Showing 15001 words to 18000 words out of 104242 words

Chapter 6 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16032

faruwane?.

Lokacin dasuka fara shigowa baba harya suma, Dan numfashinsa ya gagara fita, hayak'i ya sark'eshi, wutarma tafara bin kayansa shida Ammi.
Ihu mutane suka fara tareda d'aukar botikan ruwan dake tsakar gidan suka fara watsawa k'ofar falon, amma wutarnan kamar sake izata akeyi.

Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un.

Wutarnan batada niyyar mutuwa ko kad'an, wannan yasaka wasu fara Neman 'yan kwana-kwana. duk da haka kuma anata watsa ruwa, makwafta sai kawo ruwa sukeyi.



******

Jikin Amatallah ne yafara rawa, ta fashe da kuka tana fad'in Uncle babana da Ammina. Dan ALLAH ka kiramini su, inason ganinsu, Dan ALLAH kirasu........
A tsorace Uncle M.A ke kallonta, ga mamakin rawar jikin datakeyi, duk da luguden daka da k'irjinsa keyi shima bai hanashi lallashintaba, ya kalli agogon hannunsa, 7 ta wuce, ana gab dayin sallar isha'i.
Cikin sassanyar muryarsa yace, "Sorry my best, maybe sai sunyi sallar isha'i zasuzo kinji".
Kanta ta girgiza masa, cikin kuka tace, " Uncle kakirasu, inajin tsoro wlhy, sainakeji kamar wani Abu na faruwa dasu Uncle, kiramin baba to yanzun".
Baice mata komaiba ya fiddo wayarsa ya kira number baba, kusan kira 4 bai d'agaba. alamun tsorone suka fara bayyana a face d'insa shima, shikansa jiyake kamar akwai abinda ke faruwar.
Zumbur yamik'e yana fad'in "kinga ina zuwa......
Ruk'o rigarsa tayi, "please uncle mutafi tare, Nima zan bika, bazan iya zamaba wlhy inajin tsoro".
" haba daughter, kiyi hak'uri naje, kinga bakida lafiya, insha ALLAH yanzunnan zamu dawo tare dasu"....
Kanta ta girgiza musa alamar bata yardaba.
Ya d'anyi shiru kafin yakuma fad'in "to bara naga likitanki nadawo, saimu tafi".
Yanzu batayi musuba ta sakesa.
Fita yayi kamar zaije wajen doctor d'in, yana fita wajen motarsa yaje, yashiga da sauri yabar asibitin.

Kusan atare Uncle M.A ya iso da 'yan kwana-kwana. jikinsane yafara rawa saboda hango dandazon jama'a a k'ofar gidan brother d'insa, ga jiniyar motar 'yan kwana-kwana a bayansa, fitowa yayi da sauri yana bin hayak'in dake turnik'e da saman gidan. Zufa kawai yaji tafara ketoma jikinsa. Ya kutsa cikin mutane shima yana k'ok'arin shiga cikin gidan.
Sai dai hakan ya gagara, saboda zafin wutar dukya gauraye matsakaicin gidan, mutanen dasuke a cikima duksun fito.
Jirine ya kwashi Uncle M.A lokacinda kunnuwansa suka jiyo masa furicin wani mutum na fad'in ai Alhaji Isma'il d'in da matarsa suna ciki, wani saurayine akaga yafito daga gidan da..........
Baiji k'arshen zancenba ya sulale awajen yafad'i a sume................✍🏻




Masoya kumin afuwa😭🙏🏻nakasa cigaba da rubutun saboda kuka, wlhy kuma da gaske nake😭










*Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_Kina inane *Ummu Basheer!?* maza ki matso kusa, wannan page d'in nakine ke kad'ai, kiyi yadda kikeso dashi dear, ki tabbata kina can k'asan zuciyar bilyn Abdull, ina alfahari dake, ALLAH yacigaba da jagoanci a lamarin rubutunki kema my dear, ya raya manasu Abdul🥰🤝🏻 ke d'in tadabance👍🏻._


*_Happy marriage life Ayush Ilyasu, Ubangiji ALLAH yabaku zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba, yasa alkairi da farinciki a rayuwar aurenku🙏🏻🥰🥰😊._*
_writer's d'inmu dasuka hallacci bikin suka wakilcemu ALLAH yabar zuminci😄🥰🥰._
Nina naje, Baku ganni bane kawai, INA bayan Maman bobo da sadnaf ne, Ummu abrar ta 6oyeni da hawwer😂, saura kuce k'ayya nayi😓. A tambayi hassy da Ummu Alisha ma ehe😏.




____________________
*_Number 8_*
____________________

Tun Amatallah na sauraren dawowar Uncle M.A har tafara fidda rai, kuka sosai takeyi Wanda yafara dawo da hankalin mutane kanta, sauka tayi daga gadon tafito, duk da bazata iya gane motar Uncle M.A ba hakan baihanata waige-waige ba, amma ko maikama dashi bata ganiba, harabar asibitin tafara zagayawa tana lek'a motocin mutane, a nufinta kozataga uncle d'inta.
K show yace, "yauwa Oga kaga babyn can, maybe akwai abinda take nema, kaga tama sauk'ak'a mana aikinmu, basai mun shiga cikiba".
Wata dariya zike yayi, ya lashe la66ansa yana gyara tsayuwa. Kad'an ya bigi kafad'ar k show yana fad'in " wannan ai tanada amfani kafin ta wulla itama".
Dariya shima k show d'in ya tuntsure da ita danya gane inda ogan nasa yadosa, ahankali yace, "Oga please nima ko sid'one abani inka kammala".
" hhhhh kar ka damu k show nawa".

Amatallah ta jingina da bango takuma fashewa da kuka, ta tabbata uncle wayau yamata ya gudu.
Gani tayi wasu doctors biyu da nurses sunfito da d'an gudu, motar ambulance suka shiga ta asibitin suka fice da gudu.
Tsayawa tayi da kukan tabi k'urar motar da kallo, k'irjinta sai kuma dukan uku-uku yakeyi.
Su zike dake a la6e har yanzu suna kallonta suka fito, dai-daita Kansu sukayi suka nufota, suna daf da zuwa inda take doctor Joshua yafito yana waige-waigen nemanta, danya zo zai mata allurar k'arfe 8pm ne yaga bata nan, mutanen dake wajen suke masa bayani akan tafita kusan 18munutes, shine yafito nemanta.
Can ya hangota jikin wata mota ta tsurama waje d'aya ido tana hawaye, ga wasu samari biyu Na tunkarota. kafin ya k'arasa wajen su zike sun k'arasa, k show ya saka mata handkerchief d'in hannunsa a hanci.
Da gudu doctor Joshua ya k'araso wajen yana fad'in "kai! Kai!.....
Daga k show har zike sun tsorata, sakin Amatallah sukayi a k'asa, tafad'i yaraf saboda abinda suka shak'a mata.
Jikin doctor sai rawa yakeyi, bata su zike yakeba, dan ko kallonsu bai kumayiba har suka fice. Kin kimar Amatallah yayi yakima ciki da ita.
A dai-dai nan motar Ambulance tadawo.

Innalillahi..... Kawai nake maimaitawa saboda ganin wad'anda aka fiddo daga Ambulance d'in😭.
Ammi ne da baban Ama, sai uncle M.A, wanda daka masa kallo d'aya zaka tabbatar a rikice yake,.
Har aka shiga dasu baba ciki ban iya Na motsaba daga inda nake, saboda tashin hankali.


___________________________

Su zike na fita da gudu sukaci karo da yaran gagis, wad'anda tundaga bayan gidan Mr Pam suke binsu abaya dama, amma basu saniba.
Daga k show har zike a tsorace suke kallon dabar matasan, wad'anda zuciyarsu tarigada tagama bushewa, kowanne rik'e yake da makami mai had'arin gaske.
Fitsari kawai k show yafara a wando, Dan yasan babu makawa yau d'innan suma zasu wulla inda suke wulla wasu.
Babu 6ata lokaci yaran gagis suka far musu kawai, a cikin mintuna dabazasu wuce 20 ba suka zama labari, tuni yaran gagis suka watse a wajen, sukabar gawar zike da k show kwance jina-jina.


*******

Ramzaki kam daya kunnama su Baban Ama wuta da k'yar ya tsira shima daga farmakin matasan anguwar su Amatallah, ALLAH yabashi sa'ar fad'awa d'akin wasu matasa 'yan k'abilarsu.
Tambayarsa suka shigayi miya farune?.
Ramzaki ya tak'ark'are ya mako k'arya, wai wasune zasu kasheshi saboda sun zagi yarensu ya rama.
Tuni matasan suka mik'e suna hura hanci, kafin kace me sunshiga zaro makamai kala-kala a k'ark'ashin katifar d'akin. Wani ramine a k'asan katifar, shak'e yake da makamai kala-kala.
Dad'ine yakama Ramzaki, shima yakar6i biyu suka fice........ 🙆🏻‍♀😨


*********

Koda yaran gagis suka bar bakin asibiti sai suka nufi gidan uncle d'in zike, Dan sunyi alk'awarin k'arar da dukkan ahalinsa.
Babu maganar Neman ba'asi ko dalili suka haikema Mr Marcel Wanda baijiba bai ganiba da iyalansa, hasalima kullum cikin yima zike fad'a yake a kan rayuwar daya saka kanshi. yakashe kud'i babu adadi akan yayi karatu amma zike yay watsi da maganarsa, sai gashi yau ta sanadinsa anzo har cikin gida an kasheshi shida matarsa da yaransa biyu😭.


____________________________

A asibiti kam lamarin ba'a cewa komai, ALLAH yayima Ammi rasuwa😭.
Tunkafin wuta dama tarasu ita, saboda wuk'ar da Ramzaki ya soka mata sau biyu. Baba ma dai lamarin sai addu'a, danba k'aramar k'onewa yayiba, likitoci kusan hud'une a kansa.
Uncle M.A yakasa zaune yakasa tsaye, jiyake tamkar zuciyarsa zata fito waje daboda tashin hankali, yana tsaye a k'ofar d'akin da'aka shigadasu baba shida wasu makwaftan Baban Ama d'in, sai kaikawo sukeyi, da jimamin lamarin, abin tamkar wani film.




*_washe gari_*

A washe gari saiga k'aramar magana tazama babba, domin kuwa ba k'aramar 6arna su Ramzaki sukayi a anguwar su Amatallah ba.
6angaren yaran gagis ma saita kwa6e, dan kisan su Mr Marcel yayan zike tasaka danginsu maida murtani, kafin k'arfe 2pm komai ya cakud'e, sallar azuhur ma tagagari jama'a, sai a gida aka yita.🙆🏻‍♀


_____________________________

Hankalin Uncle M.A yayi masifar tashi, gani yayi inhar yabari suka kai dare a jos to tabbas dagashi har Amatallah d'inma bawai tsira zasuyiba, musamman yanda yaga ana kawo masu raunika asibitin, wasuma sun rasu. abinda kuma yak'ara tada hankalinsa shine bayanin likita akan jiya wasu sunzo sace Amatallah. har zuwa yanzu abunda suka shak'a mata baima saketaba.
Da sauri yamik'e ganin su doctor Joshua sunfito daga d'akin da baba ke kwance, har yanzu an hana kowa ganinsu.

"Doctor yaya?".

Numfashi doctor Joshua ya sauke, tareda fad'in lamarin babu sauk'i Alhaji, zafin wutar hayak'inta yayi mugun ilata lafiyar Alhaji Isma'il gaskiya, amma muna kan aikinmu, zakuma muyi iya k'ok'arinmu akansa".
Uncle M.A ya jin jina kansa, muryarsa na rawa yace, ''matarfa?".
Shiru doctor Joshua yayi, saikuma yad'anyi murmushi, da sauri yace, " itama dai hakan". bai jira cewar Uncle ba yay saurin barin gurin.
Cikin sauri Uncle M.A yabi bayansa yana kiran "doctor!".
Harya kama handle d'in k'ofar office d'insa zai shiga ya dakata, saurin maida kwallan sa yayi, haka kawai yaji yana tausayin Amatallah da wannan mutumin dabaisan dangan takarsa da iyayen Amatallah d'inba.
Uncle M.A daya k'araso yace, ''please doctor inason muyi magana inhar bazan shiga aikinkaba".
"Babu damuwa Alhaji, zaka iya shigowa". 'Yay maganar yana shiga office'.
Bayansa Uncle M.A yabi.
Bayan sun zauna Uncle M.A yace, " doctor inason tafiya dasu Kano gaba d'aya, kaga garinnan kuma harmutsewa yakeyi, dukda bamuna fatan damuwar da'ake ciki tawuce hakanba, amma sunada buk'atar kulawar gaggawa suda Amatallah, please doctor ka taimakeni".
Cikin tausayawa doctor Joshua yake kallonsa, ya gyara zamansa yana jinjina kai, "nabaka goyon baya d'ari bisa d'ari Alhaji, nima ina ganin hakan shine mafita. yanzuna nan zan shirya muku tafiya kawai".
Sosai Uncle M.A yaji dad'i, sai godiya yakema doctor.

Babu 6ata lokaci komai yagama kammala, aka kai su Ammi cikin Ambulance, dukda itad'in ta rasu, amma doctor Joshua yakasa fad'ama Uncle M.A d'in.
Amatallah kan a motar Uncle M.A aka sakata, haka sukatafi zuciyar uncle cikeda rauni, lokaci-lokaci yakan juya ya kalli Amatallah dake kwance a baya tamkar gawa....



*************

Tafiyar Awa 3½ ce ta kaisu garin Kano, kai tsaye asibitin Aminu Kano suka wuce.
A cikin gaggawa kuwa aka kar6esu, saboda ansan da zuwansu, tunkan subaro jos Uncle M.A yakira doctor Shu'aibu ya sanar masa zuwansu. Wannan yasaka suka Tatar da komai a ready, su kad'ai ake jira.
Amatallah ma anbata gado, Dan har zuwa yanzun batasan ina kanta yakeba.
Sai da Uncle M.A yaga komai ya dai-daita sannan yatafi gidansu danya sanarma iyayensa.
Yana shirin shiga mota doctor shu'aibu yafito da sauri yana nemansa. hangosa dayayi yana shirin shiga mota yasashi fara kwala masa kira.
"Alhaji Muhammad! Alhaji Muhammad!!".
Harya saka k'afarsa d'aya ya fito, ganin doctor shu'aibu Na tunkaroshi da sauri sai gabansa yashiga fad'uwa.
Doctor shu'aibu yak'araso, "sorry Alhaji Muhammad Labbo! na tsaidaka, so dama.......
Sai kuma yay shiru.
"Ina jinka doctor, mike faruwane?".
Tsayuwa doctor ya gyara, sannan cikin damuwa yace, " sorry Alhaji Muhammad, ko kasan macen tarasu?, kamarma tun kusan a wanni 22 dasuka wuce".
A sanyaye Uncle M.A ke kallon doctor shu'aibu, ya dafe kansa dayaji yafara sara masa.
Hak'uri doctor yafara bashi, tareda lallashi da masa Nasiha.
Uncle M.A baice komaiba yashiga motar, kansa ya kifa a sitiyarin motar yafara hawaye. Kusan mintuna 7 sannan yad'ago, motar ya tada yabar asibitin.

______________________________

Tunda yashigo gidan Innani dake tsakar gida tana alwalar magriba kebinsa da kallo.
Jingina yayi da bango, batareda ya saniba hawaye suka fara bin kumatunsa.
Da sauri Innani ta k'arasa alwalar, "kai lafiyarka kuwa? Da girmanka kake kuka? Miya faru, yaushe kadawo ma?".
Yanda Ammi ta jero masa tambayoyin saiya samu kansa dakuma fashewa da kukan.
Shiru Ammi tayi tana kallonsa, jikinta sai rawa yakeyi.
Cikin d'an daka tsawa tace, " wai baka jinane?".
Share hawensa yayi, sannan yashiga bata labari.
Innalillahi ...... Kawai Innani ke iya ambata.
Baba na daga d'aki duk yanajinsu, saidai baya iya fitowa sai an fiddoshi, maganar Uncle M.A bak'aramin girgizashi tayiba kuwa.
Ana cikin haka saiga Jabeer yashigo shima, nan suka had'u sunata jimamin abin, jabeer ma harda kukansa rurus.
Bayan Uncle M.A yashiga sun gaisa da baba, shima yak'ara masa bayani sannan yatafi gidansa danya d'an kimtsa sannan yakoma kar Amatallah ta farfad'o babu kowa a kusa............✍🏻




_Dan ALLAH ina rok'onku Ku ringa turama masu cigiya, saboda ALLAH banida time d'in turama kowa ta PC, amin afuwa saboda uzurina, hakanne zaisa nasan kuna k'aunata😄🥰🥰🥰._




One luv my fans👍🏻





*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu😭🙏🏻_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_Duk naga comments naku, kuma sun k'ayatar dani gaskiga.🥰🥰sai dai wani Abu yasakani dariya matuk'a, kunsan minene?. Masu cewa Uncle M.A yama Amatallah tsufa😂._*
*_Wai miyasa abinda zai iya kasancewa gaske Reader's ba kuson ganinshi a Novel's? Abinda na sani kuka sanine, ko a zahiri mai shekarun uncle M.A ba tsoho baneba, kisamu wani a anguwarku mai d'iyar dazata iya kaiwa 18years, tazam kuma itace d'iyarsa ta Fari ki k'iyasta dashi, ko Wanda yakai shekara 60 yana auren budurwa ai, balle 47years, kuma ko a cikinmu a kwai wad'anda mazajensu suka kai wad'an nan shekarun, my Abdull ma shekarunsa kenan🤣😜._*
_mu rubuta abinda azahiri zai iya zama gaske kuce bai daceba, muyi Wanda mu da Ku kunsan bazai yiwuba Ku zagemu kuce muncika k'arya ko🤣._
_koma Yaya dai ALLAH yabar zuminci, Dan mu daku duk munacin amfanin junane, inba mai karatu babu abinda zaisa Marubuci 6ata lokacinsa, hakama inba Marubuci mai karatu bazai samuba littafinba, mun gode sosai, irin Trillion's d'innan🤝🏻🥰🥰😘._




____________________
*_Number 10_*
____________________

An gudanar da zana'idar iyayen Amatallah a gidan mahaifan Uncle M.A, Innani tasha kuka lokacinda taga gawar Isma'il da matarsa a shinfid'e, lallai duniya batada tabbas ko kad'an.😭
Wandama ya d'aura d'ammara da ita saiya kwance.
Babama yashiga rud'ani sosai, dan sai da ciwonsa yayi tamkar zai motsa, sai allurar barci akai masa.
Har aka binne su Uncle M.A na kuka, koda suka dawo daga mak'abarta d'akin Jabeer yashige ya kwanta, kuka yake tamkar ransa zai fita.
Dolene ka gansa kaji tausayinsa. shima dai daga k'arshe dole allurar barcin Jabeer yasaka akai masa.


*_Two days later_*

Alhmdllh yau kwanakinsu Baban Ama biyu a k'asa, amma Ammi kwananta uku da rasuwa.
Duk da 'Yar Nutsuwa tazoma su Uncle M.A hakan bai hanashi warewa gefe yasha kukaba wani lokacin, musamman inyaje asibiti duba Amatallah da Nazeefa ke zaune da ita, dawata k'anwar Innani, gwaggo Rakiya.
Har yanzu Amatallah bata farfad'iba, dan doguwar suma tayi, amma tana samun kulawa daga likitoci sosai.


_______________________________

*_Jos_*

A jos kam lamari yayi k'amari, k'ank'anin Abu yajawo mutuwar d'aruruwan al'umma da asarar dukiyoyi, abinda yafaru akan SIYASA dalilin wasu marasa jin magana ya rikid'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login