Showing 18001 words to 21000 words out of 104242 words

Chapter 7 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16036

yazama fad'an k'abilanci da addini.
'Yan jaridu da kafafan yad'a labarai na social media sai baza rahotannin k'arya sukeyi, anrasa jin jinar magana akan dalilin wannan rikici na *SIYASA KO K'ABILANCI!?*.
A dalilin hakan kuma wasu gur6atattun matasa masu ruguza zaman lafiya suka kuma tada rikici a KADUNA, ik'irari sukeyi wai ankashe 'yan uwansu dake jihar Jos, dolene suma su d'auki fansa.
Ba'awani ja danisaba Kano ta d'auka, babu gaira babu sabar nanma wasu bara gurbin matasan suka haikema wasu k'abilu dake killace awata anguwa da ik'irarin d'aukar fansar abinda akaima 'ya uwansu a Kaduna da jos.
Abinda yafaru a kano yabama k'abilun kudancin k'asar suma tada tasu husumar, suka fara kisan 'yan arewacin k'asar a nufin d'aukar fansaπŸ˜¨πŸ™†πŸ»β€β™€.


_hum wane irin tunanine da matasan k'asarmune? Mike shiga kanmune? Muke za6ama kammu da k'asarmu irin wannan rayuwar? Wace riba mukeci ko nasara idan mun girmama irin wannan rikice-rikicen dabumuma San tushensuba, karfa Ku manta idan ta rikice da kai da ni duk bazamu shaba, ahalinka da nawa babu Wanda zai tsira, dukiyar k'asarmu zata ruguje, karatunka danawa Dana 'ya'yanmu duk zai zama labari, watak'ilma kaida kazama jagoran fad'ad'a tashin hankalin kaine zaka fara mutuwa ko ahalinka, Ku kalli gagis, zike, k show, dasu aka fara, an tarwatsa ahalinsu da basujiba basu ganiba, Amatallah dabatasan tushen rikicinba an rabata da iyayenta, an tarwatsa mata family saboda son zuciya irinna gur6atattun matasanmu, wad'anda mugun tunaninsu bayasa mu d'aukesu a jerin masu amfani da amfanar da k'asarmu, basuda buri saina haddasa rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI!?* Saboda son zuciyarsu, kullum zuciyarsu na karanta musu AMUTU KO AYI RAI ba damuwarsu baceba, da ance an kad'a tambarin SIYASA saikaga jikkunan matasan k'asarmu na rawar Mazarin shirye-shiryen duk yanda takama, basuda zuciyar k'yak'yk'awan fata wa k'asarsu ko nagartar ginata ta hanyar zarran mazatankar samartaka na k'uruciya da ALLAH yabasu. miye ribarka idan an siyeka dawasu 'yan kud'ad'e dankayi jagoranci wajen hallaka ahalinka da k'asarka? Wadda bakada kamarta, bakada Inda yafita, duk Inda zakaje saikazama abin tsangwama da gudu , watak'ilma akiraka d'an ta'adda mai lasisi, bakada damar shan ruwan wata k'asa cikin salama tunda ba k'asarka baceba._
Yanzu haka wad'anda suka baka kud'in duk 'ya'yensu basa k'asarma, sannan su sunada tsaronda babu wani mahalukin daya Isa ya tunkari gefen anguwanninsu ballema yasamu ganin su, amma kai anbaka kud'in siyen ahalinka batareda kayi dogon tunaninaba, basuda Matsala da watsewa ko tarwatsewar k'asar, dan sunada isassun kud'ad'e a ciki da wajen k'asar, sunada lasisin zuwa kowacce k'asa su warwasa batareda an tsangwamesu ba kamarkai daza'a kafama tantin d'akunan tamfol ko buhu ko katako a filin ALLAH ana kiranku da suma *'YAN GUDUN HIJIRA*😭.
Abincinma dazakaci ko ruwa saiya gagareka, ballantana maganar lafiyarka ko akasinta.
Haba matasanmu, kudawo cikin hankalinkufa, kubar yadda da 'yan jari hujja masu amfani daku wajen amfanuwarsu suna haddasa fad'ace-fad'acen addini ko SIYASA da K'ABILANCI ta sanadinku, ni da ku damuke a arewaci da kudanci duk munada ikon canja mummuna zuwa k'yak'yk'yawa, duk Wanda kagani Asama mune muka kaishi, kuma munada ikon ingizoshi k'asa ayayinda muka fuskanci d'an wawasone akan abinda yake mallakinmu, da wahalhalinmu suke tak'ama da baza riguna da cin zarafinmu suna zare idanu, to muma saimu gyara domun gyaro abinda ke cin dunduniyarmu, mukiyayi saidai RAYUWARMU akan rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da wasu tsiraru ke jagorancin haddasa mana domin cimma wani burinsu akanmu, sai matasanmu sunyi gyaran halayensu sannan madafun iko da ragamar k'asarmu zata iya dawowa hannunsuπŸ‘πŸ».
Wannan k'alubalen nakune matasanmuπŸ’ͺ🏻πŸ’ͺ🏻πŸ’ͺ🏻.
Amma ta sanadin zaman lafiya a k'asarmu da muhimmin sanin darajar kawunanku, kuyi fatali da duk wani banbancin addini ko k'abila kuzo mu rungumi juna domin kawo sauyi wajen tankad'e da rairayar duk wasu masu rusamu ta k'ark'ashin k'asa, karike na rike ki rike mu rike hannun juna domin maida matasanmu jagorori akan madafun ikonmuπŸ’ͺ🏻πŸ’ͺπŸ»πŸ˜„. Ta hanyar zaman lafiya da k'aunar junanmu cikin zarrar amsa suna 'yan *NIGERIA* k'asa d'aya, uwa d'aya uba d'aya.πŸ‡³πŸ‡¬
Karmu bari mu ruguje daga ansa sunanmu na 'yan k'asa d'aya dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*πŸ™πŸ»πŸ˜’
Ko shed'ancin wasu jagorori masu nemawa Kansu mutunci kawaiπŸ‘ˆπŸ».


a wannan ga6ar dolene masu karatu susojin dangan takar dake tsakanin Alhaji Isma'il Uba da Alhaji Muhammad.πŸ€”
Kubiyo bilyn Abdul domin jin tushen labarin.πŸ˜ŠπŸ‘ŽπŸ»


____________________________

Alhaji Muhammad Ahmad Labbo, shine cikakken sunan Uncle M.A.
'Dane na farko daga Alhaji Ahmad Labbo.
Alhaji Ahmad Labbo cikakken basakwace ne d'an kasuwa, kasuwancine yakawoshi garin Kano, a da yakanzo ya sari atanfofi yakoma sokoto, sai dai daga lokacin da tafiya tafara nisa saiya dawo garin na Kano baki d'aya, yasamu shago a kasuwar kwari.
A nan Kano ALLAH yahad'ashi da matar aure Zainab (innani).
Shekararsu 1 da aure ALLAH ya albarkacesu da haihuwar d'a namiji, Wanda yaci sunan Muhammad (Uncle M.A kenan). bayan Muhammad innani tasake Maijiddah, sai Barirah, (amma ALLAH yay mata rasuwa), sai Jabeer,, Shehu, Nazeefa auta.
Gwargwadon iko 'ya'yansu sunsami tarbiyya, sannan sun tsaya tsayin daka domin ganin sun sami ilimin addini dana zamani.

Muhammad yarone dayataso k'ark'ashin kulawar mahaifi, dan innani tana kawaici sosai alamarinsa irinna 'ya'yan Fari, bata fad'ar sunansa, sannan kuma bakomaine take sakashi acikiba
Amma a k'asan zuciyarta tana matuk'ar k'aunarsa fiyema da sauran 'ya'yanta.
Bayan kammala primary d'in Muhammad yadage akan boarding yakeson zuwa, babu yanda iyayensa suka iya suka shiga cuku-cukun kaishi Government secondary school Bichi.
A canne ALLAH ya had'ashi da Isma'il Uba Salisu, Wanda rana d'aya aka kaisu makarantar, shi an kawoshine daga Kusada local government dake jihar Katsina. tun daga wannan ranar suka k'ulla alak'ar abota mai k'arfi, suna kiran junansu brothers.
Kowa a makarantar ya d'auka 'yan uwan junane makusanta saboda k'auna da tattali dasuke nunama juna.
Ko kad'an Muhammad baya k'aunar yaga anta6a Isma'il, haka shima Isma'il d'in, idan aka kama d'aya da laifi, akazo hukuntasa sai d'ayan yay tsale yace shine, dan bayaso ata6a lafiyar d'an uwansa. idan kuwa d'aya bashida lafiya ai saika d'auka dukansune suke jiya. gaskiya akwai k'auna mai k'arfi a tsakaninsu mai kuma ban mamaki.
Kafin kace mi duk families nasu sunsan da wannan k'auna tasu. har yazam Isma'il kanzo Kano Hutu gidansu Muhammad, haka shima Muhammad kanje jos ko kusada hutu........


Isma'il Uba salisu shine cikakken sunan Baban Ama, d'an asalin jihar jos ne, Dan anan yataso yaga iyayensa,
Su biyu iyayensu suka Haifa, Amina itace babba, sai Isma'il. tun suna k'ananu mahaifiyarsu ta rasu, babansu wanda suke kira da kawu yak'ara auren wata makirar mace mai suna Huzaiyya, takan nuna k'aunarta a garesu agaban mahaifinsu, amma dazarar bayanan tashiga gallaza musu kenan, makircinta yahana kawu fahimtar komai akansu. ana haka ALLAH ya fiddoma da Amina miji, amma fatauci yake zuwa jos shi d'an katsina ne a kusada L.G. wannan yasa koda akai aurenta sai aka kaita Kusada.
Tunda Amina tayi aure sai Isma'il yakuma shiga uk'ubar huzayya, wannan yasakashi tada hankalinsa akan shi akaisa wajen 'yar uwarsa Amina. Mahaifinsu bai fahimci komaiba, shi duk tunaninsa Isma'il na kewar Amina ne. Haka ya d'akko Isma'il da kansa yakawoma Amina danufin yayi hutu. Sai dai koda hutun Isma'il ya k'are saiya dage akan bazai komaba, kawu yay lalla6ar duniya Isma'il yace bai komawa. haka dole kawu yabar Isma'il awajen Amina.
Mijin Amina ne ya nemawa Isma'il makarantar boarding ta Bichi danya cigaba da karatunsa, tunda yagama primary a jos.
Daga wannan lokacinne kuma suka had'u da Muhammad labbo, Wanda yazame masa d'an uwa kuma aboki.
Idan anyi Hutu Isma'il yakan fara zuwa kusada ne yay kwana biyu sannan ya wuce jos. Wani lokacin kuma a kano yakeyi gidansu Muhammad, a wani karon kuma su wuce jos shida muhammad d'in suyi acan bayan sunje kano, kokuma kowa yatafi gida, sai bayan kwanki kamar uku zuwa hud'u saiya tafi gidansu d'an uwansa hutun. har lokacin kuma Amina bata haihuba.

Ahaka suka kammala karatunsu Na secondary, sun rabu cikin damuwa sosai alokacin, Dan kokad'an basuyi murna da graduate d'in nasuba.
Kwanaki bakwai kacal dayin candy d'insu Muhammad yakasa hak'uri yashirya sai jos, sosai Isma'il yay farin cikin ganinsa, hakama kawu.
Har zuwa yanzu huzayya tananan da makircinta, amma zuwa yanzu Isma'il baya d'aukar raininta.
Haka suka maida Kansu kulum cikin yawo daga Kano zuwa jos, har results d'insu ya fito, suduka sunsami abinda suke buk'ata, wannane yasakasu farinciki.
Babu 6ata lokaci kuma aka shiga nema musu makaranta, cikin amincin ALLAH kawu mahaifin Isma'il yay nasarar sama musu a University ta jos.
Wannan ne dalilin dawowar Muhammad jos da zama, sai lokaci-lokaci yakanje Kano.
Sun fara University babu dad'ewa ALLAH yayma Amina yayar Isma'il rasuwa, sosai rasuwar ta girgiza Isma'il da kawu, hakama Muhammad danya santa sosai.

Rayuwar samartakar Isma'il da Muhammad abin sha'awace, dan zaratan samarine masu kulada addini da kare Kansu wajen rud'in zamani da samarinmu ke jefa Kansu. Sun maida hankali sosai akan karatunsu, kuma suna samun nasara sosai.
Suna a level two ALLAH yahad'asu da Khadija, yarinya nutsatstsiya itama, tunda Isma'il yaga Khadija yafara k'aunarta, sai dai ya 6oye abin a zuciyarsa da burin saisun kammala karatunsu ya furta mata.
Sai dai kash Ashe shima Muhammad ya kamu batareda sanin Isma'il ba, shikam yakasa rik'e hakan a ransa ya furtama amininsa Isma'il.
Hankalin Isma'il yatashi sosai, saboda k'aunar Khadija yakeyi sosai, amma haka yayta jarumtar dannewa, yabama brother d'insa kwarin gwiwwa da goyon baya 100%, shinema da kansa ya sanarma Khadija soyayyar da brother d'insa kemata. batawani basu wahalaba ta amince, dandanan soyayya mai k'arfi tashiga tsakanin Muhammad da Khadija. Isma'il kuma yanata yak'in cireta a ransa, dan har k'asan zuciyarsa yagama aminta yabarma d'an uwansa Muhammad ita.
Kullum Muhammad kan takura Isma'il akan yakamata shima yayi budurwa, yanda dasun kammala karatu sai ayi bikinsu tare.
Dariya kawai Isma'il keyi yace katayani nema brother, nifa har yanzu ban k'yalloba.

Suna gab da kammala karatunsu saiga Saliha shima ALLAH yabashi.
Muhammad yayi murna sosai, yakuma k'arfafa d'an uwansa.
Alk'awalin ALLAH ya cika, su Muhammad sun kammala karatunsu, nanma ansha tata 6urza akan komawar Muhammad kano.
Koda Muhammad yakoma gida sai mahaifinsa yajawosa suka cigaba da zuwa kasuwa, ahankali Muhammad ya dilmiya a harkar, ya kware sosai tareda kawo canje-canje masu yawan gaske a kasuwancin mahaifin nasa, kasancewar shi d'an zamanine kuma mai ilimi.
Shikam Isma'il yana jos babu abinda yakeyi, lokaci-lokaci dai yakanzo kano, yayi kwanaki ya koma abinsa.
A wannan tsakanin auren Isma'il yatashi, ALLAH bai cika musu burinsu nayin aure rana d'ayaba, dan Isma'il ne yafara angwancewa. batun yanda shagali ya kasance 6ata lokacine ma aii.πŸ˜„
Bayan auren Isma'il Muhammad yakawo musu shawarar sukoma suyi masters nasu, (degree na biyu), 100% Isma'il ya aminta da batun. dan haka suka fara nema a University of Lagos (Lagoon), nanma sunyi nasarar samu kuwa, dan haka suka fara karatunsu cikin nasara. A lokacin Saliha matar Isma'il nada ciki.
Rashin auren Muhammad yafara damun Isma'il, dan haka yafara takura masa akan maganar Khadija.
Amsar daya saba bashice yakuma maimaita masa, akan yana jiran Khadija ne kamar yanda iyayenta sukace saita kammala karatu ta.
"Haba brother, kaikuma saika zauna saita kammala d'in?".
Dariya Muhammad yayi, yadafa kafad'ar Isma'il yana fad'in " cool dawn mana my brother, duka kwana nawane yarage? Insha ALLAH baifi watanni 7 bafa kaima kasani".
"Haka kullum kake fad'a, amma har yau ni banga wata bakwai d'in zata k'areba, kuma mizai hana kaima baba magana a tsaida rana tun yanzu, bayan ta kammala sai musha biki kawai".
Shiru Muhammad yayi yana nazarin maganarsa, zuwa can kuma yace, " gaskiyarka fa brother, kaima kazo da shawara".
Babu 6ata lokaci sukayi amfani da shawarar Isma'il aka kai kud'i aka tsaida rana, sai ta kammala karatunta.

Watanni bakwai na cika kuwa akasha biki, lokacin Saliha ta haihu d'an baizo da raiba.
Wattani shida tsakani saliha yakuma samun wani cikin, amma Khadija dai babu labari.
Watanni tara cif Saliha ta haifi d'iyarta mace k'yak'yk'yawa.
Muhammad yayi matuk'ar farin ciki, tamkar shi aka haifamawa, komai kuwa Na hidimar sunan baby Muhammad ne yayishi, hatta da suna ma shine yarad'a mata Khadija, sunan mahaifiyar Isma'il, kuma matarsa.
Tun daga wannan lokacin Muhammad yad'auki son duniya ya azama Khadija dasuke kirada (Amatallah), komai yagani Na yara saiya siya matashi, kullun firarsa akan best daughter d'in sace.
A haka suka kammala degree d'insu Na biyu daga lagos suka dawo gida, Isma'il jos, Muhammad kano.
Muhammad yacigaba da kulada kasuwancin baba, kuma har zuwa lokacin ko 6atan wata Khadija batayiba, duk k'arshen wata Isma'il kan d'akko iyalansa suzo kano, kokuma shi Muhammad yaje danasa iyalan.................✍🏻




Kubini bashi a page 11 pleaseπŸ™πŸ»πŸ˜„





*_ALLAH ka gafartama iyayenmuπŸ˜­πŸ™πŸ»_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*πŸ’‘
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_Ku gargad'i mai gina ramin mugunta!! πŸ“»_*πŸ˜₯πŸ‘ˆπŸ»
Wannan gaskiyane
*Doctor Alhaji mamman (shata)*
ALLAH ya gafarta makaπŸ™πŸ»



____________________
*_Number 9_*
____________________


A k'ofar gida yay parking motar sa, sannan ya kama k'ofar zai bud'e, a rufe take.
Shiru yayi yana kallon k'ofar, yasan tunda baya nan bazasu ringa barin k'ofar a bud'eba. Mota ya koma ya d'akko wayarsa. Aneesa yakira.
A yangance tamasa sallama.
Shikuma ya amsa murya na rawa.
Gabantane yafad'i, tacire wayar daga kunnenta ta kuma kallon screen d'in domin tabbatarwar shine kokuwa?. ganin shid'inne yasata maidawa a kunnen.
"My dear! Lafiya kuwa?".
Ajiyar zuciya ya sauke, a raunane yace, " kizo ina k'ofar gida......
Bata jira yakai k'arsheba tafito da sauri. K'aramar k'ofar gate d'in ta bud'e ta lek'a.
A tsaye ta gansa ya jingina da jikin gate, gabanta yakuma fad'uwa, hakan ya kuma tabbatar mata babu lafiya.
Takowa yayi ahankali yashiga gidan, ta kalleshi tana fad'in "dear motarfa".
Kansa ya girgiza mata yace, " fita zan kumayi". yana maganar yana tafiya.
Wannan yasata binsa da sauri itama. babu kowa a falon k'asa, dan haka ya haye samansa, Aneesa na binsa abaya.
A kan gadonsa ya zube yana sauke numfashi, Aneesa ta zauna kusadashi tana tambayarsa miyafaru cikin damuwa.
Bai bata amsaba, sai dai cewa yayi ''had'amin ruwan wanka".
Jiki a sanyaye tamik'e zuwa bathroom d'insa, ruwa mai d'an zafi ta had'a masa, tana niyyar fitowa shikuma yashigo, matsawa tayi yashiga sannan ta fita.
Yana wanka yana hawaye, lallai duniya abar tsoroce, jiya iyanzu yana tareda amininsa, amma yanzu gashi awani hali mai rikitarwa, ALLAH sarki Saliha, ALLAH ya gafarta miki😭.

Aneesa kam da sauri ta sauka k'asa zuwa 6angaren uwargidanta.
A falo ta iskesu itada yara suna homeworks d'in makaranta.
Yanda tashigo a rikice yasaka Umman abulkhair saurin kallonta, "lafiya kuwa momyn yara?".
" inafa lafiya ummansu.........nanda ta sanar mata abinda ta Sani gameda canjawar mai gidan nasu, da dawowar babu zato babu tsammani da yay musu, alhalin gobene yakamata yadawo.
Atare suka fito zuwa d'akinsa.
Bai fitoba, dan haka suka zauna zaman jiransa. Babu dad'ewa yafito, sannu da zuwa Fateema tamasa.
Batareda ya kallesuba ya amsa yana k'ok'arin shinfid'a abin sallah. Sallar magriba ya gabatar, sannan yay isha'i, duk suna zaune suna kallonsa.
Yay addu'a yana share kwallar dake bin kumatunsa.
Sosai jikin matan nasa yakuma yin sanyi k'alau, sun k'agara ya idar suji mike damunsa.
Ganin yanda suka damu matuk'a yaga baidace yabarsu a duhuba, cikin dauriyar danne hawayensa yaymusu bayani.
Daga Aneesa har Fateema kuka suke sosai.
Mukullin mota da wayarsa kawai ya d'auka yafita zuwa asibitin, yabarsu Aneesa nacigaba da kukansu.
A motama yana driven yana hawaya, yakasa jarumtar danna kukansa, tausayin Amatallah da abokinsa kawai ke nuk'urk'usar ruhinsa. a haka ya Isa asibitin.
Jabeer da kawunsu Malam Yakubu ya tarar suna jiran isowarsa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login