Showing 69001 words to 72000 words out of 104242 words

Chapter 24 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16054

kwana, tasha kunya kamar jiya, koma nace fiye da jiya, Dan yaukam Uncle kasa barinta yayi harda 'yan wasanni, Wanda ganin ta tsorata yak'yaleta daga baya sukasha barcinsu, dukda yarigata barci ita tsorone ya yanata saida taji yayi.



*_5days ogo_*.

Kwanakin Amatallah 6 kenan da kar6ar miji, a kwana shidannan ba'a maganar shak'uwarsu, dan koyaya dai tasaki jiki dashi, dama kuma hakan shine fatan Uncle d'in. gashi kuma gobe Fateema uwargida zata kar6eshi ko Aneesa, duk kuma sai Amatallah taji babu dad'i, koba komai tasaba da kwanciyar dasukeyi tare a gado d'aya.
Da daddare suna kwance, barci sukeyi hankali kwance, Amatallah Na jikin Uncle ta dabaibayeshi kamar zata shige jikinsa. bugun k'ofane ya farkar da Uncle, ga Amatallah kam hakan bamai sauk'i baneba, saboda shegen nauyin barcinta.
Da k'yar yazame Amatallah a jikinsa yatashi gabansa na fad'uwa, tabbas yasan babu lafiya, yakumafi kawo hakan ga Fateema.
Ilai kuwa yana bud'ewa yaci karo da Aneesa wadda take a rikice, sai yarfa hannaye take tana safa da marwa.
Yana bud'e k'ofar tayo kansa, " dear Umman yarace babu lafiya, ina k'yautata zaton ko nak'uda wlhy......"
Abinda yafaru shine tun farkon dare bayan Uncle yashiga sunyi sallama takejin babu dad'i dajin alamomin ciwo, amma harya fita bata iya fad'a masaba dankarya tashi hankalinta, saima ALLAH yakawo barci ya figeta da wuri, acikin barci ta farka da matsanancin ciwo, cikin azaba ta d'akko wayarta da nufin kiransa, saidai takira har sau biyu bai d'aukaba, hakanne yasata maida akalar kiran ga Aneesa. Arikice Aneesa tashigo wajenta, ganin nak'udace ta d'auke yaran d'ai-d'ai tamaida 6angarenta, shine taje ta tado Uncle bayan itama takirasa bai d'agaba. Shikuma ya danne wayarne da filo harta shiga silent bai saniba, wannan ne yasa bai d'aga kiransuba.
Har rige-rigen shiga 6angaren Fateema sukeyi itadashi, zuwa sannan kuma Fateema nak'uda gadan-gadan.
Aneesa tace dear mutafi asibiti mana".
"Neesa kalli agogofa, 2:41am akwai had'ari gaskiya, mudai bata taimako muga ko ALLAH zaisa mudace ta haihu lafiya".
Aneesa tayi na'am da hakan, addu'a Uncle yafara tofama Fateema a ruwa, hannunsa rik'eda d'ankwalinta yana share mata gumi. Aneesa kuma Na taimaka mata dawasu dabarun...
A wannan time d'inne kuma Amatallah tafarka arikice saboda mafarkin Anty Fateema datayi tana kuka, ta laluba babu Uncle, ai babu shiri ta wantsalo daga gadon, hijjabi kawai ta d'ora a saman kayan barci ta tafito, tundaga falo tafara jiyo nishin Fatima da maganar Aneesa tana fad'in daure Umman yara, insha ALLAH kin kusa.
Wani nishi da Fateeman tasaki yasaka Amatallah fashewa da kuka saboda tausayi, saikuma tad'an tsagaita taji kukan jariri ko murnarsu Uncle d'in da haihuwar amma saitaji tsitt, saima gauron numfashi da Uncle yasaki tareda fad'in "Fateema!!"...............✍🏻


🙆🏻mun shiga d'ari, kardai Uwargida.....🤭ba ruwana😓.




🤩👎🏻

One luv my Sweet fana🥰











*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 29_*
____________________

"A'a dear karka damu tana numfashi, nakula tagajine kawai......
Aneesa batakai k'arshen zancenba Fateema takuma yin wani nishin mai k'arfi saiga jaririya ak'asa tana watsal-watsal, atare suka furta Alhmdllh.
Amatallah ma ajiyar zuciya ta sauke, tana dariya tana kuka, Uncle yafito d'aura ruwa da Aneesa ta buk'ata ya ganta tsaye ta jingina da Bango idonta arufe, ganin tana kuka da dariya saita bashi tausayi, yajawo hannunta ya rungumeta yana fad'in ''to kukan ya Isa haka ALLAH ya sauketa lafiya, yaushema kika tashi?".
Tana share hawayenta tace, " Uncle tun d'azunne".
"To shiga ki taimakawa Aneesa Ku gyarata bara Na d'ora ruwan zafi".
" to Uncle ".

Tsaf Aneesa da Amatallah sukaita hidimar taimakon Fateema, Aneeaa taima jinjira wanka, Amatallah ta gyara wajen, yayinda Uncle ya taimakawa matarsa shikuma, kafin Safiya komai yayi tsaf, tasha tea ta kwanta itada sargad'ed'iyar jaririya dansu huta. ALLAH ma ya taimaki Amatallah lecture biyune da ita suma duk Na yammane.
Da safema bayan sunyi sallar Asuba basu hutaba, saida sukaga yara suntafi makaranta, Uncle kam yana d'akinsa yanata barci tunda suka dawo salla.
Ai yara Na tafiya daga Amatallah har Aneesa kowacce takoma gado, dama yara tea and bread suka basu Dan Neman sauk'i.
Gidan yayi tsit, mai jegoma barci ta takeyi Na ramuwar kusan kwanaki, Dan tunda suka dawo bazatace ga randa tasamu isashen barciba, kullum rabi da rabine, itadama tafiya nak'udar tsaye, shiyyasa haihuwar takanzo mata da sauk'i kuma randa tatashi.
Sai kusan 9 Uncle yafara tashi, shima yau dai kasuwa dama kawai zaije.
Yasha mamakin jin gidan tsit, Fateema yafara lek'awa yaga har lokacin barci take daga ita har jinjirar, ya lek'a Aneesa itama, tayi d'ai-d'ai abinta a gado, ta danne Siddiqa da k'afa d'aya alamar k'ila barcin taso hanata shiyyasa tamata haka.
Murmushi yayi yafito zuwa d'akin Amatallah, nanma abin yabashi dariya yanda tabaje abinta tana shak'ar barci, kansa ya girgiza kawai. Aransa yace lallai su mata anji jiki yau.😂
Kitchen yashiga abinsa, ya had'a tea da soya kwai uku yad'auki bread yafito, shikam da yunwa yatashi yau, kodan jiya dayasha ruwa bai wani ci abin kirkiba saboda zuwan alhaji sabi'u gidan, bayan tafiyarsa kuma barci ya takurashi dole ya kwanta batareda ya nemi abincinba. Dole yatashi da yunwa kuwa, ga matan nasa yau kowacce taji jiki wajen kar6ar hauhuwa.
A falon k'asa yazauna yayi break fast d'insa, kafin yatashi zuwa d'akin Amatallah, har yanzu barci ta takeyi, waya yad'akko yafito babban falo.
Baban Fateema yakira kawu yakubu, ya gaidashi a ladabce kafin ya Sanar mass ansami k'aruwa, kawu yakubu yamasa barka da addu'a ga jaririya kafin suzo.
Daganan Anty maijidda yakira itama, saikuma Nazeefa Dan bazai iya fad'ama Innani ba, baba kuma bayama iya waya sosai saboda ba'ajin maganarsa da k'yau. Dan danan dangi aka rud'e da farin ciki.

Sai wajen 10 daga Aneesa har Amatallah suka tashi, hakama mai jegon kanta, shima hayaniyar su Nazeefa ne ya tadasu, dan danan gida ya kacame da surutu saboda dangi dasuka fara cikashi.
Dole Uncle yay shiri yabar musu gidan zuwa kasuwa.
Can d'inma manyan kasuwar yasamu suka zauna meeting akan kafa k'ungiyar matasa, dolene kowanne abun alkairi akwai k'alubale acikinsa, a tashin farko Uncle baisamu had'in kan wasunsuba, dukda dogon bayani Na gamsarwa dayay musu, wasuma saisuka fara d'auka Siyasa yakeson shiga kawai, dukda ransa ya6aci haka ya danne, yasamu mutane hud'u kacal acikinsu dasuka aminta da tafiyar tasu, hakanne kuma yad'an rage masa 6acin ransa.
Bayan sun kammala yakira Alhaji Sabi'u ya labarta masa yanda sukayi.
Hamdala Alhaji sabi'u yayi, yace, "to inaga zuwa yanzun saimu zauna kuma mu tattauna kafin tsare-tsare su biyo baya, yanzu dai munada manyan mutane kusan 10 kenan, kuma kowannenmu babu matsalar rayuwa dazata takurasa yakasa fidda d'an wani Abu Na taimako koda 5k ne kacal aduk wata".
" wannan gaskiyane".
"Yawwa to saimu zauna kenan a tattauna, insha ALLAH zan shigo wajjen naka zuwa dare nayi barka, daganan saimu tattauna".
" babu damuwa Alhaji ngd sosai, saikazo".
Daga haka suka yanke wayar.

Badan Amatallah tasoba taje makaranta, tasha tsokana wajen su Fa'iza kuwa wai itama insha ALLAH bad'i iyanzu itace zata haihu musu, ai ko ranarma dai zee tasha harara kamar kullum da Amatallah kemata (itako zee batama San Amatallah tana yiba ma😜.)
Bayan antashi suka ajiye magana akan ranar asabar zasuzo musu barka, dan gobe Friday basuda lectures ma ko d'aya.


____________________

Washe gari kuma Aneesa ta kar6i girki, Amatallah tashan kallo, kai kace Aneesa zata canja gidanne, saboda shirye-shiryen kar6ar boss.
Washe garima Aneesa Nata rawar k'afa, ko kunyar 'yan barka bataji ma, saima shi Uncle d'in take bari da kunyar.
Su Fa'iza dasukazo barka sukace kinga yanda ake tattalin miji aii, wlhy kimik'e idanma zaki mik'e, yanzu dai mijin nakune Ku biyu, tunda Uwargida tana jego, nanfa suka shiga fanfata da koya mata abubuwa, su goodness masu ido bud'e kam ai salon yanda ake soyayya iri-iri suka shiga koya mata, Fa'iza tasaki baki tana sauraren ikon ALLAH itada Amatallah, duk da tarigaya tasan yan dama rayuwar k'abilunnan take, baruwansu iyashegensu sukeyi tun suna a waje, saikagama yarinya tabaro k'auyensu tazo takama d'aki a binni wai tazo neman kud'i, kuma bazata ta6a amsa sunan ita karuwa baceba (ALLAH ya k'yauta dai), Fa'iza kam girman Kano Ce, bakomai tasani gameda suba sosai.
Haka dai sukasha hirarsu suka tafi.

Bayan Aneesa tagama kwanakinta Uncle yadawo hannun Amatallah, tabbas yaga canji a wannan karon, danta rage tsorata idan ya ta6ata, kuma tasaki jiki dashi babu laifi, dukda haka kuma bai nemi komai gareta ba ya had'iye kwad'ayinsa Dan bata lokaci, Duk da kuma acikin muguwar zak'uwa yake da son kasancewa da ita d'in, hakanne yasaka Ama... Sakin jiki dashi sosai, aganinta yabarta bayanzuba, k'ilama saita kammala karatunta🤭(zaki bayani lol😆).


***********

Akwana atashi babu wahala wajen Ubangiji, yau kam kwanan Fateema shida da haihuwa, gobene sunan baby, a yau d'inne kuma Uncle zaidawo hannun Amatallah bayan yagama kwana biyu ga Aneesa.
Nazeefa data dawo gidan tun haihuwar Fateema ta fahimci babu abinda yashiga tsakanin Amatallah da yayansu, hakkane yasata k'udirin kafa musu tarko yau sudukansu, tasamu Anty maijidda ta sanar mata cewar sutafi plan B akan Amatallah d'in, dukda bata fito fili ta sanarma Anty maijiddah komaiba, amma itama tadad'e da fahimtar Amatallah har yau batasan mijiba, kodan yanda bata kishin matan yayansu sosai kamar yanda su suke kishi da ita.
Dawuri ranar Anty maijiddah tazo gidan saboda aikima.
Hummm fad'a muku yanda Anty maijidda tagyara Amatallah ranar ai 6ata lokacine kawai, saidaifa hummm!! Ina mai tabbatar muku yau Uncle bai Isa iya control d'in kansaba, gashi dama kwana biyun dayay d'akin Aneesa ma tana Off.

Kusan 5pm tashiga kitchen d'inta domin yin girki, Kitchen d'in tsakar gida su Anty maijiddah sunata aikin abubuwan daza ayi Na suna gobe, Dan haka tanufi kitchen d'inta danyin girkin dare, yau kuma ne rana ta farko fazatayi girki a cikin d'inta, ta fiddo tukwane a kwali ta wanke daduk abinda tasan zata buk'ata, kafin tafara had'a miyar Agusi d'inta datasha busashen kifi ga wadataccen naman tantakwashi, tunifa gida ya d'auki k'amshi su Anty maijidda sai fad'i suke Amatallah zaki kashemu da k'amshi.
(Nima dai Amatallah zata kasheni da kwad'ayi Anty maijidda😋 lol)
Batasanma sunayiba aiki ya d'auke hankalinta, ta had'a lemon kankanarta dayasha madara da kayan k'amshi, ta fere doya mai k'yau ta d'ora, harga ALLAH bazata iya daka sakwarar mutane kusan 15 ba, Dan bayansu Kansu da yara sunkai goma ga kuma Anty maijidda nazeefa sai yayyen Maijego biyu da kanwarta zaliha ga gwaggo rakkiya, ga kuma wata dattijuwa k'anwar Maman maijegon, kuma duk gidan zasu kwana, yayyen fateemar ne kawai tasan komin dare k'ila zasu wuce, Nazeefa Amatallah takira domin Neman shawarar yazatayi.
Dariya Nazeefa tayi tana fad'in "amma ke ragguwace, kina nufin Yaya kawai zakiba sakwara? to bamu yardaba".
" kai Anty Nazeefa ki tausayamin, ALLAH ba abune mai sauk'iba dakan sakwara".
"To Na tausaya miki 'Yar Uncle, yanzu dai dafa doyan saiki d'iba iya wadda zaki daka masa, nikuma sainakai sauran babban kitchen ahad'u adaka gaba d'aya".
''Yauwa Anty Nazeefa ngd, shiyyasa nake sonki".
Dariya sukayi gaba d'aya Nazeefa tafice.

Zuwa magriba ta kammala komai, suma su Nazeefa sun daka waccan, ta had'ama Uncle abincinsa ta d'auki tukunyar miyar duka ta kaima Anty maijidda.
Abincin ta d'auka takai samansa, takuma saka turare kamar yanda Anty maijidda tace mata, saida taga komai yayi dai-dai har ruwan wanka ta had'a masa Dan tasan yana gab da dawowa, ta had'ashi da zafi sosai yanda sanda zai dawo yayi daidai wanka.
d'akinta takoma ta shirya itama, dama tayi wankanta tunkan tayi sallar magriba, kwalliya tayi mai sauk'i tayi d'aurinta mai k'yau yanda Fa'iza ta koya mata, (Amatallah duk irin wad'annan abubuwan bata iyasuba, saboda batada k'awaye gakuma yanayin inda ta tashi, barta dai da tsafta ga nutsuwa, amma irin dai iyayi Na 'yammata bata iyaba😄).
K'amshi take tamkar tayi 6arin turare a jikinta, kodai mace taji k'amshina nan nata saita firgita balle kuma.....humm.🙈lol
Ana kuwa idar da sallar isha'i Uncle yashigo gidan

Yarane kawai a falon, dan haka suka iso da gudu suna ihun murnar masa oyoyo, rungumesu yayi yana murnar ganinsu shima, harma da yaransu Anty maijidda, zaliha dake tare da yaran a falon Dan tana fashin salla ta gaidashi, cikeda fara'a ya amsa yana fad'in "autar mama kamar kiyi zamanki tare damu kawai".
'Yar dariya tayi tana fad'in " Yaya aikuma makaranta".
"Anya kuwa ba wayo bane?".
" ALLAH kuwa Yaya".
"Shikenan to na yarda". yay maganar yana nufar hanyar 6angaren Fateema, bayan Sahib ya kar6i ledojin hannunsa yanufi samansa dasu.
Ya iskesu Anty maijidda zaune a falon Fateema, Mariya Na salla itada gwaggo rakiya, risinawa yayi ya gaida inna Nafi dake zaune tanama jaririya wanka, su Anty maijidda suka gaidashi suma itada Anty maimuna, sunata d'aura kayan rabo.
Anty maimuna tace, " Yaya Muhammad fatin tana cikifa".
Murmushi yayi yanufi bedroom d'in Fateema, Anty Mariya data idar ta kalli su Anty maijidda tana murmushi "kai ya Muhammad Na birgeni saboda kunyarsa wlhy".
Duk dariya sukayi , Anty maijidda tace kad'anma kikagani Indai ya Muhammad ne.
A zaune ya tadda Fateema tana ware kayan fitar suna dayay musu suduka, amma ita kala biyar, sukuma su Amatallah uku-uku itada Aneesa.
Murmushi sukaima juna kafin ya zauna kusada ita ya rungumeta yana mata kisses zafafa a wuya, a hankali yace, " I miss you my sweet tee....".
Duk da taji dad'in maganarsa hakan bai hanata yin 'yar dariya ba, ''kai Nurrina harda zolaya abin? Kaida keda sabuwar Amarya fil a hannu".
Wani k'asaitaccen murmushi yasaki yana shafar gemunsa dakuma manna mata wani kiss d'in, "humm My tee... Amarya daban ke daban ai".
Murmushi kawai tayi batace komaiba, 'yar hira sukayi da tattaunawa gameda sunan gobe, yakuma bata za6in sunan datakeson asama baby.
" duk wanda kasaka yayi Nurri, nidai nabaka za6i kamar ko yaushe".
Yay d'an murmushi yana mik'ewa, "to shikenan ALLAH ya raya Ameenatu".
Itama murmushi tayi tace, " Amin Nurrina lallai Anty Mariya zataji dad'in wannan karamci sunan Iya babu zato".
Baice komaiba yafita yana dariya.
Ya tarar Aneesa da Nazeefa da Amatallah ma sunzo falon, Nazeefa ta gaidashi, Aneesa ma da Amatallah suka masa sannu da zuwa.
Fakar idon jama'a yayi ya kashema Aneesa ido d'aya sannan yafice.
Tayi murmushi kawai tacigaba da abunda takeyi.
Anty maijidda ta kalli Amatallah "madam atashi ko".
A kunyace Amatallah tatashi tafita, sukayi mata dariya banda Aneesa da tayi murmushin yak'e kawai saboda kishi, ga Amatallah tasaka hijjabi kan kwalliyarta babu maicewa ga yanda take, sai uban k'amshinta daya baje falon.
A hanyar 6angarensa ta iskeshi tsaye yakama k'arfen benen idonsa a k'ofar Falon Fateema.
Hakanne ya tabbatarma Amatallah fitowarta ya tsaya jira.
Suna had'a ido yad'an sakar mata harara sannan yafara takawa yana hawa.
Bayansa tabi tana gumtse dariya................✍🏻



_gaskiya 'yan bauchi state muna matuk'ar godiya da goyon bayanku ga shugaban k'asarmu mai kishinmu baba buhari, nabaku page d'innan k'yauta saboda farincikin dakuka Sani yau, ALLAH ya maida shugaban k'asa gida lafiya da dukkan 'yan uwa dasuka halacci wajen campaign d'in, ALLAH kabamu shuwagabanni nagari🙏🏻._
Bauchi inayinku irin Trillion's d'inan🥰🥰🥰🥰❤❤❤❤❤👍🏻



🤩👎🏻

One luv my sweet Fan's🥰







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Special gaisuwa gareku Haskakakku_*

_Nana Diso. Pherty xarah. Asmy b Aliyu. Maman khady. Miss Xoxo. Nuceey luv. Zainab bawa. Hafsat rano. Jiddah Aliyu. Kdeey. Slimzy. Khaleesat Haidar. Billy Galadanci. Saffiyya Huguma. Ayusher Muh'd. Ai'sha d'ansabo. Ummu basheer. Ummi Ai'sha. Hajjace. Faxy fashion. Feedhom. Bilyn Abdull (nima Na gaida kaina🤭😂)_

*ALLAH ya k'ara haskakaku!*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login