Showing 45001 words to 48000 words out of 100561 words
amfani da shi..kanta tsaye haka nan ta ke tafka ƙazantarta mafi muni dai-dai gwargwadon iyawarta.
Kwata-kwata a lokacin shekarunta ba su rufe 19 a duniya ba.
To dai ba kalar bugawar da ba ta yi ba abun ya ƙi tarwatsewa dan haka bayan ta fahimci a tsume mutumin ya ke da addu'o'i da kariya sai ta chanja salo...
Da farko messages ta fara tura masa akan Addan ta na da tarin samari!
Sai ta ce a kira wayar za a ji busy in an kira kuwa za a ji busy ɗin dan ta na gama faɗin hakan ta ke amshe wayar Addan ta hau waya
Da ta ga saurayin bai biye wa makircinta ba sai ta ce masa ae ta na neman maza...
Haka nan za ta karɓi wayarta ta yi ta tura masa messages ɗin batsa a zuwan Addan ce ta ke so ya biye mata su watse...duk wae dan ya yarda ƴar iska ce,
Kasancewar saurayin ba Yaro baneba ya sanya tun a karon farko ya fahimci sharri ne ake so a yi mata, dan shi dai ya yi duk wani binciken da ya kamata ya yi a kanta kuma ya yarda ya amince da amsoshin da ya samu da zuciya ɗaya above all tsakaninsa da Allah ya ke sonta, dan haka ya san in sha Allahu za ta zame masa alkhairi, shiyasa ya toshe kunnuwansa daga duk wata zuga kawai ya basar ya yi focusing akan zallar ƙaunar da ya ke yi mata...
Sannan ya duƙufa yin bincike dan ya na so ya gano munafukin ya hukuntasa yadda ya dace.
Hakan kuwa (ganin bai ɗauki zugar ba) ba ƙaramin fusata Anne ya yi ba gashi a lokacin batun auren ta ke gani ya na tahowa gadan-gadan kullum dan haka ta koma wajen bokanta ganin sun kasa rabawa kawai sai ya jefa masa matsananciyar jinya bayan sun samu sun kauda hankalinsa daga kan ibada na ɗan ƙanƙanin lokaci da mugun kyar! Su ka yi sauri su ka tura masa aljanu. Aljanun su ka dinga shanye jininsa bayan sun fita sun shiga sun rabasa da ibadar da ya ke yinta tuƙuuru…
Dan a lokacin Yaddikko ta sakota a gaba fiye da ko yaushe sannan uban Addan shima wannan karon ya ja baya da su hatta Addan wadda ta fara fahimtar kamar Anne na yi mata zagon ƙasa itama duk ta ja baya da su..ga shi soyayya da kulawa da gata tsantsa ta ga Addan ta na samu daga wajen saurayin shima dan haka gaba ɗaya sai ta gigice ta fita a haiyyacinta sannan
ta fusata…
Satin mutumin bakwai ya na jinya ta fitar hankali kafin ya ce ga garinku nan dan hatta bokan sai da ya ji tsoro ya kira Anne ya sanar mata in an ci gaba zai iya mutuwa amma ta ce ta ji ta gani…
Domin a wannan gaɓar ba ta ji ba ta gani kishinta ya sake tashi matuƙa sannan baƙar zuciyarta ta murɗa.
Tun daga nan kuma sai ta hau yin rigakafi dan kafin ma wani ya zo take hanawa ta koresu saboda kar ta sha wahalar rabawa kamar last one ɗin…
Wani guda ɗaya ne mai ƙarfin kuruwa ya sake zuwama Addan shima ya kafe bayan ta tarwatsa aurenta a karo na shida
Lokacin shekarun Adda Ashirin da biyu ita kuma ashirin cif-cif
Har an fara gulmar itama Addan a Unguwa ana zarginta da wani abun daban duba da yadda ta ƙi auruwa sai ƴan Unguwar su ka ce aljani ne ya aureta, Anne kuwa dama ƴan Unguwar sun ce ita da aure sai dai ta ga anayi…kaff ƴan layin sa’anninsu duk sun yi aure har ma da ƙannensu amma banda su.
Zuwa wannan lokacin Adda gudun Anne ta ke yi sosai domin kuwa ta riga ta fahimci ba ta sonta
kwata-kwata...ko ta kanta (Annen) bata yi ita kawai kar Adda ta rigata aure ta tafi ta barta…
To dai wannan Saurayin taɓin hankali Mahaifiyarsa ta samu saboda ta nace akan ba ta son aurenshi da Adda shima kuma ya na ce akan sai ya auri Adda, dan haka ganin baƙin cikin hakan ya na shirin illata masa Mahaifiya ya sanya ya janye ya haƙura ya karɓi zaɓinta (ƴar uwarsa ya aura)
Duk dauriyar Adda wannan karon kam sai da ta kwanta jinya.
A ɓangaren Uwani da Kaka Nura kuwa ita kanta Uwani ta san cewa Kaka Nura ya gaji da ita kuma akwai abunda ya ke damunsa
wanda gaba ɗaya ya sanya shi ya ke neman zama kamar ba shi ba, ganin takaicinsu shi da ƴarsa ya na nema kasheta ya sanya ta ɗauki hutu ta tafi chan wani waje (wajen makwafciyarsu lokacin ta na gida) ta ɗan huta, kafin ta dawo shi kuwa ya yi aure kuma da ta dawo ya ce wae sai dai ta zauna a wajen Baba Yusufa ae bai bata izinin tafiya ba ta yi yaji, kuma shi ba zai iya zama babu mace ba in dai ba zina ake so ya yi ba.
An sha yaƙi sosai dan ba kunya ba tsoron Allah Kaka Nura ya dage akan sai dai Uwani ta zauna a gidan Baba Yusufa ta bar musu ɓangaren tunda ita ɗin ƴar uwarsa ce Amarya kuma bare ce ba zai yiu ya kai musu ita ba! Kuma bashi da wajen sakata.
A ranar ne kuwa shima Baba Yusufa ya yi masa ɗan ƙaramin hauka ya ɗaga masa hankali ya haɗashi da ƴan sanda
Kwana uku aka ɗauka ana case kamar za su cinye juna!
Kafin hukuma ta shiga tsakani, Amarya ta koma gidansu Uwani ta shiga ɗakinta.
Ƙarshe dai kawai iyayenta su ka ce ya bata takardarta.
Tun daga wannan rana Kaka Nura ya ɗauki karar tsana ya ɗaurawa Baba Yusufa da Uwani, ko kallonta ba ya yi, kuma ya ƙi ya saketa saboda ya san arziƙinta ya ke ci a fannin muhallin dan shi Kaka Nura kamar wanda aka nuna da leda ko fili taku biyar ba shi da shi har gobe haya ma ba iya biya ya ke yi ba.
A wannan lokacin ka na ganinsa ka san bayaga tsanar Uwani da ɗanuwanta da ya ɗaurawa kansa tabbas akwai abunda ya ke damunsa…
Amaryarsa ta tafi kuma zuwa yanzu Alhamdulillah akwai buɗi dan Nuratu(Anne) kuɗaɗe ta ke samu ta koina kuma ta na bashi wanda ko tari aka yi da zummar magana game da inda ta ke samun kuɗi sai an kwana ba a rintsa ba a cikin gidan.
Duk kalar ɓarnar da Kaka Nura ya yi Uwani ko a fuska ba ta nuna masa ba bayan ta dawo an zauna
amma shi bayaga hantara, kyama da duka a ɗaka in su biyu ne yanzu ta kama har hannu ya ke saka mata a waje a gaban Uban kowa.
Gaba ɗaya ya tsaneta ta fita daga ransa dan ko a batun iyayen Nuratu ba ya ƙaunar a haɗo sunansa kusa da na Uwani duk dan ya na ganin kasancewarta ƙanwa ga Babà Yusufa shine zai fara zame masa katanga wajen mallakar Yadikko, dan shi a halin da ya tsinci kansa a wannan lokacin ji yake duk Matan duniya babu wadda ya ke so sama da Yadikko, bai san dalili ba haka kurum Ubangiji ya ɗaura masa matsanancin sonta, wanda hakan ne ya haifar masa da damuwar da ta sauya shi aka kasa gane kanshi.
A lokacin ya auri mata bila adadin wasu ma ya manta da ya auresu amma Yadikko kawai ya ke ji ya na gani a ganinsa duk ragowar muna Mata ne sai ya mallaketa tukunna zai san ya tara da Mace, kuma duk Matan Unguwa zawarawa da ƴan mata da na kewaye ba su yi masa ba, ita kawai yake so da sha’awa.
Yadda ya ke fito da kujera ya dasa ne ya na leƙenta in ta na aiki a tsakar gida ya fara tona masa asiri a wajen Uwani yayinda Baba Yusufa ya na fahimtar hakan ya yi tsalle ya dire ya ce in sama da ƙasa za su haɗe wallahi wannan karon sai sun bar masa gidansa. Da shi da ƴarsa sai sun fita a gidan nan tun kafin su janyo a yi musu girgizar ƙasa a iyaka cikin gidan nasu…
Dama tun lokacin ya duƙufa wajen yiwa ƴarsa magani dan ya soma zargin da sa hannunsu ba wai a iyaka aurarrakin Addan da su ke ta taɓarɓarewa ba har da faɗan da ya kunno Kai tsakanin Matarsa da ƴar tasa wanda zuwa yanzu Yaddiko ko sunan Adda ba ta son ji ma
ballantana ta ganta…
Ana tsaka da wannan bala’in Mustapha da Abbakar (twins) su ka dawo daga karatu, dan Abbakar ɗin shima ya dawo ne zai ɗan zauna an tsara akan sai ya yi aure sai ya sake komawa wajen Uwar goyon tasa tare shi da Matarsa, in ya nemi transfer an basa dan duk Kano aka yi posting ɗinsu.
Ta inda Mustapha ya kammala nashi karatun shima ya fito da matsayin second lietanant.
A lokacin ne kuma Anne ta ji batun Mahaifinta ya na son Yadikko daga bakinsa, wadda abun ya bata mamaki da farko amma kuma da ta fahimci in ya riga ya auri Yadikkon kamar rayuwarta ta gama tagaiyyarawa ne ita da ƴaƴanta sai ta ɗauki ɗamarar haɗasu..
Kamannin Mustapha da Abbakar(wanda su ke kira da Habu) sak ɗaya basu da bambamci sai ko ta yanayin tsayi da ɗan hasken fata dan Mustapha ya fi Abbakar haske...
Amma tunda Allah ya sa Anne ta ga Abbakar a take ta ji so da masifar ƙaunar shi sun shigeta, gashi daɗin daɗawa Abbakar ya fi Mustapha kuɗi nesa ba kusa ba dan sana'a ta karɓesa kwarai da gaske Allah ya saka masa albarka saɓanin Mustapha da zai riƙeta da albashi zallah.
Gashi Mustapha ya dawo mata da zazzafar soyayyarshi saboda shi tunda ya tafi dede da rana ɗaya sonta bai taɓa raguwa a cikin zuciyar tasa ba sai dai ƙaruwa ma da ya ke yi.
Suna waya ya na gaya mata ya na sonta amma bata taɓa tunanin da gasken gaske ya ke ba sai yanzu da ya dawo mata a hargitse sannan ya na dira ya fara yiwa iyayensa maganar aurensu waenda suma ashe duk ya daɗe ya na yi musu amma su ka banzatar da abun.
Tashi ɗaya Adda, Baba Yusufa, Yadikko da ɗan uwansa su ka ce masa in dai Anne zai aura wallahi babu su babu shi…
Shi kuma ya yi tsalle ya dire ya ce sai ita!
Dan haka sai gidan nasu ya zama kamar filin wasan kwaikwayo kullum
ana drama.
Ƴan Uwana maza da mata, ku tsaya in baku labarin amintaccen guri kuma muhalli na siyar da ingantattun *KAYAN YARA* na alfarma, siyayya cikin aminci, farashi na musamman da babu irinsa(mafi rahusa), kaya na kece raini da fita kunya sai a *H&A KIDDIES CLOTHING*
Domin samun su ku garzaya shafinsu na instagram mai suna *H&A_KIDDIES_CLOTHING*
Ko kuma ku nemesu a WhatsApp ta number waya kamar haka *08143828139*
Kar ku bari wannan damar ta wuce ku...Kaya na ƴan kwalisa sai a *H&A KIDDIES CLOTHING* ga kyau ga quality ga araha dai-dai kudin ku tested and trusted.
Za ku iya samun kayan Yara na zuwa gurin biki, suna, birthday parties, kayan zaman gida da dai sauransu....
location:Kano
Delivery:NationWide.
kar ku bari a baku labari, sai kunzo🙏
SIYEN NA GARI, MAI DA KUƊI GIDA
BULAMA ✍️
0806 402 1951
0903 441 3252[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*20*
Kaff arear zuwa wannan lokacin Anne ta daina shiga gidajensu dan ko ta shiga ba a kulata in ma bala’i ne ya kaita sai dai ta ƙaraci abunta ita kaɗai ta fito ba mai ce mata uffan. Ƙawayenta da su ka yi Makaranta kuwa kowa ya fahimci halaiyyarta dan babu wanda ba ta cuta ba
In dai ta raɓi mutum to fa sai ta cucesa
dan haka ko biki ko suna sai dai a gaiyyaci Adda kaɗai tare da warning ɗin 'kar ta zo musu da Nuratu'
Yanzun kuwa itama da ta fahimci wacece Nuratu shikenan ta kama kanta, dama Yadikko da su sun daɗe su na gaya mata amma ba ta yarda ba sai da ta gwada mata a kanta tukunna ta ji ta gani.
Ƴan Unguwar Abokan Ya Mustapha tun na baya kafin ya tafi karatu, duk sai da su ka taru su ka bashi shawara har da manya akan ya haƙura da auren Nuratu amma ya ce ya ji ya gani.
Baba Yusufa kuwa ya ce 'ko mutuwa zai yi ba zai auri Nuratu (Anne) ba'
Sarai ya san su ne silar tarwatsewar gidansa dan haka ba zai taɓa bari su sake shiga jikinsa ba....a halin da ake ciki kullum Yadikko sai ta jibgi Adda ba laifin tsaye ba na zaune gashi Yarinyar ta kwanta rashin lafiya tun tarwatsewar last aurenta...
itama Annen jinya ta ke yi a tsatstsaye tun lokacin da Baba Yusufa ya fara nemawa ƴar tashi magani..
Dama tun lokacin da soyayyar Yadikko ta shigi Kaka Nura ya tsani Baba Yusufa tsana ta fitar hankali.
Ita kuwa Nuratu tun lokacin da ya fara yiwa ƴarsa magani (ita kuma ta fara jinya) kuma bokanta ya tabbatar mata sai sun fi haka tsayawa saboda addu’a ake yi sosai kuma ba a waje ɗaya ba, ba kuma a gari ɗaya ba, shikenan gaba ɗaya ta tsani mutumin matuƙa....
Gashi Bokan ya ce mata sai dai ta kawo dubu ɗari in ba haka ba Adda sai ta warke kuma har da haske ya hango mai ƙarfi a tattare da ita muddin aka karya komai…ko kuma in ta kasa haɗa kan kuɗaɗen to ta zo akwai wata hanya ta daban!.
Mutumin ya tabbatar mata da cewar “babu abunda zai sameta ba wai asirin ne zai dawo kanta ba dan ba ƙaiƙayi ake yi a maganin Addan ba, kawai neman lafiyarta ake yi ta hanyar Addu'a, hatta wannan kwanci tashin da ta ke ta faman yi ba wani abun bane ba da zarar Adda ta warke an rage addu'o'in da ake yi itama za ta warke garau...
Amma baƙin ciki, kishi da kuma ego..... kar Adda ta yi winning against her ya sanya ta ƙi haƙura sannan ta na gani in ta barta ta yi winning it means duk wahalarta ta baya ta tafi a banza fa kenan sannan ubanta da Yadikko sun ci riba…
Sosai zuwa wannan lokacin Uwani ta fita a harkar Anne da Mahaifinta Kaka Nura.
Domin kuwa sun tartarata ne itama sun ajjiye a gefe...
Anne ko kulata bata yi saboda ko gaisheta ne in ta yi maimakon ta amsa mata sai dai ta ce mata "ki ji tsoron Allah"
Saboda ita kanta zuwa wannan lokacin sarai ta san Nuratu ta kware a neman maza da kuma bin Malamai har ma da shaye-shayen da ta soma ba da jimawa ba duk Uwani ta sani, gashi Ubanta ya kafa ya tsare ya ce in ta yaɗa to a bakin aurenta, ta bar mutane su yi ta gulmarsu amma ita dai a matsayinta na Uwarta kar ta kuskura ta bari a ji daga Bakinta.
Wae su taru su rufawa ƴarsu asiri wanda a tunaninta tsoron hakan ne ya sanya ta yi shiru sai dai abunda bata sani ba toshiyar Bakine ƴar tata ta yi mata sannan ta yi mata mutuwar tsaye dan akwai Bokan da ya tabbatar mata cewa 'in har bata kafe Uwani ba to tabbas ita za ta kafeta da sunan kariya da nema mata shiriya ta hanata jin daɗin rayuwarta kwata-kwata'
Shiyasa tun da Uwani ta dawo gidan gaba ɗaya duk sai ta koma wata sukuku kamar wata gaula...
Su Baba Yusufa su kuma a tunaninsu baƙin cikin Nuratu da Nura ne ya sanya ta koma haka da kuma Yadikko...
Dan a wannan lokacin sai da Yadikko ta kusan tarwatsawa Uwani zuciya da gori da baƙaƙen maganganu, saboda a ganinta ta hakan ne kawai za ta ɗan samu ta rage azabar baƙin cikin da ta ke ji a cikin Zuciyarta duk a ta sanadiyyarsu, kuma da ikon Allah Baba Yusufa sai ya gagara tsawatarwa Yadikkon sabida shima a ƙule ya ke da Nuratu da Ubanta sannan yau da gobe sai Allah, besides shima ɗin bai barsu ba dai kullum ana cikin case ɗin sai sun bar gidan ta inda Kaka Nura ya ɓullo da wani sabon zance wai 'tunda ya yi shekaru aru-aru har ashirin to fa gida ya zama nasa(iyaka inda su ke zaune), idan ma zai tashi dole sai an jira ya samu wajen zama tukunna.'
Kuma da ikon Allah sai ya soma samun magoya akan hakan.
Abunda ya sake kafe Uwani a auren Kaka Nura kenan a wannan lokacin saboda idan ya sake ta ta san babban case ne zai sake tashi bayan wanda ake ciki itakuma a ganinta bala'in da su ke ciki ma ya ishesu ba sai ta jangwalo wani da aurenta ba, dan a yadda ta fahimci ya na son Yadikko zuwa wannan lokacin ta san babu inda zai yarda ya tafi ya barta idan kuma ya kashe aurenta da Baba Yusufa ya ɗauketa suka yi gaba to fa ita aka cuta saboda ba ta so ya janye mata Anne gaba ɗaya, ta na so ta tsaya a kanta ta gyarata sannan a gabansu ma ga abubuwan da ta ke yi Ina kuma ga in a bayan idanunsu ne an barta da Kaka Nura da Yadikko kawai…
Jinya sosai Mustapha ya kwanta a lokacin da Baba Yusufa ya tabbatar masa da cewa 'muddin ya sake yi masa maganar Nuratu wallahi sai ya tsine masa albarka.'
Dan haka Zuciyarsa ta kumbura saboda wani kalar so ya ke yi mata na masifa musamman ma da ya dawo ya ganta ta cika ta ƙara kyau in ka ganta kamar aljana!
Shiyasa duk ya bi ya gigice kuma ya ke iƙiirarin
'Wallahi ko a karuwa ce ya yarda ya ji ya gani zai aureta…'
Wanda furucin nasa ya taka muhimmiyar rawa wajen sake tunzura Baba Yusufa shima ya sake kafewa akan in dai shi ne Ubansa to ba zai aura masa ita ba dan a yadda ya ga Mustapha ya na hauka a kan Nuratu ya san masifun da za su biyo bayan auren nan su na da yawan gaske tabbas!
Dan haka