Showing 87001 words to 90000 words out of 104242 words
kawai dai ALLAH bai kawo baneba, dama kaji nace inason saina gama karatu nafad'ane kawai wlhy, bawai har zuciyata bane, amma kayi hak'uri idan na 6ata maka rai".
Murmushi yakeyi yana shafa bayanta a hankali, yaji dad'i sosai da ba wata kwaya takesha saboda gujema cikinba, ya sumbaci kanta yana fad'in ''ngd Khadija, bakimin kaifin komaiba, ALLAH yabamu masu albarka da tarin alkairi a yau d'innanma nake fata".
Kuma cusa kanta tayi a jikinsa tana dariyar jin kunya, shima sai yayi dariyar kafin yasaketa yace tom ina zuwa, kiyi k'aton shirin k'ar6ar jikokin brother insha ALLAH.
hannu tasa tarufe fuskarta shikuma yafita yana dariya...............βπ»
Nima Uncle kad'an bani kunyafaπππ
_'yan Kaduna state nabaku wanga page k'yauta, saboda tarbar da kukaima baba buhari, kun burgeni ainun wlhy._
π»π»π»π»π»β€β€β€β€β€ππ»π
π€©ππ»
One Luv my sweet fansπ»
*_ALLAH ka jik'an iyayenmu_*πππ»
[1/19, 10:28 PM] Aysha Galadima: *_Typingβπ»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*π‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
____________________
*_Number 36_*
____________________
Da safe haka Ama... ta tashi jiki duk yana ciwo, ba k'aramar murza tashaba wajen Uncle a daren jiya, hakadai ta tak'ark'ara tayi break fast mai sauk'i, shikuma ta d'ind'uma masa tuwon, bayan ta kammala gyaran kitchen d'in da babban falo tayi wanka a gurguje tanufi samansa, tashinsa kenan a barcin daya d'an koma bayan sun dawo massalaci, toilet tawuce ta had'a masa ruwan wanka.
Ya langyare mata akan bazai iya yi da kansaba, shi jikinsa ciwo yake masa, "jiya duk kin bani wahala my best".
Idanu Amatallah tazaro waje, " Uncle wato nimace nabaka wahalar ko? nan k'asusuwana sai ciwo sukeyi tamkar naje noma, shine zaka dawo da abin kaina ma".
Dariya yamata, "oh babyna zo namiki tausa saiki warware gaba d'aya".
" wad'in? tabd'i, Uncle ni zakama wayo? ai idan ka ganni lahira kaini akayi, ni yauma nayafe kwannan wa Anty Fateema, ta had'a uku kawai".
"Lallai yarinya kinma Isa, yau ma muna tare yini guda, namaso ace girkin naki yakama asabar da lahadine, humyim dakin fad'ama jama'ar jos".
Cikin dariya tace, " Uncle!, koda yake ni kama tunaminfa, Anty Aneesa na wucewa nima zan had'a kayana sai jos, wata biyu zanyo".
Wani kallo yamata na idan na kamaki saikin fad'i dawa kike. yashige toilet yana murmushi da cije le6ensa na k'asa.
Itama dariyar tayi tahau gyaran gadon, kafin yafito tagama gyaran bedroom d'in tsaf takoma falo yafito, bai katse mata aikintaba yayi shirinsa da kansa, k'ananun kaya yasaka, Dan babu inda zaije, yana gida cikin iyalinsa yau.
Cikin nishad'i sukayi break fast atare yau ma, daganan suka fito harabar gidan shan iska, yara suna wasan 6uya tareda Amatallah, Uncle da su Aneesa suna musu dariya, abinne ya burge Uncle yashiga shima, ganin haka Fateema da Aneesa suma suka shigo, akabar Siddiqa tanama Mah-mah wasa.
Fateema ta d'aurama Uncle k'yallen a fuska aka rufe masa ido, daganan kowa yanemi wajen 6uya, Uncle kuma yafara lalubensu, daga bayansa Aneesa taja rigarsa, yajuyo da sauri yakai hannu zai kamata ta zille tana dariya, Amatallah ma ta ta6a hannunsa, itama ta zille masa, Sahib yazo gabansa yana fad'in "Abbu gani ka kamani". da sauri Uncle yajuyo inda yake shima, amma Sahib ya gudu, Dariya suketa masa suduka, shikuma yana bin sautin dariyar amma yakasa kama kowa, daga k'arshedai ya damk'i Saifudden, nanfa suka saka masa tafi da ambatar an kama Saifi! an kama saifi!!.
Handkerchief d'in Uncle yacire yana dariya shima, Saifudden aka d'aurama sa, kowa ya matsa, shima ta6asa sukaitayi suna guduwa da dariyar yanda yake laluben san kama wani, Abulkhairi yazo ta6ashi ta baya ALLAH yabama saifudden ikon damk'oshi, shima aka d'aura masa, Abulkhairi baisha wahalar damk'e Aneesa ba shima, yahau dariyar yakama momy Yakama momy, su Uncle na tayashi da tafi, itama Aneesa aka d'aura mata, aiko da k'yar takama Ummita itakuma, Ummuta koda aka d'aura mata dawayo tad'an d'aga kad'an tana gani da ido d'aya, tashin farko ta damk'o Amatallah, itama aka d'aura mata, itama tafi shan wahalar kafin ta damk'o Fateema da Sahib lokaci d'aya, akadai d'aurama Fateema, sunta zagaya gida ana dariya Sam ta kasa kamo kowa, sai can tarutsa Uncle dayaja mata d'an kwali tayi azamar kama damtsen hannunsa...π
Haka suka yini cikin nishad'i, daga wannan wasa su koma wancan har lokaci yaja, kowa yagaji suka shige ciki aka zube a falo ana maida numfashin gajiya. Amatallah tashiga kitchen ta had'a abincin rana, daganan kowa yad'an watsa ruwa saboda zufar dasukayi wajen wasa, sai bayan sallar la'asar Uncle yad'an fita zuwa gidansu.
Yau ma haka suka kashe juna da soyayya shida Amarsa.
Washe gari suka yini gidansu Innani suduka har yaran, koda suka dawo da daddare miji yakoma hannun Fateema, itama haka taita shagalin damk'e kayanta, Yakuma kar6eta tamkar ba ranar yarabu dawata macenba, ya nunu mata soyya mai tsayawa arai da tattalinta tamkar itakad'aice gareshi.
Washe gari Monday, yara da Ama..... Duk suka tafi makaranta, shima Uncle yafice harkokin gabansa, kasuwa yafara zuwa ya gaggaisa da jama'a da duba yanda komai ke tafiya, sannan yad'an Shiga B.U.K, bai dad'eba yafito danufi tafiya, Amatallah ma batasan yazoba, tanacan sunata hirarsu dasu Rita bayan sunfito lecture a gajiye sunad'an hutawa kafin ashiga wata.
Harya bud'e mota yaji ana masa sallama a bayansa, juyowa yayi batareda ya rufe k'ofarba.
Yad'an had'e fuska Dan ganin yarinyar datake Neman takura rayuwarsa a kwanakinnan (zee), inhar zaishigo b.u.k saitazo wajensa, dukda bata fito fili tace tana sonsaba take-takenta sun nuna masa hakan.
Canjin fuskarsa baisa tadamuba, ta gaisheshi cikeda ladabi.
Amsawa yayi yana tambayarta ya karatu.
Tace, "Alhmdllh ya iyali?".
Bai amsaba yace, " yau ma tambayarce?".
Murmushi tamasa tana gyaran tsayuwa, "eh to kusan haka, amma tayau tasha banban data ranar sir".
" lallaikam, gashi kuma ni INA saurine" yay maganar yana kallon agogon hannunsa da gyaran babbar rigarsa ta farar shadda.
"Babu damuwa sir, in ban takurakaba kawai kabani number d'inka, koda ta test message ne saina turo tambayar".
Yad'an kalleta kad'an, sanye take cikin gown ta material bak'i da d'igon Fari, sai siririn gyalenta Fari data yafa akanta, doguwace babu laifi, sannan tanada haske sosai, kuma yakula 'Yar gayu ce, ko magana a yangance take yinta, zata iya Girman Amatallah koda da shekara uku ne ko biyu, kauda idonsa yayi batareda ya tankaba, ya d'akko card d'insa d'aya yabata sannan yashige motar.
Cikin salonta tace, " INA godiya da wannan karamci, daka mini".
Wani murmushi kin gundireni yamata yatada motar yatafi.
Ta sumbaci card d'in tana wani lumshe idanu da shak'ar k'amshinsa daya mannewa card d'in sannan tabar wajen tana mai addu'ar ALLAH ya mallaka mata bawan ALLAHn nan.
Nace hummm.
Alhaji Sabi'u dake zaune gefensa Wanda soyayya tarufe idon zee ko ganinsama ita batayiba ya kalli Uncle d'in yana 'Yar dariya.
"Mutumina kodai ta hud'uce?".
Uncle yakuma dafe sitiyarin da k'yau yana murmushi, ''haba Alhajina ai ka tausayamin kaima, inani ina mata hud'u? Uku nan sun isheni, ni banima da kud'in aure a yanzu balle inda zan ajiye matar, kawai dai yarinyarce nima naga take-taken nata auren suka dosa".
" a kawai kashiga kaima, indai kud'in aurene matsalarka ALLAH zai kawo".
"Hhh lallaikam Alhaji Sabi'u, to aini yanzuma babu wani gurbi da wata mace zata samu a zuciyata, matana sun mamaye ko ina da ina, harma bana kallon matan dawani fasali, kainema yakamata kashiga ta uku kawai wlhy".
" a to tunda abin kaina zai dawo abar maganar kawai".
Dariya sukayi gaba d'aya suna cigaba da tsokanar juna har suka kai inda zasuyi meeting d'in nasu.
Kusan kowama ya hallara su ake jira. babu 6ata lokaci suka fara abinda ya tarasu.
Sun tattauna akan abubuwa masu yawa dasuke damun k'ungiyar sannan suka koma kan neman hanyar samun kud'in shiga, kowa yana kawo shawararsa.
Alhaji Murtala yace, "toko zamuci bashin bankine mu kafa wasu sana'oi kafin muga abinda ALLAH zaiyi".
"Amma Alhaji murtala bama tsoron gudun Matsala nan gaba? Idanfa adadin maida kud'in yayi bamu sami yanda muke soba akwai matsala kenan".
" ito dakuma wannan, to'ai munada sauran kud'i mizai hana muduba wani kasuwanci mai saurin kawo kud'i".
"Wannan shawarar tayi kam, toga wata hanya danake d'an shakkar fad'arta da".
" wace hanyace? Kafad'a kawai kanka tsaye Alhaji Isa".
Nisawa yayi kafin yace, "kwangilace dama ta gwamnati, tun kwanaki governor yamin maganar amma nad'ank'i bashi had'inkai saboda wani dalilina, to yanzu mizai hana mu kar6a amatsayin k'ungiya, ni dama banason amsane alokacin gudun gutsiri tsomar 'yan siyasar k'asarnan".
Uncle ya jinjina kai yace, " yayi sosai, yanzu saikamasa maganar kenan?".
"Shikenan, saimuje a k'ungiyane to, zan sama mana damar ganinsa kenan".
" okey shikenan to".
(Alhaji Isa sirikine ga governor, shiyyasa yakeda lasisin ganinsa cikin kwanciyar hankali akuma duk sanda yaso, yak'i kar6ar kwangilar ne abaya saboda gudun surutai na jama'a, shima kuma ALLAH yaymasa rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma yana bada muhimmiyar gudunmawa akan k'ungiyar, da kud'insa dakuma aikin kai da kai dasuka saka Kansu).
Sun dad'e suna kuma tattauna wasu hanyoyin kafin su tashi kowa yakoma kan harkokinsa.
Uncle dai kasuwa ma yakoma.
***********
*Bayan sati d'aya*.
Wannan karon kam a d'akin Fateema yagama kwanakinsa saikuma Aneesa ta kar6esa, randa zaibar wajenta ne kuma ranar tafiyarta Ghana, dayake anma yara hutun school, shiyyasa tatafi harda Sahib da saifudden da Uncle dazai mata rakkiya ya kwana biyu ya dawo.
Suntafi sunbar Fateema da Amatallah da kewa, duk saida suka had'a tsaraba suka bata ta kaima danginta. ta nunamusu jin dad'inta da godiya agaresu, shima Uncle yaji dad'i sosai, da kumajin k'aunar matan nasa sosai a ransa.
Sunsha hira harda Nazeefa data zo Dan tayasu zaman kwana biyu kafin Uncle ya dawo.
Dangin Aneesa sunji dad'in ganinta, dan haka aka musu tarba ta musamman itada boss d'inta, sai haba-haba akeyi dasu.
Kwannan Uncle biyu kuwa ya dawo bayan ya zagaya dangin Aneesa yamusu alkairi dai-dai k'arfinsa, yabarota itada Saifudden da Saheb da Siddiqa, yasha dai shagwa6a randa zai taho wajen Nessar sa, haryaji tamkar karya taho ya barta.
Hakadai yataho cikeda kewarsu. yakumazo ya iske wata tarbar ga Amatallah wadda ta mantar dashi kewar Aneesa.
Rayuwa tacigaba da shurawa, da gari ya waye sai dare yayi, saikuma wata safiyar.
Ansaka ranar auren Jabeer da Asiya k'awar Amatallah, ashe dama tun a wajen bikinta suka jone, Amatallah tayi murna sosai, koba komai tasamu 'Yar uwa akusa, Nazeefa ma an saka tata ranar da saurayinta Mubarak, sai shehu da zaliha k'anwar Fateema, wata 5 kacal indan munkai da rai.
Governor yabasu damar ganinsa ranar Monday 11am, dan haka suka tsara masu zuwan su 5 kawai. Uncle, Alhaji Sabi'u, Alhaji murtala, Alhaji Maina saikuma shi Alhaji Isa d'in.
*********
Sun sami tarba mai k'yau daga governor dan yanajin dukkan ayyukansu na alkairi, kuma duk d'insu yana musu kallon mutane masu mutunci da sanin mutuncin jama'arsu, sunci abinci a tare kafin sushiga abinda ya kawosu.
Governor yayi murmushi tareda jinjina musu "tabbas kun burgeni sosai, kuma ina marhabin da wannan k'udiri naku, nakumayi alk'awari taimaka muku nima nasaka hannu a tafiyar domin cigabanmu muda yankinmu, wannan taimakon bata fuskar SIYASA zanyishiba, zan yishine amatsayina nad'an k'ungiyar, kuma atake anan nima za'a bani form nacike dan zama a member na k'ungiya".
Atare sukayi na'am da nuna farincikinsu.
Yacigaba da fad'in " ga shawara, mubar maganar kar6ama k'ungiya kwangila domin neman kud'in shiga, dan hakan zaibama wasu damar yad'a farfaganda na nuna k'ungiyar SIYASA ce, bayan kuma naji mafi yawan bayananku na nuna kuba 'yan SIYASA bane, bance kud'in dazan bada zasu rik'e k'ungiyarba, amma zasu taimaka sosai wajen tallafa k'ungiyar takafa wasu sana'oin dazasu ringa kawo kud'ad'en shiga, sannan nayi alk'awarin saka matasan wannan k'ungiya a guraben aiki masu yawan gaske, dakuma guraben karatu awasu jami'oin arewaci da kudanci, wad'anda basuda buk'atar karatun kuma zamu tallafa musu da jari a gwamnatance, ina fata kun gamsu da hakan".
Duk mun amince mai girma gwamna, fatanmu ALLAH yashige mana gaba, yakuma cigaba da dafa maka acikin ayyukanka na alkairi, ALLAH yayta kawo mana shuwagabanni irinku masu zuciyar zinari a k'asarnan".
Dariya governor yayi, "Alhaji Muhammad Ahmad Labbo kune yakama ayi addu'ar yawaitarku acikin al'umma, dankune zinarai masu zuciyar diamond, da yankinmu sunada irinku tuntuni daba a sami damar kassaramu irin hakaba, ALLAH yak'ara muku tsawon rai da lafiya".
Duk suka amsa da amin, Uncle dai 'Yar dariya kawai yayi, azuciyarsa yace amin d'in.
Kafin subaro suka bama governor form yacike, shima saida yabiya naira dubu d'aya kamar kowa, sannan yarubuta musu zunzurutun kud'in na gudunmawarsa, suka rabu akan yana jiran takardun matasa d'ari biyar, dan nema musu aiki, damasu neman gurbin karatu, saikuma masu sana'oin hannu.
Sunyi godiya sosai da k'yak'kyawar addu'a agareshi, suka baro gidan cikin d'unbin farinciki da yabama halin dattako irin na wannan governor.
******
Watan Aneesa guda tadawo Nigeria, cikeda abubuwan tarin alkairi daga family nata, tsaraba kowa da sunansa.
Daga Fateema har Amatallah sunyi kewarta, dan haka ranar dawowarta sukai mata tarba ta musamman, itama tayi kewar tasu, abin sha'awa suka rungume juna cikin nuna d'okantuwarsu.
Mai gayya mai aiki kam aibama a maganar irin kewar Aneesar dayayi, ranar kam su Ama... Sai suka zama 'yan kallo dan Aneesa a sabuwar amaryarta tazo.π
Rayuwa tacigaba da shurawa, su Uncle matsalolin sun ragu musu, dan yanzu sunada kud'in a hannu, ga governor yacika alk'awarinsa na tallafawa matasan da guraben aiki dana karatu, sai k'ananun sana'oi na hannu, wad'anda kuma sukeda sana'oinsu aka kuma musu wani tsari na taimakonsu, kafin kace mi ayyukan wannan k'ungiya sun ratsa birni da k'auye, harsun shiga wasu jihohin arewacin k'asarnan, inda su Uncle suka wakilta amintattunsu dake a jihohin.
Abin kunya abin bak'in ciki sai wasu many an k'asar 'yan SIYASA da wasu yankuna na K'ABILUN kudanci suka fara sukar wannan KUNGIYA, da kiranta 'yan rajin raba kan matasan K'ASA, hakan baita6a damun su Uncle ba, dan ayyukan nasu sunfara fad'ad'a zuwa wasu yankunan na KUDANCI, dukda basu samun goyon baya sosai agaresuba, sukan nuna K'ABILANCINSU akan manufofin k'ungiyar kai tsaye.
Saidai kuma abinda zai birgeka matasan dake cikin halin hau na rayuwa sai suka dunga danno kai abinsu, suka ajiye maganar wata SIYASA ko K'ABILANCI agefe guda, Kan kacemi suma 'yan kudancin sun fara k'arfi acikin k'ungiyar.
Hakan bak'aramin tada hankali wasu 'yan SIYASA yayiba, dan yanzu matasan dasuke sakawa a BANGAR SIYASA da basu kwayoyin maye da makamai sunfara gagararsu, ganin matasanma yafara musu wahala, ba'a cika k'ofar gidansu neman MAULA, bare su sami damar hura hanci da watsa ma 'yan tsaki tsaba.
Idan sun taro matasan nan sukuma saisuyi can, sunce yanzu sun daina dafama k'artin banza baya, su turasu sai mota tatashi ko d'ani a gagara basu, saima akoma ana zaginsu da fad'a masu suna 'YAN TA'ADDA, to wannan lokacin yawuce yanzu.
Alhamdullah anyi za6e lafiya kuma angama lafiya, dukda zuwa yanzun su Uncle basu gama samin kammala kan matasanba suma sun taka rawar gani a za6en, dan sun nusar da matasan wad'anda yakamata su za6a dansu tallafa musu.
Hakan kuwa ya razana 'yan siyasar, dan haka bayan duk sun d'are muk'aman sai suka fara jan matasan a jikinsu ana basu wasu manyan muk'amai.
Hakan yabama su Uncle damar cigaba da yad'a manufofinsu dakuma dunk'ule matasan a waje d'aya, suma Kansu gwamnatocin sunyi k'ok'arin bama su Uncle wasu muk'amai amma su Uncle d'in suka nuna basa da buk'atar hakan, su aikinsu dabanne.
'Yan siyasarfa sun fara canja takunsu akan matasan k'asar dan sun kula zuwa yanzu kan matasan yagama waye, bakowanne raini zasu d'aukaba, kuma suna son komawa za6e nagaba, Wanda take-taken matasan yana k'ara