Showing 57001 words to 60000 words out of 104242 words
juyowa ya kalleta, dai-dai itama ta d'ago zata cemasa ga abincin suka had'a ido. Da sauri ta sauke nata. shima janye nasa yayi yatashi zaune yana murmushi, k'arar TV ya rage yana fad'in "sauke k'asa ki janye table d'in, banacin abinci a sama".
Nanma batace komaiba ta sauke kamar yanda ya umarceta, k'asa yadawo ya zauna, itakuma ta durk'usa gabansa tana sauke kulolin daga tiren, harzata fara zubawa yace, " zauna da k'yau mana".
Still nanma dai bata tankaba ta gyara zamanta tareda tankwashe k'afafunta tafara zuba masa abincin. tuwon alkama ne miyar d'anyen ku6ewa, sai k'amshin kori ketashi mai dad'i (so a 6angaren abinci babu sakarai a matan Uncle, kowacce gwanace😊).
"My best! wannan abincin yayi yawa ai, kozaki cine?".
Da sauri ta kad'a kanta alamar a'a.
Yad'an murmusa kad'an " wai an d'inke bakinne?".
A sanyaye tace, "a'a Uncle".
" Okay duk jan ajine irinna Amare?".
Ba shiri tasa hannu tarufe fuskarta tana fad'in "kai Uncle".
" ALLAH kuwa my best!, najiki tsit ne, amma ina ruwan wanke hannu".
"Bara Na d'akko na mantane".
Baice komaiba, sai dai harta fita yana binta da kallo, a fili yace " ALLAH kenan mai tsara al'amura, shi koda a mafarki yama ta6a tunanin Amatallah a jerin matansa, koda matan NASA keyin kishi da ita abaya wlhy shi bayajin komai a ransa game da ita, kallon d'iya yake mata tamkar su Sahib, amma Ubangiji gagara misali saigashi ya canja al'amura tamkar wani labarin tatsuniyoyi ko finafinai......
Sallamarta ta katse tunaninsa, ta ajiye k'aramar roba data zubo ruwan wanke hannun, zama takumayi tamkar d'azun.
"Yauwa babyna sannunku". yafad'a yana saka hannunsa a ruwan.
Itadai Amatallah mamaki komansa ke bata, tana mamakin yanda ko kad'an bayajin kunyar kiranta da kowanne irin suna yanzun, jibifa abinda yamata d'azun tamkar ba uncle d'intaba.....
Jin hannunta cikin ruwan ta sauke ajiyar zuciya da kallonsa. ido d'aya ya kashe mata, kafin yace, " nasan kema yunwar kikeji ai...
"ALLAH uncle a'a, naci abinci d'azun".
"Saiki k'ara yanzu ai ko".
Babu yanda zatayi dole tasaka hannu kamar yanda yamata umarni sukaci a tare, sai dai a kunyace Amatallah keci, ko kad'an takasa sakin jiki taci Na kirki, sunci kusan fin rabin data zuba taga ya tsame hannunsa yana fad'in "Alhamdllh".
Itama saita tsame nata hannun, dama tuni ta k'oshi, tsoron karyay mata fad'ane yahanata cire hannu.
Kallonta yayi " badai kin k'oshiba?".
Ta langa6e kanta gefe tamkar zata FASA masa kuka tace, "ALLAH uncle nak'oshi, kar cikina yafashe fa".
A mamakinta saitaga ya d'ora hannunsa saman cikinta wai zai duba yaga iyakar Girman cikin.
Da sauri tad'an matsa baya, shikuma yasaki k'asaitaccen murmushi yana shafa gemunsa, Wanda takula hakan yazame masa al'ada, inhar Abu zai faranta ransa koya 6ata ransa sai ya kai hannu yashafi gemun nan da itama kanta shaidace tasan ya k'ara masa k'yau da kwarjini.
" Uncle tunda kaci abincin bara naje Na kwanta, lectures d'in safe gareni gobe".
Wani kallo mai cikeda ma'anoni yamata kafin ya kauda Kansa yana murmushi, yakula dama tuni a d'arare take dashi, yabasar da maganar batareda ya bata izinin tafiyarba.
"Uncle Na tafi?".
Maganarta tasakashi juyowa ya kalleta, Kansa kawai ya kad'a alamar tatafi batareda yayi maganaba.
Ai ko cikin hanzari ta had'a kwanukan ta d'auka ta fice. binta kawai yayi da kallo harta kullema ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Amatallah Na sauka tayi hamdala ga ubangiji data kubtar da ita.
Nace, "humm".
******
Abinda yabani mamaki koda Na lek'a wajen Aneesa saina taddata hankali kwance, tana zaune a falo tanama Siddiqa shirin barci, harda 'yar wak'ama take rerawa abinta, sai dai kuma baitin wak'ar yasakani fahimtar bata jin dad'i baceba.
Lalla6awa nayi Na fito, itama Uwargida Na lek'ata.
zaune take ta zuba tagumi tana kallon 'ya'yanta, itakam ban fahimci mike damuntaba.
Fitowa nayi itama nabi bayan Amatallah.
Na isketa tayo brosh tafito daga toilet, harma ta cire kayanta tasaka riga da wando Na barci pink, wandon iyakarsa gwiwa, sai rigarma batada girma sosai mai hannun shimi, itama dai 'yar wak'arta naji tanayi harta bud'e Waldrob d'inta ta d'akko hula tasaka a kanta kafin ta daka tsale ta haye gadonta, duk acikin murnar Uncle baice ta kwana d'akinsaba.....
😂zakiyi bayani.
Uncle kam tana fita shima ya mik'e, TV ya kashe danji yay labaranma sun fita kansa, dama gawani abinda ake nunawa daya Sosa zuciyarsa akan MATASA, fitar Amatallah d'in saita sakashi a kewa, ya saba zama a irin wannan lokacin da matarsa zaune gefensa suna 'yar hirar rayuwa da soyayyarsu. yabar Amatallah ta tafine danya kula takasa sakewa, shikuma baya buk'atar abinda zai k'untata rayuwarta. amma mi saiyaji bazai iya kwana shikad'ai ba gaskiya, bayan kuma ga mata har uku suna amsa sunan halalinsa, bedroom d'insa yashiga ya canja kayansa zuwa na barci, vest ne da boxer, saiya d'aura jallabiya a sama kawai, yad'an fesa turare kafin yashiga toilet yayo brosh, wayoyinsa ya d'auka ya zuba a aljihu, dan shi baya kashe waya sai dai abisa kuskure ko rashin caji. Yakashe komai Na 6angaren nasa yafito. Sai dai yana fara sakkowa daga benen ana d'auke wuta, "ya salam" yafad'a yana dafe kansa. Ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunna fitila sannan ya ida sauka, dolenema ya kunna Generator kodan Sahib dabaya k'aunar zafi, koyaya zafi ya isheshi zaitashi yaytama mutane kuka, yaron yanada masifar jin zafi, gakuma Fateema da ciki kansata zufar babu gaira babu dalili. harya kama hanyar k'ofar fita kuma yadawo baya, 6angaren Fateema yashiga da sallama.
Amsawa tayi tana cire taguminta da saita kanta gudun karya fuskanci halin datake ciki, yak'araso cikin bedroom d'in idonsa akan yaran.
"Wai yanzu kuma su Ummita sun dawo nanne da kwana?".
Kallonsa tayi tace, " a'a, kawai dai kwana biyunnan ne, amma zasu koma d'akinsu ai".
Kansa kawai ya jinjina, ya matsa kusadasu yana lek'a fuskar kowa, ya gyarama Abulkhairi kwanciya daya dawo bakin kadon sosai wajen murje-murjen barci. "Nikam d'azun Shehu yakawo fetur gidannan?".
" kai, anya kuwa, gaskiya banga shehu a gidannanba, sai dai idan kuma bai shigo bane kokuma yakawo ina d'aki, amma ka tambayi Momynsu dai watak'il taga zuwansa".
''Okay, to zaman mikikeyi baki kwantaba?".
Guntun tsaki tayi kafin tace, "wlhy hakanan dai".
Matsowa yayi kusada ita ya taimaka mata ta kwanta, sannan ya tofesu da addu'a, yabisu d'ai'd'ai ya sumbata kafin yamata saida safe.
Yana shirin fita Sahib yafara motsawa yana k'unk'unin kuka, da baya ya dawo ya haskashi, harya fara tara zufa, yanad'an kad'a hannunsa alamar yima kansa firfita. " to sarkin jin zafi, zaka fara ko?" Uncle yay maganar yana sinkuyowa kansa yacire ma6allan rigar barcinsa ya cire masa.
Ita dai Fateema batace komaiba tana daga kwance tana kallonsu harya gama.
Da d'an hanzari yafita yana fad'in "bara dai Na bincika fetur d'in".
6angaren Aneesa yashiga, har yanzu tana falo zaune, sai dai tagamama Siddiqa shiri tuni, tana kan cinyarta dai har yanzu, idonta a lumshe, dan tunda aka d'auke wuta bata motsaba bare ta kunna fitila, sallamarsa tasata amsawa amma bata kalleshiba dukda haska fuskarta dayayi da fitilar wayarsa kafin ya maida Kallonsa ga Saifudden dake kwance a kujera doguwa, kuma maida kallonsa yayi kanta itada Siddiqa. Fuskarsa babu walwala yace, " shehu yakawo fetur d'azune?".
Kamar bazata tankaba, saikuma tace, "ban saniba nima, Dan bai shigo cikiba, amma ka tambayi umman yara mana".
Zai k'ara maganama aka maido wuta, ajiyar zuciya kawai ya sauke yace " Alhmdllh" ya kashe wayar yasaka aljihu, Saifudden ya d'auka yay cikin bedroom d'inta dashi, haryaje k'ofa yajuyo yana kallonsa bayan yata6a d'uwawun Saifudden. "Wai sai yaushe zaki daina sakama yaronnan Pampas ne?".
Baki tad'an tunzuro, " amma dai kasan fitsari yakemin a gado, kaga dole na saka masa pampas".
"Humm amma ai nafad'a miki ki maidashi 6angaren Fateema yana kwana cikin 'yan uwansa, tundasu katifarsu fitsari baya hudawa, tunda bazai yuwu yadinga kwana shi kad'aiba anan".
" ammafa dear kasa......."
Saikuma tayi shiru bata k'arasaba.
Yace, "nasan mi?".
Shiru tayi bata tankaba, amma idonta a kansa.
Shima shigewarsa yayi ya shifid'e Saifudden, yadawo ya d'auka Siddiqa itama, itadai Aneesa kallonsa kawai takeyi, bai fitoba saida yayi musu addu'oi kamar yanda ya saba.
Koda yafito bai kulataba yanufi hanyar ficewa.
Da sauri ta ruk'i hannunsa na dama, cak ya tsaya amma bai juyoba, sai kawai tamatsa ta rungumeshi ta baya tareda sakin wani marayan kuka.
Shiru yayi yana saurarenta dukda kukan NATA na sukar zuciyarsa, sai kawai ya lumshe idanu, kusan mintuna 3 kafin yasa hannu ya janyeta a bayansa, takuma rik'eshi da k'yau yanda bazai guduba.
"Please dear kadaina fushi dani Dan ALLAH na tuba".
Kallonta yayi ya kauda kansa, dukda tabashi tausayi bai tankaba yakuma yunk'urin fita. Sai kawai tazube a gabansa takuma sakin kuka. tamau yakuma tamke fuska, " Aneesa bani hanya na wuce" yay maganar a d'an tsawace.
"Babu inda zanje Muhammad, sai dai mu kwana anan".
Wani murmushi yasaki yana shafa gemunsa, yace "sai dai ke d'in ki kwana anan amma baniba mai amarya, tunda baki shirya fad'amin abinda ya had'aki da khadeeja ba muyita zama ahaka".
Dukda maganar ta soki zuciyarta haka ta danne, tamik'e tana fad'in "shikenan zan sanar maka, saikamin hukunci, amma ina fatan hakan bazai sakaka d'aukar wani sabon fushinba?". A tausashe take maganar, kuma dolene tabaka tausayi.
Kallon agogon falon yayi kafin ya kalleta, " kibari saida safe, yanzukam barci nakeji" ya kai karshen maganar da kama hannunta zuwa bedroom d'in ta, dama tayi shirin barci, dan haka ya taimaka mata ta kwanta, goshinta ya sumbata yafita yana fad'in "ALLAH yabamu alkairi".
Bata tanka mishiba, sai wasu hawaye masu zafi dasuka kwaranyo a kumatunta, tasan babu makawa yau zai angwance abinsa, a fili tace, "ya ALLAH ka sassautamin kishinan dai".
ALLAH saita bani tausayi masu karatu😓. Harna amsa da amin Aneesa. Dan zafin kishi bala'ine.
Komai na falonta yakashe sannan yafito babban falo, nanma yakashe abinda zai kashe, fitilar kitchen ya hango a kunne, itama ya k'arasa ya kashe tareda jawo k'ofar, saida ya tabbatar komai dai-dai sannan yanufi 6angaren Amatallah.
Ba barci takeba, tana zaune tsakkiyar gadon tana karatu, harta kwanta aka maido wuta, shine ta tashi kawai tana bincika takardunta na school, Dan watak'il gobe amusu test.
Shigowarsa babu zato sai sallamarsa dataji kusan dab da ita yasakata diriricewa, tafara laluben abundan zata rufe jikinta, saidai babu komai akusa da ita, bargone kuma ta turashi can k'arshen gadon lokacin datayi tsalle.
Shikam kallon k'yawun halittar da ALLAH yamata yasakashi manta gabanma wa yakene, saida tafara k'ok'arin sauka daga gadon Dan d'aukar hijjabi sannan ya dawo hayyacinsa.
Saurin rik'ota yayi ya maidata kan gadon, shima ya zauna gefen yana kallon takardun data baje a gadon, "dama bakiyi barciba" yay maganar murya a sanyaye kuma yana kallonta.
Kasa magana tayi, sai jijjiga masa kai datayi tanata wani takurewa da gyagygyara wuyan rigarta tamkar tamata yawa, alhalin kuma cif take a jikinta tamkar an gwadatama.
Murmushi yayi yana hayewa sosai kan gadon, ya tattare takardun waje d'aya yamaida kan drowan gefen gadon ya ajiye.
Muryarta na d'an rawa tace, "Uncle ina karatun test ne fa".
Hannu yakai yarik'o nata yana wani k'ank'ance idanu, "tunda miji yazo sai'a barshi aii ko, nima wani text d'in zamuyi yanzun aii".
Gabanta ya fad'i, ta tuno maganar Fa'iza, gefe kuma tana mamakin dama haka Uncle yake Wai?...."
Bata kai k'arshen tunanintaba tajita a jikinsa, sosai jikinta yafara rawa, hannu kawai yakai saman bango kusada fuskar gadon ya kashe fitilar d'akin.
Mi cikin Amatallah zaiyi banda k'ara kuuuuuu!!!.
Tamkar ya kwashe da dariya haka yaji, amma saiya dake ya gyara mata kwanciya sosai ajikinsa bayan yazame jallabiyar jikinsa ya zauna dagashi sai vest da boxer.
Kasa cewa uffan Amatallah tayi, saidai jikinta har yanzu rawa yakeyi, bata k'ara tsorataba saida taji babu alamar kaya a jikinsa, kasa daurewa tayi muryarta na zuga na alamar tahowar kuka tace, "please Uncle ALLAH I......
Bai bari takai k'arsheba ya d'ora hannunsa akan le6enta, acikin kunnenta yace, " ya isa haka, ni barci kawai nazo muyi madam pinky....."
'Dan k'ank'ame jikinta tayi saboda maganarsa tasaka tsigar jikinta yin yarrr. luf tayi bata kuma yunk'urin yin maganaba, taji ya janye hannunta daya d'ora saman k'irjinta ya d'ara yatsansa a bakinta.
Shirune ya biyo baya a d'akin, sai k'arar fanka kawai, shi addu'a yakeyi, itakam tunanin da fargabar wannan lamari ga d'unbin mamakin rashin kawaici na namiji sun cika kwalwar kanta, hummm komin matsayin Namiji a wajenka kafin aure, labari yakan koma bayan kazama matarsa, saisu ture Duk wata kunya da karar girmansu a wajenka su nuna maka sunma manta, kujifa Uncle yanzu harda wani cemata madam pinky, saboda komai nata pink har kayan barci kenan, wayyo Uncle zaka kasheni da kunya wlhy........
Cak tunaninta ya tsaya danjin hannunsa indama batayi zatoba da sunan yana shafa mata addu'a, k'ank'ame jikinta tayi waje guda.
Yasaki murmushi mai sauti yana janye hannun daga inda ya d'ora. Koda ya kammala addu'ar sai kawai ya rungumeta da k'yau ya lumshe ido batareda yace da ita uffanba.
Dan danan barci mai dad'i yay gaba dashi, Amatallah kam sai sak'e-sak'e takeyi, hankalinta bai kwantaba saida taji saukar numfashinsa a hankali alamar barci ya d'aukeshi, addu'a tayi tad'an tattaofa batareda ta shafaba ta lumshe idanu, barci yace muje zuwa.........
Asuba tagari Uncle and Ama........
🚶🏻♀nima natafi wajen nawa Uncle d'in😄😜.
___________________________
*Washe gari*
Kusan 3:39am ya farka kamar yanda ya saba a kowacce ranar lahadi daren litinin, dakuma laraba daren Alhamis, sauran ranakun kuma yakan tashi tun around 2 randa kuma nauyin jiki da gajiya suka hanashi shikenan, yanda Amatallah ta katantanesa saiyayi murmushi, hannu yasa k'ark'ashin filo ya d'akko k'aramar wayarsa ya kunna fitila ya haska ta, ba k'aramin shigewa jikinsa tayiba, gashi da alama andad'e da d'auke wuta ma, sanyin asuba daya fara busowa yad'an sassauta zafin garin, cikin dabara ya janyeta a jikinsa tareda gyara mata kwanciya yamaye gurbinsa da filo, gani yay tad'an gyara sosai tareda kuma k'ank'ame filon tacigaba da barcinta.
Murmushi yakumayi kafin ya fice, shaf ya manta baisa ta ajiye masa kayan tea ba, ALLAH ma yasoshi kowacce tanadashi a kitchen d'in 6angarenta, kitchen d'in falonta yashiga, wanda kowacce tanadashi, saikuma na gaba d'aya Wanda yake a babban falonsu, inda ananne kowacce keyin girki ranar duty d'inta,, haskawa yayi yana son ganin plas d'in tea d'inta da addu'ar ALLAH yasa tana ajiye Hort water kamar sauran, can ya hangoshi a kusurwa, yamatsa yana d'agawa da tunani, ''Alhmdllah" yafad'a yayinda yaji nauyi, nan dai yahad'a shayi mai sauk'in kauri, ya bud'e fright d'inta kota ajiye bread tunda ana ajiyema kowa, kusan uku yagani alamun bata cima ita kenan, saikuma k'ananun cake Wanda da alama ita tasiya kayanta ta ajiye, cake d'in dake nannad'e a ledoji gudun karya bushe ya d'auka guda 2 da ruwa yafito, bedroom d'in ya koma, ya ajiye kayan hannunsa saman k'aramin table d'in fake gaban sofa yawuce bathroom yayo brosh, yana shan tea da cake idonsa akan Amatallah, shikad'ai yasan miyake kissimama zuciyarsa, hardai yagama tsaf yakoma bayi yay alwala, abin salla ya shinfid'a sannan yasaka jallabiyarsa ya kabbara salla.
Har aka kira sallar farko yana nafilfilinsa, a lokacin yamik'e yay rakata'ainul fijir sannan yatada Amatallah da k'yar saboda tanada nauyin barci.
Ganinsa a d'akin yatuna mata tarefa suka kwana, kanta a k'asa tashige toilet, shikuma yafita yana murmushi. Kamar yanda ya saba d'akin kowaccensu yashiga yatadasu, ya taimakama Fateema tayi alwala saboda nauyin datayi, sannan yatada yara suma da taimakonsa sukayi alwalar, d'akin Aneesa yakoma shima Saifudden ya tadadashi, dukda Aneesa tatashi bata tadashiba saboda tasan shike tashinsu kullum.
Dukda k'ank'antar yaransa hakan bai hanashi horonsu da zuwa sallar asubahiba komin sanyi ko ruwa, saidai in bakada lafiya kokuma shima bazaijeba akan wani dalili mai k'arfi, saisuyi agida gaba d'aya, amma dai tilasne saika tashi kayi sallar..............✍🏻
_jiyakam kunjini shiru, dama nasanar daku inada wasu uzurirrika, wlhy da k'yarma nake cire time d'in muku typing, shiyyasa zakuga ko comments d'inku ban tankaba kwana biyu, saima yau nasami damar dubawa, ngd sosai, kuna sakani nishad'i, ina alfahari daku