejin da ke a gurin a ɓoye tuntuni wanda yanzun ya baiyyana kansa dan haka dole a yanke duka biyun saboda kar jejin ya yaɗu.
Ta na cikin wannan lissafin muryar dattijuwar mahaifiyarta ta sake dirar mata ta inda ta ƙaraso ta tsaya a kanta ta ke cewa
“Ae ba ki ga komai ba fa! Yanzu ki ka fara gani….
Dama duk wanda ya ce shi duniya ya saka a gaba to fa ya na tare da wahala!
Allah na tuba mutum ya yi mai kyau ma ya ya ƙare ballantana bai yi abunda ƙuda ma zai bi ba??
A lokacin da nake gaya miki ai gani ki ke yi kamar ƙarya nake yi!!..
Tunda na haifeki na ke fuskantar ƙalubale ba ki barni na Hutu ba, bayan kin yi aure haka ki ka tarwatsa duk wani jin daɗi da farin cikin mijinki, hatta ƴaƴan da ki ka haifa ba ki barsu sun ji