Showing 48001 words to 51000 words out of 100561 words
ya sake jajircewa akan ba fa za a yi ba, wanda jinyar tasa ce ta ci ƙarfin case ɗin tashinsu Anne da ake ta hayya-hayya a kai, dan haka ya ɗan lafa.
Yayinda gaba ɗaya hankalin Anne ya karkarta zuwa ga Ya Habu
wanda shi kuma duk duniya babu wadda ya tsana sama da ita.
Babban abinda ya sake haukata Anne ta kuma dilmiya a cikin kogon ƙaunarsa shine yadda ya ke wasa da kuɗi kamar bai san zafinsu ba....
Wani zubin tsabar yadda ta kwallafa rai a kansa ba ta iya yin barci sai ta sha wani abun saboda tunaninsa, wanda hakan ya sanya ta dilmiya kogin shaye-shaye.
Watanni biyu curr aka ɗauka Mustapha ya na jinya dan daga baya daina ɗaukar wayarsa Anne ta yi ta daina kulashi gaba ɗaya! Wanda hakan ya sake assasa abun…
Da kyar ya ɗan ji sauƙi aka dawo da shi gida zuciyoyin kowa babu daɗi dan sun tsani Anne amma kuma su na jin tsoron rasa Mustaphan saboda Likita ya tabbatar musu barinsa haka cikin wannan damuwar akwai matsala…
Kwatsam! Anne ta ji labarin an saka ranar auren Adda, nan da sati ɗaya tak! Dan iyayen ɓoyewa su ka yi saboda dama
zarginta su ke yi…
Aiki ta ke yi sosai ita da bokayenta akan ta raba Yadikko da Baba Yusufa dan Kaka Nura duk ya yi yaushi kamar wani ba shi ba!
Ita ko ba dan Kaka Nura ba ma ta na so ta kashewa Yadikko aure ko dan ita da Adda su dawo ƙarƙashin ikonta..
Sai dai kuma aikin da ta ke yi kamar ana rubutune a kan ruwa dan sam-sam ya ƙi ya ci!.
Still a wannan lokacin ne kuma ta fahimci ashe Uwani itama aikin kanta ya soma warwarewa har ta fara nema mata magani da Mijin aure a ƙauye ɗan Malamin wanda ta san zai kula da ita ya warkar da ita dan ita Uwani ciwo ta ke ganin abun na Nuratu da Mahaifinta tun lokacin da ta fahimci me su ke yi da inda su ka nufa da meye su ke da niyyar yi game da Yadikko ta tabbatar da tabbas su na da taɓin hankali saboda butulcin nasu ya yi yawa a mutum mai kai ɗaya.
Ga Habu shima ta kasa shawo kansa har gobe ba ya ma son ya ganta..gaba ɗaya dai abubuwan nata ko wanne ya ƙi ci kamar an saka mata hannu, Addan itama da ta ke ganin ta kore mata kowa kuma ana kan kore samari daga zuwa gareta gashi batun aure ya taso gadan-gadan...dan haka ta ɗaga hankalinta kwarai da gaske dan sai da takaici da damuwa su ka sauƙar mata da zazzaɓi a take a lokacin..duk ta birkice ta ma rasa ta ina za ta fara.
Zafin soyayyar Habu ce ta addabeta gashi dama ba a dai-dai ta ke ba a wannan lokacin dan haka ta gagara ci gaba da yin shiru da jiransa ya zo gareta ta yanke shawarar tunkararsa da kanta, dan gaskiya tunda ta ke bata taɓa jin matsanancin so akan kowa ba kamar yadda ta ke sonshi hatta Kaka Nura bata yi masa kalar wannan son.
Shiyasa ta zaɓi ta gaya masa ya sani wae ko ta samu ta rage wani nauyin atleast daga nan ta san nauyin zuciya da kwakwalwarta za su ragu su bada space ɗin da tunani zai shigo har ta samu damar sanin abunda ya kamata ta yi next....
Ranar ya na zaune a ɗakinsa kawai ya ganta ta shigo…
Da mamaki ya tsaya ya na kallonta kafin kuma ya ɗauke Kai ya tamke fuska tamau! Kamar bai taɓa dariya ba.
Cike da yanga da kissa ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi gefen katifarsa wanda hakan ya sanya ya miƙe tsaye da sauri cikin daka mata tsawa ya baiyyana a asalin sojansa ya ce “get out!!”
Ko ɗarr!! Anne ba ta ji ba, ta miƙe tsaye itama ta na yi masa wani kalar kallo da wani yanayin da ya sanya a take jijiyoyin jikinsa su ka amsa dan haka cikin matsanancin tsoron shaƙiyancinta ya shiga ce mata "get out!!"
Da masifar ƙarfi!
Ya na mai ja da baya amma sai dai kawai jinta ya yi ta afko kan jikinsa.
Ƴar Yarinyar da ya ke yi mata kallon ƙanwar ƙanwarsa cikin ikon Allah a ta ke ta hargitsa masa lissafinsa bayan amfani da hannayenta da ta yi a wasu sassa na jikinsa da bai fi sau biyu ba…
Sai da ya yi da gasken-gaske tukunna ya nemo ƙarfinsa ya ɓamɓareta daga jikinsa, ya yi mata shegen dukan fitar hankali dan sai da ta kasa tashi tukunna ya tsallaketa ya fice jikinsa ya na masifar karkarwa!
Ta ya ma in banda tsabar Iskanci za ta yi masa hakan bayan ta san sarai ɗan uwansa ne saurayinta, sannan ae shi ba sa'an wasanta bane ba!
Tabbas mace shu’uma ce dan gaba ɗaya ta hautsina masa tunani, ta tsoratashi matuƙa a wannan lokacin....
Habu bai ɓoyewa iyayensa komai ba amma sun ɓoyewa Mustapha, wanda gaba ɗaya tausayinsa ya fara addabarsu.
Yadikko ta na gama jin bayanin ta fita a hargitse Allah ya so Kaka Nura baya gidan sai Uwani ne kawai da Anne.
Ta na shiga ta tarar da Nuratu (Anne) a kwance fuska a kumbure Uwani ta sakata a gaba ta na ta kuka dan ɗazu Nuratun ta na shigowa Uwanin da ta tambayeta "mai ya faru?" kanta tsaye Nuratun ta ce mata "fyaɗe na so yiwa Habu shine ya yi min haka…"
Wannan dalili ya sanya Uwani ta saka ta a gaba ta dinga risgar kuka kamar ranta zai fita.
Yadikko ta na shigowa ta rarumo wata belt ɗin Kaka Nura da ta gani a saƙale kafin Nuratu ta tashi ta rufeta ta duka…
Kasancewar Yarinyar mai ƙarfin zuciya ce ya sanya ta tashi itama ta hau ramawa..
Habu ya na shigowa ya tarar tana kimar uwarsa, dan haka ya ɗaura daga inda ya tsaya ɗazu dama bai gama hucewa ba…
Yayinda Yadikko ta wuce ta shiga firfito da kayayyakinsu ta na kaiwa chan waje ta na zubarwa…
Sai da Nuratu ta suma tukunna Habu ya kyaleta ya shiga taya uwarsa fatali da kayansu har chan waje, yayinda Uwani ta ke zaune ta na kuka zuciyarta na ƙuna ta na sauraron yadda Yadikko ta ke ƙare musu zagi ta na cewa wallahi yau sai sun bar mata gidan Mijinta
Sai da su ka fitar da komai waje a
su ka watsar da shi a ƙofar gidan a bainar nasi tukunna su ka ja Nuratu itama a sumen a yadda ta ke, suka fitar da ita suka jefata akan kayan sannan suka mayar da ƙofar gidan nasu su ka rufe bayan sun kori Uwani itama ta fita salin alin dan a yadda ta ke ganin Yadikko ta san tsaf itama zata daketa in ta yi gardama.
To dae da wuƙa Kaka Nura ya dinga neman Habu bayan ya ɓalla ƙofar gidan ya shige a lokacin da ya ji ya ga halinda ƴarsa ta ke ciki
Dan awanninta uku yashe a waje babu wanda ya kulata har sai da ya dawo tukunna ya ganewa idanunsa...
Allah ya so Habu ba ya nan lokacin da ya dawo dan haka Baba Yusufa ya kirasa ya ce kar ya kuskura ya dawo Unguwar, bai gaya masa daliliba ya kashe wayar.
Ko da Nuratu ta farfaɗo da kyar aka barsu suka koma cikin gidan wanda gaba ɗaya suka muzanta…Yayinda Kaka Nura ya ɗaukarwa kansa alƙawari wallahi sai dai su su fita su bar musu gidan tunda su ka yi musu wannan tozarcin.. dan ya na ajjiye Nuratu ya tattaro Yara aka maida kayan cikin gidan saboda su san zama daram! Tukunna ya bazama neman Habu.
Ba abunda ya fi ɗagawa Nuratu hankali irin yadda wae kaff Unguwar tasu babu wanda ma ya kulata hatta Uwani to Ina ma ta yi.?
A bakin Kaka Nura ta ke jin wae gidan maƙofta ta shige a lokacin da abun ya faru saboda wae ta na jiri…
Ba kaɗan ba ran Nuratu ya ɓaci zuciyarta ta ƙuntata!!
Saboda a ganinta wacce iriyar daƙiƙiyar uwa ce za ta bar ƴarta yashe a waje kuɗa ya na bi ta shige ciki..tabbas duk sai ta gasa musu aya a tafin hannunsa wallahi in har ta haifu duk sai ta tagaiyyara musu rayuwa...
Da ya Mustapha wanda ta san saboda nacin sa ne ya janyo mata ɗan uwansa ya ke gudunta dan ta san wallahi ƙaryar Namiji ya ganta ya ce ba ya so!
Da kuma Yadikko wadda ta tozartata, dan bayaga jefar da itan da su ka yi, ta san ɗazu sarai Yadikkon ta san kayan shaye-shaye ne a leda amma ta haɗa ta watso waje bayan ta yaga ledar yadda Uban kowa zai gani ya shaida, kuma ta ci riba dan an shaida ɗin tunda gashi Kaka Nura ya tabbatar mata har an soma munafurci ana cewa 'Ashe bayan halinta har da shaye-shaye ma ta ke yi.'
Ita sam! Maganganunsu ba su yi mata zafi ba wallahi ko a jikinta dan maganganun mutane ba sa taɓa damunta! Tunda ita dai ta san ba ta jin tsoro, shakkah ko kunyar Uban kowa!
Kawai ita yadda Yadikkon ta yi da gangan kuma ta ci riba aka gani aka shaida ne ya ɓata mata rai dan haka ta ciwa kanta alwashin in har ta haifu to itama Yadikko sai an gani an tabbatar ta na shaye-shaye, saboda duk abinda aka yi mata sai ta rama ba ta Mantuwa.
Da kuma Uwani!
Uwar da ta banzatar da ita ta bari ta tozarta!
Wallahi itama sai ta tozartata ta azabtar da ita domin kuwa Nuratu ba ta yafiya....
Sai kuma Baba Yusufa da Adda suma duk sai sun karɓi rabonsu....
DA ƙyar aka iya controlling Kaka Nura sannan ƴan Unguwa kowa ya bi bayan Baba Yusufa aka ce tunda zama ya ƙi yin daɗi an basu sati ɗaya tak! Su tartara su bar Unguwar dan gaskiya sun addabi kowa kuma kar a je a yi kisan kai a zo a na cizon yatsa.
Dan shima Habun a fusace ya ke da Kaka Nura wanda hakan da iyayensa su ka gani ne ya sanya su ka ce masa kar ya dawo saboda sun san kalar zuciya irin tasa tabbas in har Kaka Nura ya tunkaresa a haka za a iya yin kisan kai.
Sai da aka haɗa kan sojoji suka yiwa Kaka Nura warning tukunna da mugun kyar ya yarda ya kyale batun Habu a wannan time ɗin ba wai dan ya yafe masa ba!
Domin ya yi alƙawarin sai ya rama mata wallahi....
Ta na samun kanta daga raɗaɗin dukan da Habu ya yi mata ta ta ƙarasa wajen bokanta akan batun auren Adda, Habu, kashe auren Yadikkko da kuma tashin da aka basu notice ɗin su yi!
Tun da ta je ta ke nanata masa cewa
Ko menene aka ce ta yi za ta yi....ya faɗa mata ɗayar hanyar da ya ce akwai tunda dai wadda su ke kai ta ƙi ɓillewa ita kuma ba ta da dubu ɗari a wannan lokacin, ko wacce hanya ce ko me aka ce ta yi za ta yi saboda wallahi wallahi ta yiwa kanta alƙawari sai ta ida manufarta a kan dukkansu kuma babu uban wanda ya isa ya tashesu a cikin gidan, ba za su tozarta ba.
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*21*
Kanshi tsaye ya sanar mata sacrifice za ta yi musu...wata biyu zai bata ta yi sacrifice ɗin amma aiki kam tun daga ranar za ta fara gani ya na ci muddin ta ɗauki alƙawari za ta yi abunda aka ce ta yi...
Sai da ta sake amsa masa da 'eh, ta ji ta gani' tukunna ya bata wani ruwa ya ce ta dinga wanka da shi kullum babu fashi a ranar da ta shirya yin abun kuma ta watsawa wanda za ta basu daga nan kar ta sake amfani da ruwan ta zubar! Ba wai sai ta sheƙa masa ba ko da ɗigo ɗaya ne a samu ya taɓa jikin wanda ta shirya basu, in ya so sai ta kashesa a lokacin ko ranar da ruwan ya taɓa jikinsa ko ta tura a kashesa duk dai yadda ta yi amma an fi so ta ƙona mutum da ransa har lahira, kuma an fi buƙatar Namiji sannan ba Yaro ba.
Su kuma sun yi alƙawari za su yi mata aiki mai zafin da duk wanda ya yi yunƙurin yin abunda bata so ɗin ma zai iya rasa ransa.
Rai ko kuma dubu ɗari…wanda a wannan lokacin dubu ɗari ba ƙaramin kuɗi bane ba dan haka ta zaɓi ɗayan option ɗin zuciyarta a dake ta ƙudirtawa kanta za ta iya, dan a take ta gama tsara wa za ta bayar da kuma yadda za ta yi da wanda za ta jinginawa alhakin laifin.
Shi kuma Habu wani ruwa daban shima aka bata aka ce kawai in sun kasance a waje ɗaya ita da shi ta fasa ruwan a nan za ta ga amfaninsa. Dan in har ta fasa to tsawon watanni uku ma bai isa ya fita daga ƙarƙashin ikonta ba ta inda ko wacce iriyar buƙata ta je masa da ita ko ta nuna ta na so sai ya yi mata tukunna zai samu kansa da nutsuwa, sannan shi da kansa bokan ya tsafeta tass da sunan Habu kuma ya saka mata tashi albarkar(a cewarsa) tukunna ya yi mata alƙawarin duk ranar da Habu ya kwanta da ita to ta tabbata ya zama a cikin tafin hannunta ne.
Adda da Yadikko suma duk sai da aka yi mata maganinsu sannan ta ɗaure su, yayinda ba ta yi aikin uwar komai akan Baba Yusufa ba saboda shi ɗin mai kankat ta tsara za ta yi masa, ta inda za ta jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya....
A haka ta ƙaraso gida zuciyarta ta na tafarfasa dan in ta tuna abunda su ka yi mata sai ta ji kamar ta cinna musu wuta gaba ɗayansu amma kuma in ta yi hakan to ta yiwa Yadikko gata ne wadda ita kuma so ta ke yi ta dinga kasheta da zafin takaici da ciwon duniya every single day har tsufanta.
Maƙil! Haka gidan ya cika taff da maƙwabta ƙawayen Yadikko Da wasu daga cikin relatives ɗinta ƴan ƙalilan dan ba ta kasance ƴar dangi sosai ba daga ita sai yayanta da Addanta ne family ɗinta.
Baba Ali kuwa dama ya yi alƙawari in dae Nura ya na gidan ba zai sake zuwa ba, dan haka bai zo ba amma ya aiko musu da matarsa har da body guard soja guda ɗaya a cewarsa in an taɓa ta ya ɗauki mataki, dan ya sanar musu akwai mahaukaci a gidan.
Dan haka gidan ya kasance da albarka wae ana sakun lalle.......
Haka nan ake ta hada-hadar bikin Adda wanda za a ɗaura auren ne jibi (a wannan lokacin) idan Allah ya kaimu, Uwani tunda aka fitar da ita daga gidan yau kwana huɗu kenan ta ke gidan makwaftansu ta na jinya, ba su ce ta tafi ba itama ba ta ce za ta tafin ba kuma babu wanda ya nemeta, Sai da Nuratu ta dawo yau daga wajen Bokayenta tukunna ta shiga gidan ta ce "Kaka Nura ya na kiranta"
Kamar ba zata bi ta ba sai kuma ta yi musu sallama ta tashi ta fita…dan ita kanta ta san sun yi mata ƙarshen kara ta na gudun kar su gaji.
Nuratu ta bita a baya mutanen gidan su na girmama tsaurin ido da taurin zuciya irin na Yarinyar…
Da ace wata ce wannan abun kunyar ya faru da ita kwanaki huɗu da su ka wuce to da tuni ta ɓoye kanta ruff a ɗaka amma ita kalli har ta warke ta fito abunta kuma da kwarinta!
Ɗazu ma shegen duka ta yi wa wani Yaro saboda ya yi mata dariya a waje....
Da ikon Allah har cikin gidansu ta zo amma "Salam" kawai ta ce ta gayawa Uwani saƙonta cikinsu babu wadda ta gaisar.
Sau uku Uwani ta na tare kanta daga faɗuwa ta hanyar dafa bango dan jiri ta ke yi sosai
amma ko hannunta Nuratu bata taɓa ba ballantana ta taimaka mata dan wani kalar haushin Matar ta ke ji zuciya ta na sake yunƙuro mata a duk lokacin da kwakwalwarta ta haska mata yadda Uwanin ta banzatar da ita ko la'akari da yanayinta na rashin lafiya da ta yi yanzun bai sanya ta ji za ta iya yi mata uziri ba... shiyasa sam ta gagara tausar kanta daga abunda ta shirya mata.
Misalin ƙarfe 1 na dare lokacin kusan kowa ya kwanta barci sai
ragowar ƴan biki da su ke ɗan hira, ta zo ta wuce ta shige ɗakin Habu wanda ya ke a tsakar gida, kanta tsaye babu gargada…
Ɗiff!! Haka su ka ɗauke wuta gaba ɗayansu sai kuma aka fara ƙus-ƙus kafin su miƙe su ka yi cikin parlourn gidan da gudu cikinsu har da masu tuntuɓe saboda tsantsar firgici da mamaki dan su dai sun san Habu idanunsa biyu bai daɗe da shiga ɗakin nasa ba daga banɗaki.
Sannan ga wutar ɗakinsa wadda ta ke a kunne har kawo yanzu...amma kuma tunda ta shiga su ka yi lufff, bai korota ba.
Ta na shiga ya miƙe tsaye amma abun hannunta da ta fasa sai ya sanya ya kasa motsi daga baya ma komawa ya yi ya zauna kawai ya na mamakin kansa…
Minti