Showing 75001 words to 78000 words out of 104242 words

Chapter 26 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16057

breakfast ga......."
Baima bari Takai k'arsheba yajawota saman gadon sosai "yo karsuci breakfast d'in Indai saikin sauka kinyi musu, ai idan wani ya ganki a k'asa saidai nanda 12 Na rana", ya rungumeta a jikinsa " kinga muyi barcinmu ma".
"Uncle!" tafad'a tamkar zatayi kuka.
Hannu yasaka kan la66anta yay mata Alamar zip🤐.
Shiru kuwa tayi Dan dolenta, wani salo yafara mata, ahankali tafara lumshe idanu Dan sak'on Na shigarta, jin yana neman canja hanya sai hankalinta yatashi (karfa Uncle yace zai k'arayine nashiga uku ni Khadija), shiru tayi tahau barcin k'arya, dukda zuciyarta Na bugawa da sauri-sauri saboda tsoro, a sannu dai har barcin gaskiya ya kwasheta, dama barcin takeji dauriyace kawai yasata son saukar dakuma kunyar aganta da safe tafito daga 6angarensa.
Jin shiru da saukar numfashinta ahankali bisa k'irjinsa yasashi lek'a face d'inta, goshinta ya sumbata Yakuma rungumeta da k'yau yana murmushi da jero mata wasu addu'oin fatan alkairi zuciyarsa, shima babu jimawa barcin yay gaba dashi.

Babu wanda ya nemeta acikinsu Anty maijidda, saima hidimar d'aura breakfast dasukeyi abinsu.
Garama Aneesa tasoyin magana saikuma tayi shiru.
Dasuka kammala breakfast d'inma Anty maijidda tace Nazeefa ta d'auka takai sama.
Har Nazeefa tashiga ta ajiye bataji koda motsinsuba, hasalima k'ofar bedroom d'in arufe take. 'Yar dariyar mugunta tayi kafin tafara gyaran falon nashi, a zuciyarta kuma tana addu'ar ALLAH yasa an gamune, sai zabga murmushi takeyi harta kammala, ta saka turaren wuta sannan taja musu k'ofar tafice abinta.
A k'asama ta iske su Anty maijidda sunata gyaran gidan, an kora yaran duka waje, 6angaren Amatallah tashiga, tayi mamakin yanda taga mirror d'in a hargitse, batace dai komai tagyara mata ko'ina, ta saka turaren wuta sannan tarufo tafito.
Bayan sunyi breakfast kuma suka shiga kujiba-kujibar d'aura girkin suna da duk abinda za'a buk'ata, zuwa lokacin kuma su Anty Mariya yayyen maijego sun dawo, Dan da daddarennan duk suka tafi gida, yanzn kuma suka dawo Dan kama girki.

*****

😀
Koda Amatallah da Uncle basukai 12 ba kamar yanda Uncle yay fata sun kai dai 10 suna barci abinsu, Amatallah ce tafara farkawa,bayan tayi addu'ar tashi barci ta kalli yanda ta kanannad'e jikin Uncle, kai kace zata komane jikin nashi, ta tsurama fuskarsa ido tana kallo, Uncle yanada k'yau dai-dai misali, kuma yanada haske babu laifi, amma bak'ine, gemumsa da zagayayyen gashin bakinsa sune suka k'ara masa kwarjini da cikar haiba, hannu takai a hankali ta shafa gemunda tadad'e tana kwad'ayin ta6ashi saboda burgeta dayakeyi, masha ALLAH tafad'a a zuciyarta, saboda wani laushi da santsi ga k'amshi da gemun keyi, (ba dole yayi laushiba, kud'in da gemunnan ke lashewa aiba Na wasa bane).
Tunda tafara ta6a gemunsa ya farka, kokad'an bashida nauyin barci, amma bai nuna mata yatashiba, danya kula tanajin dad'in shafa gemun nasa.
Ringing d'in wayarsa yasaka ta janye hannunta da sauri, tayi k'ok'arin janye jikinta amma yak'i bata damar hakan, kallonta takai ga agogon d'akin kafin tadawo da kallonta kansa tana zare idon tsorata da mamakin yanda lokaci yatafi, amma takasa magana bare ta tadashi.
Aka kuma kiran wayar, batareda ya bud'e idoba, baikuma saketaba yamik'a hannunsa d'aya ya d'auka, kad'an ya kalli screen d'in wayar kafin yad'aga yasa a kunne yana fad'in "Assalamu alaika".
Daga can Alhaji Sabi'u yace, " Alahji Muhammad lafiya naji muryarka haka?".
Murmushi Uncle yayi sannan yace, "a barci ka tadani".
" barcifa kace? wasa ko gaske?".
"Da gaske" yay maganar yana kuma k'ank'ame Amatallah kamar za'a kwaceta🤭.
"Lallaikam, kaiko wane aiki ya hanaka barcin dare? Saikace dakai ake abincin sunan".
'Yar dariya Uncle yayi, kafin yace, " mutumina bazaka ganeba ne kawai, yanzudai miya faru?".
"Uhhm nakirake dama naji kokana kasuwa, amma badamuwa, idan kafito kakirani inason mu had'une".
"OK, saina fitod'in".
"An rad'a suna ko? Gashi ko 'Yar walima bamu had'aba".
"hhh Alhajina kainane yad'au zafi, shiyyasama ko maganar walimar banyiba, mata kawai suyi nasu, mu munyi namu da asuba ai, baby taci sunan Aminatu".
" Masha ALLAH, ALLAH ya raya manasu akan sunna, ya albarkaci rayuwarsu, yasa masu mana addu'ane bayan k'asa ta rufe idonmu".
"Amin ya rabbi. Insha ALLAH zuwa 12 zan sameka a office kawai".
"okay babu damuwa saina ganka".

Kallonta yayi bayan ya kashe wayar, ta lumshe idanunta dan bataso su had'a ido.
Murmushi yayi yashiga zagaya yatsansa kan la66anta, murya k'asa-k'asa yace " 'yammatana da guduwa zakiyi ki barni kenan?".
Wayyo ALLAH, tafad'a a zuciyarta.
Jin bata amsa mishiba ya yunk'ura yatashi da ita a jikinsa, "shikenan tunda bazakiyi maganaba, tashi muje namiki wanka kar 'yan suna sufara jajenki".
Babu shiri ta ware manyan idanunta kansa.
Ido d'aya ya kashe mata😉, tai azamar janyewa.
Sauka yayi itama yakamo hannunta zai saukar da ita ta tirje tana langa6e kai, " please Uncle zanyi da kaina Dan ALLAH".
"ban yardabafa my best, dolene nakuma gasaki karkije kina tafiya agane yau......"
Hannu tasa ta rufe masa baki tana cewa "kai Uncle".
Hannun ya janye yana dariya, " to naji bazan fad'aba, muje Na had'a miki ruwan kawai".
Batak'iba wannan tabishi, yahad'a mata dad'an zafi yace "ki daure karki cuci kanki, kisan yau taron jama'ane agidan kinji".
Ta d'aga masa kai idonta a k'asa.
Kumatunta ya sumbata yafice.
Bakuwa ta cuci kan nataba tagasa ko ina yanda yakamata, dan bawani zafi sosai takejiba dai mai cutarwa, tundama Uncle yamata gashi Na musamman da daddaren, amma tanajin jikinta ko'ina yana ciwo, gakuma wani canji Na musamman dukdai ba yanda tasaba jiba.
Tadad'e tsaye tana kunyar fitowa da guntun towel d'insa dake bathroom d'in, amma babu yanda zatayi ganin time nakuma tafiya a banza tafito a takure.
Babu kowama a d'akin, hakanne yasata sakin ajiyar zuciya, kayanta tagani a saman gado, tayi mamaki sosai, amma haka ta d'auka a gaggauce ta shafa mai da body spry, sannan tashirya tsaf, sosai kayan suka mata d'as ajiki.
Bawata kwalliya tatsaya yiba, tana cikin shafa fauda yashigo da sallama, da alama shima wankan yayo a d'ayan d'akin dake 6angarensa inda Nazeefa ta zauna sanda yana Dubai.
" hummm my Heartbeat Ashe nasan kala nima, kinyi k'yau kamar Na zauna naita kallonki abuna".
Murmushi tayi tace "ngd Uncle".
Shima murmushin yayi yahau shirinsa, ko sau d'aya Amatallah bata kalli inda yakeba.
" my best zoki za6amin kaya ko".
Tad'an kallesa kafin tace "Uncle nikuma?".
Gira ya d'aga mata kawai.
Mik'ewa tayi tanufeshi, danta tuna (maganar Anty furera). Yana tsaye gaban Waldrop d'in, hakanne yasa yad'an matsa tashigo gaba, kallon kayan ta tsayayi, tsarin komai ya birgeta.
Jitai ya sak'alo hannunsa kan cikinta ya rungumeta tareda d'ora kansa akan kafad'arta, itako yazatayi da wannan lamari Na Uncle....
Maganarsa ta katse mata zancen zucin datakeyi.
" kifa za6amin kalar naki ehe".
Murmushi tayi ta jawo wata sky blue d'in shadda d'anya, tad'an juyo ta kalleshi da nuna masa kayan. Wuyanta ya sumbata yana fad'in ke tadabance my best! kamar yanda komanki yake nadaban".
Taji fad'in kalaminsa sosai, Dan haka ta danne kunya ta taimaka masa ya shirya, cikin janfa da wando Na kayan, rigar tawuce gwiwarsa da kad'an, amma sunmasa k'yau ainun, saikace wani d'an 30+ (😆...lol).
Tana saka masa ma6allin gaban rigar suna murmushi, tagama tafesa masa turarensa.
Yace "saura hula my best".
Murmushi tayi ta za6o masa derk blue acikin hulinan data gani birjit. A mamakinsa saiyaga tana karin hular..... (Abinda nakasa iyawa🤭 Ama... Zanzo ki koyamin narigama boss d'ina nima😂) tsayawa yayi kallonta cikeda birgewa. Bayan tagama tamatso kusadashi, yafita tsawo, danhaka yad'an duk'o ta saka masa, tareda dai-daitata da k'yau.
Kallon kansa yayi a madubi yana murmushi, " my best ina kika iya Karin hula haka?".
"Uncle wajen baba mana, tun ina masa yanacewa baiyiba harna dage Na iya kala-kala".
"Masha ALLAH my best!" Yafad'a yana kuma kallonsu a madubin, tabbas yasha ganin karin hularnan akan brother d'insa, ringumeta yayi yashiga bata masu zafi....(😘 kundai gane).
Saida tasha dad'ad'an kalamai sannan suka fito falo, dakansa yabata brekfast d'in dasuka gani a falon.
Bayan sun kammala kuwa babu yanda baiyiba su fita tare tak'i, yamata kisses yafice tana masa addu'a.

Murmushi tayi tareda shafa fuskarta tana fad'in my Uncle I love you so much, lallai ka cancanci kowacce mace ta haukace a kishinka, hummm wani sirrin saidai *RUHI* kawai".
Dahaka ta koma bedroom d'in ta gyara, ta tartare kayanta a ledar ta ajiye gefe. Saidaifa wlhy bazata iya fitaba, to dawane idon zata kalli jama'a?.
Nazeefa takira wai Dan ALLAH tazo.
"Nazo namiki mi? yarinya kima sakko idan zaki sakko, ai gidan babu mutane sosai".
" please Anty Nazeefa, ALLAH bazan iyaba inajin kunya".
"Meyasa baki biyo mijinkiba, kinga shi gashina yanata gaisawa da dangi, kuma mai hotoma ya Jabeer ya kawo, gakuma 'yan jos nan su Anty Sadiya sun iso yanzunan".
" da gaske Dan ALLAH Anty Nazeefa su Anaty furerane?".
"ALLAH kuwa, gasuma Suna gaisawa da Yaya a falonki........."
Ai tuni Ama....ta manta dawata kunya bare abinda yafaru da ita, dukda tanad'anjin zafi hakan bai hanata sauka dad'an guduntaba, wannan yasa duk kallon k'urillarka bazaka gane mitake cikiba. Ta wuce su anty maijidda Afalo.
Duk dariya suka saka mata, har Aneesa kasa daurewa tayi ta dara, (a ranta tana kuma jinjina tsantsar k'uruciyar Amatallah).
Anty maijidda tace "k'uruci kenan dangin hauka".
Nanma dariyar dai akayi, kishiyar Anty maijidda tace nikam tana birgeni, ko kad'an batada damuwa Amatallah wlhy".
Aneesa tayi murmushi tace, " gaskiya tanada hak'uri, tunda babu mai cewa tamasa wani Abu Mara k'yau a gidannan wlhy, ALLAH dai yacigaba dabamu zaman lfy".
Gaba d'aya akace amin.
Kowa yasan Aneesa tanada kishi, amma macece mai fad'ar gaskiya da mutunci idan taso, gashi bata iya wulak'anta dangin mijiba, ita kowa natane, duk sharrinka wlhy bazakace kazo gidan ta wulak'antaba, ko Fateema datake 'Yar uwarsu jininsu iyaka dai kenan, (kishine dai kam ba'a cewa komai a wajen Aneesa😂). amma kam tanada fada sosai wajen dangin mijinta dana kishiyarta, (zatayi kishi kam dake, amma danginki komai a mutumce)................✍🏻








🤩👎🏻

One luv my sweet Fan's







*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu_*😭🙏🏻
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 32_*
____________________


Amatallah Na shiga ta cikukuye Anty Sadiya dake kujerar farko, "fad'i take oyoyo anutys d'ina, saikuma tasaki Sadiya takoma kan Anty furera da Asiya.
Uncle dai murmushi kawai yake zubawa, yaji dad'in ganin Amatallah a farinciki, kullum haka yake fatan ganinta, bayason ta yawaita kukan maraici.......
Maganar Anty furera ta katse masa tunani.
" uch Amatallah, wai yaushe zakisan kin girmane?".
"Babu rana Anty furera". Amatallah tafad'a tana dariya, suka had'a ido da Uncle, gira yad'an d'aga mata.
Ta kauda idonta tana murmushin itama.


Humm yau Amatallah fa ba'a magana, tana nanik'e da Aunty's d'inta sunata shan hira dabata labarin jos.
Suma sunji dad'in yanda sukaga ta murje tayi k'yau, hakan ya nuna musu hankalinta ya kwanta, Alhaji Muhammad yarik'e amanar d'an uwansa, dukda sunga kamar batada walwala sosai, amma jin dad'in ganinsu Na k'ok'arin danne hakan, babu Wanda ya tambayeta damuwarta cikin su, tunda sunsan zaman aure saidai hak'uri, komin San da kukema juna dolene wataran a k'untatama juna, bakomai ake samu 100% ba.
Ansha hotuna kafin Uncle yafice sabgar gabansa.
Ita ta rakasu d'akin maijego Uwargida, taci gayunta cikin had'ad'd'iyar shadda popul, hakama jaririyar anmata gayu, Ummita tana nanik'e da ita, saikuma wasu daga cikin danginta dake cin abinci, wasu kuma hirarsu sukeyi.
Duk suka gaisa a mutunce.
Fateema ta kalli yanda Amatallah tayi k'yau cikin kwalliyarta, k'ok'arin danne kishinta tayi kamar yanda ta saba, tayi murmushi tana fad'in Anty yara kinyi k'yaufa, kamarma kece mai jegon".
Murmuahi Amatallah tayi, ta 6oye fuskarta jikin Ummita dake kan cinyarta tace ''kai Anty kecema ai sarauniyar k'yau d'in, kinganki kuwa?".
Dariya wad'anda ke kusadasu sukayi, abin kuma ya birgesu tamkar ba kishiyoyiba.
Aneesa tashigo itama ta cakire cikin less jaa, tayi k'yau sosai, fleets takawo saboda bak'i, itama Fateema saida ta tsokaneta wajen yaba kwalliyarta.
Aneesa ma ta danne zuciyarta da kishi tayi murmushi tana fad'in "lallaima Umman yara, bakiga kankiba kenan keda Antyn yara?, karfa Ku rud'a mana Abbun Abulkhairi wlhy".
Sosai akeyin dariya a d'akin, kasancewar Aneesa a tsaye take sai kowa yaji maganar datayi.
Sosai suka birge kowa, (har nimafa😉, sainaji ina sha'awar kishiya amma ta yini d'aya🤭😂lol).
Cikin girmamawa Aneesa tafara gaida su Anty furera.......
Amatallah ta katseta dafad'in " Anty Aneesa zafasuzo Ku gaisa".
Murmushi Aneesa tayi (saboda taji dad'in wannan girmamawa, damafa Aneesa akwai son girma🤭😆) tace, "to shikenan, bara naje Na jiraku, dama an bani sak'o nabaku keda Umman yara".
Atare sukace to, Fateema ta kalli Aneesar tana fad'in mu taso kenan?".
"A Ku k'arasa tu kunna, nima akwai abinda nakeyi."
Okey.

Su Anty Sadiya sund'an dad'e a 6angaren Fateema kafin suje 6angaren Aneesa ma, anan Aneesa ta had'a musu abinci, takumace anan zasuyi sallah.
Godiya sukai mata da k'ara yaba kirkin kishiyoyin Na d'iyarsu Amatallah.

Aneesa da Fateema da Amatallah kam sunacan saman Uncle, Aneesa tasanar dasu cewa Uncle yace zaizo da bak'ine wai da la'asar, " yakuke ganin zamuyi kenan? Yace yakiraki baki d'agaba Antyn yara".
Amatallah tace, "Na manta wayarne a d'akina mukaje 6angaren Anty".
" okey, yanzu miye shawarar abinda za'a tanadar musu?".
Fateema tace, "kai Abbun Abulkhairi ma dai akwai kwak'ule-kwak'ule, yanzu Dan ALLAH d'azun dazai fita ba'a gabanki Na tambayi kozaiyi bak'iba a jiye musu abinci?, amma yace a'a". Tayi maganar tana kallon Aneesa.
" to yazamuyi umman yara, kinsanshi dai ai, yanzu kawai mu nemi solution, Dan yace bak'infa Na kunyane. Antyn yara bakice komaiba fa?".
Murmushi Amatallah tayi, "to Anty mizance, Abinne Na Uncle saishi, yanzu kawai inaga ayi jaloff d'in shinkafa mana, ahad'a da tuwon shinkafa ko semo...., tunda ga masa za'a kawo daga idansu Innani kamar yanda naji su Anty maijidda nafad'a. Kobaiyiba?".
" yayi kuwa sosai wlhy, akwai zo6oma, dukda muma munada namu mutanen, sai a d'an d'iba kad'an".
''Shikenanto, dama yace shehu zai kawo drinks da ruwa asaka musu k'ank'ara". Cewar Aneesa kenan.
Amatallah tace, "to inhakane ahad'a da kunun aya".
Fateema tace, " amma har ayi? Yanzufa biyu saura, kumafa 4 yace?".
"Walhy har ayi Anty, aigasu Anty Nazeefa ga Asiya duk zasu taimaka mana da aikin".
" to shikenan, gasuma Ramla nan, aikin mi sukeyi, duk saisu had'u ai su taimaka muku, (k'annen Fateema ne suma, amma duk da aurensu).
Sund'an k'ara shawarta abinda zasu k'ara dashi sannan suka sakko k'asa.

Da taimakon su Nazeefa suka had'a abinci da abinsha masu k'ayatarwa, harda suyar kaji, abinka da hannu dayawa dandanan asuka kammala, aka had'a komai a falon bak'i dakecan waje, komai yayi babu yanda za'ayi suji kunya kuma, harda alalan dasukayi Na jama'arsu duk suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login