Showing 3001 words to 6000 words out of 104242 words
ke cikin kofin.
Sallamarsa ce tasaka yaron k'ara k'arfin kukansa, itakuma tad'ago kai tana kallonsa da amsa sallamar.
Da d'an sauri yak'araso falon, kusada yaron ya zauna, "Saifudden miyafaru kuma da kuka haka? mi kika masa?".
A sanyaye tace, " nikam mizan masa dear?, tea kawai nace yasha nabasa magani shinefa yake wannan kukan iskancin, kadai san Saifudden ai".
Kar6ar kifin shayin yayi, ya ajiye saman table d'in gabansu, yajawo yaron jikinsa yana ta6a goshinsa da wuyansa, jin zafi zazza6i zau, ya kalleta a k'ufule, "yanzu nan Aneesa kina nufin saima yanzu zaki basa Magani? tun d'azun kin barmin yaro da ciwo ajiki?".
" a'a wallahi dear, nabashi Magani tun d'azun, sai dai kasanshi bayason maganin, ina gama bashi yayi amansa, daganan yay barci, Ummansu cema tace nabarsa saiya tashi, kuma tashinsa kenan d'in, amma Dan ALLAH kayi hak'uri".
Baice komaiba yafara k'ok'arin cirema yaron rigarsa da wando, ita dai kallonsu take, harya gama ya d'auki yaron yashiga bedroom d'in ta, ajiyar zuciya ta sauke, tacire siddiqa daga jikin nonon saboda tayi barci.
Bedroom d'in ta bisu, jin motsin ruwa a bathroom tagane wanka yake masa. Kwantar da siddiqa tashiga k'ok'arin yi. tana zaune a bakin gadon yafito d'aukeda saif daya nad'o a towel.
Shima bakin gadon ya zauna nesa da ita, yace, "bani kaya masu kauri".
Tashi tayi da sauri ta d'ako kayan sanyi takawo masa. da kansa yasaka masa, ya d'aukesa suka fice batareda yakuma tanka mataba.
Binsa kawai tayi da kallo itama. Tasan zaimayi abinda yafi haka, indai akan 'ya'yan sane.
A babban falo ya iske Umma uwargidansa ta had'a masa abinci a k'asa kan carpet, zama yayi, ya zaunar da deen kusadashi, kafin ya maida kallonsa kansu Sahib, "Abul-khair kutaso muchi abinci ko.
A tare sukace "to Abbu".
Umma ta ta6a wuyan Saifudden tana fad'in ''Deen ya jikin? zazza6in ya sauka ko?".
Yaron yad'aga kansa yace, " Umma zansha ruwa".
"To deeni na".
Ruwan tazuba a Kofi sannan tasaka masa abaki, yasha kusan rabi, Abbu yace, " barsa haka, karya cika cikin da ruwa".
Batace komaiba ta janye kofin daga bakin Saifudden. tadawo gabansa ta had'a masa abinci Suma yaran haka.
Fruits salad yafara sha, idonsa nakan yaransa dakecin abinci a tsanake, babu mai magana, saboda ya kafa musu dokar duk Wanda yake cin abinci yana magana saiya zanesa, shiyyasa ko Ummita k'aramarsu bata surutu in sunacin abin.
Ya maida kallonsa kan Umma dake zaune gefe tana canja charnel a TV. "Ku bazaku ci abincin ba?".
Murmushi tamasa, kafin tace, "zamuci mana".
Bai ce komaiba ya maida kansa ga bowl d'in dayake shan fruita salad d'in.
____________________________
Dole Baban Ama... Sai a gida yayi salla, dan baisan yanda yanayin garin ya kwanaba.
Amatallah kam sai gabannin asubahi barci ya d'auketa, ga zazza6i mai zafi daya saukar mata.
Bayan sun idar da salla baba ya kalli Ammi dake zaune bayansa kad'an tana azkar,
" yakamata ki tada mamana tayi salla saimu tafi asibiti ko?".
Kanta ta jinjina masa, sannan ta mik'e.
Da taimakon Ammi Amatallah tayi salla, sai rawar sanyi takeyi tana hawaye, manyan idanun nan sunyi luhu-luhu saboda rashin isashen barci, ga kuka datasha.
Tana idarwa basu 6ata lokaciba suka nufi asibiti. Alhmdllah garin ya kwana lafiya, saboda 'yan sanda sun kama mafiya yawa daga cikinsu zike.
Sun d'an jima a zaune, kafin su sami ganin doctor, saboda halin da Amatallah take ciki doctor ya kwantar dasu za'a mata k'arin ruwa da allurar barci tasamu nutsuwa.
_________________________
*_Two days ogo_*
Har zuwa yau Amatallah tana hospital, doctor ya rik'esu, saboda firgita da takeyi bata samun isashshen barci, sai dai ayita mata allurar barci.
Sosai lamarin yafara tsorata iyayenta, Dan basuyi zaton abin zaiyi tsamari hakaba, duk da sunsan dama Amatallah tanada tsoro sosai, gata da rik'e Abu a zuciya.
Ammi taje gida danta watsa ruwa, Baban Ama.. Ne kawai a asibitin, yana zaune kusada gadon da Amatallah ke jinya, hankalinsa nakan waya yana latsawa, da alama wani yake son kira.
Amatallah na zaune ta jingina da gadon, dukta rame, sai idanu kwala-kwala, rik'e take da kofi tana shan fura, bata iya cin abinci, daga fura sai tea, duk da dama abincin bai dametaba.
Baba yay saurin kara wayar a kunne, kasancewar wanda ya kira ya d'auka.
"Assalamu alaika my brother".
Daga can aka amsa masa, bayan sun gaisa da tambayar iyaliansu.
yace, " ya jikin baba?".
Daga can ya amsa da "Alhmdllh my brother, ina my best daughter?".
" gatanan a gadon asibiti".
"Gadon Asibiti kuma? Miya farune?".
" humm, kabari kawai brother, d'iyar takace sai ahankali, sai dai kashigo Mayi maganar, nazata ma wlhy yau zaka shigo mu koma wajen maganin baba".
A jiyar zuciya ya sauke daga can yace, "brother ya jikin nata yanzu?".
" lah karfa ka tada hankalin ka, da sauk'i Alhmdllh, barama mugama magana nabata kaji, nasan ka da girmama Abu. yanzu yaushe zaka shigo?.
"Okey".
" kabari kawai, yau nai niyar shigowa wlhy, saboda naga maganin yana aiki, dan kwana biyunnan baba baya Complain d'in ciwon baya sosai, saikuma wani meeting da za'ayi Na kasuwa ya rik'eni, amma babu damuwa insha ALLAH da an gama zan taho, saina kwana kawai".
"Kodai ka hak'ura zuwa goben brother? tafiyar dare batada dad'i aii".
" no, karka damu, insha ALLAH zanzo da wuri, bazan iya hak'uri banga jikin my best daughter yanda yakeba, batama phone d'in naji muryarta".
Murmushi kawai baba yayi yamik'ama Amatallah wayar. kar6a uncle d'inkine.
Duk da halin datake ciki sai da tayi d'an murmushi, tanason Uncle M.A a rayuwarta, saboda yanda yake matuk'ar nuna mata kulawa....
Maganarsa ta katse mata tunani.
"My best daughter! baki da lafiya amma brother bai fad'a minba? ya jikin naki?".
A hankali ta lumshe idanunta, saboda jin dad'in sassanyar muryarsa, tana son muryar uncle d'inta over.
tace, " uncle da sauk'i, na warke ai".
"Kai my best ban yardaba, kinji muryarki yanda tazama very slowly kuwa?. duk da nasan dama daughter d'ina cool girl ce. anyway koma yaya insha ALLAH yau a jos zan kwana".
" Uncle da gaske?".
"Insha ALLAH my Darling".
" thanks you uncle, please ka tahomin dasu Abul-khair to".
"To amma my best daughter school fa? kokin manta gobe akwai? kiyi hak'uri next time insha ALLAH zasuzo miki hutu".
Idonta harya tara kwalla tace, " to uncle saika zo, amma ka gaidamin su, hardasu Aunty's da innani da baba dasu anty Nazeefa".
" okey, zasuji insha ALLAH, saina zo".
Kanta ta gyad'a batareda tayi maganaba ta mik'ama babanta dake kallonta tun d'azun yana murmushi wayar, duk yanajin hirar d'iyar tasa da abokinsa.
Kar6a yayi suka cigaba da tattaunawa..........✍🏻
*_Assalamu alaikum_*
_please maganar gaskiya a wannan karon bazan turama kowa buk ta PC ba idan nayi nisa, saboda wasu uzurina dana had'a da typing d'in, inkinga kinmin magana kan turomin daga farko ban amsakiba karkiji haushi. idan ba yanzu zaki karantaba, please ki tara, amin afuwa🙏🏻😊._
*Nasa kogi state acikin jihohin Yoruba, wasu suna ganin kamar nayi kuskure.*
*akan Sani na rubuta hakan, dukda kogi ba tsagwaron Yoruba bane acikinta, akwai wani yanki Na jihar da Yoruba sukeda yawa kwarai da gaske. shiyyasa kogi tashigo lissfi.*
*kogi state tana iyaka da kwara state ne, kwara kuma k'asar Yoruba ne, kunga dolene yarabawa su sami kutsawa cikin kogi state ai, kokuma wasu k'auyikansu su shafi jihar, akwai garin KABBA zamu iya cewa 90% Yoruba ne aciki. So nima bisa binciken masana nake, su sukasan dalilinsu nadaka kogi cikin yankin Yoruba d'in*
Wannan shine hujjata, ba kai tsaye nayiba😅👌🏼.
(Wad'an da sukamin gyara kuma, kumin afuwa ba gwaleku nayiba, saida nayi bincike nima😊🤝🏻, amma ngd da tunatarwa🥰.)
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu🙏🏻😭_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_HASKE WRITER'S ASSOCIATION_*
```{Home of expert & perfect writer's}```
*Assalamu alaikum*
_nasan zakuyi mamakin fara typing d'ina, so nayi dubu da yanayin buk d'in, dakuma time d'in damuke ciki, idan nace sai new year lokacin zai k'ure saboda sak'on dazan Isar insha ALLAH, kuma za6e yana tunkaromu. sai dai kuma banyi alk'awarin muku typing kullumba gaskiya🙈, ALLAH yasa zaku bani had'inkai._
Love you so much all❤❤😘
____________________
*_Number 2_*
____________________
.........Matasa ne Kusan su ashirin suka fito daga wani k'aton gida, Wanda kallo d'aya zakamasa kasan mamallakin gidan yagama jik'uwa da Naira.
Duk d'insu Matasane da shekarunsu bazasu haura daga talatin zuwa k'asaba.
Hayaniyar dasukece taja hankalina Kansu.
Wani yadaka tsale yadire yana fad'in "impossible wallahi!!, bamu yarda da wannan shawaranba, a raba kawai abama kowa kasonsa yakama gabansa!!".
Wanda alamomi suka nuna shine babbansu yaja birki daga tafiyar dayakeyi, manyan idanunsa dake jajur yashiga juyawa, ransa a 6ace yace, " kaifa zike! Shiyyasa banason harka dakai wallahi, wai kai wakafi iya shegene? dama tun agaban Oga saiwani fa zak'ewa kake, kakama kankafa guy, idan ka kaini bango babu ruwana dawata sanayyarmu ko SIYASAR data had'amu, am telling you saina maka eyane, ka dai sanni aii".
A fusace zike ya matso yana hura hanci, "kai gagis karka fad'amin mai d'aci mana, kasanfa bawai zan raga maka baneba, barganin katara wannan sharan yaran naka, dagani harkai Abu d'ayane ya taramu, shine *BANGAR SIYASA*, to kawai tun muna shaida juna karaba mana kud'i da kayan harka kamar yanda Oga yace maka, bamu yarda da wata shawarar sai gobeba, danni da yarana tun yau da daddare zamu fara lik'a posters d'in mai gida. Zuwa dasafe kuma muga tsageran da zai cireta a garinnan."
Tsaki gagis yayi, ya fiddo kud'in dami guda daga aljihunsa yana harar zike, Wanda yafara k'ok'arin zaro wuk'a a k'ugunsa, amma ganin gagis ya fiddo kud'in saiya maida wuk'ar yana gyara riga.
Tafiya take cikin d'an sauri da sassarfa, saboda hadarin daya gama gauraye garin, yanda sararin samaniya kawai tayi bak'ik'k'irin zai tabbatar maka ruwan yana gab da sakkowa.
Wani d'an lungu tabi, dan a ganinta shine zai zame mata shortcut d'in da zataje gida da wuri.
Gaban tane yay wata fad'uwa, saboda hango gungun matasan anguwarsu marasa jin magana (su zike), yanda suke hayaniya kawai zai tabbatar maka fad'a sukeyi. jitai kamar takoma da baya, amma babu dama, saboda tazo gab dasu, wasu kuma sun ganta.
Ta kuma yin k'asa da kanta tana karanta *"Hasbinallahu wa ni'imal wakil"* a zuciyarta. Harta giftasu babu wanda ya tanka mata acikinsu, saboda hankalinsu nakan kud'in dake hannun gagis yana irgawa, ga kuma kwali Wanda batasan komiye acikiba dake hannun wani.
Ta kusa k'ure lungun taji sun saki ihu gaba d'ayansu, waigowa tayi dantaga miya sakasu ihun......?
A razane tazaro ido waje, dan ganin gagis kwance a k'asa wanwar, gawani a kansa yana zare wuk'a daga cikinsa.
Tamkar Amatallah zata suma dan firgici, ta kwasa da gudu tareda sakin jakkar makarantar ta a wajen, dama daga islamiyya take.
Gudu take iya k'arfinta, ga ruwa yafara sauka, gakuma duhun magriba data kawo jiki.
Ta gaban majalissar wasu dattijai tabi zata wuce, yawancinsu duk abokan baban tane ma, Baban natama nanne wajen hirarsa, majalissar tasu rumface, shiyyasa duk da ruwan da aka fara suna a wajen, saima shirin sallar magriba dasukeyi, wad'anda kuma basa sallan suna zaune kan tabarmar dake wajen, wasu kuma saman kujerun plastics.
A guje tashigo rumfar tana kwala kiran babana! Sun kasheshi, wlhy sun kasheshi.......
Tun shigowarta duk suka mik'e tsaye, harda masu alwala, Wanda ke kusada ita yarik'o hannunta, danya fuskanci a rikice take.
"K! Amatallah nutsu kifad'a mana miya farune?".
"Uncle wallahi agabana suka kasheshi, na rantse nagansu da idona". sai kuma tafashe da kuka, jikinta sai rawa yakeyi.
Sukam su zike, gagis ne yakasa kud'in uku, yabama zike da yaransa kashi d'aya, kayan mayenma dake cikin kwali kad'an ya d'ibo.
Da sauri Zike yace, " miye kake nufi?".
Gagis yace, "abinda kagani, wannan shine Rabon naku, nikuma sauran nida yarana, tunda mun fiku yawa, kuma munfiku iya aiki, shi Kansas Oga baisan kud'in k'ananun kwari bane shiyyasa ya had'amu aiki daku, amma gobe zan masa bayani....
Kafin gagis ya k'arasa maganar wani acikin yaran zike ya caka masa wuk'a, yana ''fad'in aiko zaka fad'a inka mutu".
duk sunga Amatallah wannan yasa koda takwaso da gudu wasu suka biyota. Suna ganin tashiga majalissar dattijan nan sukaja birki, basu k'arasoba.
'Daya a cikinsu yace, " o shit!! Banzan yarinyar can fa a gabanta K show yakashe gagis, yanzu yazamuyi kenan? Karta tona mana asiri fa".
Wanda ke kusada shi yaja gajeren tsaki, cikin fusata yace, "ta fad'a mana stupid girl kawai, magana d'aya ce, kawai kowa ya kwanta da shirinsa, dan tabbas komai zai iya faruwa.....
Bai kai k'arshen maganarba ya hango abokansu guys Na gudu, hakan ya tabbatar musu fad'a ya kaure tsakanin dabarsu da yaran gagis.
Basu jira komaiba suma suka kwasa da gudu.
Amatallah kam tana kuka tana bama su babanta daya k'araso wajen yanzu dan yin sallar magriba labarin abinda tagani.
Duk d'insu sun razana.
Kafin su sami damar magana suka hango mutane Na gudu. a take suma suka tarwatse, Baban Ama... Yaja hannunta suma suka bar wajen, suka nufi gida dan Neman tsira.
*
A tsorace Ammi da ke alwala tad'ago tana kallon Amatallah da babanta.
"Lafiya kuwa baban Ama...?".
" da sauk'i dai kam....... a ta k'aice yabata labarin abin da yafaru".
Ta zaro manyan idanunta da Amatallah ta gada awajenta, tana sallallami da tafa hannaye, jiki a sanyaye tace, ''to ALLAH ka sauk'ak'a mana ".
Amatallah da babanta sukace amin.
Sallar da baban Ama... Bai fitaba kenan, sai a gida yaja iyalansa jam'i.
__________________________
*KANO STATE*
Kallo d'aya zaka masa ka tabbatar a gajiye yake Driven d'in, a hankali ya furta "ya sallam". saboda go slow d'in daya hango agabansa, ya sauke ajiyar zuciya, tareda yamutse fuskarsa mai cikeda kwarjini, a gogonsa ya kalla dake d'aure a tsintsiyar hannunsa Na haggu, ya dafe goshinsa dan ganin yanda lokacin sallar magriba ya gabato sosai.
Gaba d'aya ransa a 6ace yake, dayasan zai gamu da go slow d'inan daya hak'ura yayi salla kafin ya taho.....
Tunanin sane yakatse saboda Ringing da wayarsa tafara. batareda ya d'aukaba ya kai dubansa kan screen d'in wayar.
My wife tee..
Yagani 6aro-6aro yana yawo a fuskar wayar, ya d'an furzo iska kad'an daga bakinsa. d'aukar wayar yayi yana k'ok'arin kiranta sai kuma takuma kira.
Koda ya d'aga saiya saka Hans free, muryarsa mai matuk'ar sanyi da nutsuwa yace, " Assalamu allaiki Ummu Abul-khair".
"Wa'alaikassalam Nurrina, lafiya kuwa har yanzu baka shigoba? ko ka manta kana azumi ne?".
Murmushin sa ya saki mai k'ayatarwa, ya kai hannu yana shafa gemunsa daya k'awatu da bak'in gashi dakuma fari d'ai-d'ai (furfura). "Ban manta ba My tee.., wlhy go slow ne ya rik'eni, gashi har an shiga sallah".
Ya karashe maganar cikin 6acin rai.
A san yaye tace, " sorry Nurri, ALLAH ya kawoka lafiya to".
"Amin nagode, su Abul-khair fa? Kundai turasu masallaci ko?".
" eh sun tafi shida Sahib".
"Saifuddin fa?".
" bayajin dad'i,
koma islamiyya bai jeba".
"Amma shine bata fad'a min ba?".
Har zata bashi amsa saiya katseta, " kinga ina zuwa, naga motocin sun ragu". 'Bai jira cewartaba ya yanke wayar'. Motar yay ma key yay gaba, saboda hanya data bud'e, dama dai wani abunne ya haddasa go slow d'in.
Cikin mintunan dabasufi 30 ba ya k'araso gida, a k'ofar gida yay parking, yafito yay alwala a nan massalacin k'ofar gidansa, hankalinsa duk yana kan sallar magriba data wucesa, a gaggauce ya gaisa da mutanene dake k'ofar massalacin zaune suna jiran kiran sallar isha'i, ya shige yay sallar magriba, ya idar babu dad'ewa akayi isha'i.
Bayan an idar ya tsaya gaisuwa da jama'a makwafta sannan yakoma mota, horn yayi sau biyu.
Kusan mintuna 5, aka bud'e gate d'in. bayan ya shige ta maida gate d'in ta rufe. Sannan ta k'araso wajen motar tasa.
Yana zaune har yanzu a ciki, wayoyinsa yake k'ok'arin sakawa a aljihu, ta bud'e motar tana fad'in ''sannu da zuwa".
"Yauwa Uwargida na, ya gidan?".
"Lafiya lau yake". K'o k'arin fitowar dayake yasata matsawa baya, ya fito idonsa akanta, kwalliyar tata tamasa k'yau, haka kullum matan nasa suke