Showing 30001 words to 33000 words out of 104242 words
" uhm, dama haka kika iya dariya my best?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta, "ALLAH uncle kaine kaban dariya, shagwa6afa kayi".
" lah da gaske? aini bamma San nayi wani abuba. tashi ki wanke hannu kizo muyi maganar School d'in da kikeso".
"To". Tafad'a tana mik'ewa d'auke da kwanon.
Har taje k'ofa ta juyo, yanda taga yana kallontane yasata k'asa da kanta sannan tace, " uncle tuwonfa?".
"Kansa ya girgiza mata sannan yace, " a'a Na k'oshi, wasa nake miki, ban dad'a dacin abinciba ne da naci".
Kai kawai takad'a ta fice tana mamakin wannan sabon salon da Uncle kemata a yanzu, tamkar ba Uncle d'in taba, babuma abinda ke takurata kamar yawan kallonta da yakeyi.
*******
Ganin yara sun dawo babu shi yasaka Aneesa kiran Abulkhairi ta tambayesa.
"Momy bansan ina yajeba, yacene mu shigo gida shi zaije wani waje".
Shiru Aneesa tayi tana kallon yaron, k'asan ranta haushi da kishi na cinta.
Sallamar Abulkhairi tayi, ta d'auki waya ta kirasa.
Amatallah na fita daga falon kiran Aneesa na shigowa, murmushi yayi dayaga my Wife Neesa.
d'agawa yayi, cikin sanyin muryarsa yamata sallama.
Batareda ta amsaba tace, " dear wai ina kuma kaje a darenan?".
Bai iya k'aryaba, dan haka kai tsaye yace, "ina wajen Khadija ne my Neesa".
Ai tamkar yadaki zuciyarta da mashi, ta dai daure tace, ''amma a darennan?".
"uhm akwai abinda najeyine mai muhimmanci, amma bazan dad'eba zan dawo, kedai kawai kishirya kar6ar tsoho yau, dan dolene mu goga raini ki tabbatar da saurana har yau".
Shiru tayi, takasa cewa komai.
" hello, bak'ya jinane Neesa? ko harma kin tsoratane?".
Dariyar basarwa tayi, "saika zo d'in, nima na shirya".
" ko babyna?".
"Eh mana". cewar Aneesa.
Murmushi yayi mai sauti, dan hartana jiyosa, yace, " my Siddiqa zatayi k'ani ko k'anwa kenan yau"....
Da sauri ta katseshi da fad'in ''my dear!, dan ALLAH bar fad'e, wasa nakeyi wlhy, sai ka dawo...."
Bata jira cewarsaba ta yanke wayar.
Girgiza kansa yayi yana murmushi, A fili yace, ''my Neesa m......
Shiru yayi bai k'arasaba sabida ganin Amatallah tsaye a bakin k'ofa, baisan tashigoba ko kad'an.
Itakam bama tadad'e da shigowarba taji yana waya, duk da taji da wacce yakeyi hakan baisa taji komaiba azuciyarta, zama tayi nesa dashi.
Shikam duk saiyaji babu dad'i, a zatonsa zatayi kamar yanda su Aneesa ke masa, sai yaga ko'a jikinta. Saima Neman waje tayi ta zauna.
Nikam nace, "Hhhh, yo Uncle ita kishin mi zatayi? tunda har yanzu batasan mi akema kishinba🤣 ai da sauran time🤐.
List d'in sunayen Schools yabata taza6a, tace itadai kowacce ma ya za6a mata, daga k'arshe dai sai Nazeefa da ya Jabeer ne suka za6ar mata.
Kusan 10pm yay musu sallama ya tafi, akan zuwa gobe zai kawo mata form ta cike.
*********
Ai ko daya koma gida saida yasha fama da Aneesa kafin su dai-daita.
Kishi kumallon mata kenan, bana ganin laifin Aneesa kam, sai dai gaskiya mata kud'an ringa rage zafin kishi, musamman ma agaban miji, dan yana ragema mace daraja wlhy. ko zakiyi kishin kiyi mai aji kamar na uwargida Fateema😉👌🏼.
____________________________
Alhmdllh komai ya kammala gameda exam d'in Amatallah, ta kuma maida hankali sosai a karatun, musamman da taimakon da Nazeefa ke bata sosai, shima Uncle idan yaje gidan yata bata haske kenan akan abubuwan, tunda yasan sirrin jarabawar. kowa k'arfafa mata gwiwwa yakeyi agidan.
Baba kuma ya sanarma Uncle M.A yakamata yaje Jos dan Neman dangin Ammin Amatallah, yakamata a sanar dasu komai gameda rasuwar 'Yar uwarsu da mijinta, dakuma aurensa da Amatallah tunda hankali yad'an kwanta zuwa yanzu saboda sojoji aka zuba a jihar jos d'in da Kaduna.
Sosai Uncle M.A yayi Na'am da batun, bai kumayi k'asa a gwiwwa ba ya shirya yaje jos.
Sosai lamarin ya tsa6a zuciyarsa, yanda yaga gagarumar 6arnar da akayi a jihar sakamakon rikicin da ya afku, har yay sanadin rasa d'an uwansa.
A dangin Ammi ma mutane da yawa sun rasu, wasu kuma suna asibiti suna jiyya, nan dai ya kwashe komai ya sanar musu, sunsha kuka sosai, dan dama sunata nemansu, ashema sune farko-farkon rasuwa.
Duk sunyi na'am da zancen auren, sun kuma saka albarka, sai dai sun rok'i alfarma ya dawo musu da Amatallah nan bayan ta kammala Exam, sai ayi biki kafin a maidota Kano gidansa.
Godiya yamusu, da alk'awarin maido Amatallah d'in, dan aganinsa hakan ma zaisata tad'an rage wani rad'ad'in, takuma dingajin an mata aure irin na kowacce mace.
Sosai yamusu alkairi sannan yatafi suna zabga masa albarka da addu'oin fatan alkairi.
Su Amatallah sun cigaba da zana jarabawa cikin nasara, ahaka suka kammala NECO & WAEC cikin farin ciki.
Har zuwa yanzu kullum Amatallah saitayi kukan rashin iyayenta k'oda a 6oyene saboda kar Innani ko Nazeefa wani yagani, bakamar randa suka gama exam tasha kuka tamkar ranta zai fita, jitake inama Ammi da baba nada rai, suga wannan rana dasukaita buri.
Da k'yar ranar aka samu kanta a gidan, harda zazza6i tayi.
Satinsu d'aya da kammala exam Uncle M.A da Nazeefa suka kaita Jos wajen dangin mahaifiyarta, tayi matuk'ar farin ciki da ganinsu, sai dai ansha kuka ranar itada dangi, daga baya dai suka sakama ransu dangana tunda kuka bazai dawo da wad'anda aka rasaba.
Zamanta cikin dangin mahaifiyarta saiya rage mata wani rad'ad'in, tad'an samu sauk'in k'unar zuciyar datake ciki sosai, gashi kowa tattalinta yakeyi saboda tausayin datake basu.
**********
Uncle M.A kam dasu Nazeefa sai suka shiga kewarta, dan d'an zaman datayi yakawo sabo da shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakaninsu.
Su Aneesa kam da Fateema dad'i sukaji, dan koba komai yanzu yarage zarya gidansu, sai dai yana zuwa kamar yanda yakeyi da, da safe kafin yatafi kasuwa ko aiki, kokuma idan ya taso.
A kuma wannan tsakaninne tafiya wani Cause a Dubai na tsawon watanni tara ya sameshi. kuma cikin gaggawa.
A daddafe yaje sukai sallama da Amatallah, yakuma sanar mata data shirya Jabeer zaizo akan makarantarta idan result ya fito, amma sai dai tayi hak'uri, k'ilan zata koma Kano da zama fa.
Kanta ta jinjina masa tana k'ok'arin maida hawayenta.
Shiru yayi yana kallonta, murya a sanyaye yace, "bak'yason Kano ko my best?".
Da sauri tace, " a'a Uncle, inaso wlhy".
Guntun murmushi yayi kawai, yace, "OK shikenan to, ammafa ba wajen Innani ba wannan karon".
Kallonsa tayi, murya na rawa tace, "Uncle ina to?".
Shima saiya kalleta da d'an murmushi yace, " gidana, kobak'ya son zama?".
Hawayen datake mak'alewane suka zubo, amma batace komaiba.
Hannunsa kawai taji akan kumatunta yana goge mata hawayen, muryarsa can k'asan mak'oshi yafara lallashinta.
"Kiyi hak'uri Khadija, mu kar6i jarabawar mu da hannu biyu, ni kaina ina cikin rud'ani wlhy, bansan yanda zuciyata zata d'aukeki a matsayin matata ba, bayan kuma matsayin d'iya mafi soyuwa kike dashi agareni, banida wata mafitane akan hakan, saboda alk'awarin rik'eki naima Brother yayinda Numfashinsa yarage k'iris ya k'are daga gangar jikinsa."
"Kullum cikin tunanin mafita nake, amma nakasa samowa, ni kaina inajin tamkar mun cutar dake, gashi kuma bakin alk'alami yarigada ya bushe, dan banida damar ruguje alk'awarin danaima brother bayan k'asa ta rufe idonsa. kiyi hak'uri, insha ALLAH komai zai zama labari, lokaci na zuwa dazamu fara kallon kammu ni da ke amatsayin miji da mata kinji".
Kai kawai ta iya d'aga masa.
Waya mai k'yau ya bata a kwalinta, " ga wannan ki rik'e, nasaka miki Number ta, duk abinda kike buk'ata kobai mikiba ki kirani ki sanar mini, da nayi tunanin kicigaba da zama wajen Innani harna dawo. to sai kuma baba yace hakan bai daceba, gara kawai a kaiki gidan, k'ila kafin na dawo kin saki jikinki, ga 🏧 d'ina nan duk sanda kike buk'atar kud'i saikiyi amfani dashi, Nazeefa zata dawo gidan itama harna dawo, karki yarda wani Abu ya had'aki da Aunty's naki kinji, (duk da ma dai bayan tafiyata d'aya a cikinsu zata Bini) kibasu girmansu kamar yanda na sanki, kuma kicigaba da hak'uri akan duk abinda za'a miki bai mikiba, (duk da dama nasan ked'in mai hak'urice), duk Wanda yamiki wani Abu a cikinsu ki kirani ki sanarmin kinji."
Nanma kanta kawai ta jinjina masa.
"Yawwa my best D.. , ALLAH yay miki albarka, d'inkunanki nacan Nazeefa takai da duk abinda kike buk'ata, banda wasa da karatu, banda tarkacen k'awaye, ki maida hankali sosai, kuma dan ALLAH kirage yawan damuwarnan kinji ko".
Yanzuma kanta ta jinjina.
Yace, " kimin magana please naji mana".
Yanda yay maganarne yasakata murmushi, ta share ragowar guntun hawayenta, "ngd sosai Uncle, ALLAH ya biyaka da mafificin alkairi, Yakuma Baka nasara akan abinda zaka nema".
" amin my best D..., ngd da addu'arki, yanzu miza'a bani dazan ringa tunawa".
"Uncle mikake so?".
" komai nasamu inaso my best D.."
Shiru tayi alamar tunani, zuwa can ta kalleshi, "Uncle kafad'a, ni narasa mizan Baka ai".
Murmushi yayi yana kamo hannun damarta.
Kallo tabishi dashi dantaga mizaiyi da hannun.
Bud'e yatsunta yayi sosai sannan yakai bakinsa tsakkiyar tafin hannunta ya sumbata.
Wani yarrr taji ajikinta, harda 'yar girgiza da runtse ido.
Ya d'ago yana kallon fuskarta da murmushi.
Saurin kama k'ofar motar tayi zata gudu. Yay saurin rik'o hannunta yana fad'in " yazaki gudu baki baniba?".
Wata matsananciyar kunya da mamakin sane ya cika Amatallah, a zuciyarta tace dama haka Uncle yake? naga ta kaina.
Ba yanda baiyiba amma tak'i juyowa ta kalleshi, ganin bazata juyo d'inba saiya zame gyalen kanta tareda d'an kwalin.
Idanu Amatallah ta zaro waje dan mamaki wannan aiki na Uncle.....
Kafin takai k'arshen mamakinta taji ya zare pink d'in Ribbon d'in data d'aure tsaka tsakin gashinta daba wani tsawone dashiba.
Yana zarewa tasamu ta fice, da gudu tashige gidan kakanninta da yayan Ammi da k'aninsa ke ciki yanzu.
tabar Uncle da dariya.
Ribbon d'in ya saka a hannunsa sannan ya d'auki d'ankwalin atanfarta data bari ya d'ora a cinyarsa, ya tada motar kawai yatafi, yanamai jin wani nishad'i dashi kansa baisan ma'anarsaba...........✍🏻
🤩👎🏻
*_ALLAH ka gafartama Mahaifanmu😭🙏🏻_*
[1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
____________________
*_Number 13_*
____________________
Da sallama ya shiga d'akin.
Amatallah dake zaune a bakin katifar Nazeefa tana canja rigar filo da sauri ta juyo tana amsa sallamar cikin rawar murya. jikinta har rawa yakeyi.
Shiru yay yana kallonta. Sai yaji babu dad'i ganin yanda yanzu kamar tsoronsa takeji, saima yazo gidan sau uku bata bari sun had'uba, yau ma yasan k'ila batasan yazo ba.
Murmushi gefen baki yayi, ya d'an kauda kwayar idonsa daga kanta saboda zanine kawai da vest a jikinta.
''My best D......", sai kuma yakasa k'arasawa, yace, " kintashi lafiya?".
Da sauri tace, "Uncle sorry ina kwana".
Yanzun ma murmushin gefen baki yayi, kafin ya amsa, ya kuma kallonta kad'an, "bak'ya jin sanyine? Kika zauna haka?".
Gaban tane yafad'i, tama manta da kayan dake jikinta, hijjab tajawo da sauri ta saka, wata matsanan ciyar kunya takuma lullu6eta, saita koma ta zauna bakin katifar ta kifa kanta a cinya.
Zama yayi bisa wani stool dake d'akin, cikin sanyin muryarsa yace, " yanzu yaya kikejin jikinki?".
Bata d'agoba, ta amsa da "naji sauk'i, sai dai yawan ciwon kai".
" tunanifa kenan my best?".
Kanta ta d'ago, idanunta cikeda kwallah ta girgiza masa kai batareda tayi maganaba.
Shima kan ya girgiza mata alamar kartayi kuka.
Ta saka hannu ta share hawayen dasuka fara bin kumatunta.
Mik'ewa yayi tsaye dan bayaso ta karya masa zuciya, yace, ''inaga zuwa Monday zan nema miki school d'in dazaki koma, anfara Reghestiretion d'in SSCE, koba k'yason ki zana a wanan year d'in sai next year?".
Share hawayenta ta shigayi tana murmushi, "a'a Uncle inaso zanyi".
Murmushi yayi saboda ganin tana kuka tana dariya, ya matso kusada ita Yakuma k'asa da muryarsa kamar mai tsoron kar a jisu, yace, "kimin alk'awari to".
Yanda yay maganar sai bugun zuciyar Amatallah ya k'aru, ta d'ago manyan idanunta dasuka yi d'an ja ta kalleshi.
Ya jinjina kai alamar ta amince.
" uncle alk'awari kuma?".
"Yes my best".
" uhm Uncle nami to?".
Komawa yayi inda yatashi zaune yasake zama kan stool d'in, "my best inason kimin alk'awari zaki rage yawan damuwa, rashin kwanciyar hankalinki nawane, kukanki yana ta6amin zuciya ainun Khadija, ki daure wajen kar6ar wannan jarabawar tamu, duk sanda kikaji zuciyarki cikin k'unci ki d'auki alkur'ani ki karanta, su brother addu'armu suke buk'ata kawai a yanzu kinji".
Kanta ta d'aga masa tana share hawaye, " uncle insha ALLAHU duk zanyi".
''Yauwa my dear, ALLAH yay miki albarka". 'Yay maganar yana mik'ewa'.
Amatallah tace, "amin".
Agogon hannunsa ya kalla yana fad'in " bara naje to, idan na dawo saimuyi magana ki za6i school d'in da kikeso ko?".
"To Uncle, amma ko wacce kaza6amin tamayi".
"Shikenan, amma baradai Na dawo d'in".
Kanta ta jinjina masa, sannan tamasa addu'ar dawowa lafiya.
Yana murmushi ya amsa sannan ya fice.
A tsakar gida yatarar da Nazeefa.
"Lah Yaya dama kana gidannan?".
Murmushi yayi yana kallonta gaidashi tayi, ya amsa yana tambayarta babu dai wata Matsala akan Amatallah ko?.
" eh wlhy Yaya tarege yawan kukan bakamar da ba, kuma danaga zata fara tunani sainayita janta da hira danta saki jikinta, amma nakula kamar bata isashen barci".
"Nima nalura da haka kam Nazeefa, Dan tama min complain akan kanta yana ciwo".
" rashin barcine da tunani Yaya".
"Babu damuwa, insha ALLAH zan d'auki mataki, kedai kicigaba da k'ok'ari wajen rage mata yawan tunani da damuwar, a satin nan zan nema mata school dazata zana SSCE d'inta, maybe hakan yad'an d'auke hankalinta".
" yawwa yaya, hakan ma yayi sosai".
"Yawwa bara na wuce time Na tafiya, yau bazakije school bane?".
" eh Yaya. Yau bamuda exam......
Fitowar Shehu daga d'akinsa yana mik'a da hamma, babu zancen rufe baki a tsarinsa, dagashi sai gajeren wando da vest.
kallonsa sukayi suduka.
Uncle M.A ya had'e fuska yana kallonsa, cikin daka tsawa wadda bata hana muryarsa fita da sanyiba yace, "kai! Shehu!, wane irin iskancine wannan? zaka fitoma mutane tsakar gida da boxer? kamar kai kad'aine a gidan?".
Shehu ya yad'an Sosa k'eyarsa yana duk'ar da kansa, " kayi hak'uri Yaya, ni bansan kana gidanba ai".
"Lallai kam, wato sai ina gidanne zakayi shigar mutunci? Nazeefa da Amatallah ba k'annenka baneba? kai bakajin kunyar su ganka a haka? to ni abindama nakeson na sani,