Showing 24001 words to 27000 words out of 104242 words

Chapter 9 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16033

Uncle M.A sukaji a gaske Amatallah tazama matar mijinsu, kishiyarsu, tabbas a kwai cakwakiya.😄
Ku dai Ku kasance dani bilynku kawai.


*_WASA FARIN GIRKI!! My fans_*🤩

Mukoma labari👎🏻



_____________________________

Hankalin Uncle M.A yatashi, yanda yaga rikicin ya fad'ad'a har zuwa wasu jihohin, bak'amin ta6a zuciyarsa lamarin yay ba, musamman daya tuna babu brother d'insa yanzu a doron k'asa, dama a wajensane yasamu kwarin gwiwwar kafa k'ungiyar dazata farkar da matasan, a yanzun kam baisan ta Yaya zai tunkari lamarinba, sai dai insha ALLAH zaiyi k'ok'ari wajen hana kansa rashin k'warin gwiwwar aikin alkairin daya kulla niyya, shawarar da amininsa brother d'insa yabashi itace zata zam jagora wajen k'aiminsa da wanzuwar himmarsa........
Ringing d'in wayarsane yasashi sakin ajiyar zuciya, hannunsa yasa yafara lalubenta a gefensa, Dan kwance yake a kan gado, tunda yadawo sallar asubahi yakuma d'an kwanciya, saboda tunani baya barinsa samun isashen barci, tunanin jikin baba da rashin d'an uwansa, ga kuma Amatallah da aurenta, Dan har zuwa yanzu bata farfad'oba, iyalansa kuma basusan da aurenba.
Ganin sunan doctor Shu'aibu yasashi d'aga wayar da hanzari, ko gaisawa basuyiba doctor Shu'aibu ya shaida masa Amatallah ta farfad'o, kuma Alhamdllh cikin hayyacinta, sai dai tanata kuka da kiran iyayenta.
Da hanzari ya diro daga kan gadon, jallabiyarsa daya dawo masallaci ya d'auka ya Sanya, ya d'au key d'in mota yafita da sauri.
A falon k'asa yaci karo da Fateema dake k'ok'arin had'a break fast saboda yara zasuje makaranta.
"A'a lafiya kuwa Nurri? Saurin mikakeyi haka?".
Bai ko juyo ya kalletaba yace, " zanje asibiti ne, Amatallah ta farfad'o".
Duk da tana matuk'ar tausayin yarinyar, amma sai da zuciyarta ta sosu, taraka bayansa da kallo harya fice daga falon, wani takaici yadaki zuciyarta akan mazarin da mijin nasu keyi. (Wata zuciyarta tace, aiko baikamata kiji haushinsaba, Dan babu Wanda ya cancanci damuwa da lamarin yarinyarnan sama dashi, kiduba halin data shiga mana).
A sanyaye Fateema tace, "hakane kuma, ALLAH kabani hak'urin jure duk abinda zan gani".


Nace, " to amin uwargida".😊



********

Uncle M.A a rikice ya isa asibitin, tun a k'ofar d'aki yay karo da gwaggo Rakiya tana kuka, bai ce komai ba yashiga d'akin da Amatallah take.
Doctor Shu'aibu Na tsaye kanta, sai Nazeefa dake zaune gefen gadon rungume da ita, kuka takeyi rurus da fad'in a kaita taga babanta da Amminta.
A hankali Uncle M.A ya sauke ajiyar zuciya, ya k'araso gaban gadon idonsa akan Amatallah. d'ayan gefen gadon yaje ya tsaya, ya kalli doctor Shu'aibu a raunane.
Jin jina masa kai doctor Shu'aibu yayi, tareda masa nuni ya lallasheta da idanu.
Uncle M.A ya jinjina kansa, sannan yay k'ok'arin maida kwallar idonsa yana cije le6ensa Na k'asa. Alama yayma Nazeefa ta barta ta fita itama, saboda doctor Shu'aibu shima yafitan.
Nazeefa ta zare jikinta daga Na Amatallah, ta sakko daga gadon.
Hakanne yasaka Amatallah d'ago jajayen idanunta, tana ganin Uncle M.A tak'ara k'arfin kukanta tana fad'in "Uncle ka kaini naga babana da Ammina Dan ALLAH".
Bai ce komai ba har Nazeefa tafita. Sannan ya zauna a bakin gadon kusada ita, hannu yasa ya jawota kusadashi ya rungumeta kawai, tuni idonsa suncika da kwallah, harsun fara taruwa a gefen idonsa.
Rud'anin da Amatallah take cikine yahanata mamakin rungumar da uncle yaymata, Dan tunda tafara girma da wayo ya daina rik'e koda hannuntama. jinta a jikinsa yasakata kuma fashewa dawani kukan mai tsuma rai.
d'an yatsa d'aya Uncle yasaka ya d'auke hawayen dasuka taru masa a gefen ido, ya k'ara rungume Amatallah sosai ajikinsa, cikin daidaita muryarsa yace, " Khadija! ".
Yanda yakira sunantane yasakata tsaigaitawa da kukan, amma bata amsaba.
Ya kuma fad'in " Khadija! Kina jina?".
Cikin da shashshiyar muryarta ta amsa da "Na'am uncle"..............✍🏻


🤩👎🏻


Inaga maybe gobe idan ALLAH ya kaimu bazaku ganniba gaskiya🥰🥰🥰🥰.
Idan kuma naga comments yanzu idan nadawo anguwa nayi muku😂.

One Luv my fans🥰







*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 12_*
____________________

Shiru yad'anyi Na wani lokaci, kafin yagyara mata kwanciya a jikinsa, murmushi yayi mai ciwo sannan yace, "Khadija duk duniya wayafi kowa a halittun ALLAH?".
'Dan d'agowa tayi ta kalleshi kad'an, sai kuma ta maida kanta a gefen hannunsa, muryarta a dusashe tace, " MAZON ALLAH (S.A.W) Uncle ".
Lumshe idanunsa yayi yana fad'in " masha ALLAH Khadija, yanzu yana ina?".
Yanzun kam tashi tayi sosai tabar jikinsa, jingina tayi dagadon
idonsa Na kanta.

"Uncle ya koma ga Ubangijin sammai da k'assai".
''Alhmdllh Khadija, yakikeji darashin kasancewarsa a duniya".
Mamakin tambayoyin Uncle suka fara bata, amma saita dake tace, " inajin babu dad'i, amma nayi hak'uri tunda ubangijine ya tsara hakan, ina dai Addu'ar ALLAH ya sadamu dashi a ranar ceto".
Kansa yakad'a mata, muryarsa takuma sanyi fiyeda sanyin datake dashi, yakamo hannayenta biyu yarik'e a nasa, "Khadija ke musulma ce kuma mumina, kinsan k'addara da jarabawa, duk wani mumini akwai irin jarabtar da ALLAH kanyima rayuwarsa, wani yabashi dukiya mai tarin yawa, amma bashida lafiya, wani talauci amma yanada lafiya da 'ya'ya, wani ilimi amma sai ya jarabceshi da hatsabibiyar mace ko shi d'in ya kasance hatsabibin, ko cikin 'ya'yansa, wani haihuwace ALLAH bai bashiba, wani ya haihu 'ya'yan sun zame masa fitina, wata macen gidan mijine jarabtarta, wata rashin aure, wata rashin lafiya, wasu kuma saikiga ALLAH ya had'a musu komai Na rayuwa, sai dai kinsan wani Abu?".

Amatallah ta girgiza masa kanta.

Yacigaba da fad'in kowanne irin matsayi ka taka a rayuwarka inhar bakajin tsoron ALLAH ba to kaifa ba komai baneba, duk k'ask'ancin waninka inya kasance mai tsoron ALLAH toya fika agareshi, ubangiji shika d'ai yasan iya adadin halittun daya halitta masu numfashi a duniya, kuma shine ya tabbatar mana duk sai ya d'and'ana mana mutuwa, wad'anda suka rigamu tafiya ba sauri sukayiba, muda muka rage bamuyi jinkiriba. A wannan ga6ar ina mai baki hak'uri, da rok'onki akan kizama cikin bayi masu ambaton Alhamdullahi ala kulli halin aduk yanayin dasuka tsinci Kansu a rayuwa, ki kar6i jabawarki da hannu biyu dankizama cikin salihan bayi muminai..........."
Hawayene masu zafi suka fara zarya a kumatun Amatallah, tabbas bayanan uncle namata nuni akan babu babanta a duniya, ahankali tace, "uncle babana yarasu ko? Karka 6oyemin, kafad'amin, insha ALLAH zuciyata zata iya d'auka, domin ubangiji baya jarabtar bawa da a binda bazai iyaba. namaka alk'awarin kasancewa cikin bayin ALLAH masu hak'uri da kar6ar jarabawa ko wacce iri".
Da k'yar ya iya had'iye wani kulutu daya tokare masa k'irji, sannan ya d'aga mata kai a hankali shima hawaye nabin nasa kumatun.
Jikinsa kawai tafad'a tasaki kuka mai tsuma rai, hannu biyu ya kar6eta ya rungume, suka cigaba da rairawa a tare, abin gwanin ban tausayi.
Sun d'auki tsawon lokaci ahaka kafin Amatallah cikin kuka tace, " uncle Ammina fa?".
"Sai hak'uri Khadija, Saliha tama rigayi brother ra..s....u...wa...".
yak'arashe maganar da k'yar, saboda wani d'aci dayakeji a zuciyarsa.
Sunyi kuka mai isarsu shida ita, kafin doctor Shu'aibu yazo yana lallashinsu, dole akama Amatallah allurar barci danta samu nutsuwa.


*_One week later_*

Alhamdllh a sati d'ayannan daya gabata abubuwa masu yawa sun faru, ciki harda rud'ani mai rikitarwa da Amatallah ta shiga, dole aka d'akkota daga asibiti aka maidota gida wajen innani.
Basu 6ata lokaciba aka dage mata da addu'oin dangana da hak'uri, Alhmdllhi ansamu nasarori kam, Dan addu'a takobin mumini Ce.
Nutsuwa tazo mata sosai, sai dai yawan kuka datakeyi, sannan maganama yanzu kam saita wunima batayiba.
Kullum uncle Na hanyar gidansu innani.
Nazeefa da Innani suna matuk'ar k'ok'ari wajen rage mata kewa da yawan damuwa, hakama jabeer, Shehu kam sai a hankali, danshi dama bayajin magana, zaman gidamma bayi yakeyiba, danma yana masifar tsoron uncle Muhammad d'inne yake rage wani abun.
Har zuwa yanzun daga Amatallah har matansa babu Wanda yasan da zancen aurensu, innani da babane kurum sai jabeer da maijiddah suka Sani, ko Nazeefa batasan komaiba.


Bayan sati uku da rasuwarsu Ammi cif baba yace yakamata asanarma Amatallah zancen auren, karya zam saita saki jiki kuma akuma maidata ruwa, gamma taji komai yanzun tahak'ura baki d'aya, hakama matan uncle yakamata Susan halin da'ake ciki.
Innani tayi na'am da wannan batu, Dan haka aka kira kawu yakubu da doctor shu'aibu, sai Su jabeer kuma.
Kowa dai ya hallara.
Aneesa da Fateema sai mamakin wanna taro sukeyi, su duk zatonsu akan ruk'on Amatallah ne, anason aza6i wadda za'a bamawa acikinsu, tunda sunsan dolene mijinsu zai cigaba da rik'onta.
Fargaba dukta cika Uncle, damuwarsa d'aya akan yanda Amatallah zata kar6i zancen auren ne.
Bayan addu'oi da aka gabatar kawu yakubu yamik'e a nutse yafara jawabi tundaga farko har k'arshen abinda ya wakana aranar da Baban Ama zai rasu.
Tun jikin Amatallah Na rawa a 6oye harya fito fili, tafara karkarwar rawar sanyi sosai, kuka kam tama nemesa tarasa gaba d'aya.
Anty maijiddah dake kusada itace tajawota jikinta tana lallashinta.
Idon uncle k'yam akanta, ko k'yaftawa bayayi balle yatuna akwai wasu halittu su Aneesa awajen.
Daga Aneesa har Fateema kam mutuwar zaune sukayi, kowacce takasa motsin kirki, har kawu yakubu yagama jawabi yakoma nasiha agaresu.
Tashin hankali kenan, Wanda ba'a samasa rana.
Wannanfa shine ana wata gawata tazo.
Dad'i sosai yakama Nazeefa, Dan aganinta babu Wanda Amatallah tadace dashi kamar yayansu Muhammad, lallai wannan shinefa ake kirada *HA'DIN ALLAH*.
har taro yatashi mutum uku basu iya koda tariba, Aneesa, Fateema, garama Amatallah tanata hawaye da rawar sanyi.
Ranar kam haka ta kwana rijif da zazza6i mai zafi ajikinta, sai sambatu takeyi dakiran sunan Amminta da baba.
Da k'yar innani tasamu tayi barci, dama ita ba had'in auren ba, halinda yarinyar zata tsinci kanta, dakuma yanda zata kalli al'amarinne damuwar.


___________________________

Alhmdllh k'ura ta kwanta, zuwa yanzu jos da Kaduna abubuwa sunfara dai'daita, sai dai bak'aramar asarar rayuka dana dukiyoyi akayiba, lamarin ko k'yan gani babu, abin tashin hankalin abin yafi shafar matasanmu, kusan duk sune aka kashe da raunika kuma ga wad'anda suka rayu.
A kudancin k'asarma Alhmdllh komai ya lafa, sai kuma yad'a 6arnar da akayi a kafafen yad'a labarai Na waje dana gida, hanyar samun kud'i kuma ta bud'ema 'yan jaridu.
Jami'an tsaroma sai fankama suke, hakama 'yan siyasa abin kamfen dayima jam'iyya mai mulki gugar zana tasamu, muma kammu talakawan ba'a barmu abayaba, sai zabga kalaman ALLAH wadai muke ga gwamnati batareda dubi da mune muka haddasama kanmuba.
K'asar duk tabi ta rud'e da surutai marasa kan gado, kowa k'abilarsa da addininsane mai gaskiya, babu mai yarda a jingina masa koda laifi d'ayane, masu tsoro kuwa harsun tattara inasu-inasu sunma k'auyikansu da yankinsu saukar angulu, Na kudanci sunkoma yankinsu hakama arewaci, kowa 'yancin fad'ar albarkacin baki dayake ik'irari dashi tasashi kasa yima k'asar k'yak'yk'yawan fata, saima k'ara Neman hanyar kare kai Dan aganin wasunmu bata mutuba rufa tayi, akwai sauran yak'i agaba, kowa yakoma gidane yasawo sulken yak'i.
A 6angaren manyan k'asar kam d'if kakejinsu, kaikace babu sarakunan gargajiya ak'asar, malaman k'asar da pastors sunyi gum da bakunansu basa cewa komai sai sunsami ke6ancewa da mabiyansu a k'uryar lunguna, wasunsu suzama masu tunzura matasan da nuna musu sune masu gaskiya, k'alilan dasuke Na kirki sune masu tsawatarwa da nuna kuskure da illar abinda yafaru.
Kowa yazama d'an jari hujja, mutuncinsa kawai yake k'ok'arin karewa da yankinsu, zancen nuna gaskiyar muzama k'asa d'aya al'umma d'aya son zuciya yasa mungina rami duk mun binne furucin bakunanmu, mai k'ok'arin so a gyara saikaji jama'ar yankinsa sun rad'a masa suna *MARA KISHIN KAI*.
humm kai da shi mai tada husuma komai yanka albashin had'a rikice-rikice wanene mara kishin kai aciki?.
Wlhy idan bamu gyaraba wankin wula tana dab dashirin kaimu tsakiyyar dare mai duhuwar dazamu kasa koda ganin tafikan hannunmu.
Da ni da kai duk 'yan k'asane, munada zarrar kawo canji koda ta hanyar tsarkake zukatanmu ne da gyara halayyarmu.
Ba gwamnati da shuwagabanni ne kad'ai ke buk'atar gyaraba, hatta damu talakawan masu ik'irarin Neman gyara da hura haccin sai an gyara d'in muna buk'atar gyara kanmu.
Taya kakeson k'asarka tazama mai tsafta ta hanyar jagorancin shuwagabanni amma kai talakan k'asar kullum kana tebirin 6arna.
Bakasan darajar zuminciba, bakasan muhimmancin addininka da koyi da k'yawawan aiyyukan daya kawo makaba, bakasan wace k'yautatawa yakamata iyalanka su samu daga garekaba, balle ajega zancen makwafta da abokan zamanka Wanda addini ya banbantaku, baka Neman abincinka ta hanyar hallal balle kaciyar da iyalanka suzama nagartattu masu tsafata, kullum harshenka yana kan aibanta 'ya'yan jama'a da zund'en matan mutane, sai hassada da ganin k'yashin cigaban d'an uwanka fal ruhinka.
Kina mace kinkasa son abokiyar zamanki balle 'ya'yanta, kullum zuciyarki cik'in k'yashi da bak'inciki take idan mijinki ya k'yautatama iyayensa da 'yan uwansa, kinkasa nutsuwa wajen bautama ubangijinki amma kece sahun gaba agidan uwar gulma ko gidajen Malam tsubbu da bokaye anufin Neman taimako, burinki kullum ace kece sama dakowacce mace a6angaren k'yale-k'yale da kayan k'awa Na duniya, buri dason burga yahanki fad'ama mijinki gaskiya yayinda kikaganshi bisa karkatacciyar hanyar dazata iya kaiku wuta ke da shi da 'ya'yan dakuka haifa,
Kana matashi amma kullun burinka akan kayi kud'i kake, ka auri mace ajin farko a k'yawawa kasaka acikin gidanka Na k'awa danta zame maka fure, babu ruwanka da tarbiyyarta ko addininta balle nasabar data fito, jin kanka kake on top kai yanzu kafara zamaninka mutuwa da sauran tak'i a tsakaninku da ita, baka ganin kowa da gashin arzik'i saboda kai ka iya kuma karanka yakai tsaiko, kasani sai dai ka sanar babu mai sanar da kai saboda kasha boko ka k'oshi, da ance kayya kaine sahun farko a masu d'akko makami afara y'ar rere tsakaninka da jama'ar gari, aganinka kai dai-daine bakada matsala da duniya, koyanzu kabarta hankalinka a kwance tunda baka haihuba.
Wlhy muji tsoron ALLAH, mufara tuna komu su waye kafin gangar shaid'an tamana tasiri a zukata mu kwashi filin rawa muna tangad'in maye dajin kanmu can k'ololuwar sararin samaniya muna yawo cikin giza-gizai.
Kowa yaje inda zashi yadawo akwai rana d'aya tak da za'a baka littafin ayyukanka a hannun haggunka ko damarka, wannan za6in yarage naka.
Duk nau'in shed'ancin dakakeji ka gawurta tarihi ya nuna anyi wani kafinka, kuma anshafeshi yazama labari tamkarma bai zoba.
To kaikuma asuwa da naka tak'adarancin bazai zama labariba harma ayo Wanda yafika k'warewa.
Abin mamaki dukfa da wannan halayen namu amma mukeson samun shugabanni nagari, bayan ALLAH yafad'a mana, dai-dai sugabanninmu dai halayenmu kuma.
Tab d'i, ashe kam da sauran kallo😨🤔.
Kayi nazari, kiyi nazari, nayi nazari, muyi nazari domin gano illolin takubban shed'anarmu komunada rabon gyarawa kafin randa mala'ikan mutuwa da rundunarsa zasu zagaye sashinmu Dan k'udundunar ruhinmu zuwaga Wanda yayka yayni dama duniyar da abinda ke cikinta.
ALLAH ka ganar damu gaskiya koda bazata mana dad'iba, ka tasirantar da ita agaremu, mu kar6eta mukumayi aiki da ita danmu samu komawa ga ALLAH cikin salama😭🙏🏻.



_____________________________

"Wai kana nufin bazakayi break fast ba agida dear?".
Gyara zaman hular kansa yayi, sannan ya d'auki turare ya fesa, kafin ya juyo sosai yana fuskantarta, cikin sassanyar muryarsa yace, ''sorry my neesa, wlhy ina saurine, dan inada meeting a da lectures k'arfe 12, gashi inason shiga naga jikin baba, nakumaje kasuwa, yau kayanmu zasu iso. Please kimin afuwa mana my sweet".
Ya k'are maganar da matsawa kusada ita ya rungumeta a jikinsa.
Bakinta ta d'an turo kad'an, cikin d'aurewar fuska tace, " kai dai kanason ganin Amatallah kawai, babu wani duba baba".
Lumshe idanunsa yayi yana guntun murmushi, ya d'agota daga jikinsa yana mai zuba idanunsa kan k'yak'yk'yawar fuskarta datasha kwalliya.
"My neesa! kina ganin nayi laifi kenan koda ganin Khadija zanje? a tunanina koda babu aurena a kanta ta cancanci irin wanman kulawar daga gareni, karfa ki manta jinin brother d'inace ita. a zatona kodan halin da yarinyar ta tsinci kanta ta cancanci kubar mata ni gaba d'ayama ai".
Sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login