Showing 60001 words to 63000 words out of 104242 words

Chapter 21 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16037

dajin dad'in yanda kukema mahaifina addu'a, ALLAH yabar k'auna, kuma kunan araina daram, shiyyasa nake daurewa nayi typing danna sakaku farin ciki wlhy😄😘._




🤩👎🏻

One luv my sweet Fan's🥰





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


______________________
*_Number 24 and 25_*
______________________

Ta6a k'ofar yay yajita arufe dan haka ya kwankwasa, da k'wankwasa k'ofar da bugawar zuyar Amatallah lokaci d'aya suka kasance, dan tabbas tasan shine, tunda tajiyo hayaniyar yaransa suna ihun murnar dawowarsa.
K'ara bugawarsace tasakata mik'ewa dole tanufi k'ofar tana k'ara gyara zaman siririn gyalenta da k'yau. ta bud'e k'ofar cikeda fargabar k'arfa fama kanta gwiwa, sai dai me suna had'a ido da boss jarumtar ta tafara k'ok'arin su6uce mata, matsawa tayi yashigo yana sa6a babbar rigarsa a kafad'a idonsa a kanta yana binta da kallon k'urulla, gani yayi kayan sun kuma k'ank'antar da ita, amma tayi k'yau sosai.
Zama yayi a kujerar kusa dashi, wadda ta kasance 2seaters, Amatallah kam tuni ta zube a k'asa tana gaisheshi cikin d'an rawar murya, dan dukkan ALWASHIN ta (Ummu Aysha) dataci bayan barowarta makaranta zuwa yanzu saitaji kwarjininsa ya fatattakeshi.
Bai amsa gaisuwarba sai kiran sunanta dayayi cikin sassanyar muryarsa.
Ta d'ago manyan idanunta tad'an kalleshi, saikuma ta maidasu k'asa tana cigaba dayin wasa da yatsun hannunta.
Yatsun hannun yabi da kallo, wad'anda haryau rad'am suke da zanen jan llalli da 6ak'i, yasaki guntun murmushi mai sauti Wanda har Amatallah d'inma saida tajishi.
"My best zonan". ya fad'a yana mik'a mata hannu kamar wata tata🙇‍♀.
Batayi musuba tamik'e kanta a k'asa taje inda yake, tana k'ok'arin zama a k'asa yaruk'o hannunta tareda jawota ta fad'o saman cinyarsa.
A fili tace, "ya sallam!!, Uncle Sorry". tayi yunk'urin mik'ewa, a zatonta ko asfa kuskure tafad'a kansa. illahirin jikinta duk rawa yakeyi, dan tunda uwarda ta haifeta duniya hakan baita6a faruwa da itaba ko'a mafarki, dukda cud'anya cikin k'abilu daban-daban da Amatallah tayi hakan baisa koda kuskure wani namiji yata6a rik'e hannuntaba bayan mahaifinta da Uncle M.A, shima kuma saida igiyar aure ta tabbata kansu sannan yafara mata hakan, sai dai kuma idan ta mantane.........
Kuma mannata dayay da jikinsa yana sauke sassanyar ajiyar zuciyane ya maido Amatallah daga tunaninta, " Uncle please ". tafad'a tana kuma yunk'urin kwace jikinta.
A cikin kunnenta yace, " aji tausayin bawan ALLAH mana my heartbeat".
Tsigar jikin Amatallah Ce tatashi yarrr tareda yamutsawar 'yan hanjin cikinta Na tsoro. tafara tuno maganar Fa'iza, ta girgiza kai a zuciyarta tana fad'in bazan iyaba Fa'iza, kimar Uncle tawuce zaton kowa a garen..........
Batakai k'arsheba taji wani bak'on al'amarin dayafi Na zama cinyarsa girgizata, rufe idonta datayi yabama Uncle damar k'arema fuskarta kallo har zuwa la66anta da sukasha lipstick sunata k'yalli, kasa hak'uri yayi kamar yanda yaso, sai kawai ya manna bakinsa akai.
Saida ya tabbatar yashanye lipstick d'inan tas sannan ya janye bakinsa.
Ai da gudu Amatallah ta sauka daga jikinsa tashige bedroom d'inta, bataja birki a ko inaba sai toilet d'inta. jingina tayi da k'ofar tana hakkin gudun datayi da sauke numfashi, ga hawaye sha6e-sha6e a face d'inta.
Shikam tana barin jikinsa yabita da kallo, harta shige sannan yay wani k'asaitaccen murmushi maihad'eda guntuwar dariya, shikansa yana mamakin kansa akan zurfafa cik'in k'auna da begen d'iyar cikinsa, abinda ko'a mafarki bai ta6a wanan tunaninba, hargashi yau takaishi ga rashin hak'uri ya aikata abinda shi Kansas kunyar Kansa yakeji, ya lumshe idanunsa yana furzo iskar bakinsa dawani murmushin dayake k'ara fidda ainahin k'yawunsa da kwarjinin kamala da ALLAH ya azurtashi dashi. ganin bazata fitoba kusan mintuna uku yatashi ya fice.
A falo Yakuma iske yara suna kallon Cartoon Na larabci, sun maida hankalinsu sosai akan TV, dan haka baiyi maganaba yashiga 6angaren Aneesa.
Zaune ya taddata a fallo, sai dai kallo d'aya yamata yagane tasha kuka, zama yay kujerar dake kallonta, cikin tsare gida yace, "lafiya dai ko?".
Maganarsa takuma tunzuro Aneesa, tawani turo baki gaba tana kuma d'aure fuska itama, a tsiwace tace, " wai minamaka kake wulak'antani irin haka? miye laifina danna soka? kokuwa wannan shine salon sakayyar dazakamin bayan karaboni da k'asata da iyayena......."
Wani banzan kallo yamata, Wanda yasata 6ame bakinta babu shiri, tasan halinsa sarai yatsani raini da rashin tausasa harshe, amma itama rantane yagama 6aci akan abinda yamata da safe bai isheshiba yak'ara mata wani yanzun.
Maimakon yabata amsoshin maganganunta se cewa yayai "miya had'aki da Amatallah da safe?".
Ranta Yakuma 6aci, shaid'an Na angiza zuciyarta tace, "Woow! dama munafuncina akayi a wajenka shiyyasa kake wulak'antani? itakuma da salon data shigo gidan kenan? kaima miji munafuncin kishiyoyi...."
''Aneesa!! Karfa kibari fushina yakai k'arshe a kanki, ki sanarmin abinda Na tambayeki". a fad'ace yayi maganar, amma hakan bai hana muryarsa fita cikin sanyiba da nutsuwa.
Dukda Aneesa takai k'arshe a 6acin ranta hakan bai hanata tsorata da Shiba, tasan halinsa sarai, Duk abinda kaga ya tanka a Kansa, to lallai ya d'aukeshi da girma, amma komi matarsa zata masa Na 6acin rai bata Isa ya mata ihu ba, saidai yayi abinda kema zai bak'anta ranki cikin ruwan sanyi, rabonta dataga irin wannan Fushun a taredashi tun fad'an k'arshe dasukayi da Fateema lokacin daya had'esu gida d'aya, dan lokacinma dukansu gida yace su tafi saiyazo, saida babansa ya hana sannan ya hak'ura saboda gaya masa da sukaje sukayi.........
Tunaninta ya katse lokacin dataga yamik'e yafice bai sake cemata komaiba, binsa tayi da kallo ranta Na suya da mamakin Amatallah, lallai zata gyarama yarinyarnan zama a gidannan, wato ita kuma NATA salon had'a fad'a da miji ko, idonta harya kai tsaurin haka, ai ko tayi Na farko tayi Na k'arshe, zata shayar da ita mamaki.




Nace ''hummm".


Yanzunma yaran basu luraba harya haye samansa, ransa gaba d'aya a 6ace yake da Aneesa, dan harga ALLAH bazai d'auki k'untatama marainiyar ALLAH ba, mahaifinta yabashi itane dan ganin zai iya rik'e masa ita, bakuma zai yuwu wani ya k'untata ta yabariba koda wanene wlhy. kayansa ya cire yashiga wanka, koda yafito k'ananun kaya yasaka bak'in dogon wando da farar t-shirt mai gajeren hannu, yad'an fesa turare yadawo falonsa, saida yabud'e freight ya d'akko ruwa ya d'auki kofi da aka jere a wata 'yar glass drawer sannan ya zauna saman kujera, koda yasha ruwan saiya zame ya kwanta tareda lumshe idanunsa, ba barci yakeba tunanin tattaunawarsu da Alahaji sabi'u yakeyi, dakuma yanda suka tsara abubuwa, ahaka har tunaninsa yakoma kan rayuwar data shud'e, kewar Brother d'insa tadawo masa sabuwa a zuciya, ayanzu abubuwa dayawa suna damun zuciyarsa amma babu Wanda zai sanarmawa, yashare 'yan kwallan dasuka taru masa a gefen ido kafin yakai dubansa ga agogo, 9:34pm, wayarsa ya jawo da zummar kiran Fateema saikuma ga kiranta ya shigo, guntun murmushi yayi sannan ya d'aga, saida tamasa sallama ya amsa sannan tace, ''najika shirune Nurrina, koka fasa ne?".
d'an huci ya furzar, kafin yace ''a'a my tee...., yara fa?".
"Gasunan harsun gaji da jiranka sun kwanta saboda school".
" oh sumin afuwa, tunda sun kwanta kuzo kawai".
"Okey". kawai tafad'a ta yanke wayar.
Amatallah ya kira, tana ganin kiransa gabanta yafad'i, a tsorace ta d'aga wayar, muryarta har zuga take, kansa kawai yad'an girgiza, yace, " khadeeja kin kwantane?".
Sunan daya kirata dashine yasata d'anjin sassauci a zuciyarta, danta kula sai akan muhimmin Abu yake kiran ainahin sunan nata. a sanyaye tace, "a'a karatu nakeyi".
Murmushi yayi mai sauti yace, " okay, tom kizo samana yanzunnan". bai jira amsartaba ya kashe kiran.
Hannu tasa aka tana fad'in "nashi 100 ni Khadija, mikuma zanma Uncle a darenan?". maganar Fa'iza takuma fad'o mata a rai. _inhar yau ya buk'aci ki kar6i kwananki wlhy ki kar6a, kuma ya buk'aceki karki bijire masa, yanda yanzu ake yayin mutuwarnan._ da sauri tace, " bazan iyaba wlhy Fa'iza, bazan iya had'a shinfid'a da Uncle ba, Na shiga uku ni Khadija, wayyo Ammina".
Yanda take safa da marwa a tsakar falon saita bani dariya da tausayi.
A can kuwa Uncle itama Aneeaa ya kirata, cikeda tsoro ta d'aga, "ki sameni a sama". Kawai yace ya yanke wayar.
Takuma tsorata, dan haka tatafi sukuku zuciyarta Na nadamar abinda tamasa d'azun.
Kusan a tare suka iso da Fateema, dan zaman Fateema kenan tashigo, murmushin dayakema Fateema tuni ya d'auke daga fuskarsa ganin Aneesa, bayan ya taimakama Fateema ta zauna kusadashi ya maida idonsa ga TV batareda ya kalli ko sashen da Aneesa takeba.
duk da Fateema ta lura da canjawarsa hakan baisa ta fuskanci wani abububa tsakaninsa da Aneesa.
Kusan mintuna biyar da zamansu babu labarin Amatallah. Wayarsa ya d'auka yakuma kiranta.
tana d'agawa da sauri tace " ganinan zuwa Uncle toilet na shiga".
Baice komaiba ya yanke wayar.
K'irjin Amatallah Na dukan d'ari-d'ari ta yayi sallama a k'ofar falon.
Su duk suka amsa banda Aneesa.
"Shigo mana". tajiyo muryar Uncle.
Kanta a k'asa tashigo, dan duk taga slifas d'in su Fateema a k'ofar falon. maimakon ta zauna a kujera kamar yanda sukayi saita zauna a k'asa.
Fateema tace, " haba Amatallah! tashi ki hau kujera mana".
"A'a Anty, nanma yayi, ina yini".
Amsawa Fateema tayi cikin fara'a dason k'ular da Aneesa.
Aiko ta shak'a🤣.
Amatallah ta kalli sashen da Aneesa take tace, "ina yini?".
Shiru Aneesa tayi tak'i amsawa tamkar batajiba.
Wata uwar harara Uncle ya maka mata, babu shiri ta amsa gaisuwar.
Amatallah kam baki ta ta6e, tad'an saci kallon Uncle taga shima itad'in yake kallo, amma fuskarsa babu walwala.
Kauda idon tayi azamaryi tana gyara zamanta sosai.
Kusan mintuna biyu yayi gyaran murya sannan yamusu sallama.
Atare suka amsa masa.
Addu'a yayi kafin yafara da abinda ya tarasu.

_"Alhmdllh, da farko dai zan fara da muku nasiha akan halin zaman takewar rayuwa. duk yanda karayu dawani mala'ikun ALLAH kan rubuta k'yautatawarka gareshi ko cutarwarka agareshi, kuma aranar kiyama zaimuku hisabi akan wannan zaman tabbas, dan haka akeson ka kasance mai k'yak'yk'awar zuciya akowanne irin hali, karik'e kowa da zuciya d'aya, shi kishi ba hauka baneba, duk abinda kaga ubangiji ya halatta ga bawansa to shiyasan dalilin hakan, inamai gargad'arku dakuji tsoron ALLAH akan cutar da juna koda da mummunan kallone bare magana, nidai harga ALLAH ban auri kowaccenku dan bana sontaba, duk d'inku so iri d'aya nake muku, banbanci yanaga yanayin yanda kowaccenku ta k'yautatamin, dan ita zuciya takan karkatane gamai k'yautata mata. insha ALLAHU kuma nayi alk'awarin kare ma kowaccenku mutuncinta da hak'inta, bance muku nid'in dabanne acikin mazan duniya ko Hausa fulaniba, saidai inamai tabbatar muku zanyi duk wani k'ok'arin samun tazara wajen k'yautatama iyalina tsakanina da sauran maza, dan tabbas kawai kuskure da sauran maza kanyi musamman mazan HAUSA FULANI ma, zakuga namijin bahaushe mafi aksarinsu sun dauka cewa, aure ba komai ba ne face jima'i da tara zuri'a. Hakan ne ma ya sa Yana da wuya ka ga ma'aurata suna sumbatar juna a goshi koh a kumatu, kuma idan ka ga sun rungume juna, toh labari mai dadi ne ya samu."_
_"Yana da wuya ka ga miji yana baiwa matarsa abinci a baki, Idan ka ga hakan kuwa toh ka tabbata matar ce bata da lafiya, shima ba kowanne kema yin wannan k'ok'arinba, wanima yana kallon matar zai tsallake yatafi ga harkokinsa, a ganinsa bashida lokacin zama ya kula da ita ma a haukarsa."_
_"ldan ba a drama ko Novels ba, zai yi wuya ka ga miji ya bude wa matarsa kofar mota ko taimaka mata da rainon yaransu ko ma d'aukar yaron gaba d'aya, wani saiki samu in anmasa haihuwa daga ya d'auki d'an yamasa hud'ubar suna bazai sakeba sai idan yaron yana cikin matsanancin ciwo koya mutu yad'auki gawarsa, amma bawai haka kawaiba danjin dad'i, a tunaninsa raino sai mata, shi nashi kawai yanemo abincine yabasu, babu maganar neman shak'uwa tsakanin 'ya'ya da mahaifi, to mahaifiyarsuma bata samuba bare kuma su yaran"._
_"Abu guda daya da yake sanya magidanci a Arewa ya taba wuyan matarsa shine lokacin da take korafin zazzabi yana damun ta, ba zai kuma kara tabawa ba sai wani sabon zazzabin ya zo, ko fad'a ya had'asu 6acin rai yasakashi shak'e wuyan domin mata hukunci, saikace yasamu dabba ko baiwarsa"._
_"Lokaci daya ne za ka ga miji ya dauko matarsa a hannu, lokacin kuwa shine idan ta fara labour (nakuda) zai kai ta asibiti, ko daren farkonsu yanaji da zumud'in son samun biyan buk'atarsa, kokuma inta mutu ya fiddo gawarta daga asibitin ko d'akinta, hakama yimata wanka ko suyi tare, idan kaga haka sai dai wankan gawarta bayan mutuwarta, shima idan ansamu mai mata shikenan, amma koda wasa bata isa gifta band'akiba idan yana wanka, koda wani Abu ya manta zaice ta kawo masa, kodai tamik'a ta katanga kokuma yad'an bud'e k'ofar kad'an ya kar6a yakoma ita kuma fuskarta Na gefe gudunma karta kalleshi yace batada kunya."_
_"ldan ka ga ma'aurata na zaune a waje da daddare, kada ka dauka tsabar soyayya ce, maganin sauro suka watsa a dakin suna jira warin ya ragu, kokuma 6era yamutu sun kasa zama a d'akin ko zafine, mafi yawama zakaga tabarmar kowa daban"._
_"Yawancin mata idan ka ga sun sayawa mazajensu wani abu kyauta, toh ka tabbatar an kwantar da mazajen ne a gadon asibiti, sannan ne mai tausayi za ka ga ta sayi lemo da ayaba ta kawo masa. ldan ka ga ma'aurata suna tsere-tsere, toh ka tabbata abin tsoro suka gani kowa yana ta kansa, kokuma fad'a suke yanason dukanta ta tsere dan tsoro shikuma yabiyota yana banbamin masifar son kamata yamata hukunci. Amma ba soyayyaba"_
_"ldan ka ga ma'aurata tare sun fito da yammaci suna tafiya, ba wai shawagi suka fito ba, yawanci k'ara za su kai na wani da ya doki ɗan su, kokuma wani Abu tashin hankali ya riskesu kowanne yana gida saisu fito atare domin zuwa. a lokaci daya ne mace ke kallon idon mijinta dab da dab, lokacin da ya nemi taimakon ta don wani abu da ya faɗa cikin idanun sa kokuma ita ya fad'a mata anata idon"._
_"Idan aka yi sa'a miji ya zama mai bawa iyalin sa kulawa, sai ka ji jama'a suna cewa : Ai mijin Hajiya ne, Bawan mata, ko kuma ta gama dashi ko d'ankwali yaja hula, k'arshe ma ka ji ana kiran sa da Mijin tace"._
_"gabaki daya an dauki aure tamkar azaba, abin da ake yin sa bisa turbar soyayya da k'auna da koyi da fiyayyen halitta ANNABI MUHAMMAD S.A.W, idan zaka binciki gidan auren malam bahaushe 99 zaka samu sunbar koyarwar addini sunkoma nasu tsarin Mara 6illewa, shiyyasa kullum matan ke cutuwa da azabtuwa suna kallon gidan auren prison ma yafishi sauk'in zama, da mace tayi watanni biyu gidan miji akai rashin sa'a tasamu ciki a wannan tsakanin to tazama tsohuwa ga mijinta, komin k'ok'arin ta Na gyara masa kanta a d'age yake kallonta, yanzu idonsa yakoma kan 'yan mayan waje kuma, shiyyasa saikiga ka ajiye mace hud'u a gidanka amma idonka bai daina hange-hangen 'yan matan layinkuba, soyayyar tazama ta titice kawai saboda ana d'aukin juna. to tayaya za'a samu raguwar mace-macen aure a arewacin k'asarnan, babu abinda ADDININMU baizo mana dashiba, amma duk munzubar sai yahudawa keyi, yanzun kuma muna k'ok'arin komawa koyi dasu, shiyyasa kuma saikuga soyyayar babu wani tsarin birgewa saboda ancire muhimman abubuwan da Manzon ALLAH yakoyar damu, tunda babu kunya, babu girmama juna a soyayyar d'an boko ko kad'an, a kowane waje gaban kowa zaimata duk abinda yazo kansa koshima yamata don nuna sunason juna, sannan kowannensu yanada 'yanci babu tazarar girmama juna tsakaninsu dazai nuna shi mijine ita matace, to tayaya za'a samu yanda ake buk'ata a ganinku?"._

Suduka ukun suka girgiza kai suna fad'in "babu".
Ya nisa yana binsu da kallo d'ai-d'ai, cikin tausasa harshe yace, " to ina rok'onku banason irin wannan makauniyar rayuwar,, kuzo mugudu tare mu tsira tare, Fateema kece babba, kicigaba da rik'e girmanki, idan lamarin gidana ya 6aci kezan fara zarga, haka kuma Aneesa da Khadeeja, karna sake naji wani raini yashiga takaninku da Fateema, dukda ke Aneesa kina ganin kusan shekarunku d'aya, to agidana itace babbarki koda kuwa kin girmeta, ki rik'e girmanki kema Aneesa, dan kina sama da Amatallah, idan kika ringa mata Abu marasa k'yau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login