Showing 63001 words to 66000 words out of 104242 words

Chapter 22 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16042

kece zaki zubar da kimarki a idonta, sannan kekuma Khadija ki Sani daga Fateema har Aneesa gaba dake suke, koda ban aurekiba amatsayin iyaye suke a wajenki, ki kiyayi ma wata rashin kunya a cikinsu, idan naji hakan zanyi matuk'ar 6ata rankine."
Gaba d'ayansu kowacce gyad'a kanta tayi alamar amsawa.
Yace, "ALLAH yay muku albarka, yakuma bamu zaman lafiya gaba d'aya".
Suka amsa da amin.
" yauwa sai maganar kwana, daga yau Khadija zata fara kwanakinta bakwai da shari'a ta tsara, saikuma bayan tagama acigaba da kwanakin dazaku za6a a yanzun. nabaku za6i, kwana bubbiyu ko uku-uku ko d'aid'aya? Wannene za6inku?".
Duk shiru sukayi alamar tunani, Aneesa tace, "nidai anawa ra'ayin kwana d'ai-d'ai, amma idan ana ganin bibbiyun zaifi shima banda matsala, kwana uku dai yaymin nisa, bazakaga minjin kaba har kwana shida kenan, haba kudai duba lamarinnan".
Murmushi kawai Uncle yayi baice komaiba, sai kallon Fateema dayayi alamar tace wani Abu itama.
Murmushin mugunta tayi, itama tafison bibbiyun amma danta bak'anta ran Aneesa tace " nikuma a nawa ganin ukun zaifi, sai ka more sosai da mijinka yanda ya kamata kokuwa? amma idan an tsaya a biyun ma banida matsala nima".
Wani azababben kallo Aneesa tamata, badai tace komaiba.
Nanma murmushi Yayi, yakai dubansa ga Amatallah, wadda tunda aka fara maganar kanta a k'asa tana wasa da bezar gyalenta, tana jinsu sarai, amma aganinta maganar ta manyace, shiyyasa ma tayi k'asa da kanta.
"Khadija kefa, bakice komaiba?".
Kanta ta girgiza amalar batada abin fad'a.
" miyasa? Kema matar gidance aii, kuma kinada hak'k'in fad'in ra'ayinki, fad'i kwana nawa kike buk'ata ke?".
Duk da tahowar wani kuka haka ta dannesa, dan batason suga lagonta, murya a sanyaye tace, "Uncle nidai duk yanda su Aunty's suka tsaya yamin, ni dama za'a cireni a ciki nafi buk'atar hakan".
A zuciyar Fateema tace gulma kenan yarinya, itako Aneesa bayan ta antayama Amatallah harara tace " munafuka". a zuciyarta.
Uncle kam wani k'asaitaccen murmushi yayi yakuma gyara zamansa yace, "ai cirekinnan ba abune mai yuwuwaba Khadija. daga nan ya maida kallonsa gasu Aneesa da kowa haushi ke nuk'urk'usar ranta, yace, " Anyway duk naji za6inku, amma tunda naga kowannenku nada za6in ra'ayi d'aya way not muzauna akansa kawai, inaga kwana bibbiyun yayi OK?".
Gaba d'aya sukace yayi, amma banda Amatallah da ko kallonsu takasa yi.
Daga nan Nasiha yakuma musu mai ratsa jiki da 6anrgo, sannan suk rufe da addu'a ya sallamesu.
Bayan sun mik'e ya kalli Amatallah daketa hanzarin fara fita yace, "Khadija!".
Cak ta tsaya zuciyarta na dukan hamsin-hamsin, tajuyo da k'yar amma bata kalleahiba.
Murmushi yayi yace, "a kawomin abinci inajin yunwa".
Fateema harta saka k'afarta waje taji abinda yace, murmushin mugunta tayi, dan tasan Aneesa ce tayi abincin ba Amatallah ba.
Itama Amatallah d'in yawu ta had'iye da k'yar sanan tace, " Uncle Anty Aneesa ce tayi girkin ai".
Kallon Aneesa yayi kad'an ya kauda kai dan ganin tacika fam, "uhm koda ita tayi ai kece yadace ki bani d'in ko".
Kanta ta jinjina masa kawai tafice a sanyaye.
Aneesa har zatayi maganar kuma, komi ta tuna saitayi shiru ta juya tafita rai a 6ace.
Wata 'Yar dariyar mugunta yayi ya gyara zamansa...............โœ๐Ÿป



Mace hummm, Uncle karfa Aneesa ta ๐Ÿคญbabu ruwana dai, baza'aji mutuwar 'yan group d'ina a bakinaba๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜œ
๐Ÿƒโ€โ™€






๐Ÿคฉ๐Ÿ‘Ž๐Ÿป




*_ALLAH ka jik'an iyayenmu_*๐Ÿ˜ญ๐Ÿ™๐Ÿป
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingโœ๐Ÿป_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*๐Ÿ’ก
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* โ‰
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce๐Ÿค™๐Ÿป_*


____________________
*_Number 27_*
____________________


Koda suka dawo massalaci Uncle 6angarensa ya koma, dama Amatallah nata addu'ar ALLAH yasa karya dawo. gadon takoma ta kwanta, tajawo filon daya d'ora kansa tana shinshinar k'amshin turarensa daya manne ajiki, tuni tana matuk'ar son k'amshinsa, dan bata mantawa lokacin tana kusan 11years sannan tazo hutu, ta ta6a cewa yabata turarensa tanason k'amshin, lokacin kam dazata tafi yabata, babanta yayta fad'a akan yazai bata turarensa mai tsada haka. Uncle yace ina ruwanka, wannan tsakanin uba da d'iyane. Dole baba yay shiru ya barta da turaren. A saninta da k'amshinnan tasansa tun fil azal, dukda takula yanad'an had'awa dawasu turaren yanzu, takuma baje hanci tana shinshinawa sosai. wani tunanine ya fad'o mata a rai, anya kuwa Aneesa zatayi break fast yau?, ganin batada Amsa ta jawo wayarta da nufin kiran Fa'iza tabata haske, dan tace mata a jiya Amaryarsu zata kar6i miji.
Bugu d'aya kuwa Fa'iza ta d'aga.
Da kirarin amarya kinsha k'amshi tafara mata.
Amatallah tace, "kai Fa'iza banason tsokana wlhy, ni babu wata amarya anan".
"Hhhh 'yammata zaki magantu, inba amaryaba miyasa kikaimin wannan kiran sassafen?".
" humm bazaki ganebane kawai, nifa tambayarki zanyi?".
''To ina saurarenki".
"Yanzu kenan nizanyi girki a gidan". Amatallah tafad'a kamar zatayi kuka.
Sosai Fa'iza takeyin dariya, " kai Amarsu irin wannan shagwa6a haka, tuna dai banine Uncle d'inba".
Amatallah tafara k'uluwa, tace, "ni inbazaki fad'a minba Na kashe wayata".
" sorry amaryar Muhammad labbo" Fa'iza ta fad'a tana danne dariyarta, "yanzu dai kinga inda da had'inkai ai suyakamata sucigaba dayin abincin harki gama kwana bakwanki, amma dai nasan dakamar wahala tunda Aneesa cema mai girkin kawai, Uwargida Na fama da kanta, kawai kije kiyi, kuma wlhy ki matse basira kiyi Wanda zai tada kunnensa sama dan dad'i, kindai San d'and'anon abincin kowacce acikinsu, dan haka kema saikizo danaki salon, tunta ALLAH bai hana mijinku ajiye muku abubuwan buk'ataba dai-dai gwargwadon iko".
"Hakane Fa'iza ngd sosai, bara naje nayi komai da wuri, kinsan yau dai Lectures d'inmu duk Na safene".
" hakane kam, ALLAH yabada nasara".
"Amin saimun had'e a school".
Duk suka yanke wayar.


(Kunsanfa Amatallah batasan Uncle Na azumiba).

Ajiye wayar tayi tafito domin shiga kichin.
Tad'an dad'e tsaye tana nazarin mizatayi, Google tashiga tayo searching break fast mai k'ayatarwa, taduba taga alhamdllh sunada mafi yawan abinda ake buk'ata, Wanda babu kuma tabarsa akan zatayi manage kawai ahaka.
Dan danan gida yafara d'aukar k'amshi, abinka da kitchen a falo.
Daga Aneesa har Fateema suna can sunama yaransu shirin makaranta. Cikin abinda bai wuce 1ยฝ ba ta kammala komai, kamar yanda taga masu gidan kanyi tagyara babban falo ta jere komai a tsakkiya, takoma ta gyara kitchen d'in ta wanke abinda ta 6ata, a gaggauce takoma 6angarenta nanma ta gyara dukda bawani datti kedashiba tunda itama ba zama takeyiba.
Sai lokacin ta lura da mug d'in shayi da ledan cake dana per water, kofin ta d'auka tad'an jujjuya da mamakin waye yasha tea?, itadai tasan batashaba, a fili tace, " ko yunwa ta tashi Uncle ne yasha? "Inaga hakane kam". tafad'a tana kwashewa tanufi kitchen d'inta, d'auraye kofin tayi ta maidashi mazauninsa, tadawo takarasa gyaran bedroom d'in, annan taci karo da wayoyinsa, kwashesu tayi ta zube a drowar gefen gadon, su Kansu k'amshin sukeyi, gaba d'aya k'amshinsa yakama komai nasa Na mu'amular yau da kullum.
Saida ta tabbatar ta kammala komai sannan tashiga wanka. babu 6ata lokaci tafito tayi shirinta cikin zani da Riga Na atanfa green da ratsin Orange, kayan sunmata k'yau sosai, dansun haska bak'ar fatarta datasha gyara tanata walk'iya da shek'i, bawata kwalliya tayiba kamar kullum, tana cikin d'aura d'ankwali yaturo k'ofar yashigo da sallama.
Ta amsa kanta ak'asa batareda ta kalleshiba, har k'asa ta tsugunna ta gaisheshi, idonsa akanta ko k'yaftawa bayayi ya amsa yana guntun murmushi, gabanta yak'araso yasa hannu biyu ya kamo kafad'unta ya mik'ar da ita, "my best! Kin iya gayu fa, koda yake agayama 'yan jos gayu, dama anan 6angaren Ku kwararrrune (sai dai k'arya inji ni......lol๐Ÿคญ๐Ÿ˜œ) jasawa amin afuwa tsokana ce.
Ita duk kunyarsa ta isheta, kanta ak'asa tana murmushi dan jin furicinsa.
Ya matso da ita jikinsa ya rungumeta, a kunnenta yace, "miyasa bakizo kin shiryani ba? Ko bakiga haka matana su keyi ba?".
Kunya takuma kamata, takuma lafewa sosai ajikinsa tana shak'ar daddad'an k'amshinsa, kusan mimtuna 2 ya d'agota yana fad'in " my best karki karyamun azumifa".
Yanzun kam sosai ta kallesa danjin furicinsa, sanye yake cikin farar d'anyar shadda wadda tad'au aikin wuta mai masifar k'yau, yaukam babu malum-malum, rigar kuma kad'an ta wuce gwiwarsa, hularsa Brown color tamkar surfanin gaban rigar, (duk a abunda baifi 3Seconds tayi wannan kallonba.....lol๐Ÿ˜‰), ta marairaice fuska a shagwa6e tace, "Uncle azumi kuma?".
Gira ya d'aga mata yana murmushi kafin yace, " kin manta yau alhamis ne".
Kad'an ta turo bakinta gaba Dan tuna wahalar datasha wajen had'a break fast, wlhy datasan yana azumi baza tayi mai dad'in haka ba.
Hannu yasa ya d'ago ha6arta "ya dai? sarkin shagwa6a".
Dariya yabata dayace sarkin shagwa6a, ta murmusa har hakwaranta Na bayyana, " Uncle banfa san kana azumiba, natashi naita wahalar had'a break fast ".
" ooh my best! Sorry, kaina bisa wuya kinji, amma kiyimin irinsa a bud'a baki zanci kinji. kar6a wannan ki sakamin". ya kamo hannunta ya zuba link d'in hannu yana mik'a mata hannunsa na dama.
Dukda tanajin nauyi haka takama hannun tafara k'ok'arin saka masa, danta iya, wani lokacin takan sakama babanta idan Ammi tana busy zai fita. tsaf ta saka masa har yayi mamaki. "My best dama kin iya?".
Kallonsa tayi tana murmushi, " Uncle ai ina sakama baba".
Shima murmushi yayi tareda kai hannu ya shafa fuskarta yana fad'in ''oo dadys girl ".
Dariya duk sukayi.
Yace, " k'arasa shirin muje kiyi break nima school d'inku zanje yau".
"To Uncle".
Fita yayi, itakuma ta k'arasa shirin nata, ta saka hijjab da takalmi tafito, duk suna falo, yara nayin break fast, gaishe da kowannensu tayi cikin girmamawa, kowacce ta amsa cikin danne kishinta, Dan tunda ta fito sukebinta da kallo kozasuga canji a tafiyarta, saidai kuma normal take tafiya babu wani alamun tangard'a. tsaf Uncle duk ya fahimcesu saboda duk yanda suke kallon Amatallah d'in akan idonsane, 6oyayyan murmushi kawai yayi, aransa yace " mikukeci nabaka Na zuba guy's ".
Yaran duk suka gaidata, ta amsa cikeda kulawa kamar yanda ta saba. Itama zama tayi taci abincin kad'an, data d'ago saita kama Uncle na kallonta, daga k'arshe dai ta d'auke kanta gaba d'aya data kula duk idon matansa a kansune. Shiko gogan ko a jikinsa.
Suna kammalawa suka mik'e, mai napep d'in dake kai yara school yazo, atare suka fito, yaran suka shiga napep sukuma motarsa, Amatallah ta bud'e musu gate d'in dansu Aneesa babu Wanda yamasa rakkiya (kishi ya hana ...lol๐Ÿ˜‚๐Ÿ˜œ).
Sunama ficewa Fateema da Aneesa duk sukaja tsaki, saikuma suka kalli juna danjin tsakin nasu yafita lokaci d'aya, basarwa Fateema tayi tad'iba break fast tafara ci, Dan yanzun batada jimirin yunwa.
Murmushi mugunta Aneesa tayi, a ranta tace, " muguwa kawai, a fuska tamkar ta kwarai, amma zuciyarki saidai ALLAH. a fili kam tashi tayi tashige 6angarenta.
Fateema tarakata da harara๐Ÿ˜†.

Uncle kam tunda suka tafi Amatallah tayi tsit, cikin raba hankalinsa biyu yafara janta da hira, yana kallon jama'ar gari da yara 'yan makaranta, saikuma tuk'i.
Amatallah dai nata murmushine, wani lokacin kuma tace, ''eh ko a'a". Bai damuba dan yasan muskilancin ta, ahakanma washi anajin kunyarsa da kimarsane, amma da Jabeer yana bashi labarin yanda suke kasancewa idan zai kaita school kozai d'akkota yaci dariya.
Maimakon yawuce makaranta kai tsaye saiya wuce gidansu, batayi maganaba saima dad'i taji, shi kansa yaga farin cikin a fuskarta, murmushi kawai yayi baice komaiba.
Cikin zumud'i tawuceshi ta fara shiga gidan.
Da shehu tafara cin karo yana alwala a tsakar gida, da alama sai yanzu zaiyi sallar asuba.
Cikin tsokana tace, "su Ya Shehu dai baza'a canjaba, k'ara'i dai kullum".
Dariya yayi yana mik'ewa, " kece da farar safiya haka Antynmu?....."
Bai k'arasaba Uncle shigo, hakan kuma yayi dai-dai da fitowar Nazeefa itama daga kitchen saboda muryar Amatallah data jiyo, rungume juna sukayi suna murna, yayinda shikuma Uncle kema Shehu fad'an k'inyin salla da wuri, harma 8 ta wuce yau.
Tare suka shiga d'akin baba, innani ma nacan, sun taddashi zaune innani na bashi kunu, aladabce suka gaidasu da tambayar jikin baba.
Baba Yaji dad'in ganinsu a tare kuwa, hakama Innani dukda bata nuna a fuskaba.
Baba yace, "Muhammadu idan kadawo aiki inason ganinka". a hankali yake maganar.
''To baba, insha ALLAH dana taso zanzo".
Basu dad'eba sosai suka musu sallama suka fito. bayan sun gaisa da Jabeer shima, Dan sanda suka zo yana wankane.
Sun tafi da alk'awarin Nazeefa na zuwa weekend d'inan.
Yauma ta iske su Rita na jiranta, Dan harma F'aiza tarigata zuwa, ta k'arasa tana tsokanar Fa'iza da wak'ar mai ciki eye ganinan tafe.
Duk dariya sukayi, Fa'iza tace, " haba yarinya kema kwana nawane".
Hararta Amatallah tayi, tace, "fatan tsiya".
Goodness tace, " na arzik'i dai".
Dariya duk suka kumayi.

Kusan 12 Lecturer d'insu na English bai shigoba, dukma sun fidda rai da zuwansa, wasuma suna k'ok'arin barin hall d'in sai suka hango wani malami na tahowa. Gabatowarsa ta saka wani d'alibi fad'in "kuttt wlhy kowa ya nutsu boss ne da kansa zai mana lecture yau......"
Bai gama rufe bakiba Uncle yashigo, mamaki sosai Yakama Amatallah, dama Uncle yanada alak'a da school d'innan har haka? Tasan dai kamar yana aiki anan, amma bata d'auka yana Lectures ba. Mamakinsa yakuma kamata, yayi masifar tsare gida alamun babu wasa kenan, ta tuna Uncle mai yawan fara'a ashe haka yake a waje. Sai dai yanda 'yan class d'in suka nutsu abin yaso bata dariya, musamman idan tayi dubi da yanda aka raina wasu lecturers d'in, bakamar wasu group na samari da 'yammata da ake kira *Gayun zamani* kallonta takai mazauninsu tagansu a nutse kamar basuba.
Kallonta ta maida ga Uncle d'in dake magana cikin nutsuwa dakuma kwararren Turanci. Yana bayanine akan zai d'aukesu lecture d'in saboda lecturer mai d'aukarsu yasamu Accident a daren jiya.
Nan suka shiga mishi addu'a.
Tunda yashigo yaga Amatallah, amma yashare tamkarma baisan da ita a hall d'in ba, saidai tuni Fa'iza dasu Rita suka ga kallon dayake satarta dashi, hakanne yasasu shan jinin jikinsu kodai shine Uncle? dukda Amatallah bata sanar dasu Uncle na aiki ananba.
Harya gama lecture d'in yafita sannan suka samu damar tanbayarta, dariya kawai tayi batace komaiba, yayinda Rabin hankalinta ke kan 'yan class d'in dake gulmar Uncle, wani d'alibi harda mik'ewa yaje inda lecturers kan tsaya idan zasuyi lecture ya kwaikwayi salon Uncle d'in, nanfa aka kwashe da dariya, d'alibin yace, "please guys bai burge kuba?".
Nanma suka amsa da sosaima ana dariya, wata ma a 'yan matan ta mik'e tana fad'in " aini babu abinda yafi d'aukar hankalina gareshi sai salon maganarsa mai sanyi da takunsa, kai jama'a malamin nan yayi over, inama zan dace da na tsinci tsuntsu daga sama".
Nanma dariyar aka Sanya da sakin ihu.
Ta kuma kwaikwayon muryarsa yanda yafad'i sunansa, my Name is Muhammad Ahmad labbo, nine zan cigaba da jagirantarku kafin mai d'aukarku yasamu sauk'i.......
Salon nata yasakasu kwashewa da dariyar ihu suna kiran saikinyi zee-zee.
Ta shafi inda ya d'ora hannunsa ta sumbaci hannunta da fad'in "I love you so much Muhammad mai babban suna".
Nanma dai bata sake zaninba ihu sukayi.
Dukda wannan Abu dake faruwa Amatallah tayi kicin-kicin da fuska ko sau d'aya batayi dariyaba tunda budurwarnan tafara kwaikwayon Uncle.......
Maganar zee takuma katse mata tunaninta, " kai my guys, ammafa bawan ALLAH nan akwai tsare gida, ya matarsa keyi?".
Wani yay caraf yace "zee-zee dakin Shiga daga ciki zaki canja manashi".
Dariya ta tuntsure dashi, sannan ta rungume hannunta ak'irji tana lumshe ido, " wayyo! ALLAH Da nikam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login