Showing 6001 words to 9000 words out of 104242 words

Chapter 3 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16063

cikin kwalliya, kowa burinta tazama gwana awajensa.
Murmushi yamata yana kashe ido d'aya, cikin sassanyar muryarsa yace, " kinyi k'yau my tee...".
Itama murmushin tamasa, kafin tace, "thanks you Nurrina".
Kansa ya jinjina mata, "da akwai kaya a backseat ki d'ebo su".

"Okey".

Yara ukune suka fito da gudunsu suna fad'in "oyoyo abbunmu!!".
Murmushi yasaki, har fararen hakwaransa Na bayyana, idonsa akan yaran nasa, ya bud'e masu hannayen sa, hakanne yabama babbar rigarsa ta blue black d'in shadda bud'ewa. gaba d'ayansu suka shige ciki, ya had'asu ya rungume shima yana fad'in " oyoyo my children's, I Miss you all".
Matarsa data gama kwaso ledojin dake kujerar baya tatsaya tana kallonsu fuskarta d'auke da murmushi.
Tace, "oya to a sakeshi ko yagaji, kumuje ciki".
Sakinsa sukayi su duka, yakama hannun Sahib da Ummita, Abul-khair mai d'an wayon ya kar6i wasu daga cikin ledojin hannun mamansa, suka nufi hanyar k'ofar babban falon gidan.
Sahib da Ummita kam sai zabga masa labarin school sukeyi, murmushi kawai yakeyi.

Da sallama suka shigo falon, nanma wata matar nagani tsaye a falon, hannunta rik'eda yarinya dake kunshe cikin kayan sanyi.

Wannan ya tabbatar min cewa matansa biyu😊.

Fuskarta d'auke da murmushi ta k'araso inda suke tana masa sannu da zuwa.
Amsawa yayi shima yana murmushin da k'arema amaryar tasa kallo cikin jin dad'i, dan itama cikin kwalliyar take mai d'aukar hankali. (A raina nace, ''wannan ai sai a gaza gane mai girki🤥🤔").
Hannu ya mik'a mata alamun tabasa babyn hannunta.
Ta saka masa babyn dabazata wuce 3month ba a hannun nasa.
"O, my Siddiqa barci kikeyi?". Yay maganar a hankali yana sumbatar goshin yarinyar. Sannan ya mik'a mata ita, " bara naje Na d'an watsa ruwa Neesa!".
Cikin salon kissa tace, "okey Dear".
Harya fara tafiya saiya tsaya, ya juyo yana kallonta, " Saifudden fa?".
"Jimm tayi alamar tsoro, ta kauda idonta daga kansa tace, " yana barci".

"Barci? A wannan time d'in? Halan lafiya?".
Yanzunma a cikin jimamin tace, " bashida lafiya".
"Shine kika kasa kirana ki sanar min?". bai jira amsarta ba yafara hawa matattakalar benen dake tsakkiyar falon, dama tuni yaran mamansu tajasu sunyi 6angaren ta.
Kamar zata fasa kuka tabishi da kallo, tasan haushi yaji, Dan mijin nasu bai had'a matsalar 'ya'yansa data kowaba, yanason yaransa sosai, kodan yadad'e bai samu haihuwarba ne? Oho.
Jiki a sanyaye tashige nata 6angaren itama.

Tun daga falon k'amshi mai dad'i yabugi hancinsa, ya shak'a ya lumshe idanunsa, babbar rigarsa yafara k'ok'arin cirewa, ta k'araso da sauri ta taimaka masa suka cire tare.
Cikin kashe murya tace, " da kanka Nurrina? ".
Murmushi kawai yay yana shigewa bedroom d'insa. da sauri ta d'auki babbar rigar tabi bayansa domin taimaka masa yayi wanka...............✍🏻










*_ya rabbi ka gafartama mahaifanmu 😭🙏🏻_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 6_*
____________________

Baban Ama.. ne ya kalli uncle M.A dake zaune gefenshi bayan sun kalla cin abinci, hankalinsa ya maida gaba d'aya agareshi. "Brother ina saurarenka".
Uncle M.A ya d'an gyara zamansa, kafin yay gyaran murya kad'an.
"hugm!, brother kasan mi nake tunani kuwa? Akwai wani Abu kusan 1year data shige daya d'aga hankalina, dawo da maganar bashida wata ma'ana, amma yanda rikicin ya kasancene yata6a zuciyata. matasan k'asarnan sunada buk'atar mai jagorancin tunaninsu, saboda duk wani Abu da zaije yadawo akansu yake k'arewa, dasu ake amfanin wajen haddasa duk wani rikicin SIYASA KO K'ABILANCI da ADDINI a k'asar nan, sannan kuma sune akafi kashewa, su akafi lalatama rayuwa. (kuma kullum sune cikin k'orafin gwamnati batayi dasu). Al'halin sune suka maida darajarsu can k'asa har kowacce gwamnati idan tazo take tunin k'ask'antar dasu, ni aganina matasanmu sunada hanya mafi sauk'i dazasu jagoranci k'asarnan brother, amma bata hanyar rikicin siyasa ko k'abilanci ko 6angaranci ko fad'an addiniba.......".

"Hakane brother, amma tayaya kai kake ganin zasu fahimci manufarmu, kafa tuna cewa matasan namu, ba kowan nensu ke maida hankali akan karatu ba, idanma sunyi sai domin aiki, ta wacce hanya kake ganin yakamata su fahimci sune k'asar?".
Murmushi uncle M.A yayi, "yauwa brother anzo wajen, wannan tambayar nakeso kamin dama".
" bara kaji brother, tunfa farko mu SIYASA bata kar6i Africa ba gaba d'aya, wlhy sanadin SIYASA komai namu ya LALACE, da bamusan k'abilanciba, saboda kowa yana a 6angarensa, idan kaga d'an wancan k'abila cikin waccan to harkar kasuwancice ta kaisa. amma tundaga lokacin da Turawa sukace ga SIYASA komai namu ya canja salonsa, tundaga lokacinda turawan mulkin mallaka suka bama wasu 'yan k'asarnan shugabancin wasu yankunan kasarnan komai yafara dagulewa, domin hakanne yazama ummul aba'isin haifar mana da rikice-rikicen ADDINI DA K'ABILANCI a sassa daban-daban na k'asar nan, sannan sukazo suka kuma fasaltamu a yankuna kashi uku, yankin HAUSA FULANI, YORUBA, IGBO, wannanma ya taka rawar gani wajen raba kawunanmu. wannan suna d'aya daga tushen matsalolinmu a NIGERIA, Dan sune suke jagorancin duk wani rikicin siyasa ko K'abilanci har yanzun a k'asarmu wlhy, wad'anda suka fara suntafi sunbar baya da k'ura, har kuma yanzun mun rasa samun nagartattun dazasu kawoma k'asar gyara, saima komai dayake k'ara ta6ar6arewa da lalacewa a kullum, daga talakawan har masu mulkin kowa yana buk'atar gyara Kansa da ahalinsa ma farko, to amma baikamata mu maidasu hujjar farko dazata hallakamuba ai. Abubuwa dayawa sun faru a k'asar nan, Wanda maimatasu bashida wani amfani, dan kamar k'ara dagula komaine, a yanzu hanyar gyara kawai yakamata mu fuskanta, shine zai zama NEXT LEVEL namu."

Sai baba😜, ammafa inji bilyn Abdul😂.

Dariya sukayi suduka, wadda nikaina bansan dalilin taba.
Baban Ama yace, "to minene shirinka a next level brother?".
" kafa *KUNGIYAR MATASA* domin nusar dasu illar rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI, FA'DAN 6ANGARANCI KO ADDINI*, yakamata mu fiddo hanya ta wayarma matasanmu kai dansu san k'alubalen dake tare dasu, sannan suma sufito adama dasu a k'asarsu, kamar yanda sauran k'ashen duniya keyi, duba tsarin CHINA, abin birgewa, mafi yawa matasan sune akan madafun iko, akwai k'asashe daban-daban dasuke cikin wannan tsarin, Amma mufa Africa son mulki yahana mu bama matasan dama, sukuma matasanma idan zakayi dubi tawani 6angaren saika gane basu cancanci madafun ikonba, saboda rashin nutsuwarsu da sanin muhimmancin Kansu. to amatsayinmu Na matasa tayaya zamu kawo CANGI a wannan tafiyar? yanda za'a fuskanci mumafa 'yan k'asane NAGARTATTATU kuma ababen ALFAHARIN al'ummar k'asarmu da yankunanmu, kaga dolene saimun sami had'inkan matasanmu Na KUDANCI DA AREWACI kenan". sai dai inda gizo ke sak'ar tayaya zamu samu hakan ta kasance?, matasan su fahimcemu sukuma k'aunaci Kansu, dan maganar gaskiya SIYASA DA K'ABILANCI tuni sun rarraba kanmu a k'asarnan dama Africa baki d'aya".
Baban Ama yasaki ajiyar zuciya kafin yace, "hanya d'ayace brother nake gani".
" wace hanyace brother? ". cewar uncle M.A.
" masu taimakonmu brother, bawai 'yan yima dukiyar k'asa babakere da handamaba, nidai nabaka goyon baya 100%, saimu fara Neman wad'anda tafiyarmu zatai dai-dai da tsarinsu, kamar mutum 8 ni da kai cikon Na goma, daganan komaima saiya biyo baya".
Uncle M.A yarasama mizaiyi saboda Nuna jin dad'in goyon bayan abokin nasa, sai kawai ya rungumeshi yana jero adu'oin fatan alkairi agaresa, shima Baban Ama addu'ar yake masa. Acewarsa shiyadace da wannan addu'ar, tunda shiya k'irk'iro cigaban, Wanda duk da yasan zasu fuskanci k'alubale iri-iri, saboda aikine bamai sauk'iba, musamman idan akayi dubi da yanda k'asar tagama lalacewa ta 6angarori daban-daban Na Siyasa da k'abilanci da Addini, dukda yana hango nasara wataran insha ALLAH.
haka sukaita tattauna batun, har aka kira sallar magriba, alwala sukayi suka fita massalaci.



_______________________________
"Wai oga wuk'armi kaketa faman wasawane haka kuma tun d'azun?".
Jajayen idanunsa yad'ago yana kallonsa, yasa bayan hannunsa ya shafi gefen hancinsa, fuskarsa ata6e tamkar yaga mala'ikin mutuwa akansa, d'auke idonsa yayi yamaida kan madai-daiciyar wuk'arsa maikamada *fad'ama jini nawuce* saboda tsabar d'aukar ido datakeyi Na kaifi, amma dukda haka kaifin baimasaba yake sake wasata.
K show bai daddaraba yakuma maimaita tambayar ga Zike.
Wani banzan kallo yamasa, sannan ya tofar da yawu, da yare yace, "aikin daka 6ata zaka koma ka gyara, inba hakaba hummm....". Yay shiru batareda ya k'arasaba.
K show ya hura hanci gaba, amma baice komaiba.
Su manu duk suna tsaye ake wannan dramar, amma basuji mi zike yafad'ama k show ba, saboda da yare yay maganar, k show da zike kuma yarensu d'ayane.
Ramzaki dake zaune gefe yana busa taba yajuyo yana kallonsu, cikin harshen turanci yace, Oga sir dangin waccan babynfa? Inason abani kwangilarsu, dama nadad'e inajin haushin old man d'inta, dan nata6a zuwa k'ofar gidan wajen babynnan amma ya koreni, wai shi ba mahaukaci bane dazai had'a jini dani, kasanfa hausawannan akwai shegen k'abilanci da nuna addininsu yafi Na kowa......
Da Sauri manu ya tsaidashi, " kai! Kai Ramzaki, please kama kankafa, karda tabarka tagayamaka hauka ka rainamin yare, kai k'abilar taka basama mutane k'abilanci ne? 'yan kad'an daku sai shegen gadara, wama yasan da k'abilar takune? Iyakarta jos fa, wlhy yanzu zamu kwashi 'yan kallo a wajenan........
Shima katseshin yayi, tareda mik'ewa da sauri yaje yadaki kafad'ar manu, "to kozaka gwadane?". Yay maganar yana hankad'a manu baya.
Shima manu duka ya kai masa.
Kafin kace me fad'a ya hark'ume, da k'yar sauran matasan suka rabasu.
Zike Na zaune yana jinsu, ko kallo basu isheshiba, wuk'arsa yake wasawa har yanzun.
K'ala baice dasuba kuma yamik'e ya tura wuk'ar gefen cikinsa, ya gyara rigarsa yay gaba abinsa yabarsu.
Da sauri wasunsu suka bi bayansa, akabar manu da ramzaki a wajen, harar juna sukayi kafin subi bayansu sunajan tsaki was juna, kowanne na zage-zage da yarensa.


(Nidai bilyn ku nace, " ALLAH ya k'yauta to".)
🚶🏻‍♀da sauri nabi bayansu Dan ganema idona ina zasuje kuma😨?.



______________________________

Zaune take akan abin salla, tunda ta idar da sallar isha'i bata tashiba, Ammi Na zaune akan d'aya daga kujerun plastic namasu jiyyasa. tunkan su shigo k'amshin turarensa yayo gaba.
K'irjintane yafara bugawa da sauri-sauri kamar yanda yakeyi koyaushe, hannu tasa ta dafe tana mamakin wannan lamari, aranta tace, miye ma'anar hakan ni Khadija?.....
Sassanyar muryarsace ta tadaki kunnenta. Ammi ta amsa sallamarsa tana mik'ewa, tareda musu sannu da zuwa.
Shikad'ai ya amsa, Dan Baban Ama waya yakeyi.
Ta gefen ido Amatallah ta ke satar kallonsa, ya canja kaya zuwa fara tas d'in jallabiya mai dogon hannu, sai bak'in wando daya lek'o kad'an da silifas d'in babanta a k'afarsa.
Kujerar da Ammi ta tashi ta tura masa, ya ajiye ledojin hannunsa kafin ya zauna yana fad'in "sorry madam mun barku Ku kad'ai ko?".
" lah babu komai wlhy, kaida kasha hanya ma, kamata yay kayi kwanciyarka ka huta basai kadawoba".
Kafin yabata amsa Baban Ama yagama wayar. matsowa yayi inda suke yana dariya, kibari kawai, babu yanda banyi dashiba ya zauna yak'i, wai saiyaga mamana". Yay maganar yana kallon direction d'in da Amatallah ke zaune.
duk tana jinsu, saita k'irk'iri addu'ar k'arya, bayan kuma tadad'e da idar da salla. shafawa tayi sannan tataso, kanta a k'asa ta rissina tana gaishesu.
Atare suka amsa da tambayarta ya k'arfin jiki?.
tace, "Alhmdllh".

Uncle M.A yace, ''My best daughter kinci abinci kuwa?".
Da sauri ta d'aga masa kai alamar eh taci.
Hararta Ammi tayi, " k'arya dai babu k'yau Amatallah, yaushe kikaci abincin?".
Kanta tad'ago ta kalli Ammi, idonta taf da kwalla tace, "kai Ammi".
" kai Ammin uwar mi?, tashimin anan kafin na bigeki ak'ara miki kwanaki a asibitinnan".
Da sauri Amatallah ta haye gadon datake jiyya.
Uncle M.A yace, "madam inafa jin kunyarki, naga kin tasomin d'iya a gaba".
" haka kullum takeyi wlhy brother, nafad'a mata rashin cin abinci halittane, harma ina mata misali dakai, amma bata d'agama mamana k'afa ko kad'an.
Uncle M.A ya kalli Ammi yana murmushi, sorry madam, rashin cin abinci halittace, haka kusan koda yaushe innani kemin, sai dai in baba Na kusa ya kareni ko Maijidda, yanzu haka matsalar kenan nidasu Fateema, kowacce da irin tunaninta, nifa har asibiti innani takaini ina yaro ban mantawa wlhy, wai likita ya dubani banacin abinci, kowani ciwone dani?.
Dariya sukayi gaba d'aya, harda Amatallah datayi murmushi tana satar kallon uncle M.A d'in.
sun d'an ta6a hira, harya kira Fateema da Aneesa suka gaisa da Amatallah da Amminta, amma kowacce badan ranta yasoba, musamman Aneesa dakejin zafin Amatallah sosai, (koda yake halintane, tanada zafin kishi, akan Alhaji Muhammad d'in😄, saboda auren soyayya sukayi).
Sai wajen tara suka tafi da k'yar, akabar Ammi da Amatallah.
dukda baba Ama Na fargabar barinsu su kad'ai, saboda halin da Amatallah ke kwana aciki, gefe kuma yanajin kunyar barin abokinsa ya kwana shika d'ai, haka dai suka tafi yana addu'ar ALLAH yasa su kwana lfy..........✍🏻



*_masoya, INA alfahari daku over wlhy_*💃🏻💃🏻





One Luv my fan's🥰

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_(home of expert and perfect writer's)_




*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 4_*
____________________


........"Haba dan yanzu Ku kun k'yauta kenan? har a kama su zike kusan 2days amma babu Wanda ya sanarmin acikinku?".
"To yanzu da ace shi gagis ya mutu fa? Kenan bazaku sanarminba? Kunsanfa yarannan sunada maruk'ar amfani a garemu yanzu, dolene komai k'ank'antar Abu mu tsaya musu....".
" sorry sir!, muma bamuji zancenba sai d'azun wani acikinsu Daba'a kamaba yazo yafad'a mana".
"Yaza'ayi ku sani kuwa? tunda bakwa maida hankali wajen kula da aikinku. yanzu ina gagis yake?".
" sir! Yana asibiti kwance, sukuma su zike suna police station."
"Mtsoww!!, aikin banza kawai, yanzu saiku shirya muje mu kar6o su zike, dan sunada matuk'ar amfani a tafiyarmu. Shikuma gagis zuwa gobe sai wasu acikinku suje su dubashi a asibiti".
" okey sir!.


_(Nace, "hummm, hattara matasa, kun gadai halin 'yan siyasar k'asar tamu, wannan d'an takarar bata gagis dake kwance a gadon asibiti yakeba, a'a, tasu zike yakeyi, dansu sunada lafiyar dazaiyi amfani dasu, shiyyasa zaije da kansa ya kar6osu a hannun police, amma gagis, zai tura wasune daga mutanensa su duboshi, tunda shi bashida amfani agareshi a halin yanzu. to wlhy haka kuke a wajensu, sai zaku musu amfanine suke kulaku, idan kuma rashin lafiya ko wani tsautsayi ya sameku basuda matsala daku🤷🏽‍, bare kuma idan sun d'ane kujerar💺 dasuke nema🤦‍♀)._


_____________________________

"Dear amma dakayi hak'uri da tafiyar nan sai da safe idan ALLAH ya kaimu mana".
d'ago idanunsa yayi yana kallonta da murmushi, saboda yanda tayi maganar.
cikin tsokana yace " my Neesa kodai bakison kwananki ya gudune?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana 'Yar dariya, "kai my dear! Nidai ALLAH bance haka ba, ai nasan maganin baba zaka amsone".
"Tom shikenan my Sweet Neesa, amma ba maganin babane kawai yasani tafiyar yammarba gaskiya, dan Alhmdllh jikin baba da sauk'i, bakamar wata d'aya daya shige ba. Amatallah ce batada lafiya, suna asibiti ma an kwantar dasu".
Tuni fara'ar fuskarta ta ragu, babu yabo babu fallasa tace, " ALLAH yabata lafiya".
Daganan tamik'e ta hau had'a masa kayansa.
Binta yayi da kallo kawai, yad'an girgiza kansa yana murmushi, baisan miyasa dukkan matan nasa suke nuna kishi akan Amatallah ba?, bayan sunsan jinjinar alak'ar dake tsakaninsa da mahaifin yarinyar, sun kuma san babu yanda za'ayi ya iya auren Amatallah, danshi matsayin d'iyarsa yake kallonta, bai ta6a banbanta matsayin Amatallah dasu Abul-khair ba. Sai dai kuma matansa sun gaza gane hakan, ayanzu haka suduka insunga Amatallah d'in bazasu iya ganetaba, saboda tadad'e batazo kano

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login