Showing 42001 words to 45000 words out of 104242 words
wadda yake mata kallon d'iya abaya, a yanzunkan yafara ganin canjawar wancan matsayi. Datake dashi aransa, dan ko yaushe tunaninta Na mak'ale da zuciyarsa, a da yakan d'auki hakan tausayinta ne dayakeyi, amma a yanzu shi kansa yafara k'aryata zuciyarsa,
Ita kanta Amatallah bazatace batajin wani Abu dangane da Uncle d'intaba, sai dai kunya da d'aukarshi a matsayi kamar babanta yagaza ganar da ita har k'agara take ya kirata a waya Dan taji muryarsa kawai, Dan dama can tana bala'in son muryar Uncle d'in nata.
Gameda damuwar rashin iyayenta kam tana nan tanayi, kullum ta ALLAH saitayi kukan rashinsu da kewarsu, kuma takan dage wajen musu addu'ar Neman gafarar ALLAH kamar yanda Uncle kullum kan tunatar da ita.
Ana cikin haka Result d'insu ya fito, Alhmdllh Amatallah tasamu kaso mai tsoka a WAEC d'inta, NECO ma haka dukda batakai WAEC d'inba, tayi farinciki sosai. hakama Uncle M.A.
A kuma wannan tsakanin ne Fateema tafara laulayin ciki, hakanne yasaka Alhaji Muhammad yanke hukuncin Aneesa saita biyoshi, amma za'a bar Saifudden anan saboda school. zatayi wata hud'u tadawo sai Fateema taje, lokacin tasamu lafiya cikinta yayi kwari.
Hhhh, tofa abin mema yasamu ga Aneesa dan batasan tsarinsa natayi wata hud'u bane ta dawo, ta d'auka indan ta tafi shikenan sai kuma ya kammala karatu su dawo tare🤣😜.
Ai kam tashiga yauk'i da gwalangwaso anama Fatima kallon nice a sama.
Duk da hakan ya Sosa ran Fateema saita danne, ta nuna murnarta da tafiyar Aneesa, dan itama batasan cewar Aneesar wata hud'u zatayi ta dawoba, duk ya 6oye musu bai fad'aba.
Shiri sosai Aneesa tayi, Jabeer yashiga shigi da fici wajen shirya tafiyar tata.
Watansa 1 da sati 2 Aneesa tabi bayansa.
Ranar Fateema tasha kuka, dan 100% tagama yadda mijinta yafison Aneesa, ko kad'an bata bari Nazeefa da yaranta sun gane halin datake cikiba, saima ta wayance da laulayin cikine kawai.
Nazeefa mutumce mai bin kwaf-kwaf akan mutaneba, wannan yasa itama bata kawo komai a rantaba ta d'auka gaske laulayine ya maida fateemar haka.
Tafiyar Aneesa babu dad'ewa aka kammala komai Na makarantar Amatallah, kasan cewar Uncle M.A yanada fad'a aji a B.U.K d'in.
Komai ya kammala zata karanci Medicine
Amatallah tayi murna sosai, dan kullum burinta kenan ta karanci fannin lafiya, tun iyayenta Na da rai kullum labarinta kenan, Uncle M.A yarigaya yasan da wannan burin nata, shiyyasa ya cika matashi da amicewar Ubangijin al'arshi.
Aikam ranar tayi tamkar ta fasa masa dodon kunne saboda murna.
Farin cikin data shigane shima ya jagoraci nasa farincikin, har yakejin bashida wata matsala a rayuwarsa dan kullum burinsa yaga farinciki Amatallah baiwar ALLAH, marainiya.
Samun makarantar Amatallah kuma yasa aka fara 'yan gyare-gyare agidan Uncle M.A, dan saita tare zata fara school.
6angaren daya ware dama dan babanta idan sunzo Kano su ringa sauka aka gyara, dan shima girmansa d'aya da 6angaren matansa, sai dai shi k'ofarsa ba ai nahin cikin babban falon gidan takeba, tana cikin corridor d'in dazai sadaka da falon ne, wannan yasa Uncle yace a maido k'ofar tadawo cikin falon, sai a toshe waccan.
Haka kuwa akayi, Shehu ne yatsaya akan aikin, aka kammala komai tsaf aka sake sabon fenti har waje, dan danan gida ya d'auki haske da shek'i, daka gani kasan sabuwar amarya zata shigone.
Fatima bataji zafin kishiba sosai kamar sanda akai aure Aneesa, dan yanzu harda ita akaje wajen had'a lefen Amatallah.
Ita da Anty Maijiddah da Nazeefa da Jabeer, sai Gwaggo Rakiya k'anwar Innani, akwatina Hud'u masu k'yau, kuma sun zubo kaya masu k'yau da inganci.
Kwana biyu da had'o lefen suka shirya suka kai jos.
Ranar Amatallah kam tasha kuka sosai, dan abin Na bata mamaki, wai Uncle ne mijinta, mutumin datake kallo a matsayin babanta, wayyo tasan dasu baba nada rai da hakan bazai ta6a ya faruba, shi kansa Uncle bazai kawo hakan a ransaba, amma yanzu k'addara taragayi fata.
Babu Wanda bai zubda kwallaba a wajen, haka akama su Anty Maijiddah shatara ta arzik'i suka dawo Kano a ranar, suna mai jin tausayin Amatallah sosai.
An tsaida tarewarta nanda kwanaki goma, ta tare da sati d'aya zata fara school d'inta.
Tun kuma daga wannan lokacin ko Uncle ya kira Amatallah a waya bata d'agawa, daga k'arshrma saita kashe wayar baki d'aya. a ganin inta d'aga bazata iya masa maganaba, dan sai a yanzune batun Auren nasu ke matuk'ar damunta, dan ta tabbatar da gaskefa akeyi Uncle yazama mijinta.
Abin ya damu Uncle M.A matuk'a, da rashin d'aga wayarsa da Amatallah keyi yana cin zuciyarsa, daga k'arshe ma saiyabar samuntaba kwata-kwata
___________________________
Aneesa na zaune kusada Alhaji Muhammad dake shan fruits salad data had'a masa na bud'a baki, (dan duk litinin da alhamis d'in duniya sai yayi azumi), tsaf take cikin kwalliyar d'aukar hankali, Siddiqa na gefe zaune (danta fara zama) an barbaje mata kayan wasa.
Lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta suma juna murmushi, haka Aneesa keso, takasance daga ita sai Muhammad d'inta, shiyyasa wannan damar data samu take tattalinsa tamkar kwai a cokali, a 6angaren kula da miji daga Aneesa har Fateema kowa kwararrene.
Kiran wayarsa da akayine yasaka Siddiqa tsorata harta fashe da kuka.
Su duka dariya sukayi, Aneesa ta d'auketa tare da d'akko masa wayarsa ta mik'a masa, dama tana hannun Siddiqa ne tana wasa da ita cikin kayan wasanta, wayar ta fad'a jikintane babu zato kuma aka kira, sai ringing d'in ya tsoratar da ita shine ta razana.
Hakanne yabama iyayenta dariya.
Har wayar ta tsinke Alhaji Muhammad bai d'agaba saboda dariyar da Siddiqa ta basu, sai da ta tsinke sannan shi ya kira, dama Jabeer ne ya kirashi.
Bayan sun gaisa ya tambayi jikin baba da sauran abubuwa.
Jabeer yace komai Alhamdllhi.
"To masha ALLAH, akwai matsalane?".
" eh to Yaya matsalarnan kam Alhmdllhi babu ita, sai sai kawu Hafizu ne ya kirani, wai akan punches d'in Amatallah ne, yace na tura masa Account Number d'ina zai turo kud'in daza'a saya mata anan Kano basai ansha wahalar saye daga can jos ba. shine nace masa to yad'an bani lokaci ina office amma zan kirashi. to shine nakiraka na sanar maka".
"ALLAH sarki Hafizu, to in banda abunsa ko dai Isma'il nada rai ai inaga nine maima Khadija kayan d'aki ko, wannan maganarma a barta kawai, dama nayi niyyar maka magana akan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu kuje kai da maijidda Ku za6o mata duk wani abinda ake buk'ata".
" OK Yaya babu damuwa, shi yazan cemasa yanzun kenan?".
"Ka barni dashi zan kirasa kawai".
" hakan yayi to Yaya".
"Yauwa, waifa jiya saina manta na sanar maka inason nafara turo kaya daga nan, muga kuma abinda ALLAH zaiyi".
" kai Yaya wlhy nayi farin ciki, dama inata tunani akan kaje garin Business amma banji kana maganar d'ebo mana hajaba, ashe abin na ranka".
Dariya Alhaji Muhammad yayi yace, "tom zan turo maka wasu kaya ta WhatsApp ka gani, idan sunyi saina turosu k'arshen watannan mugani koza'a fad'a".
" to ALLAH ya tabbatar mana da alkairi Yaya".
"Amin Jabeer, ya Shehu fa? yana zuwa kasuwan kuwa?".
" da dai yafara wasa kam, amma tunda innani tamasa magana saiya maida hankali da zuwa sosai, kuma Alhamdllh zuwan nasa yana d'auke hankalinsa dan naga kamar shaye-shayen ma yarage".
"Alhmdllhi, ALLAH ya shirya manasu baki d'aya".
" amin Yaya, a gaidamun Siddiqa da Anty Aneesa".
"Ok, zasuji, inka koma gida zan kiraka muyi magana da baba da innani".
" shike nan saina koma d'in".
Daga nana suka yanke wayar.
Duk wayar nan da yakeyi babu Aneesa a wajen, tatashi tunda yafara wayar saboda kukan Siddiqa, har kuma yagama bata dawoba saboda tsayawa lalla6a Siddiqa tayi barci datayi.
Har ya kammala shan fruits salad d'in bata dawoba, yashiga toilet d'in falon yay alwala yafita sallar Isha'i a masallaci..............✍🏻
🤩👎🏻
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu🙏🏻😭_*
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
____________________
*_Number 18_*
____________________
Rashin samun Amatallah a waya yana k'ara damun Uncle M.A, sai yake ganin kamar tana cikin k'unci da damuwane.
Yarasa wazai kira yahad'asu.
Duk da yakira kawu Hafizu akan pinches d'in Amatallah d'in, yakuma nuna masa koda da ran Isma'il shine ya cancanci yama Amatallah kayan d'aki aii, bare kuma yanzu ma amatsayin matarsa take.
Da k'yar kawu Hafizu ya amince, amma dukda haka yace zasu mata kayan ketchin, dole Uncle M.A ya amince da hakan.
Duk da bawani gagarumin biki za'ayiba dai sunyi shiri bakin gwargwado.
Su Anty Sadiya nata bama Amatallah magunguna, amma saita faki idonsu ta zubar batasha, duk basusan ta6argazar datakeyiba.
Ahaka dai yarage saura kwana biyu kacal.
Sosai Amatallah ta birkice musu, sai lallashinta kowa keyi daban baki, hardai ranar kaita kam batama da lafiya. Zazza6i sosai da ciwon kai sun addaba mata, harma k'ara narkewa takeyi wai koza'a d'aga😄.
Amma saitagama sai kuma shiryawa sukeyi. Ranar daza'a kaita gida yacika da dangi da makwafta, akad'anyi shagali na mata kawai a cikin gida.
Da k'yar Anty Furera tasaka Amatallah tayi wanka, babu zancen kwalliya dantak'i amincewa, farar hodama dak'yar tayarda ta shafa.
Kusan k'arfe 11am saiga mutanen Kano sunzo d'aukar amarya, sai dai gayyar duk abokan Jabeer ne, kaikace shine angon, saikuma samarin family d'insu da mata kad'an su Anty Maijiddah da Nazeefa da Gwaggo Rakiya, saikuma wasu dangin baba na sokoto, dan sunzo suma.
Amatallah tasha nasiha wajen iyayenta, kuka kam ai ba'a magana, dan kowa saida ya tayata ranar, kodan tuna iyayenta.😭
Ahaka aka d'akko Amarya Amatallah sai Kano, (gashi ango baya kusa bare yay lalashi🤭).
Kai tsaye gidan Uncle M.A aka wuce da ita, sun iske gida cike taf da dangi na Sokoto dana nan Kano, makwafta da abokan arzik'i, (dan biki sosai sukayi abinsu dukda babu ango), nanfa gida ya rud'e da tarbar amarya 'yar k'amshi, aka rakata har d'akinta.
Masha ALLAH na fad'a, dan ganin yanda aka tsara 6angaren nata, lallai Amatallah 'yar gatan Uncle d'inta, komai Pink colour ne da milk kad'an, (Uncle yadad'e da sanin Amatallah nason pink sosai, shiyyasa yace komai Jabeer ya d'auki pink). Aikam Kodai mak'iyi yagani dolene ya yaba, dan komai yayi acan-acan a talauce ba'a sarauce ba.
Sunci sunsha Alhmdllhi, duk kuma sun yaba da karamcin da akai musu, musamman ma na Fateema, dan tanata rawar gani gaskiya.
Amatallah kam tak'i yarda taci komai sai kuka take. Sai da k'yar Nazeefa da Asiya suka lalla6ata tasha fura da Nazeefa tasayo mata.
Da daddare koda Uncle yakira yace Nazeefa tabama Amatallah wayar.
Nazeefa batace mata komaiba tasaka mata wayar a kunne kawai, dansu ukune a d'akin, 'yan rakiyarta duk suna d'aya d'akin 6angarentan, Asiya kuma tayi barci saboda gajiyar tafiya..
Saukar Muryarshi kawai taji acikin kunnenta.
A zabure tatashi, jikinta har wani rawa yake, azatontama koyana a d'akinne, ganin Nazeefa zaune kusada ita da waya a hannun saita saki ajiyar zuciya.
Nazeefa kam dariyama tabata, amma saita gumtse batayiba, tasake mik'a mata wayar, dan Uncle nakan layi bai kasheba, "kar6a mana Amatallah, yanafa jiranki".
Kunyar Nazeefa takeji, shiyyasa ta amshi wayar tasaka a kunne. Nazeefa kuma yashiga toilet d'in d'akin.
Sallama yasake mata.
Dak'yar ta iya amsawa, muryarta na rawa, hawaye harsun fara zirara a kumatunta.
Jikinsane yay sanyi, yatashi daga kwancen dayake yafito corridor d'in falon, Aneesa da fitowarta kenan daga ketchin ta had'o masa shayi tabishi da kallon, rantane ya 6aci, ita tamayi zaton Fateema Ce, dan batasan yau Amatallah zata tareba.
A kujerar dake corridor d'in ya zauna, muryarsa a matuk'ar sanyaye yace, " My best! kuka kikeyi dan kindawo gidana da zama?".
Kanta ta girgiza masa tamkar tana gabansa batareda tace komaiba.
Jin bata amsaba, saidai shashshekar kukanta yake jiyowa yace ''kinason nima namiki kukan?".
Da sauri tace, "A'a Uncle na daina".
" haba Khadija! Bak'yason zama dani?".
"A'a inaso Uncle". tayi maganar da fashewa da kuka.
" to Amma miyasa kike kuka Khadija!? ".
" ba komai Uncle, ina tuna su babane".
Ajiyar zuciya yayi, Yakuma raunana muryarsa sosai, "kiyi hak'uri Khadija kinji, badan ALLAH baya sonki bane ya d'aukesu, Kimusu addu'a ba kukaba, su tasuma tayi k'yau, dan koba komai mutuwar shahada sukayi, wannan kad'ai ya Isa muyima su brother murna ba kukaba kinji ko?".
" to Uncle zan daina insha ALLAHU".
''Yauwa my best, yanzu ki share hawayenki kinji ko".
"To" ta amsa tana share hawayen tamkar yana ganinta.
"Yauwa babyna kokefa, yanzu dai fad'amin kobak'yason zama Kano nasa Jabeer yamiki visa ki dawo nan Inda nake?".
Da Sauri tace, " A'a Uncle, inason nan, ba makaranta zanjeba?".
"Makaranta zakije my best, amma sainake ganin kamar bazaki iya karatunba, saboda damuwar dakike ciki".
''Wlhy Uncle zan iya, inason karatu, indai kukane na daina bazan sakeba".
" promise".
"Promise Uncle".
" tom ngd, yanzu kinci abinci ko?".
"Eh nasha fura".
" fura aiba abinci bace my best, nasan tunda aka sake tarewarnan bak'yacin abinci ko?".
"Inaci Uncle".
" kai ban yardaba".
"ALLAH kuwa".
" to shikenan, yanzu mikike sha'awar ci nasa a kawo miki?".
"Babu komai Uncle na k'oshi, furan ya isheni".
" kin tabbata".
"Eh Uncle, ALLAH kuwa".
" shikenan, karna kumajin kinyi kuka, yanzu kitashi kiyi wanka, saikiyi alwala kiyi nafilfili da karatun alku'ani, insha ALLAH zakiji zuciyarki tayi sanyi da salama, kima su brother addu'a, ALLAH yay miki albarka kinji".
"Amin Uncle, ngd zanyi to".
''Yauwa my best D.., saida safe ko, zan sake kira bayan kin kammala naji kinbar kuka ko an karya alk'awarin Uncle bawan ALLAH".
hannun tasaka tarufe fuskarta kamar tana gabansa, ta saki wayar a kan gadon, dariya yayi ya kashe wayar, dan yanajiyo mutsu-mutsunta kasancewar sabuwar katifa ko ledar ba'a cireba aka shinfid'a bedsheets d'in.
Nazeefa ma dake tsaye a bakin toilet dariyar tayi, aranta tana jin sha'awar wannan soyayya ta uncle da d'iyarsa, a ranta tace ALLAH ya daidaita komai cikin sauk'i Amatallah. K'arasowa tayi ta d'auki wayarta, saitaga yakashe, ta kalli Amatallah dake shirin sauka a gadon tayi murmushi. Batace mata komaiba tafice d'akinta.
Duk yanda Uncle yace haka Amatallah tayi, ai kam Alhmdllhi tasamu nutsuwa, saigata suna 'Yar hira da Asiya data farka har barci ya kwashesu.
Washe gari akayi walima 'yan jos suka koma da yamma, bayan sunje gidansu Uncle sun gaida baba da jiki.
Shatara ta arzik'i Uncle yasa Jabeer ya had'a musu, sun tafi sunbar Amatallah Na kuka tamkar ranta zai fita Anty Maijidda da Nazeefa sai lallashinta sukeyi, daga k'arshe dai saida aka kira Uncle yay lallashi da tuna mata alk'awarin datayi Na ta daina kuka sannan tayi shiru, amma sai zazza6i mai zafi ya rufeta, dole jabeer ya nemo mata Magani tasha.
____________________________
Tunda Aneesa ta fuskanci Amatallah Ce ta tare saita hau zum6u-zum6ure wa Alhaji Muhammad.
Shareta yayi, yay tamkar baisan mitakema fushinba, saima ya maida hankalinsa wajen yima Siddiqa wasa, da daddare kuma yakira Fateema tabama yaran sukasha hirarsu. yakira Nazeefa tabama Amatallah tace tayi barci, saboda maganin datasha da yamma, da k'yarma tayi salloli takoma ta kwanta. sallama yamata ya yanke wayar.
_____________________________
Rayuwa tacigaba da