Showing 102001 words to 104242 words out of 104242 words
takuma maimata masa tambaya, " Dear maganafa mukeyi! Wacece wannan kilakin?".
"To mikukeso Na fad'a muku? Nace ba abinda kuke tunanin bane, kumin kallon mayaudari, kokuwa nace sona take ni bana sonta ku kirani mak'aryaci, inama mai baku shawarar karku tasirantar da abinda bakuda ilimi akansa a zuciyarku.
Babu wacce ta tanka masa acikinsu, sukayima ficewarsu suka barmasa falon.
Kallo kawai yabisu dashi, ya sauke ajiyar zuciya ta 6acin rai, tabbas lokaci yayi dazai takama yarinyarnan Zainab birki akan haukarta, tunda har tsaurin idonta yakai ta kwaso k'awaye tazo masa gida wajen iyalansa, harma tadunga musu furuci mara k'yau, (dan yana jiyo duk abinda yafaru bayan barinsa wajen), iyalinsa sune mutuncinsa, martabarsa da dukkan sirrinsa, bazai lamunci wata ko wani ya raina masa suba ko 6ata rayukansu, yayi kwafa yana jingina kansa jikin kujerar da lumshe idanu.
Yakai tsawon lokaci yana tunani awajen kafin ya sakko k'asa, babu kowa a falon, yarama suna tsakar gida suna wasa, ya kalli 6angaren Aneesa yaga arufe, Fateema ma a rufe, saiya nufi Na Amatullah.
Tunda Ama... tajiyo k'amshin turarensa ta ajiye Rayyan datake bama nono tashige bathroom, tanajin Rayyan d'in ya fashe da kuka amma bata kulaba tarufe bayin.
Da sauri Uncle ya k'araso ya d'aukeshi, jijjigashi yafraayi yana fad'in "oh my brother na, waye yasaka kuka? Ina Antyn tajene?".
Rayyan yayi shiru tareda lafewa jikin babansa, sai ajiyar zuciya, zama yay falon yana jiran fitowarta, amma bulum, mamaki yakamashi, yatashi yalek'a bedroom d'in babu kowa, sai Raihana a kan gado data koma barci, zama yayi abakin gadon yana jiran fitowarta, nanma shiru kakeji.
Ama.... kuwa zamantama tayi a toilet d'in tana charting hankalinta kwance, duk kuma bidirin da Uncle keyi tana jiyoshi. tashiyay yafara knocking d'in k'ofar bathroom d'in, amma shiru kakeji. mamaki yakamashi, kodaima bata d'akinne? wannan tunaninne yasakashi ficewa da Rayyan a hannu, tsakar gida yafita inda yaran ke ball, zama yay yana kallonsu da tunanin lamarin matan nasa fal a kansa, wato dai sun had'e masa kai kenan, yay murmushi da k'arajin k'aunar matan nasa a ransa๐.
Kiran Sallar magriba tasakashi tasa yaran maza gaba suka tafi masallaci kamar yanda yasaba, yabama Ummita Rayyan suka koma falo itada Siddiqa da mah-mah.
Jin sunfita masallaci Ama.... tayi sallah sannan tashiga kitchen nata, tadafa cus-cus. taimaza takai masa nasa ta sakko kafin su dawo.
Koda yadawo bai nemesuba, yaransa yatasa gaba suka tafi falonsa, acan sukaci abinci sunata masa hirar makaranta, shikuma yabiye musu, dan yau sune abokan hirar tashi.
Saida yaga wasunsu sun fara gyangyad'i sannan yatashesu, yarakosu k'asa, kowa yashiga d'akin mamansa, shikuma yashiga 6angaren Ama.... domin kaimata Rayyan da shima yay barci.
Kwance ya taddata tana bama Raihana nono, wadda keta d'aga k'afa d'aya tana wasa dashi saboda dad'in shan nonon datakeji. Kallo d'aya Ama... tayi masa ta kauda kanta, guntun murmushi yayi, ya sauke Rayyan dake a kafad'arsa saman gadon, baimata maganaba yabud'e dirowar yaran ya d'akko kayan barcin Rayyan ya fara saka masa, sai lokacin idon Raihana yakai Kansa, sakin nonon tayi da sauri ta rarrafo wajensa tana murnar ganinsa (yanda Uncle yake tattalin yaransa da yawan d'aukarsu yasa sukayi mugun sabo dashi, zakiga duk k'iwar da yaronsa zaiyi dawuya shi yayi masa), d'aukarta yayi yafara cillata sama tana dariya shima yanayi, sai Rayyan kuma yasaka kuka shima a d'aukesa. dariya Uncle yayi tareda zama yajawoshi jikinsa shima yana fad'in "jealous ko my Sweetheart".
Amatullah dai duk tana jinsu amma tayi kamarma batasan sunayiba, shirin barcinta kawai tayi tazo gefen gadon ta kwanta.
Shima shareta yayi, saida yaga ya lalla6a yaransa sunyi barci sannan yatashi ya fice.
Mintuna k'alilan yadawo bayan ya shishshiga sashen su Aneesa yayima yara addu'a yafito bai kula kowaccensuba. Shi dariyama suke bashi wlhy.
Idon Ama.... biyu, tanajin sanda ya shigo harya kashe fitilar d'akin ya hawo gadon.
6oyayyar Ajiyar zuciya tasaki, shikam yayi tashi a fili yana fad'in " I miss you my heartbest".
Shiru tamasa.
Acikin kunnenta yace, "wai duk kishinne ginbiyata? kinsan ko matan duniya sun k'are babu abinda zanyi da yarinyar can, yakamata Ku shedeni aii, amma keda 'yan Uwanki kun had'e min kai kunata fushi dani".
"Fushinmi zamuyi dakai, namu ALLAH ya sanya alkairine aii, miye namu danzakayi amarya".
Sassanyan Murmushi yayi yana shafa kanta, ganin kalaman baki bazasu mataba yakoma salon dazata fahimcesa. (๐โโnayi nan).
Bayan wani d'an lokaci Na koma, saina taras Uncle Na lallashin Ama... dake kuka, yabata labarin tundaga farkon had'uwarsa da Zainab (zee) har zuwa yanzun, yak'are damata kalaman kwantar da hankali da lallashi, ya tabbatar mata itace autar mata a gidansa har Abadan insha ALLAH. cikin dai hikimarsa ya shawo kanta harta yarda dashi da bashi hak'uri.
Yay dariya da kuma rungumeta yana mata daddad'an kalamai.
Hakama Aneesa saida yakoma d'akinta ya lallashi abinsa, damata bayani dallah-dallah akan zee kamar yanda yayma Ama...., itama Fateema hakan yamata, duk suka gamsu da komawa tattalin mijinsu tamkar da, amma saida suka saci number zee a wayar Uncle suka had'a kai su uku bayan sun kirata sun saka Hans Free suka mata tatas da gargad'i mai zafi akan mijinsu.
Hakanne yasaka zee kiransa tana kuka dafad'a masa abinda matansa sukai mata, yana k'ayataccen murmushi yana saurararenta, saida takai k'arshe sannan yay k'aramar dariya yana gyara zama a kujera (dayake a kasuwa yake).
Cikin sasaanyar muryarsa dake kashe ga6o6in Zee๐ yace
"To kinga ai saikiji gargad'insu kifita hanyar mijinsu, nidai babu ruwana, tuni na sanar dake banida burin k'ara aure, matana sun isheni, dan haka kisama zuciyarki salama ki sami miji kiyi aurenki, nabarki lafiya inakuma baki shawarar karkiyi gigin sake zuwa gidana, Dan babu ruwana idan matana suka miki wani Abu, nid'in mijin hajiyoyine๐, ALLAH yabamu alkairi.๐
Tundaga wannan ranar zee tafita harkar Uncle, bata sake kiransaba balle turo masa messenges.
Haka kuma rayuwar tacigaba da turawa.
3years later๐๐คฃ
ALLAH mai girma da d'aukaka, yau gasu Ama... ana bikin yayesu amatsayin manyan likitoci kwararru, bakunansu sunkasa rufuwa saboda tsabar farin ciki, hakama Na danginsu wad'ada sukayi tururuwa halattar taron.
Ciki hardasu Uncle da matansa duka, Anty maijiddah Nazeefa zaliha Asiya su aunty Firera da mazansu su kawu Hafizu, matansu Alhaji Sabi'u da dangin su Fa'iza, harda dangin Su Aysha (goodness) wad'anda ayanzu sun sakko suna ziyarar 'Yar uwarsu itama tana ziyaryarsu, harda d'anta Muhammad (Wanda taima Uncle takwara๐) suna kiransa Yaseer.
Angudanar da taro cikin sha'awa da birgewa, tareda kar6ar k'yaututtuka dasu Ama.... suka samu, Uncle jiyake tamkar ya had'iyeta saboda dad'i da k'ara sonta, Dan har yanzu Ama.... tana cikin k'uruciyarta, yanzunema take kuma kilewa tana zama hamshak'iyar mace, ga 'yan yaranta su Rayyan abin sha'awa, sunyi girma sosai da wayo, har sun shiga school tuni, tundagasu kuma bata sakeba, koda yake Fateema ma da Aneesa shiru, tundaga Abubakar Aneesa ma bata sakeba, hakama Fateema tunga mah-mah.
Sunsha hotuna tamkar babu gobe, harda Innani da gwaggo Rakiya wadda su shehu suka matsa tilas sukazo suma, Nazeefa da Zaliha da Asiya ma duksun sake haihuwa tuni.
Tarodai yatashi lafiya cikin farinciki da annashuwa, kowa yakama gabansa.
Su Uncle suka nufi gida inda acanma Uncle yahad'a liyafar cin abinci saboda farantama Amatullah rai, anci ansha an gyatse kuwa, lamarin sai sambarka.
*_Kishi kumallon mata๐คฃ_*
Tunda su Fateema sukaga Amatullah tafara aiki sukayi tsalle suka dire akan suma aiki zasuyi, kowacce ta kakka6o takardunta daga k'asan jaka.
Uncle yay dariya sosai sannan ya had'e fuska.
"Amma lallai bakuda hankali, ai kuda aiki saidai Na gidana, idan kun manta bara Na tuna muku to, alokacin dana aureku babu wacce ta shekara a gidana Na tuntu6eku akan kozakuyi aiki?, ince kowaccenku nunamin tayi batada ra'ayi, Ku kulawa dani kawai kukasa agaba, ban gajiyaba nakuma muku hannunka mai sanda akan Sana'a, nannama kukayi kunnen uwar shegu dani, saikuma yanzu dan kunga Khadeeja kuma kuce saikunyi? to idanfa ba 6acin rai kuke nemarwa gidanmu ba kuma ajiye wannan maganar mucigaba da rayuwarmu, itama data nuna batason aikin ko karatun bazan bartaba, amma tun farko ta tabbatarmin hakanne burinta, shiyyasa nabata goyon baya wajen cikarsa, Ku kama kanku, mud'in ba yara baneba balle kuce, yanzu inada k'aton saurayin yaro dake shirin kammala Secondary, banason shashanci, dan haka kutashi ku bani waje".
Haka suka tashi kowacce ranta a jagule da Dana Sanin k'in amincewarsu tun farko, dayanzu suma sunzama manyan hajiyoyi da ake damawa dasu, amma sukaima Kansu sakkiyar da babu ruwa, gashinan suna zaune Ama... tafara karatu harta mammala tazama hamshak'iyar likita abin alfahari ga mata๐๐.
Bayan kwana biyu suka bashi hak'uri ganin yanata faman fushi dasu.
Shima saiya hak'ura, harma ya k'ara musu da k'yautar jari akan suyi kasuwanci, harda Ama.... itama yabata kamar yanda yabasu dukda dai bawasu kud'i masu yawa baneba.
Tundaga lokacin kowacce takama kasuwancinta, Amatullah kan su kawu hafizu tabamawa akan sucigaba da juya mata anasu kasuwancin, itakuma tarik'e aikinta kawai tunda batada matsalar ci ko sha balle sutura, mijinsu yana iyakar iyawarsa wajen sauke wannan hak'in nasu.
Humm, idanfa kukaga Amatullah dolene takuma birgeku yanzu, tayi k'iba ta murje, daka ganta kaga mata hamshak'ai masu aji, gata da k'ok'arin taimakon mata akan kowanne fanni, kullum cikin basu shawarwari takeyi ta yanda zasu tattali Kansu da yaransu, gata da sauk'in kai da tausayin marasa lafiya, koyaya kake Ama... bata k'yamatarka, dantace ai itama talakance, mizaisa ta k'yamaci 'yan uwanta talakawa, gata da taimako, Rabin albashinta duk kan marasa lafiya mabuk'ata suke tafiya, 'yan yaranta abin sha'awa, kullum cikin godiya takema ALLAH dayabata su da miji irin Uncle, Wanda ayanzu shine duniyarta, shine babanta shine Amminta, shine Uncle d'inta shine kuma miji shine dangi shida danginsa, takowanne fanni sun kare mata mutuncinta da nuna mata k'auna da d'unbin tausayi saboda rasa mahaifanta wad'anda kullum cikin musu addu'ar Neman gafara take dayin sadaka domin ladan yakai garesu, itakam babu abinda zatacema ALLAH sai godiya, danya canja mata rayuwa fiyeda zaton mai tunani, kullum cikin ambaton ALHAMDULLAH takeโ๐ป๐๐ผ.
๐
Tonima dai bilynku nace ALHAMDULLAHI.
_ina godiya ga UBANGIJIN Al'arshi daya bani ikon fara wannan littafi da kammalashi cikin Aminci, Abinda nafad'a dai-dai ALLAH kabani lada, wanda nayi kuskure ALLAH ka gafarta mini._
_Kulum ina k'ara rok'on masoyana akan su kasance masumin gyara yayinda sukaga kuskure a buks d'ina, insha ALLAH zan kuma fahimcesu da ganin k'imarsu, ina ganin darajar Wanda zaicemin Na gyara kuskurena, Dan haka karkuyi sanya Dan ALLAH, gyaran kuma yazamto ta k'yak'yk'yawar hanyar dazan fahimta, Ngd da k'aunar dakuke nunamin, nima ina matuk'ar k'aunarku wlhy._๐ฅฐ
Naso buk d'innan yafi haka fad'ad'a, amma matsalar wayata yasakani tilas Na datse labarin iya nan, kumin afuwa, ina kuma fatan iya hakanma zai gamsar daku da amfanar daku.
_Babbar nasarata shine Ku tasirantu akan abinda yake mai k'yau a labarinnan, sannan kuyi watsi da kuskurena kasancewar nid'in 'Yar adamce Azija.๐, ina kuskure, bakuma komai nasaniba._
*_Tawan Miss xoxo ina godiya agareki, ked'in tadabannce a zuciyar Bily, babu abinda zance sai ALLAH yabar mana zuminci._*๐ค๐ป๐ฝ๐ป๐ป
_Masu min comments kullum dama mahaifina addu'a batareda gajiyawaba kuma ngd sosai, ina alfahari daku, matsalar wayata bazai bari Na lissafokuba, amma kuna k'asan raina, kuma bazan manta dakuba, zuwa nan gaba kuma zan tabbatar muku da hakan.๐๐ค๐ป๐๐ป._
*Bilkisa Ibrahim musa (bilyn Abdull).๐*
๐คฉ๐๐ป
Marubuciyar...
_Rashin sani!!_
_Auren k'addara ko biyayya!?_
_K'anwar uwace ko kishiyar uwa!?_
_Ni da Aminiyata!!_
_Nawaff!!_
_Ban saketaba!!_
_Abdul-maleek bobo!!_
_karayar arzeek'i!!_
_Ciki da gaskiya!!_
_Sanadin bikin sallah!!_
_Sabon Al'amaree!!_
_Kukan kurciya.....!!_
_Siyasa ko k'abilanci!!?_
_Wanda bai karantaba ya nema a kasuwar social media๐คฃ, karku bari ayi babuku๐๐๐๐ผ._
Ngd sosai.
One Luv๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐๐๐ผ.
*ALLAH ka gafartama mahaifanmu dadukkan sauran 'yan uwa musulmai dasuka rigamu kwanta dama, ALLAH ka jagoranci al'amuranmu akan wannan za6e dake tunkaromu, Rabbi ka azurtamu da shuwagabbani nagari masu zinariyar zuciya, ALLAH karkabama dukkan wani azzalimin shugaba damar hawa kujerar da suke kwad'ayi, ALLAH yasa ayi lafiya a gama lafiya batareda tada rikicin SIYASA KO K'ABILANCI ba, ALLAH ka d'aukaka Nigeria yarmu.*
NIGERIA is One Nation One people.๐ณ๐ฌ๐๐๐ป๐๐ผ
*_HATTAR MATASANMU๐๐ป๐๐ป, Idan k'asarmu tarikece kune๐๐ป, idan anyi tsaftataccen za6e kune๐๐ป, Dan da k'arfin samartakarku da wautarku ake amfani wajen tada rikice-rikice yayin za6e, inkunk'i bada had'inkai amfaninkune, dan kowa rai yayma dad'i BARAN MAI SHINE๐๐ค๐ป._*
_masoyana saikuma bayan Sallah k'arama idan munkai da darai, ALLAH ya had'amu da alkairi, kushirya da k'yau, zandawo muku da sabon salo insha ALLAH๐, buk d'ina nagaba hummmm bara dai nayi shiru๐คญ๐, kuma karkuce komaifa๐คซ๐ค._
*_NEXT LEVEL_*๐ฌ๐ฅฐ๐
*_BILYN ABDUL CE๐ค๐ป_*๐ป๐ป๐ป๐ป๐ป๐ฝ๐น.