Showing 18001 words to 21000 words out of 100561 words

Chapter 7 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

450

daban an haka ƙasa a saka su a ciki da layoyi, kayan tsafi, rubuce-rubuce da dai abubuwa kala-kala aka ce Anne za ta iya aikata abunda ya fi tsafi ma dan haka a bata tsaro babba sannan a keɓanceta saboda gudun kar ta cutar da wani…

Su na shiga aka juyo mata da fuskar Anne, Ashe matar da tsuminta ta ke tafe..
Ta na kuka ta ɗaga hannunta babu wanda ya yi la'akari da kwalbar hannunta sai da ta fara tsiyayeta a fuskar Anne wadda azabar zafin acid ɗin ya farfaɗo da ita daga doguwar suman tsoratar da ta yi sai kuma ta sake sumewa...


So su ke yi su wafce kwalbar amma matar ba ta basu damar yin hakan ba dan in su ka kwata ta ƙarfi to fa tabbas za su ɓata kansu da ita kanta matar da aka ce musu su tabbata sun bata kariya daga Anne under any circumstances..kuma sun fahimci acid ne a ciki.
Gashi ta na cewa ‘in su ka taɓata sai ta ɓata kowa a wajen shiyasa ba dan ransu ya so ba su ka gagara kwace kwalbar na tsahon wasu ƴan sakanni daga hannunta…
Ya Abba ne ya ƙaraso wajen daga jin hayaniyar, ya na zuwa bai yi wata-wata ba ya buge hannunta gefe kwalbar ta faɗi ta fashe a wajen
Sai a lokacin su ka shiga ƙoƙarin bawa Anne kariya wadda aka juyewa acid ɗin gaba ɗaya a fuskarta da ƙirjinta.

Ko da su ka yi waya su ka sanar da halinda ake ciki dole aka basu umarnin su kaita asibitin da ke a kusa..
Amma su tabbata sun saka mata ankwa sannan ana tsaronta gudun kar ta gudu…

Su kansu sun yi mamakin yadda ta ke a raye har kawo yanzun amma kawai sai su ka wuce da ita zuwa Asibitin da a ka ce su kaita ɗin.


Su na gama fita da Anne Ya Asad ya juya shima ya fice ba tare da ya ko kalli inda Ya Abba ya ke tsaye ba.

Kamar ba zai yi yinƙurin fita ba sai kuma ya sa kai idanunsa a kan police ɗin da ya ga kowa ya wuce ya barshi kamar an ce ya yi gadinsa ne…
Dakatar da shi kawai ya yi da hannunsa sannan ya ce masa “ɗan jira tukunna"
A hankali Ya Abba ya lumshe idanunsa kawai sannan ya saki wani ɗan guntun murmushi ya koma ya zauna zuciyarsa na ƙarasa ƙuntata.


Amal da ta riga su fita ja ta yi ta tsaya ta na haki sosai jiri ya na ɗiibarta haka suma ragowar duk su na jiran Anne ta fito a tafi tare gaba ɗaya a kaita asibiti su wuce dan mutanen da ya Asad ya zo da su sun gama saka kowa a mota su na shirin kunnata Adda ta ce "a jira akwai Ya Abba Aliya Amir da Anne.."
Dama shi Asad ya zo da su ne akan su kwashi kowa a kai asibiti a yi checkup a duba lafiyarsu dan haka su ka ja su ka tsaya, ana tunanin abunda ya hana su fitowa..


Fitowar Ya Amir da Aliya ta na kuka ne ya sake kiɗima su dan haka aka ƙarasa aka shiga tambayarta "mai ya faru?"
Cikin sheshshek’ar kuka ta ce
“Anne ce…”
Sai kuma ta sake rushewa da kuka
Dai-dai ta ƙarasowar Kaka Nura cikin wajen shi da waensu polisawa waenda ko ƙadangare ba lalle su iya arresting ba..
Dan su na shigowa aka dakatar da su shi kuma aka barshi ya wuce bayan wani a cikin drebobin Asad ya shaida shi ya sanar musu cewa jikokinsa ne aka kama dan haka aka barshi ya wuce ciki.

Yana shiga kuwa ya hangosu dan haka ya ƙarasa zuwa garesu ya na haki ya na kallonsu one by one ya na neman ƴarsa a cikinsu, ya ce “awanni na ashirin da bakwai Ina neman polisawa da kyar na same su.
Ga su chan sai dai na ga kamar har an fito da ku an sake ku kenan.
Wallahi bari mu fita a nan, sai na ci ****uban Sajida, bayan an kawoku nan fa sake komawa su ka yi, bincike kala-kala babu inda ba su fasa ba a cikin gidan nan da kyar na gudu na sha...na bazama neman ƴan sanda"
Sai kuma ya dasa aya kafin ya ce
"Ina Nuratu?"
Ya yi maganar ya na sake kallonsu sosai har yanzu ya na haki....

Kuka Aliya ta fashe da shi
dan haka a rikice ya kamota yana mai karɓar jaririn hannunta yanna salati wanda masifaffen warin da ya ji ya sanya bai iya ci gaba da riƙewa ba dan haka ya miƙawa Amal ba tare da ya ko kalleta ba saboda haushin Yarinyar ya ke ji sosai, ya ce “Ina ƴata?”
Cikin tsantsar ɓaacin rai.

A hankali Aliya ta ce
"Maciji ne ya cijeta tun jiya ba su duba ba
ta na ciki, kuma yanzu sun ce
wae mu sun sake mu mu tafi ita kuma za su ci gaba da tsareta wae ta yi garkuwa….”
Ashar ɗin da ya zabga ne ya sanya ta gagara ci gaba da maganar kawai ta sake rushewa da kuka.
Bai Ida rufe bakinsa ba aka fito da Anne a kan wani zani da su ka ware kamar labule su ka zurata a ciki.

Kasancewar fuskarta a tsundume ta ke cikin zanin ya sanya duk ba su gane a yanayin da ta ke ciki ba, kayan jikinta ne ma da ya leƙo ta wajen ƙafafunta da leɓunan ƴan kwalayensu da su ke reto ya sanya su ka shaidata dan haka duk su ka ɗunguma zuwa gareta.
Kafin su ƙarasa Ya Abba shima ya fito sai dai shi da ganinsa ba sakinsa aka yi ba dan tsaronsa ake ci gaba da yi da alama, tunda gashi bayan wanda ya hanasa fitowa har da wani poliçe aka sake k’ara masa su ka zama su biyu.


Da sauri Ya Amir ya ja da baya sai kuma ya fashe da kuka, ragowar mutanen suma duk baya su ka ja aka hau salati yayinda Kaka Nura ya ƙarasa da sauri ya na mai riƙe zanin dan mutanen ba su tsaya ba…
Wani kalar masifaffen tashin hankali ya shiga a take dan gaba ɗaya kasa motsawa ma ya yi da ganin fuskar tilon ƴar tasa a haka kafin ya tafi luuuuu ya zube a wajen kamar mai shirin suma cikin tsantsar tashin hankali…
Da kyar su Ya Amir su ka taro shi shi da Ya Abba wanda ya ƙarasa garesu cikin zafin nama, dan ya basu tsoro sosai.

Cikin tsantsar firgici su ka tsayar da shi ya tsaya da kyar ya na faman tangaɗi..
Ganinsu cikin tashin hankali ya sanya Adda ta buɗe ƙofar van ɗin ta fito ta ƙaraso wanda hakan ya bawa Kaka Nura damar hango Baba a zaune a ciki ya na kallonsu bai ko motsa ba.

Aikuwa bai bari ya kai ga Ida dawowa dai-dai ba ya ƙarasa gaban motar ya finciko Baba sannan ya saita fuskarsa ya kifa masa mari sai kuma ya hankad’esa ya faɗi kana ya bi shi ya danne da niyyar fara kimarsa aka ɗaukesa yaana ta kici-kici ya na hawaye sosai ya na cewa "tabbaas kam ka kasheni, kisan murus ka yi mini wanan kisan tsaye kenan, amma wallahi ba ka isa ba mutuwar kasko za a yi wallahi Allah...."
Ya yi maganar ya na mai fincikewa ya sake yin kan Baba wanda ya Amir ya taimakawa aka miƙar, amma sai aka tarosa...
So ya ke yi ya isa garesa wallahi yau sai ya yi ajalinsa dan a yadda ya ke jin kansa tsaf sai ya tabbatar masa shi ɗin fa ba tshoho bane ba alhalin a zahirin gaskiya ko tureshi aka yi sai ya faɗi ya ji babban rauni dan a hakan yadda ya ke ta fisge-fisge mutum ɗaya ne tak ya riƙesa da hannu ɗaya.

Daga gefe wasu ƴan sanda guda biyu su ka hangosu dan ragowar har sun wuce da Anne
bayan an dakatar da kowa daga binsu. Ya Abba shima sun wuce su uku ba tare da kowa ya lura ba..
Ɗayan ne ya taɓo ɗayan ya ce masa "duba ka ga wani tsoho mai k’arfin Hali"
Dan haka su ka tunkarosu wanda zuwan na su ne ya taimaka Kaka Nura bai sauƙewa Baba uban dutsen da ya rarumo bayan ya kwaci kansa ba.

Da kyar aka rabasa da dutsen sannan aka rirriƙesa ya na ta faman fisge- fisge ya na cewa “tabbas kam ka kasheni!
Ka cika alƙawarinka da ka yi mini shekaran jiya..
Allah ya Isa tsakanina da kai!
Mai ta yi maka haka da zafi?
Laifi ae ni ne na yi maka!…”
Ko ta kan su Ya Amir da su ke sanar masa ba fa Baba ne ya yiwa fuskar Annen haka bai bi ba gani ya ke makircin Baban ne ya sanya ba su fahimci shi d’inne ba…dan haka bai yarda da zantukansu ba sai ma zaginsu da ya fara yi
yana cewa "ae suma sun san maciji ya cijeta amma su ka barta a ciki a haka kowa ya fito maimakon su tsaya da ita har a sake ta, saboda su ɗin ƴaƴan iska ne!”
Ya na bala'i da zage zage ya na kuka sosai yadda duk wanda ya gansa daga nesa bai ji kalar zagin da ya ke ba sannan bai san wayene asalin Kaka Nura ba tabbas sai ya koka masa..dan ashar in ya lailayo wani sai ya yi kusan minti ɗaya tukunna zai kai ƙarshen ashar d’in….

Tsabar bala’i da tashin hankali a take numfashinsa ya sarƙe amma dukda haka iƙirari ya ke yi wallahi wallahi sai ya kashe Baba. Ko kallon Yadukko bai yi ba wadda ya gani a cikin moto itama bata da maraba da gawa kawai shi ta tashi ƴar ya ke..

Cikin bada umarni wani babban mutumin ya fito daga cikin building ɗin da alamun shi ne oga, ya umarcesu da
"Su shiga moto duk a kaisu asibiti kamar yadda Asad ya bada umarni, Kaka Nura kuma ya wuce ya tafi shi kaɗai kar ya bisu,
duk su watse, su fice musu daga harabar gurin.."
Dan ya ga mutanen dramar su ta fi ƙarfinsu.

Sai a lokacin ne da Adda ta duba ta nemi Ya Abba ta rasa da kusan duk baƙaƙen motocin da su ka fito su ka tarar a harabar wajen.....


BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

HUMAIRAH BULAMA

Yota

*09*

Dama Amal ba ta so ta tsaya ta sake ganin Ya Abba kuma duk ji ta ke kamar ta nutse dama, ganin ba ta ganshi kusa ba ya sanya ta wuce ta shige ta zauna a chan inda ko ya shigo ba lalle ma ya hangeta ba, saboda wata masifaffiyar kunyarsa ta ke ji da duk mutanen wajen ma, ita dae ta san Ya Abba ba ɗan iska bane ba amma ba ta san mai ya sa ya yi mata hakan yau ba, fisabilillahi in zai bata kariya ae ba haka ya kamata ya yi mata ba sannan tsabar neman magana maimakon ya haɗa ita da Adda shine ya zaɓi ya ja mata magana a idanun kowa ta hanyar damƙota da ya yi ita kaɗai sannan ya wani matseta gashi yanzu kowa ya gani ya shaida.....

Adda kuwa tsayawa ta yi ta na rarraba idanu
ganin babu shi (Ya Abba) ba alamunsa kamar walƙiya ya ɓace a wajen ya sanya ta ƙarasa gun mutumin ta shiga yi masa bayanin 'nata ɗan bai kai ga fitowa ba tukunna, ko lafiya?'.

Kansa tsaye ya ce mata "ta wuce ta tafi zai taho daga baya” sannan ya umarci mutanen da su ka dawo daga fidda Kaka Nura daga wajen itama su fitar da ita in ta yi taurin kai.

Amal ta na ƙarasa zama a cikin motar wani nannauyan jiri ya kwasheta, ragowar mutanen suma har su Ya Amir kowa a wahale ya ke ba iya gane abubuwa su ke yi ba zuwa wannan lokacin, shiyasa ko da Adda ta leƙo ta ce su wuce kawai su ka zaɓi su kaisu asibitin ita a barta kamar yadda ta buƙata saboda ranta ita kaɗai da ɗan da ake ta ce mata an wuce da shi wani wajen wataƙila shima dubasa za a yi bai kai ya janyo a rasa rayuwar mutanen da su ke cikin motar ba...
Baba ya so ya yi gardama amma ta ce "ya je kawai, ya tafi ya kula da su Yadikko shi da Amir, za ta jira Asad a gate, ta na son yin magana da shi."
Dan haka su ka ja motar su ka wuce ita kuma ta nemi waje a wajen ta zauna wanda nan ɗin ma masu gadi su ka ce sai dai ta tashi.


Sai da kuwa aka yi mata alƙawarin sake arresting ɗinta muddin ba ta bar wajen ba tukunna ta yarda ta bar wajen ta na wani kalar kuka mai cin rai dan kanta tsaye da farko ta ce musu
"babu inda za ta je ba tare da ɗanta ba.
Za ta zauna ta jira shi a wajen, sai dai su kamata."
Ganin su na shirin kinkimarta su matsar ta ƙarfin tsiya ya sanya ta bar wajen ta koma chan da nesa inda za ta iya ganin gate ɗin, da niyyar ta na gani an buɗe za ta taso ta zo ta tsaya ta tare hanyar sai dai motocin Asad su bi ta kanta wallahi amma bai isa ya tafi ba tare da ya saki Abba ba.....dan ko shakka babu wata uwar muguntar sabuwa fil zai sake gwada masa...
Dama tunda ta ga yadda Asad ɗin ya yi bayan ya gansu shi (Abba) da Amal a wannan yanayin ɗazu tabbas ta san a rina…saboda tsabar kishi ya rufe masa idanu ya ma gagara fahimtar kariyar da Abba ya ke bawa Amal ɗin a wannan lokacin itace abar dubawa sama da yanayin da ya gansu...a yadda ya ke tsagwaron marar imanin nan kuwa ba za ta barshi da Abba wanda ta san ba shi da wani wanda ya tsana sama da shi ba, sannan yanzu ga abunda ya sake gani...Mutumin da ba a san matsafi ne ko aljani ko maye ba, Anne ita ta ga suruki amma ita kam ko a mafarki ba ta ƙaunar dama Allah ya haɗa Amal da Asad....
Ta na wannan lissafin idanunta kyar akan gate ɗin wajen ta na sharar kwallah...
Wallahi ba za ta barshi ba yau kam ko zai lashe mata kuruwa itama sai dai ya lashe.
Rashin imaninsa ya yi yawa a Abban..abubuwan da su ke gwada masa its not fair...
Haba mana!
Kamar ba uba ɗaya ya ke iƙirarin ya haifesu ba!...
Ta san ba ta da ƙarfin komai akan Asad amma tabbas ko za ta bada ranta fansa a tilon ɗanta za ta yi domin ta yi freeying nasa da ga azabtarwar da Asad ya ke yi masa....
dan haka ta gyara zama ta ci burin haɗuwarsu a yau wanda abunda Addan ba ta sani ba shine
tun ɗazu kafin su fita Asad ɗin ya wuce ya fice ta gate ɗin baya shi da motocinsa lokacin hankalinsu gaba ɗaya ya na a kan Anne da faɗan Kaka Nura da Baba, dan ji ya ke yi ko da zai zuƙe iskar wajen gaba ɗaaya ba za ta ishesa ba shiyasa ya yi wuff ya wuce gudun kar a samu matsala.



Sai da aka kusa arresting Kaka Nura shima ɗazu, fahimtar da ya yi faɗa da Baba ba shine mafita ba a lokacin ya sanya kawai ya rabu da shi ya nufi inda ya samu aka gaya masa Annen ta ke da kyar bayan ya samu ya lallaɓa ya rabu da ƴan sandan da ya lura sun fusata da behaviour nashi, lafiya.


Su Ya Amir kuwa, duk yadda su ka so ba a barsu sun je sun dubata bayan an gama duddubasu ba..an tabbatar musu ba za a barsu su ganta ba sannan Asad gida ya ce a kaisu kawai, dan haka direct gidan aka nufa da su aka kaisu har layinsu ƙofar gidan Baba aka sauƙesu, Yadikko ma an dawo da ita dan ta dawo dai-dai...
Wannan tsohon da ya faɗi ne ba a dawo da shi ba saboda sun duba sun ce still ya na buƙaatar hutu, sai wani a cikin mazan shima sugar ɗinsa an ce ya taɓu sosai....sai gawar ɗan gidan Aliya wadda su ka yiwa wanka a chan a ka shirya su Baba su ka je su ka binne su ka sake komawa wajen.


Ko da su ka isa unguwar tasu chaa aka yi musu tun daga bakin titi wasu su ka biyo motar ana tambayarsu mai ya faru tare da jaje yayinda waensu gulma ne da farin ciki ta fito da su…
Ragowar mutanen yawanci ake ta kulawa dan gidansu Baba an ce su suka janyowa kansu.

Iyalan waenda ba su kai ga dawowa ba kuma su ka bi maaikatan lafiyan aka koma da su domin su je su gansu su yi jinya.


Tabbas kam an yi musu bincike na rashin mutunci ma kuwa dan babu abunda ba a fasa a cikin gidan ba.

Ba su da nutsuwar tattarewa dan haka ɗakin Yadikko kawai aka gyara aka shimfiɗar da ita, su ka barta da nurse ɗin da aka ce za ta dinga monitoring Amal na kwana huɗu, tukunna Ya Amir da Abokinsa dan Aliya sai da aka sake yi mata wani ɗinki shiyasa ko tsayuwa ba ta iya yi sosai tsabar azaba da zazzaɓi...dan haka su ka bazama su biyu wajen mai Unguwa da fatan ko akwai abunda zai iya yi musu a lamarin na Anne wadda ya kamata a ce jinya ta ke yi yanzu ba wai a tsareta a hannun ƴan sanda ba. Dukda sun san asibiti a ka ce an kaita amma still tsarone tunda gashi sun ƙi su bari a ganta ko a yi jinyarta dan haka sun san ba za a bata kulawar da ta kamata ba. Yayinda Baba ya tafi neman Adda da jin baasin rashin sakin Ya Abba da aka yi.


Tashi ɗaya mai unguwa ya sanar musu babu taimakon da zai iya yi musu a kan Anne sannan ya basu tabbacin in har case ɗinta ma ya na shirin taɓa masa area

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login