Showing 39001 words to 42000 words out of 100561 words
a cikinsu ta ce " Yaro mu ce mana aka yi bai da mata, da hankalinmu ta ina za mu yarda a saka wata a ɗakin wata?" Yadikko kawai ya sanar mana mata a gidan nan wato matar mai gidan, kuma kamar yadda ya kwatanta mun ga ɓangarenta ga shi chan ita da mijinta da ƴaƴanta.
Wani kalar taɓe Baki Mustapha ya yi kalar na takaicin nan sannan ya ɗaura da cewa "maganinku kenan! Daga an je muku da maganar aure kun yi caraff kun amshe ba tare da kun yi kwakkwaran bincike ba, sannan daɗin daɗawa ko zuwa ba a yi an ɗauko ku ba kun taho da ƙafafunku...yanzu ae ga irinta nan.
Wannan ɗakin, ɗakin Mahaifiyar wannan Yarinyar ce kuma yanzu haka ma ta na kwance ne a gadon asibiti ta na jinya, sai ku gaya mini in kun yi wa kanku adalci muddin ku ka yarda ku ka saka wata a cikin ɗakinnta.."
Ɗayar ce ta hau salati idanunta a kan Nuratu ta ce "ƴar nan ki ka ce mana Mahaifiyarki ta rasu?"
Girgiza kai ta yi kawai ta kawar da kanta dan ba ta so magana ta yi yawa ta yi kwaɓa a gaban Ya Mustapha.....
To dai Allah ya so Matan an samu masu hankali da fahimta, dan a take su ka yanke shawarar juyawa da Amaryar bayan itama Amaryar ta tabbatar musu ba za ta shiga ɗakin wata ba....
Haka nan su ka juya da ita zuciyoyinsu fal mamakin sha'anin Nura da ƴarsa wadda ta kashe Uwarta da ranta.
Shi kuma ya fake da ce musu a sirrince ya ke so a yi auren ashe abubuwa a ƙaasa dunƙule ya ke ɓoyewa.
Su na fita ta fashe da kuka ta ce "ba na so in yarfa Baba ne a gabansu shiyasa na ce musu haka...."
Cikin damuwa Mustapha ya ce "ko ma dai menene bai kamata ki ce Mamanki ta rasu ba, hakan ba kyau..."
Kamar ba Nuratu ba haka nan ta sunkuyar da kanta ƙasa kawai ta yi kalar tausayi sosai.
Ya jima ya na kallonta a ransa ya na lissafin yadda za ta kaya shi da Kaka Nura a yau idan ya dawo gidan bai tadda Amarya ba, sai kuma kawai ya jaa numfashi ya sauƙe ya ce mata "je ki ɗauko kayanki in kaiki wajen Adda ina so zan wuce wajen Mama ta na jira na..."
Ya yi maganar tausayin matar ya na sake shigarsa bai ma san ta ina zai fara yi mata bayani ba wallahi.
A tsakar gida su ka tarar da Yadikko, Zainab da Mai aikinsu su na gyaran kifi.....
Sun ji guɗa kuma sun ga shigowar mata, sarai Yadikko ta fahimci Kaka Nura ne ya yi abun shiyasa ta Umarci Zainab da su matsa daga inda za a iya ganinsu, mai aiki kuma aikata ta tsaya a bakin hanya su na dosowa ta sanar musu Yadikkon ba ta nan ta nuna musu inda za su saka Amarya direct.
Dan duk wata sabga ta Kaka Nura ƙoƙari kawai Yadikko ta ke yi ta ga ta yakice shi daga kanta.
Ɗagowa su ka yi kusan a tare su ka kallesu, a take Yadikko ta haɗe rai tamau! Kamar ba ta taɓa dariya ba sannan ta ɗauke dubanta daga kallon Nuratu ta maida a Mustapha ta na jira ta ji dalilansa na shigo mata da Nuratu har inda ta ke bayan ya san ba ta so.
Miƙewa Zainab ta yi ta wuce ciki dan a ƙa'idar Yadikko ko magana ta hana ta yi da Nuratun sai dai ta yi a ɓoye...
Ƙasa-ƙasa yadda Nuratu ta san Yadikko za ta ji ta ce "shegiya Zainab, ji wani gudu kamar mahaukaciya."
Sarai Yadikkon ta fahimci domin ta kunnata ne Yarinyar ta yi hakan, hatta Baba Yusufa ba ya kiran Zainab da sunanta saboda Yadikkon ba ta so kasancewar Zainab ɗin sunan Addanta ne wadda ta riƙeta kamar Uwa ta aurar da ita, dan ita mahaifiyarta ta na haifarta ta rasu...
Shiyasa sunan ya ke da matuƙar daraja a gidan sannan ba ta so a taɓa Zainab ko da wasa.......
Ta na cikin wannan nazarin ta ji muryar Nuratu da ɗan sautin da kowa zai ji ta ce "ina wuni..."
Shiruuu kawai Yadikko ta yi ta gagara magana mamaki gaba ɗaya ya hargitsa mata lissafi wai yau ita wannan ƴar ƙanƙanuwar ƴar ta ke gwadawa kissa da karuwanci....'oh, duniya ina za ki da mu??' ta furta hakan a fili ba tare da ita kanta ta san ta furta ba sannan ta ɗago ta kalli Mustapha ta ce masa "fitar mini da ƴar nan.."
Kwaɓe fuska ya yi kamar zai yi kuka sannan ya ce " ko gaisuwarta ba ki amsa ba ballanta ki ji abunda ya kawota"
A harzuƙe sosai Yadiikko ta miƙe Baki da kumfa ta na cewa"wai har yaushe ka soma ƙetare Umarni na ne? In ce dai na hana ka hatta shiga ɓangaren nasu? Ko kaima ta koya maka raina iyayen ne? Na ce ba na sonta ba na son in ganta kusa da ni da duk wani jinina amma shine za ka shigo mini da ita salon ta hargitsa mini nawa gidan nima ta kwantar da ni a gadon asibiti ko?
Ka san kuwa me ta yi mini daga shigowarta?"
Bata jira jin ta Bakinsa ba ta juya ta kalli Nuratu sannan ta ce" to ba ki isa ba, tunda na fahimci wayon manya gareki gara in gaya miki dan na san za ki fahimta! Wallahi ba ki isa ba sarai na san mai ya kawoki nan kuma ba za ki taka way forward zuwa cikin gidana ba ballantana har ki samu ki cimma manufarki, ba bu ke babu gidana babu duk wani jinina na saka almakashi na datse....."
Cikin tarar numfashinta Mustapha ya ce " haba mana dan Allah....
Yarinyar nan fa shiryuwa ta yi, in muka nuna mata kyama ta koma ruwa mu na da kamosho fa, sannan ba za ki taɓa iya raba jininki da ita ba saboda mu jinin naki ƴan uwa muke a gareta dole duk abu ɗaya ne ya yo mu....
Kamata ya yi ace kin taimaka wajen gyaruwar Nuratu tunda dai duk tsiya ta mu ce ita ba a chanjawa tuwo suna kuma hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar ba
"
Cikin ɓacin rai sosai kamar za ta mareshi Yadikko ta ce
"ba ni da haɗi da ƴar nan, kuma shima uban naka tsaf hannu ya kan ruɓe a yanke a ƴar in aka ga ya na shirin tarwatsa garkuwar jiki.."
Sannan ta runtse idunta ƙam! Ta nuna Nuratu kamar mai shirin tada aljanu ta ce "Mustapha ka fitar mini da ƴar nan daga cikin gidana na ce ko?"
Da sauri mai aikin ta shiga tsakani ta ce "Mustapha yaushe ka zama mai taurin kai ne?
Tunda ba ta so ka fitar da ita mana......"
Cikin ƙoƙarin son ganin sun fahimcesa ya ce "Gwaggo Yarinyar nan shiryuwa ta ke yi, kwaɗayin ladan da za mu samu in mu ka taru mu ka bada gudummawa wajen shiryuwar Yarinya kamar Nuratu na ke yi mana gaba ɗayanmu.
Kuma ni a ganina ko baya ga haka ma in mu ka koreta kamar mun raba zumunci ne, kuma na san duk kun san hakan babu kyau.
Sannan ta ce mini tsoro ta ke ji....."
Buɗe idanuwanta Yadikko ta yi ta sake nuna Nuratu sannan ta ce "wannan aljannar shegiyar Yarinyar ce, ta ce maka ta na jin tsoro kai kuma ka yarda? Shegiya ƴar iska Uban me ki ka yiwa ɗa na ne wai!?"
Ta ƙarashe maganar ta na kallon idanun Nuratu wadda itama ta ke kallonta ƙurr!!Farin ciki fall zuciyarta.
A fusace ta ɗaura da cewa " kalli fa kallon da take min ta na min dariya....ba fa za a taɓa samun chanji daga gareta ba dan haka ka bar kwaɗayin samun ladan abunda babu shi kwata kwata a tsarin rayuwarta dan wallahi wannan ta riga ta tafi ita da ubanta har abada ba za su taɓa shiryuwa ba wutar jahannama ce kawai za ta shirya su, shegiya tsinanniya, kissa ce ta ke maka babu wani shiryuwa da ta yi..."
Cikinn ɗaga murya Mustapha wanda ya gama ƙarewa Nuratu kallo dan ya na so ya ga dariyar da Yadikko ta ce ta na mata amma bai gani ba ya ce "ya isa haka dan Allah, ki na ta tsine mata ba gaira ba dalili sannan fisabilillahi Ina wannan ƴar ƙanƙanuwar Yarinyar ina wata kissa?? Ba na jin ma ta san me ake nufi da hakan..."
Ya lura in aka biyewa Yadikko sai ta raba zumunci sannan ta kai Babansu wuta, dan gashi ƙiri-ƙiri ko sunan Uwani yanzu Baba Yusufa ba ya ƙaunar ya ji an kira, wadda a baya ta kasance wadda ya ke tsananin so da tattali, kuma gashi ana so a haɗu a taimaka a gyara Nuratu (da ita ce sila) wadda Alhamdulillah a yanzu ta ɗauko hanya amma ta na so ta sake turata ga halaka. Ya san a yadda Nuratu ta ke in aka kyamace ta tsaff za ta koma ruwa....
Dan haka cikin son fahimtar da ita da ɓacin rai sosai kwance a kan fuskarsa ya kalleta, dan tunda ya daka mata tsawa ta ƙame ba ta sake iya cewa komai ba hakan ya bashi damar ɗaurawa daga inda ya ke so
"Ballantana har ta gwada mana, shiryuwa ce ta yi amma gashi ki na so ki sa mu kyamace ta a maida hannun agogo baya.
Kin san cewa in da ace Nuratu ba ta shiryu ta nutsu ba da ba ki isa ki dinga zaginta haka ta kyale ki ba..."
Sai kuma ya yi shiruuu dan shima sai da ya furta sai kuma ya ji maganar ta yi masa nauyi sosai.
Sai da Yadikko ta sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta kalli mai Aikinta wadda itama jikinta ya yi sanyi matuƙa ta ce "kin gani ko? Kinga somu-somun abunda barin wannan annobar a cikin gidana ka iya janyowa ko? Wai yau ni Mustapha ɗan da ko musu ba ya iya yi mini ya ke kallon cikin idanuna ya na daka mini tsawa har ya ke ce mini ban isa b...."
Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ta gagara sake cewa komai dan haka ta toshe Bakinta sannan ta juya da sauri ta yi hanyar da za ta kaita parlourn gidan.....
Shiruuu Mustapha ya yi dan a take a lokacin jikinsa ya sake yin sanyi sosai, shiyasa ko da mai aikin nasu ta bashi shawarar ya maida Nuratu ya mayar da ita ba wai dan ya yarda an fishi gaskiya ba sai dan ya ga ran Yadikkon ya ɓaci sosai.
Da ya je bai koma da wuri ba dan wajen Uwani ma ya tafi, sai da ya tabbatar Yadikko ta ɗan sauƙo tukunna ya je ya bata Haƙuri.....
Bayan sallar isha Mai Unguwa ya biyo limami su ka shigo cikin gidan su ka samu Baba Yusufa da Yadikko su ka yi musu nasiha akan yadda su ka banzatar da Uwani wadsa ta ke jinya, dan sun zuba ido sun ga ba su je ba Mustapha ne kawai ta ce ya ke zuwa dan haka su ka basu shawara kasancewar a ganinsu an zama ɗaya.
Su na zaune a yadda su ke ko gama tashi daga wajen ba su yi ba su ka fara jiyo ashar ɗin Kaka Nura kafin ya baiyyana a gabansu hannunsa riƙe da bulalar darbejiya da ya tsinko daga jikin bishiya ya na cewa "yau sai na illata Yaron nan wallahi." Bayan idanunsa sun sauƙa a kan Mustapha.
A ƙalla Mustapha ya kai shekaru goma sha takwas a wannan lokacin amma haka Kaka Nura ya shiga zuba masa darbejiya
duk wae a kan ya yi masa raashin kunya ta inda ya fatattaki Amaryarsa da ƴan kawota.....
Mustapha bai ko motsa ba sai wanda su ka zo shi da liman da mai ungwa ne da takaicin abin ya ishesa ya zo ya hankaɗe Kaka Nura ya tafi ya faɗa akan Nuratu (wadda au ka shigo tare) ita kuma ta faɗi akan glass cup ɗin da aka kawowa baƙi ruwa ta fashe hanunta sosai ta ji ciwo.
To dai kusan za a ce an kwasheta babu daɗi dan sai da Kaka Nura ya fasa duk wani abu mai kama da kwalba ko glass a parlourn TV, show glass da kayan turaren wutar ciki, da centre table da duk wani abu dai da za a iya fasawa saboda an taɓa hannun ƴarsa ta yanke by mistake, gashi da shegen ƙarfi duk yawansu su ka kasa riƙesa in aka takura shi kuma ya fara yunƙurin yankar mutum da glass ɗin...
Ko da su mai Unguwa su ka yi magana zagesu ya yi tas dan dama haushinsu ya ke ji tunda aka yanke musu kuɗin haya ya ce duk munafukai ne saboda Baba Yusufa ya na ɗan yi musu ihsani shiyasa duk in aka yi faɗa su ke bin bayansa shi kuma ake bashi rashin gaskiya.
Rikici sosai aka yi dan har sai da wasu daga cikin makwafta su ka shigo ana ta so a raba faɗan amma abu ya-ƙi-ci-ya-ƙi- cinyewa dan Baba Yusufa shima kafewa ya yi akan sai Kaka Nura ya bar masa gida abun nasa ya ishesa haka yayinda Kaka Nura ya ce bai isa ba ae Uwani ta riga ta biya kuɗi dan haka bai isa ya tashesu ba.
Da mugun kyar mutanen wajen su ka shawo kan Baba Yusufa ganin ana shirin tado wani ballin saboda su so suke yi su gyara zumucin Uwani da Yusufa da ya ke shirin tarwatsewa dan haka su ka lallaɓashi akan ya yi haƙuri ya jira zuwa ƙarshen shekarar sai su tashi ɗin, yanzu ya bari komai ya daidaitu kuma duk wata ɓarna ma da aka yi musu za su haɗa ƙarfi da ƙarfe a gyara, a bar Kaka Nura da halinsa kawai.
Da to Baba Yusufa ya bisu saboda ya na ganin darajar mutanen matuƙa, batun Amarya ne dai ya ce gaskiya ba zai yiu Uwani ta biya kuɗin ɗaki kuma a saka wata Mace a ɗakinba.
Still hakan bai sanya zuciyar Kaka Nura ta yi sanyi ba ya ƙara ɗaukar glass mai kaifi ya nufi Mustapha wai ya yi masa laifi kuma bai bashi haƙuri ba.
Garin kiciniya Yadikko ta shiga ya yanketa a hannu hakan ya sanya jikinsa ya yi sanyi dan haka ya jaa hannun Nuratu su ka fice ba tare da ya ci gaba da haukar tasa ba.
Bayan kamar awa huɗu(har ya kai Nuratu an yi mata dressing sun je sun lallaɓo Amarya, sun dawo)
Kaka Nura ya fito tsakar gida ya ware murya ya dinga maganganu ya na cewa "yekuwa jama'ar gida, ga Amarya nan ta zo in akwai wanda ya san ya isa ya fito dan ubansa."
Kasancewar mutanen sun samu sun shawo kan Baba Yusufa a daren har ya je wajen Uwani sun shirya kuma ta tabbatar masa in har aure Kaka Nura ya yi to ya bar shi kawai ba komai gara auren akan ya bi matan banza ga ƴarta a gabansa, in sun yi haƙuri ma in dai auren Kaka Nura ne da wuya ya ɗoure, dan haka ita shiryawar da su ka yi ma ya fiye mata komai ya kawar mata da duk wani baƙin ciki, dan haka batun lafiyarta ce a gabanta yanzu ba wani Kaka Nura ba.
In Allah ya sa ta warke sai ta kama wani hayan kafin kuɗin hayan da ta biya ya ƙare ta san dole Amarya za ta fita a nema mata wani dan ba biya zai iya yi ba, in ya so ita sai ta dawo ta ci gaba da zama...
Sarai ta san da kuɗinta ya yi auren amma hakan ma ba ta ce komai ba akai, a ganinta tunda ta samu ta biya kuɗin gadon dan haka ba ta tada tarzoma ba.
Shiyasa Baba Yusufa shima ya yi shiru kawai ya bar zancen ya na sake tabbatarwa kansa tabbas ba haka banza Kaka Nura ya bar Uwani ba.
Sai kusan ƙarfe ɗayan dare tukunna Kaka Nura ya haƙura ya koma ɗaki dan ko magen gidan ba ta kulashi ba haka nan ya ƙaraci neman bala'insa ya haƙura muryarsa har sai da ta disashe.
Kamar kullum yadda ya saba wannan karon ma a ɗaki ɗaya ya kwana da Nuratu da Amarya bayan sun tabbatar ta yi barci
Wanda shi kansa ya san ife-ifen da ya dinga yi ya ci ya tada maƙwafcinsa ma ba Yarinyar da ya ke tare a ɗaki ɗaya da ita ba amma saboda runtse idanu daga ganin gaskiya sai ya kawar da wannan tunaninn kawai.
Dan shi dai ba zai kai Amarya ɗakin gumama ko ya jira Nuratu ta fita daga gidan kamar yadda su ke yi da Uwani ba, a ganinsa kwana ɗaki ɗaya da ita tunda ta yi barci ba wani laifi bane ba.
Ita kuwa Amarya dama ya shanyesu tas ita da iyayenta shiyasa ba ta taɓa iya yi masa musu, wanda hakan ne ya sake faruwa a yau ɗinma ya na zuwa da ya shirga musu ƙarya da ƙarairayi game da Uwani iyayen su ka ce ta biyosu, itanma jiki na rawa ta biyoshi.
BAYAN SHEKARU SHIDA.
BULAMA ✍️
0806 402 1951
[10/22, 8:24 AM] Maimoo 3: *BAƘAR TUKUNYA…*
HUMAIRAH BULAMA
Yota
*18*
Satin Amaryar Kaka Nura biyar, ya saketa bayan ya yi sati biyu a hannun ƴan sanda, dan yayanta ɗaureshi ya yi saboda dukan da ya yi mata a ta dalilin wae sun yi faɗa da Nuratu ta daki Nuratun. An sha case kuma ya sha wahala gashi duk duniya aka rasa mai tsaya masa ballanta a taimakamasa a fiddashi sai da kyar tukunna su ka sake shi dan kansu.
A wajen Uwani Nuratu ta zauna a Asibiti bayan an tafi da shi, wanda a ɗan wannan zaman nasu sai da ta kusan kashe Uwani da takaicinta.
In a gaban mutanene rumi-rumi kamar za ta goyata amma in su biyu ne ko kallonta ba ta yi gashi halinta na rashin kunya ya soma dawowa a Uwanin. Takaicin kissar da ƴartata ta ke yi ya sanya Uwani ta ƙi warkewa gashi in ta ga maza (likitocin ko nurses) kamar ta ɗafe musu, har wasu kalar karye-karye ta ke yi na