Showing 21001 words to 24000 words out of 104242 words

Chapter 8 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16061

Gaida kawu Yakubu yayi, ya amsa tareda masa ta'aziyya sannan suka k'arasa ciki.

Inda aka kwantar da baba sukaje, suduka kallo d'aya suka masa suka fara hawaye. Ba k'aramar k'una baba yasamuba gaskiya, abin ko dad'in kallo babu. barci yakeyi saboda sunmasa allurar barci kozai samu sauk'in rad'ad'in dayakeji.
Jiki a sanyaye sukabar d'akin, inda Amatallah take sukaje, tana kwance kamar yanda ya barta. matuk'ar tausayinta ya mamaye zukatansu, Uncle M.A ya kauda kansa daga kallonta saboda hawayen dasuka cika idonsa, d'an yatsa d'aya yasa ya goge sannan yanemi gefe ya zauna.


______________________________

Uncle M.A da Jabeer a asibitin suka kwana.
Wajen k'arfe 7:am suna shirin tafiya da gawar Ammi gida dan amata sutura Amatallah ta farfad'o.
Da sunan iyayenta ta farka a baki, tana kuka tana kiran Ammi da baba ta. da sauri wata Nurse taje ta sanarma doctor shu'aibu Amatallah ta farka.
Dagashi har Uncle M.A a hanzarce suka k'araso.
Tana ganin Uncle M.A tamik'e da sauri tana fad'in Uncle ina Ammina da babana!, suna ina dan ALLAH Uncle? ".
Rasa mizai fad'a mata yayi, yay tsaye kawai yana kallonta, idonsa taf da hawaye. Doctor shu'aibu ne kawai ke lallashinta. da k'yar yasamu ta tsagaita da kukan.
Doctor yamatso kusada Uncle M.A, ahankali yace, " Alhaji Muhammad yakamata mubarta taga gawar mahaifiyarta........
Bai k'arasaba Jabeer yashigo yana hakki, ''yaya! Yaya! Kuzo yaya Isma'il ne, gashi can.......
Suduka basuji k'arshen maganarba suka fice da gudu, harda Amatallah dake binsu cikin layin rashin k'arfin jiki.
'Dakin da Baban Ama ke kwance suka shiga.

Hannunsa dabai k'oneba sosai yake mik'oma Uncle M.A, yana kiran brother a ahankali. ga numfashin sa Na fita da k'yar.
Uncle M.A ya k'arasa da hanzari gareshi, shima hannun ya mik'a masa yana hawaye da fad'in sannu brother.......
Dai-dai nan Amatallah tashigo tana tangad'i, kawu yakubu da wasu mutane hud'u suma suka shigo d'akin.
K'ara Amatallah ta kwala tazube awajen saboda tozali datayi da babanta.
Dukansu kanta sukayi har Uncle M.A daya zare hannunsa daga na babanta.
Baisan ya cacumotaba yana kiran Khadija! Ke Khadija!! Please karkimin haka kema dan ALLAH Khadija. Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ya ALLAH gareka nake, a gareka kuma nake neman taimako......yak'arashe maganar yana fashewa da matsanancin kuka.
Shima Jabeer kukan yafara ganin yanda yayansa ke kuka sai kace ba babban mutum ba.
Baban Ama ma hawaye yake yana murmushi da kallon abokinsa da d'iyarsa.
Da k'yar doctor shu'aibu yasamu ya janye Amatallah daga jikin Uncle M.A.

😭kai jama'a, ALLAH ka gafarta mana.🙏🏻

Kusan mintuna 16 aka samu komai ya lafa, amma Amatallah tana a halin doguwar suma.
Uncle M.A ya koma inda Baban Ama yake, saboda kiran sunansa kawai yake.
Yanzuma hannunsa yarik'e, ahankali yake iya magana, amma duk suna jinsa sabida shiru da d'akin yayi.

_"d'an uwana kaga yanda k'addara tayi damu, tsakanin jiya kawai zuwa yau, mungodema ALLAH brother, danshine mafi hikimar masu hikima akan hakan, mutuwa tabbatacen abune akan kowanne bawa, saidai kowa akwai sanadin tafiyarsa brother, wannan mu shine namu sanadin d'an uwana, duk duniya banida kamarka, dukda inada dangi amma kafisu matsayi agareni, sun kashemin Saliha ta hanyar soka mata wuk'a, awannan halin na isketa bayan dawowata sallar magriba, nikuma sun kunnamin wuta, tabbas nasan yaran da Khadija taganine sukai wannan aikin, brother! Na d'auki hakan a matsayin K'ADDARARMU, ga Khadija nan nabaka halak malak, ita kad'aice tarage mini, babu kuma mai iya rik'emin ita tamkar ni sai kai d'an uwana Muhammad, ba ruk'on Amatallah kawai nakeso kayi nawani d'an lokaciba, sonake ta kasance a gareka har k'arshen rayuwarka. brother inaso yanzunan a d'auramaka aure da Khadija..."_

Wata muguwar zabura Uncle M.A yayi, jikinsa da muryarsa na rawa yace, ''brother mikake fad'ane haka?, haba brother khadija fa d'iyatace, inajinta tamkar su Saifudden ne a zuciyata, karkayi haka dan ALLAH brother, gara kace na aurama j........

_Da sauri Baban Ama ya katseshi cikin hawaye, "a'a brother karkace komai dan ALLAH, inhar nid'in d'an uwankane da gaske, bakuma k'yamar had'a zuri'a kakeyi daniba ka amince da auren Khadija tunda ALLAH bai haramta makaba, karkayi dubi da d'iyatace, kasancewarta a wajen kane kawai zaisaka ruhina nutsuwa a cikin kabarina, inada tabbacin har Abadan bazaka ta6a barinta tayi kukan rashina ni da mahaifiyarta ba, duk Wanda zaisan muhimmancin Khadija ko kulawa da ita bayankane, dan ALLAH ka amince, danni lokuta k'alilanne suka rage a cikin dak'ik'un rayuwata, brother nima mutuwa zanyi, insha ALLAHU tare zaku bunne gawata data matata, bazan rayuba brother, Nika d'ai nasan minakeji, please ka amince dan girman ALLAH da k'aunar dake a tsakaninmu._

Kowa a d'akin kuka yakeyi saboda tausayi.
Uncle M.A yana kuka yace, " indai hakan zai sakaka farinciki na AMINCE brother, na amince da auren Khadija dukda ina kallonta a matsayin d'iyata, insha ALLAHU zaka tashi brother, cuta ba mutuwa baceba..........
Kasa k'arasawa yayi saboda kuka daya sark'esa.
Baban Ama ya k'ara k'ank'ame hannun Uncle M.A yana fad'in "ngd da amincewarka brother, kasani farinciki, zanbar duniya cikin shauk'in farincikin ganin auren Khadija da ALLAH yabani ita d'aya tilo a duniya, ALLAH yasaka farinciki da kwanciyar hankali a rayuwarku, ALLAH ya hana duk wani azzalumi tasiri akan wannan aure, ina rok'on alfarmar a d'aura yanzunan brother kafin numfashina ya k'are.
Kai kawai Uncle M.A ke d'aga masa yana zubda kwallah



*****
Kawu yakubu da sauran mutane hud'u, sai doctor shu'aibu da abokan aikinsa doctors kusan 10+, sai Jabeer dawasu mutane k'alilan masu jiyya suka shaida d'aurin auren *_Alhaji Muhammad Ahmad labbo da Khadija Isma'il uba (Amatallah)_* akan sadaki naira dubu 30 da kawu yakubu yabada, bayan Jabeer yayi saurin zuwa ATM ya fidda, kawu yakubu ne wakilin ango, yayinda Baban Ama da kansa yay waliccin auren d'iyarsa tilo Khadija (Amatallah).
Ana gudanar da d'aurin aure cikin dariya da tsantsar farinciki, amma nasu Amatallah acikin kuka da tsantsar k'unar rai aka d'aurashi, babantane kawai keyin kuka da murmushi lokaci d'aya.
Cikin farin ciki ya k'ank'ame hannun Uncle M.A yana masa godiya, tareda k'ara jaddada masa Amanar Amatallah.
Kuka kawai Uncle M.A keyi yana fad'in "brother bazaka mutuba, kabar fad'a domin ALLAH, cuta ba mutuwa baceba brother....
Murmushi mai ciwo Baban Ama yayi, " brother sai dai hak'uri, mutuwa kam tazama tilas, ka tabbatarma Khadija na yafe mata, ALLAH ya albarkaci rayuwarta, yasaka mata hak'uri da juriyar danganar rashinmu, tayi hak'uri da k'addarar data shigowa rayuwarta, watarana sai labari, badan ALLAH baya sonta bane ya d'aukemu, watak'il hakan shine mafi alkairi a rayuwarta, ngdma ubangiji dayabamu damar rayuwa da ita na tsawon shekaru 18, har zuwa yau danaga aurenta, ALLAH yayi mata al ....bar.... ka.......
Baban Ama ya k'arasa maganar a rarrabe, ahankali kuma yafara kalmar shahada.
Lamarin daya rikita Uncle M.A kenan ya rungume Baban Ama yana kuka mai ciwo da k'unar zuciya......
Jin jikin Baban Ama ya saki yasaka Uncle M.A d'agowa yana girgizashi da kiran Isma'il! Isma'il!!!! Please karka tafi kabarni dan ALLAH, brother karka tafi please.........
Yanda Uncle M.A ke kuka da sambatu sai da kowa ya koka awajen, da k'yar aka iya janyeshi akan gawar Baban Ama, aka lullu6eshi da farin bedsheet d'in dake kan gadon.


😭😭😭😭😭
🙏🏻ya ALLAH ka gafarta mana.
Mutuwa kenan 'yan uwa, bata kwankwasa k'ofar kowa, babu d'an sak'on isowarta, babu alama ko yanayin alamomin kusantuwarta.
Saika gama shagala da duniyar kawai saikajita, babu shamaki tsakanin mutuwa da d'an Adam, koka shirya, kobaka shiryaba saita d'auka, komai girman mulkinka ko dukiyarka ko talauci, komin yawan mak'iyanka ko masoya saika tafi, karki manta, karka manta, karna manta, 😢😓😥😰😭👈🏻, ni da kai da ke da su duk zata iya d'aukarmu yanzunnan, wlhy duk sai mun mutu muma😭😭😭😭😭.
Suda suka tafi basuyi sauriba, muda muka rage bamuyi jinkiriba narantse muku😭..............✍🏻




*_Yau kam inason naga comments ruwa-ruwa akan auren Amatallah da Uncle M.A, a kowanne groups, inba hakaba ALLAH bazan cigaba da typing ba sai sabuwar shekara idan ALLAH ya kaimu. Yawan comments d'inku yawan kwarin gwiwwarku gareni, inhar banji k'yashin typing ba, baikama kuji k'yashin comments dabai wuce layi biyu zuwa uku ba gaskiya. Idan kunason naciga, nagani a k'asa🤷🏽‍♀. Dan yanzune labari zai fara😊_*








*_YA ALLAH ka gafartama banana._*😭🙏🏻

[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 11_*
____________________

Rayuwa tacigaba da tafiya musu a cikin nasarori, Isma'il yafara aiki anan jos, amma Muhammad yacigaba da kasuwanci, babu ma maganar Neman aiki a tsarinsa.
Kwanaki sunyi saurin zama shekaru, harga Amatallah da shekaru bakwai a duniya, duk hutun duniya kuma a kano takeyinsa, tattali da kulawa mai ban mamamki take samu daga khadija da muhammad, bazaka ta6a cewa ba d'iyarsu baceba, tayi masifar sabo dasu sosai. itama dai mamanta tundaga ita babu wani labari, haihuwar taimusu cak ta tsaya. kamar yanda matar Muhammad itakuma sai a lokacinne ALLAH yabata ciki, fad'a muku murna da farincikin dasukayima 6ata lomacine, amma kam lamarin ba'a magana kam.
Watannin cikin Khadija 9 da kwana 9 tafara nak'uda, tasha wahala matuk'a wajen wannan haihuwa, da k'yar ALLAH yabata ikon haihuwar yaro namiji, sai dai tana haihuwarsa koma ganinsa bataiba ALLAH ya d'auke kayansa, ta rasu😭.
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, fad'a muku rud'anin da Muhammad yashiga 6ata lokacine ma, murnar haihuwa tazama kukan rasuwar Khadija da rud'anin da Uncle M.A ya tsinci kansa. yaronma kwanansa uku a duniya yakoma.
Halinda uncle M.A yashiga sai da yakaishi ga kwanciya asibiti, kusan tsawon sati biyu sannan aka sallamosa, suka cigaba da masa addu'ar ALLAH yabashi dan gana.
Tundaga wannan lokacin rayuwar uncle M.A ta canja baki d'aya, yazama silently, maganama bayasonyi, inkaga maganarsa babane kokuwa isma'il Baban Ama.
Shima Baban Ama a 6angarensa lokacinne kawu mahaifinsa ALLAH yamasa rasuwa, wata d'aya tsakaninsa da Khadija, shima kan yashiga rud'ani sosai, Dan yana k'aunar mahaifinsa, shikad'ai ya rage masa, gashi kuma yatafi.
Aifa rasuwar kawu takuma rikita Uncle M.A, dole baba yaymasa shiri yabar k'asar, yakoma Ghana da zama wajen wani abokin Baban.
Uncle M.A yacigaba da zama a Ghana har tsawon shekara uku, ganin karyayta zaman banza sai kawai yafara karatu na wani cause.
A Ghana Uncle M.A yahad'u da Aneesa, anan makwaftan abokin baba take, tunda tagansa tarikice, sai dai takula yana cikin matuk'ar damuwa, wannan yasata d'aura d'ammarar dawo masa da farincikinsa, musamman data samu cikakken bayani akan tarihin rayuwarsa.
Tasha matuk'ar wahala kafin tasamu kan Uncle M.A, kafin komai ya dai-daita Soyayya mai k'arfi tashiga a tsakaninsu.
Aneesa k'yak'yk'yawace sosai gaskiya, gata nitsatstsiya, ga kuma ilimi, (kunsan dai 'yan Ghana suna karatu sosai), k'yawwawan halayen Aneesa ne sukajawo k'aunarta mai k'arfi a zuciyar Uncle M.A.
Sai dai kuma lokacin da Uncle M.A yashirya yazo Nigeria danya fad'ama baba a kai kud'in aurensa saiya tarara an saka masa ranar aure shida Fateema d'iyar kawu yakubu k'anin innani, hankalinsa yatashi, amma bashida yanda zayyi, danshi mutumne dabai k'etare maganar iyayensa, dasunce yayi yakeyi, Dan haka ko'a fuska bai ta6a nuna bayason auren Fateema ba, sai dai yasanarma mahaifinsa abinda yazo dashi shima.
Baba yaji dad'i sosai, babu kuma 6ata lokacin aka d'aura aurensa da Fateema, bayan sati uku sukaje Ghana kai kud'i, sai dai iyayen Aneesa basu wahalar dasuba sukace kawai a d'aura auren ya d'auki matarsa, tunda abune ba k'asa d'ayaba, su baba sunyi farinciki dakuma jinjina dattako irinna iyayen Aneesa.
A kwana biyu akayi komai aka gama, aka basu amaryarsu.
Uncle M.A bai gayama Aneesa aurensa da Fateema ba saida suka iso Nigeria.
Ai kuwa Aneesa tayi matuk'ar birkice masa, sai da yasha bak'ar wahala kafin yasamu kanta lokacin.
Aneesa da Fateema ba gida d'aya yahad'asuba lokacin, Dan gidanshi da yazauna da Khadija ginin mace d'ayane, kuma bashida k'arfin yin gini, dole yakamawa Aneesa haya anan cikin anguwar, babu nisa da gidansa Inda Fateema take.
Dukkan hidimar bikinsa biyu Isma'il ne tsaye, (Baban Ama), Dan zumincinsu nan, duk da yanzu yanayin aiki kansasu yin watanni basuga junaba, amma kullum suna mak'ale da waya. Bakuma ko yaushe iyalansu ke zuwa gidajen junaba, saboda Saliha ta girmi su Fateema, kuma batawani saba dasuba sosai kamar Khadija, amma suna girmamata gaskiya.
Baba ya tattara dukkan kasuwancinsa ya mik'ama Muhammad gaba d'aya, yace yacigaba da juyawa kawai, tundaga lokacin uncle M.A yakoma kasuwa baki d'aya, dukda yana wani aiki a nan B.U.K
Ubangiji ya sakama kasuwancin hannu, dandanan shagon atanfofi ya bunk'asa, har suka bud'e wani. Shekara d'aya da auren matansa duk suka haihu, amma Fateema Ce tafara haihuwar Namiji, aka saka masa Ahmad suna kiransa (Abulkhairi) saboda sunan babane, Aneesa ma ta haihuwa, sai dai d'iyar batazo da raiba.
A cikin shekara biyu Uncle M.A harkar kasuwa takuma fad'ad'a, dan zuwa yanzu sunada kusan shaguna Hud'u, sunada shagon atanfofi, shaddoji, materials, gale, kaya 'yan kanti, dakuma kayan yara, kowanne nau'in sittira kaje saika samu a shagonsu.
Zuwa lokacin Aneesa ma ta haihu, Namiji, Wanda yaci sunan Abdul'aziz (Saifudden), sunan babanta.
Shekara d'aya tsakani itama Fateema tasake haihuwar Namiji Isma'il (yayma Baban Ama takwara😄), yana cemasa Sahibi, (Sahib) kenan.
A lokacinne kuma yagama ginin gidansa daya d'auki tsawon shekaru uku yanayi, ya had'e matansa duka a waje d'aya.
Had'uwar Aneesa da Fateema kam bata zama da sauk'iba, Dan rikici sosai akaita sha, Aneesa tanada kishi sosai, bata k'aunar ganin abinda zai ra6uda mijinta ko kad'an😄.
Itama Fateema a kwai kishin, amma tafi Aneesa wayau Na 6oyewa. Sai da yaymusu zagir-zagir sannan yasamu sauk'in yawan rikicinsu, daganan aka koma kishin kissa, to duk masu ilimi aka tara, dolene salon kishinsu yayi matuk'ar bigeka gaskiya, Dan kowa sotake tazama star a wajen boss.
Zuwa yanzu Fateema Nada 'ya'ya uku, Ahmad (Abulkhairi) Isma'il (Sahib) Ai'sha mai sunan mamanta (Ummita).
Aneesa nada biyu, Abdul'aziz mai sunan babanta (Saifudden), Sai Zainab mai sunan Innani (Siddiqa).

Shekaru uku dasuka wuce ciyo yasamu baba, kad'an-kad'an abin ya fara masa, tun suna magani a tsaitsaye harya kwanta rijuf, sosai Alhaji Muhammad ke tsaye akan ciwon baba, sunje asibitoci da dama Nigeria amma lamarin sai dai addu'a kawai, ciwon koya tafi saiya dawo, saboda yahad'a da girma, ciwon baba dakuma harkar kasuwancinsa daya bunk'asa, ga aiki yahanashi ziyarar jos, sai dai koyaushe Baban Ama Na hanyar duba jikin baba, wani lokacin suzo da Ammi wani lokacin shi kad'ai, Amatallah kam bata biyosu, tun wani zuwa datayi ita kad'ai Hutu su Aneesa sukayi fad'a a kanta itada Fateema tace bata sake zuwa.
Koyaya su Ammi sukayi da ita saitak'i biyosu, in zasuzo saitayi tafiyarta gidan ka kanninta iyayen Ammi, Dan zuwa lokacin tafara zama budurwa, tana secondary kusan js 2, duk da yakamata acema taje SS, amma yawan rikin da jihar jos ke fuskanta yasaka karatun yana samun koma baya a jihar sosai.
Kullum zancen Uncle M.A ina best daughter d'insa? yakamata tazo masa Hutu.
Amma k'iri-k'iri Amatallah tak'i.
Hak'ura yayi yabarta saboda shima ciwon Baban da dawowar nauyin gidansu gana iyali ya gama d'auke hankalinsa, ga kuma aiki dayakeyi duk da ba kullum yake a office ba dai.

Kwatsam sai Baban Ama yasamu wani mai Maganin gargajiya, ya d'aukeshi sukaje har Kano domin duba baba, Alhmdllh kuma aka dace, Dan baba nasamun sauk'i sosai da wannan Magani, bayan yak'arene Uncle M.A yazo jos kuma kar6awa baba wannan Magani.
Anan yaga yanda Amatallah ta girma, duk saiya rikice da mamaki da al'ajabi, Dan yanzu tana shekara 19, SS 3 kuma a Secondary, sune zasu zana SSCE a wannan shekarar.
ya d'aukko hotunanta dan nunama matansa suga yanda ta koma, amma sai kishi ya rufe musu ido, suka fara tunanin ko sonta yakeyi, saboda motsi kad'an yace, "my best daughter".
Shikuma kawai mamakin yanda tayi girmane ya tsaya masa a zuciya bawani abuba. amma matansa sun hau sun zauna sonta yakeyi. To kuma ga yanda al'amarin ubangiji ya kasance, Ashe ALLAH ya k'addarata acikin matansa Na aure😭.


Wannan shine asalin labarin wad'annan brothers guda biyu.

Hummmm koya zata kaya kuma idan matan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login