Showing 27001 words to 30000 words out of 100561 words
daɗi ba!
Ɗaya bayan ɗaya duk sai da ki ka lalata musu dukkan farin cikinsu…
Yanzu gashi ai kema kin fara gani da idanunki kuma wallahi wallahi Nuratu kin ji dai har na rantse miki ba ki ga komai ba!!."
Cikin faɗa sosai Kaka Nura ya ce da Uwani wadda ta gama wannan furucin ga Anne "Haba mana Uwani!! Ashe kuwa ba alkairin ya kawoki ba kamar yadda na ke zato! Ke da aka ce ki zo ki yafe mata shine za ki zo ki na sake rura mana zafin zuciya?
To kuwa wallahi idan ba ki rufewa mutane baki ba zan yi fatali da ke a wajen nan!! Ashe ke Jahila ce ban gama sani ba sai yau? Mahaukaciya kawai!!.
Yo Idan ba mahaukaciya ba wacce iriyar daƙiƙiyar uwa ce zata ke furta wannan mugun alkaba’in ga ɗiyar da ta Haifa a cikinta? Haba mana!!! Ba ki da tausayi ne?
Kalli fa halin da ta ke ciki!
Ke da ya kamata ace mun taru mun kwantar mata da hankali shine za ki dinga binta da mugun fata ba ki da imani ne ? Ko kuwa dai zuciyarki ta ruɓe ta lalace ne??".
Cikin Hali na ko in kula Uwani ta sake zubawa ɗiyartata idanu waadda itanma ita ta ke kallo da idonta guda ɗaya wanda ya yi saura don ɗayan ya riga ya tsiyaye hancinta shima kusan za a ce babu ne yayinda bakinta ya tauye..gaba ɗaya kamanninta su ka sauya dan ita kanta dukda kasancewarta mahaifiyarta wallahi da kyar ta ke iya sake shaidata…
Kwafa Uwani ta yi bayan ta gama ƙare mata kallo tukunna ta ce "ƙarshen ki ki ka fara gani Nuratu, kamar yadda na faɗa da farko wallahi ba ki ga komai ba!
Batun yafiya kuwa ba lalle ki samu daga wajen kowa ba har shi mijin naki dan haka in dae wahala ce da azaba ba ki ga komai ba, in kin mutu yanzu ta chan ta na jiran ki wadda ta fi nan... in kuma kin samu kin rayu to wannan halin da ki ke ciki shine farkon wahalarki..halinki da hakƙin jama'a su ka janyo miki..ko ni ban yafe miki ba dan da baƙin cikinki zan Mutu…"
Daga haka ta juya ta fita wanda fitar da ta yin ne bai bawa Kaka Nura damar samunta da sandarsa wadda ya ɗaga da niyyar sauƙe mata ba…….
Ta na fita wani azababban hawayen da saida Anne ta ji inama ba a halitta mata yin hawaye a duniya ba ya shiga zubo mata..kuka ne ta ke yi da idanu biyu amma hawayen ido ɗaya ake iya gani domin d’ayan idon ya rufe ya tsiyaye ya zagwanye wanda hawayen da ya ke fita daga cikinsa ya na fama mata jagwalgwalewar da wajen ya yi ya ke sanyata ta na jin kamar za ta bar duniya tsabar Azaba!.
A rikice Kaka Nura wanda ya rasa abunyi duk ya bi ya ruɗe ya juyo daga zabgawa inda Uwani ta bi ta fice da kallo harara ya ƙarasa ya zauna a bakin gadon….kamar shima ya rushe da kuka tsabar tashin hankali da bala’i haka ya ke ji…da kyar da mugun kyar ya ɗan yi controlling kanshi ya aro jarumta ya yafa domin ya san ƴarsa tana da buƙatar jarumtar tasa a halin yanzu, cike da taka tsantsan kamar wanda zai taɓa kwai ya shiga shafa kanta a hankali kafin cikin tsananin lallashi ya fara magana "ki yi haƙuri ki yi shiru, ki daina kuka dan Allah.
Allah ya na tare da ke zai bi miki hakƙinki, sannan in sha Allahu za ki rayu da izinin Allah kuma ba za a yanke miki hukuncin komai ba ki na gama jinya gida za mu koma ba wai prison ba...kuma matar da ta aikata haka a gareki wallahi sai mun ɗauki fansa sai ta yi da na sani wallahi….ki bar ɗaga hankalinki zan tsaya komai ya koma kamar da
kar ki saka damuwa a ranki dan Allah kin san ba na son ganin hawayenki kar ki saka jinina ya hau wani abun ya same ni ki rasa mai tsaya miki…ki daina kuka komai zai yi dai-dai in shaa Allah kuma da hannunki za ki hukunta matar ita da Habu (Baba) dan na san shi ne ya turota ko ba ya raye sai mun azabtar da Amal kwatankwacin azabar da su ka gana miki wannan alƙawarina ne gareki, ki yi shiru kin ji ko, fuskar ma za mu samu kuɗi mu tafi turai a gyara miki ki kwantar da hankalinki kar ki sakawa kanki ciwon zuciya…."
Ya ƙarashe maganar ya na huci...
Dukda su Aliya sun tabbatar masa ba Baba bane ba amma shi ya ke zargi, batun garkuwa wannan ma ya san in ba kyar ba duk Baban ne ya yi mata chune ya cewa sojojin Sajida su bincika har cikin ƙasa ko kuma dae wani abun makamancin haka duba da yadda surukin nasa ya tsani ƴar tasa kamar mutuwarsa.
Shigowar Likita wanda ya yi alƙawarin dawowa yanzun ne ya katsewa Kaka Nura aikin rarrashi da tunanin da ya ke yi.
Da sauri ya miƙe sannan ya juyo ya mayar da hankalinsa kachokam ga Likitan ya na jira ya ji bayani……
Kallonta Likitan ya yi ya ɗan kalli Kaka Nura kafin ya ce "Baba a ɗan bamu guri…Ina so zan yi mata magana in private…"
Cikin fushi Kaka Nura ya ce”zancen banza kenan!!! A wannan halin da ta ke buƙatata a ko da yaushe ka ke tsammanin in fita?? Ba ka ganin hatta sojiji sun sarara mini saboda sun san darajar Uba?
Dan haka Mallan faɗi duk abunda ka zo da shi ba ni da tamkar ta itama ba ta da ya ni!!"
Kallonta sosai Likitan ya yi kafin ya ce "in faɗi komai a gabansa?"
Cikin fushi Kaka Nura ya buɗe Baki zai yi magana sai kuma ya juya ya kalli Anne wadda a hankali ya ji motsi ya ga ta ɗan girgizawa Likitan Kai alamun A’a…shiruu Kaka Nura ya ɗan yi kafin ya ƙarasa ya shafa kanta ya ce "idan kun gama sai ki sakashi ya shigo da ni ko?Allah ya yi miki albarka ki kwantar da hankalinki" daga haka ya wuce da sauri ya fita gudun kar ya ɓata musu lokaci……
Sun riga sun saba da Likitan ya santa ta sanshi farin sani shiyasa ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita nan gefen gadon kafin ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya ya furzar da iska ya zare gilashin idanunsa ya ɗan mitsitstsika idanunsa kafin ya mayar da gilashin ya sake sauƙe ajiyar zuciya tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba saboda har ga Allah tausayinta ya ke ji matuƙa.
“Nuratu da farko dai inaso duk abunda zan faɗa miki a yanzu ya zamana kin runguma kin karɓi jarabawarki hannu bibbiyu, hakan ake so musulmi ya kasance a ko da yaushe idan musiba ko ƙaddara ta same shi mummuna ko kyakkyawa….."
Numfashi ya sauƙe wanda ita kuma Anne tuni tashin hankali da masifar da take ciki ya sake hauhawa....tsoro da firgici ba sa daga cikin ɗabi’arta amma a yau kam tsoron da ta tsinci kanta a ciki ba zai misaltu ba, ga wani Irin firgici da banɗokin zullumin jin abunda zai fito daga bakin Likita…tuni rigarta ta jiƙe sharkaf da gumi tsabar masifa har ma da gashin kanta ga azabar da fuskarta da ƙirjinta su ke yi mata ba na wasa ba ne! Tabbas ta san koma menene zai fito daga bakin Likita ba abun alkhairi bane ba tunda ya fara furta mata irin waennan kalaman a gabannin bayanin nasa....ga shi ta rasa fuskarta da ƙirjinta wanda surar jikinta kyan fuskarta su ne abun taƙamarta, ta san ko da ace za a gyara mata ba zata koma kamar da ba shiyasa kawai ta shiga addu’ar Ubangiji ya ɗauki ranta a take saboda bayaga musibar da take a ciki ba ta jin za ta sake karbar wata sabuwar jarabawar…..
Cike da alhini muryar Likita ta dira a dodon kunnuwanta ta inda ya ci gaba da cewe "Ɗazu dama na gaya miki kuma kema kin ga yadda acid ɗinnan ya tauye Mamanki na hannun dama(right breast) kasancewar ya shafi na hannun hagun shima ya sanya jejin da ke ɓoye a jikinki ya ruru matuƙa! dan haka a gaskiya dole sai dai mu haɗa duka biyu a yanke saboda na yi testing acid ɗin mai mugun ƙarfi ne dan haka gara a yi maganin sa da jejin gaba ɗaya tun kafin jejin ya yaɗu a jikinki sannan ɓarnar acid ɗin ta fi haka.
Karkarwa jikinta ya ɗauka a take, zuciyarta tana wani irin ƙuna…Bata gama nemawa bal’in masauƙi a cikin zuciyarta ba ƙirjinta ya yi wani kalar mahaukacin bugawa zuciyarta ta hantsila kamar za ta faso ƙirjinta ta fito sakamokon sautin muryarsa da ta ji yana daɗa cewa "Sannan nan da kwana biyu sun ce za su wuce da ke prison a ta sakamokon laifin garkuwa da Yara har biyu da ki ka yi ki kai tsafi da su, dan haka za mu kammala komai da wuri in yi miki duk abubuwan da ki ke buƙata sai ku wuce, ki ci gaba da jinya a cikin asibitin da yake prison ɗin in mun saka ranar da za a miki aikin za mu je mu ɗaukoki a yi miku in ya so a sake mayar da ke chan ɗin ki ci gaba da jinyar kafin a yanke miki hukunci."
Cikin sauƙe numfashi ya ɗaura da cewa “mun yi miki gwajin jini saboda musan ta yadda za mu fi baki kulawa da kuma jinin da za'a samu a ƙara miki in an shiga dake aikin da za a yi miki a ƙirjin ki unfortunately Nuratu ki na ɗauke da cutarnan mai karya garkuwar jiki na san baki sani ba saboda ko last time da kuka zo da ke da Alhaji Nasiru aka
duba sam babu ita a jikinki, sannan hantarki ta taɓu amma ita ba mu yi scanning mun tabbatar da matsalar wacca iri bace ba.."
Cikin sauƙe numfashi ya ce "na gwada neman alfarmar a barki a nan dan sai kin fi samun kulawa duba da tarin ciwukan da su ke damunki gashi akwai wani aikin a gaba wanda dole sai an yi amma kuma kasancewar ba a daɗe da miki aiki a ƙafa ba ya sanya dole sai an jira..
But sun ƙi yarda, sannan duk yadda na so in samu wata ƙofa da za ta bani damar da za a yi miki aikin lokaci guda hakan ba zai taɓa yiwuwa ba, dan haka nan za mu haƙura mu yi addu'ar Allah ya sa kar abun ya fi haka mu jira har nan da tsawom mako biyu tukunna sai ki dawo a yi miki aikin ƙirjin...."
Shiruu ya ɗan yi sai kuma ya fesar da numfashi kafin ya ce
"Anyways...
Za mu ɗauraki a kan magunguna yanzu kafin a dawo yi miki aikin, sai ki wuce da su chan ki ci gaba da sha
Allah ya rufa asiri ya baki lafiya ….."
Tabbas duk wanda ya ce bala’i ya ishe shi ya ke ganin kamar babu yadda za a yi ya sake shiga cikin wata masifar to Allah ne kawai bai so ba….Allah ne kawai ya barshi amma duk ta inda ka kai ga shiga tashin hankali ka ke ganin ka kai peak in dai Allah ya ƙaddara to akwai gaba da shi… da aka watsa mata acid gani ta ke yi kamar kawai ƙarshen masifar da za ta iya samunta kenan…da ta kalli ƙirjinta ta ga yadda ya koma sannan babu ƙafafu sai ta ga Ashe akwai level two, kwarin guiwar da Mahaifinta ya bata ne ya sanya ta ɗan yarda akan wataƙila za ta iya samu rayuwarta ta ɗan daidaita ta samu ta zama mutum ta ci gaba da rayuwarta dukda babu ƙafafu da ƙirji ta san za ta lallaɓa da babu gara ba daɗi sai dai abunda ba ta sani ba ashe ba ta ga komai ba kuma ba ta ji komai ba..a haka ma ba a zo kan maganar hukuncin da za a yanke mata ba na laifin da take da tabbacin ita ta aikata ita da tshohon saurayinta ɗan fashi ta inda ya sace Yaran su ka daɗe a wajensa ya na ta amshe kuɗaɗe a wajen iyayen Yaran, wanchan satin da ya gabata bokanta ya ce ta kawo Yara maza biyu a yi mata aiki da ta gaya masa(saurayin nata) ya ce akwai su ka kai Yaran ta yanka su da hannunta bayan ta yi zina da ko wanne a cikinsu tukunna aka yiwa yaran filla filla kamar yadda ake daddatsa kaza aka tsafe su tass aka haɗa da kayan tsafi aka saka mata a cikin tukunyar ƙasa da wani ruwan da boka ya rantse mata akan ba zai bari su ɓaci ko su yi wari ba ita kuma ta karɓa ta binne a ƙasan drawer kayanta har da kayan jikinsu ta binne a gefe da zobunansu na azurfa dan gudun kar ta je jefarwa ko ta yar a kamata...kuma sai da bokan ya tabbatar mata kar ta bari a gani in ba haka ba aikin ya lalace amma in ta ɓoye da kyau to har abada asiri ya na nan kuma ba zai lalace ba kamar yadda tsoka da halittun gangar jikin yaran za ta kasance fresh saboda ruwan da ya zuba aljanun za su dinga kula da shi ba zai lalace ba…
Wanda abunda ba ta sani ba ma warin ne ya janyo hankalin sojojin zuwa inda ajiyar tata ta ke....
Kuka Anne ta saki wanda ba a ji ba a gani ta na sake jaddadawa kanta tabbas tata fa ta ƙare...Dan a yadda Allah ya yi fushi da ita ɗinnan ta fara ganin jarabawa kamar ruwan sama ta koina tabbas ta san wataƙila azabar da za ta gwammaci mutuwa za a yi ta gana mata a prison ɗinnan dan ita kanta ta san ƴaƴan waye ne amma da ya ke idanunta sun rufe a lokacin ta ce a yi mata aikin da su………ita da farko da ta ji Kaka Nura ya na batun police da hukunci sannan da ta ga soja a ɗakin ta ɗauka duk Sajida ce ba ta barsu ba ashe wannan ɗanyen aikin nata aka binciko....
A hankali ta samu da kyar ta rufe idonta tana karɓar azaba ta ko wanne fanni zuci, kwanya da gangar jikinta zuwa yanzu ta daina jin abunda Likita yake faɗi da bayanan sa dan iyakacin abunda ta sani shine tata ta ƙare!! Gashi komai ya lalace mata ya taɓarɓare mata! Tabbas wannan shine asalin mutuwar tsaye haƙiƙa babu yadda Ubangiji baya iya juya al’amari kuma ɗan Adam ba a bakin komai yake ba duniya da abunda ke cikinta zancen banza! wai yau ita Nuratu ita ce ake yiwa zancen babu Nonuwa babu ido babu fuskar data tsolewa dubu ido fuskar da take taƙama da ita sannan gata dumu dumu a hannun hukuma, dan haka babu isa sannan babu gadara..wani irin kukan zuci ta ke yi saboda ta riga ta san ba ta da wata sauran mamora gashi dai da sauran shan miyarta dan bata kai arba’in da biyar ba ma a duniya amma ta san ko tshohuwar mahaukaciya sai ta fita daraja da mutunci a idanun maza da duniya ma gaba ɗaya dan ko da ace ta tsallake case ɗin da yake jiranta ta fito ba a kashe ta ba, kuma ciwukan jikinta suma ba su tarwatsata ba tabbas a yadda halittunta suka koma ita kam ta san an gama yi mata mutuwar tsaye.……………
SHEKARUN BAYA DA SU KA SHUƊE
(Waiwaye)
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*13*
SHEKARUN BAYA DA SU KA SHUƊE..
(Waiwaye)
KANO
ƘOFAR MATA
Asalin sunan Anne Nuratu Muhammad Nura, Mahaifiyarta cikakkiyar ƴar Kano ce anguwar zage ƙofar mata yayinda Mahaifinta ya kasance bafulatanin chad ɗan sarkin rugarsu a wanchan lokacin….faɗa ne ya korosa shi da Mahaifinsa daga chad tun lokacin da aka ci Mahaifin nasa da yaƙi wanda hakan ya sanya aka kwace matarsa da ragowar magoya bayansa waenda basu fi mutum biyar ba, sarkin da ya karɓi mulki shi ya auri matarsa shi kuma kakanta aka koresa kora ta har abada daga ƙasar gaba ɗaya da shi da mahaifinta (Kaka Nura) wanda a lokacin ya ke Yaro ƙarami.
A Nigeria suka yada zango garin Kano unguwar ƙofar mata a lokacin Mahaifin Mahaifiyarta shine Mai Unguwa..shi ya karɓesu hannu bibbiyu ya musuluntar da shi da ɗan nasa (Kaka Nura) su ka zaɓi sunayen musulunci ya koya musu karatu har ta kai ga sun zama kwararru suma dan har koyarwa Mahaifin Mahaifinta ya ke yi a tsangayar kakanta (na ɓangaren uwa), Mahaifin Mahaifinta bai kai ga yin wani auren ba, kwata-kwata shekaru bakwai Ubangiji ya bashi ikon ƙarawa a duniya ya karɓi ransa….ya rage saura Mahaifinta (Nura) kaɗai wanda da shi da maraya ba su da maraba dan ko da wasa a yadda Mahaifinsa ya faiyyace tsarin rugar tasu ba a isa a mayar da shi garin ba tsaff za su yi masa yankan rago tunda korar su aka yi….
Mahain Mahaifiyarta (Mallan) ya yi iyaka bakin ƙoƙarinsa wajen ganin ya inganta rayuwar Nura, bayan karatun allo har a makarantar da ƴaƴansa su ke zuwa ya saka shi dan Mahaifinta (Nura) yanada shiga rai farin bafulatani ne kwarai kyakkyawan gaske sai dai kuma tun Nuratu ta na ƙarama ta ke ji a wajen Mahaifiyarta da ƴan uwan Mahaifiyarta kuma itama ta ji ta gani cewa ‘Mahaifinta sam ba mutumin kirki bane ba’
Dan tun ya na Yaro yana da taurin kai, riƙeƙƙen ra’ayi, cin amana, sata, ƙarya, son abun duniya da shegen son abunsa ga kwaɗayi da son abun wani…ƴan uwan Mahaifiyarta (Uwani) maza su uku ne Yusufa, Ali da Garba! Ita kaɗai ce mace a gidansu, ƴar auta..hakanan a ka ja shi a jiki a ka mayar da shi ɗan gida duk wani abu idan suka samu tare su ke rabawa da shi haka iyayen suma tare su ke yi musu komai da shi amma shi ko ruwa pure water idan ya siya ya na sha ka ce ya rage maka ba zai bayar ba sai dai ya ce 'shima ba zai ishe