Showing 96001 words to 99000 words out of 100561 words

Chapter 33 - BAKAR TUKUNYA hausa novel

07 Feb 2026

455

mai ya faru ki ke so mu sake komawa?
Yanzu ina yi mata maganar nan wallahi gani za ta yi kamar zarginta ne na ke yi….”
Ya ƙarashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka


Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*

Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudinku tested and trusted.

Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kun zo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA

BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:25 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*

*36*

A fusace Mama ta ce “ta gani Mana! Sai me?
Ɓacin ranta ya fi safety ɗinka ne.”

Salati Isma’il ya yi kafin ya ce “Mama safety kuma kamar yaaya? Zargin nata ki ke yi kenan?”
Ya yi mata maganar a ɗan
tsorace.

Itama Mama a ɗan tsorace sannan rai a ɓace ta ce “Isma’il ja’inja ka ke yi da ni? Gardama za ka yi mini
ko me!?
Ka na so mu rabu lafiya da kai kuwa?…
Gaba ɗaya tashi ɗaya ka sauya, halayenka sun chanja duk a kan soyayya, ko sirrin cikinka ba ka iya riƙewa, komai sai ka gaya mata…”
Girgiza kai ya shiga yi, ya yi
kalar tausayi sosai, Mama ba ta barshi ya yi magana ba ta ce “eh mana, maganar zamanta a Kaduna da komai da aka yi ae duk kwashewa ka yi ka je ka sanar mata tun kafin Mahaifinka ya ce komai.
Anya kuwa Isma’il!? Tsoronta ka ke ji ne ko yaya?”
A hankali ya lumshe idanunsa hankalinsa chaaa! A tashe, kafin da mugun kyar ya iya buɗesu ya sauƙesu a kanta, tukunna ya ce “ki yi haƙuri, Allah ya huci zuciyarki, zan je in sameta a sake yin sabo sai mu kawo miki in sha Allah..
Batun Kaduna kuma ban ce komai ba Mama, ki yarda da ni”

“A mafarki aka sanar musu hala?”

Wani abu ne ya tokare masa maƙoshi ganin yadda yau ƙiri-ƙiri Mama ba ta yarda da shi bane, sannan tashi ɗaya ya fahimci daga wajen Anne ta ke kenan fitar da ta yi kuma tabbas Anne ce ta zugota ta haɗa komai shiyasanya ya ganta a haka, dan haka takaicin Matar(Anne) a take ya ƙarasa hassala shi ya na mai ji kamar ya saka mata bomb kowa ma ya huta.
Da kyar ya iya buɗe bakinsa ya ce “ki yi haƙuri Mama dan Allah”
Dan ba ya son magana da ja’injar da ta ce ya na yi da ita, shiyasa kawai ya katse batun.
Daga haka ya miƙe sannan ya ɗaura da cewa “bara in watsa ruwa daga nan sai in tadda ita, na barki lafiya, ki yi haƙuri dan Allah.”

Kauda kai Mama ta yi, da mugun kyar ta iya ce masa “tam”
Dan a yadda ta ji abubuwa daga Anne dukda Isma’il ɗin ya ce ya amince za a sake yin wani test ɗin sabo kawai sai ta ke ji ko da ace Afra ta fito negative ta na ji kamar still ta dakatar da auren….ba ta so a samu ɓaragurbi a cikin zuriarta sam! Dan ta lura ta fahimci abun nasu jini ya ke bi.


Hankalinsa a masifar tashe ya ƙarasa ɓangarensa ya nemi waje ya zauna ya na tunanin ta ina zai fara cewa Afra ta zo su koma a sake yi mata wani gwajin bayan wanda su ka yi aka tabbatar ƙalau duk su biyun su ke, har an haɗa ana shirin kaiwa masallaci! After what he did to her da safe da questions ɗinsa gareta ya san ba lalle ta yarda ba sannan ko da ace ta yardan ma dole za ta gane zarginta ne ake yi kuma hakan ba daɗi….
Sam-sam ba haka Mama ta ke ba!
Anne ce ta zugota ta hautsina komai ko shakka babu, amma in sha Allahu zai yi tackling komai bi’izinillahi ta’ala babu sheɗan, mutum ko aljan da ya isa ya raba aurensa da Afra…..
Ya aiyyana hakan a cikin ransa zuciyarsa ta na wani kalar tafarfasa…dan sai yanzu ya sake tabbatarwa tabbas akwai gulmace-gulmace a lamarin, tun farkon komai.
………….
“Afra haƙiƙa na cuceku na zalinceku! Ko da ace ku kun yafe mini ni ba zan taɓa yafewa kaina ba, ƙiri-ƙiri ba ki ji ba sannan ba ki gani ba amma gashi yanzu aurenki ya na shirin tarwatsewa duk domin kurakuraina.”
Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanyata yin shiru..

Cikin share hawaye Afra ta ce “Anne sai yau Allah ya yi za ki gane hakan kenan?! Sai da ki ka gama yiwa rayuwarmu giɓi?”
Sai kuma ta yi shiruuu, kafin ta ɗaura da cewa “Amma hakan ma abun farin cikine tabbas dukda dai kin gama goga mana baƙin fentin da ba na jin zai taɓa goguwa a rayuwarmu har gaban abada”
Sannan cikin sanyin murya ta jeho mata tambayar “me ya kawo Mama yau?”.
Wani sabon kukan Anne ta sake saki sannan ta ce “zuwan nata na yau ya sanya na sake shan jinin jikina…ki yi haƙuri ki yafe mini Afra duk ni na jawo miki…”
Cikin rawar murya Afra wadda ta ke ji kamar ta zaƙulo maganar daga cikin bakin Anne ta ce “Anne me ta ce? Mai ya faru?”

Share hawayenta ta yi ta ɗan yi shiruuu sannan ta soma magana cikin jan hanci da muryar kuka… “Shekaran jiya Mama ta kirani, akan wae ta na so ni da ita mu taru mu sanya ‘a dakata da auren…’
Na so in yi mata jainja amma sai ta ce ‘in yi ƙoƙarin ganin na yi controlling Babanku ta yadda ko su Usman ɗin sun kirashi zai ce musu ba yanzu ba, dan ta ji ƙishin-ƙishin game da abunda su ke shiryawa.
In ta samu lokaci za ta zo mu yi magana da ita.’
To dai nima na ga ƙanƙantar lokacin bayan an sanar mini kuma ina so in yi miki kayan ɗaki sannan ga rashin kirkin da su ka soma yi shiyasa na je wajen Malam Ƙasimu akan ya ɗaure bakunansu ya zamana sai yadda muka yi da su, sannan kar ta hana auren kuma ko bayan auren ina so ya kasance sai yadda ki ka yi da su saboda bana so a ci miki tuwo a ka ko a wulaƙantaki tunda kinga bana kusa Kaduna za su kai ki kuma kinji dai kalar maganganu da cin kashin da su ka soma yi a kanmu.
To sai gashi ban kai ga yin abunba ku ka taru aka tozartani aka jefar shi gaba ɗaya…..amma wallahi wallahi Afra iyaka akan abunda ya sa na karɓo tsuntsuwarnan kenan aikin ke zan yiwa saboda nima abun ya fara damuna kar rayuwata ta shiga rayuwarku ta tarwatsa farincikinku, tunda ni dai an gama goga mini baƙin fenti da abunda na yi da wanda ban yi ba da ƙarya da sharri duk an haɗa a cikin tarihina ba zan taɓa iya gogewa ba…”
Cikin sauƙe numfashi still ta na jan hanci ta na sharar hawaye, ta ci gaba da cewa “to kuma a yau dai Mama da ta zo ba ta sanar mini taƙameme dalilin da ya sanya ta ke so a dakata ɗin ba kamar yadda ta alƙawaranta cewa za ta gaya mini in mun haɗu, kawai dai ta ce kin yi laiifi, wae bayan ganinki da aka yi a hotel akwai wani laifin da ki ka sake yi, sannan Isma’il ya zo kin masa rashin kunya ɗazu da safe kenan inaga ta ke nufi, ta nuna tafiya ba za ta yiu a hakan ba, sannan da na ce mata na kuma dage akan ba ki yi komai ba alamu sun nuna ta fusata, dan ƙarshe dai shi ya sanya ta tafi ko cikakkiyar sallama ba mu yi ba, amma ni dai na san akan laifukana ne kawai har yanzu ba ta son auren fakewa ne ta yi take so ta ɓillo da basaja tunda tun farko sun nuna ba komai shiyasa ba ta so su yi fuska biyu, dan haka abunda na ke so da ke yanzu shine ki je ki amsa laifin da take ta cewa kin yi, kawai ki na zuwa ki ce mata eh kin yi amma kuskure ne kar ki bari ku jaa maganar sannan ki yi mata alƙawarin ba za ki sake ba kinga in kin yi hakan ae kin rufe mata baki kenan ko? Saboda ni na riga na san ba wani laifi da ki ka yi, kame-kame ne kawai take yi auren ne ba ta so a yi saboda sharrin da ake yi mini da kuma wasu daga cikin halayena, Mallan ya tabbatar mini ba ta so ba ta ƙaunar auren ne sam-sam! Akwai ma wadda ta ke so ta bawa shi Isma’il ɗin (ƴar uwarta)”

Cikin tarar numfashinta Afra wadda ta ke ji kamar zuciyarta za ta hantsilo ta fito waje ta ce “Anne har yanzu ba za ki rabu ki daina yarda da boka da Mallan ba kenan! Ba za ki daina ɗabbaka abunda su ke ce miki ba! Astaghfirullah Mallan Allah ne? Ya isa ya ga ko ya ji abunda ya ke a baɗini ko wanda zai faru a gaba! Yarda da ki ke yi ki ke saka abun a ranki shiyasa kawai Ubangiji ya ke barinki da halinki.
Kuma ae dama na daɗe ina gaya miki, ko dan mu Anne ya kamata ace kin rage wasu abubuwan amma kalli a satin aurena aka kama ki da laifin aikata da yunƙurin yin tsafi sannan Anne kalli abunda ki ka aikata a Ya Amir dole a dinga gudunmu.
Sannan na roƙeƙi da girman Allah kar ki sake yin tsafi ko wani asirin saboda ni ko ƴan uwana akan a so mu ko wani abun makamancin haka ki bari kar ki yiwa Ubangiji shishshigi, ba ruwanki…”

Cikin sake rushewa da kuka Anne ta ce “na ji, na ji Afra ba zan sake ba duk na ruɗe ne, gashi ƴan gidan nan gani su ke yi kamar ba na son auren, duk rashin imanina fa Afra ba zan ƙi farin cikinki ba, ina son ku ƴaƴana…
Mama ta yunƙuro da zafinta ne wannan karon, dan haka kawai ki wanke ƙafa yanzu muna gama maganar nan da ke, ki je ki sameta har ƙasa ki durƙusa ki basu haƙuri sannan ki yi alƙawarin ba za ki sake yi ba kuma ki amsa laifinki kar ki yi musu, kamar yadda ta buƙata, ki tsohe mata baki a samu a zauna lafiya……dan in wani abun ya samu auren nan na san bayaga takaicin da zan kwasa tsaf iyayenki cewa za su yi ni na tarwatsa komai….”

“Anne ba zan taɓa amsa laifin abunda ban yi ba wallahi, sannan kamar ke ce jiya na ji kin dage akan kar in bari a ci mini fuska”

“A’a! A’a!! Afra ni kam na sauya yanzu, ki yi yadda su ke so kawai a zauna lafiya, ki je ki ce kin amsa duk abunda ta ce kin yi kar ki yi gardama ko jainja dan Allah. Saboda kin ga jainjar da na yi ce ta janyo ta yi fushi ta tafi.”

Da sauri Adda wadda ta kasa zama a ɗakinta ta taho tun lokacin fitar Mama ta ɗaga labulen ɗakin ta shigo dan ta ji abunda Anne ta ke yi ta ji sentences ɗinta na ƙarshe-ƙarshen nan.

Ba ta jira ko sallamarta an amsa ba ta ƙaraso, ta na zuwa ta kamo Afra ta miƙar da ita, dan masifa Yarinyar da kyar ta iya tsayuwa ruwan hawaye kuwa kamar an kunna famfo…
Tattaɓa fuskarta Adda ta yi sosai sai da kwayoyin idanun Afra su ka daidaitu a kan fuskarta tukunna itama ta na kallon cikin nata idanun sosai ta ce “kar ki ji, sannan ko da wasa kar ki taɓa yarda da duk wasu abubuwan da take gaya miki! Kar ki bari ta shiga cikin kanki ta yi miki wasa da hankali…kin ji ko?”
Girgiza kai Afra ta yi sannan ta ce “Adda ba kya ganin abubuwan da su ke ta faruwa ne?”
Har Anne ta yunƙura za ta tashi a kan Adda, sai kuma ta koma ta zauna ta na mai sauraron Afra ta na ci gaba da cewa “Adda duk a yadda munin ƙaddarata ta zo bai kamata a ɗaura mini abunda ban ji ba ban gani ba kuma ace in amsa bayan an bini da sharri, dan wallahi ban yi mishi rashin kunya ba ko da ya fara hayaniya barin wajen kawai na yi….”
Wani guntun murmushi Anne ta saki ganin ta yi sara kenan dai-dai a kan gaɓa!
Daɗi har kwanyarta ta gyara zama ta na mai sauraron Afra ta na ci gaba da cewa “amma ki ji abunda ya ce ita kuma ta bi bayan ɗanta, ko da na gaida ita fa ɗazun ba ta yarda ta amsa ni ba, a tunanina bai kamata ta yarda da duk wasu jita-jita a kaina ba daga ita har Ya Isma’il ɗin ballanta su ji haushina…ba fa a aure da zargi. Kuma me na yi masa da zai mini sharri shima akan cewa na yi masa rashin kunya?
Sannan wallahi ba zan je in bada haƙuri ko in amsa laifin komai ba tunda ban yi komai ba, in zai aurena ya aura in ya haƙura nima na haƙura…”
Ta ƙarashe maganar cikin rushewa da kuka sosai.

Rungumeta Adda ta yi idanunta a kan Anne baƙin ciki kamar ya kar ta, itama Annen su ta ke kallo kawai ba ta ce musu komaiba…
“Allah ya shiryeki…”
kawai Adda ta ce da ita dan ko shakka babu ba ta san me da me duk su ka faru ba amma tabbas Anne ce ta haɗa komai! Ba wai.
……..
Da Amal da Adda da Aliya (ta waya) duk su ka taru da kyar su ka rarrashi Afra ta daina kuka sannan kawai ta ce musu “to” akan abunda su ke ta so ta fahimta dan da ikon Allah lissafinta ya soma karkata zuwa chan wani waje daban, ba dan komai ba sai dan yadda su ka yiyyiwa juna alƙawari ita da Ya Isma’il da yadda su ka yarda da juna bai kamata ace tashi ɗaya saboda ƙanƙanin mistake ɗin da ta yi ba komai ya tarwatse kalli yadda su ke zaryar zuwa gidansu one by one shi da Mahaifiyarsa akan abunda ta tabbata inda ace ita ce wallahi kalmar ‘sorry’ kaɗai daga wajensa ta yi yawa wajen mantar da ita an yi ma.

Dan Adda ta yi ƙoƙarin fahimtar da ita batun rashin kunya da Anne ta ce Isma’il ya ce ta yi masa sharri ne, wanda wannan kaɗai ne Afra ta yarda ta fahimta ta saka a kanta ƙarin gishiri da Maggin Anne ne a cikin lamarin amma ragowar abubuwa batun laifin da bata san shi ba da zuwa hotel da case ɗin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kam duk sai a hankali ta kasa ɗauka ta fahimta ko ta gane duk shirin Anne ne..
dan karatun Annen ya tafi straight zuwa cikin kanta babu mistake komai ya yi dai-dai.

Shiyasa duk yadda suka kai ga dagewa wajen fahimtar da ita
Ta yi haƙuri ta danni zuciyarta ta samu ta yi auren nan ta kawar da kanta wannan duk aikin sheɗan ne, ko wanne aure in ya matso dama akan samu irin haka.
Kar ta yi fushi da Ya Isma’il ko
Mama sannan ta kiyaye ta yi taka tsantsan sosai.
Kar ta ɗauki maganar Anne ko da wasa……
Gaba ɗaya abun ya ci tura, jinsu kawai take yi ta na gyaɗa musu kai amma ita a ganinta duk abunda Anne ta ƙara na ƙarya ta sani ta gane tunda ita ba Yarinya bace ba, ragowar maganganun kuma da ta ke yi musu kallon gaskiya ta zauna daram a kansu ta gagara sauƙa.
•••••••••••
Magaji Rumfa (Nasarawa G.r.a) Kano, Nigeria.


Babban Gida ne sosai, dan kai tsaye za ka kirashi da mansion.
Iyaka space ɗin da yake a cikin front raillings ɗin da akayiwa gidan kafin ka kai ga ƙarasawa gate da asalin katangar gidan..ta tsaye ya kai a yi gini 1 bedroom ƙarami a cikinsa har a samu ɗan tsakar gida faɗinsa kuwa dogo ne sosai ta both sides.
Gate na gidan kaɗai abun kallo
ne ba wai a iyaka fannin girma ba har da tsaruwa da kyau da inganci.


Motoci guda uku ne su ka karyo kwanar street ɗin wanda duk wanda ya sansu ya san Gidan su ka nufa, dan haka da mugun sauri wani mutumi ya miƙe daga ƴar majalisarsu ta benci ya nufi gidan da saurin gaske. Direct ya buɗe ƙaramar ƙofa ya shiga ciki kafin jim kaɗan ya hangame makeken tsadadden gate ɗin wanda ya yi hakan ne da taimakom remote na gate ɗin da ya ɗauka a wajen ajiyarsa a cikin gidan.


A dunƙule mansion ɗin ya ke a waje guda wanda kana kallonsa shape na circle za ka gani, in ka ƙura masa idanu sosai muddin ba ka cika son ganin abu mai girma ba (megalaphobia) to a take za ka burkice! Dan hawa biyu gareshi kuma a hakan a cikinsa part har guda uku ne, sai dai ko wanne part akwai ƙofar da zata sadaku a tsakani sai dai in son ran mutum ne zai sanya ya rufeta.

A babban parking lot na gidan motocin uku su ka yi parking.
Da sauri drivern da ya tuƙo ta ya buɗe ƙofar inda ya ke ya fito ya zagayo ya buɗewa Ummie ƙofa ta side na owners corner inda ta ke zaune ta hakimce.

Sai da ta gama shan ƙamshi ya na nan tsaye ƙyam!!! Ragowar drebobin suma duk sun fito sun tsatstsaya, tukunna ta fito wanda fitowar tata ya yi dai-dai da kiran wayarta da aka yi.


Ta na ganin sunan mai kiran ta yi murmushi tukunna ta ɗauka ta kara a kunnenta at the same time ta na mai ƙarewa gidan kallo ta ce “hala kin ji good news ko?”

Murmushi ɗayar Matar ta yi kafin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login