Showing 66001 words to 69000 words out of 104242 words

Chapter 23 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16039

nasamu duniya, saidai kumin addu'ar samun lahira kuma, wlhy da gaske yasace zuciyata sonsa nak.........
Amatallah bataji k'arshen zancenba tatashi tafice saboda wani masifar tsanar zee daya turnik'eta, harma da sauran 'yan ajin dake tayata da ihu.
Rita dasu Fa'iza suka take mata baya da sauri suna kiran sunanta.
Baki zee ta ta6e tana rakasu da harara, kafin ta kalli 'yan ajin tace "tofa kunga wani Sabon salo, ko wata ke sonsa a cikinsu? Tab wlhy Ashe da anyi yak'i a bayaro".
Sosai yanzu ihunsu yafi na d'azun, wasu dasuma abinda zee take bai birgesuba suka fara ficewa, wasu kam suma abinda kedamun zee shike damunsu wato son Uncle d'in (basusan tsoho bane......lol😉😜).

Da k'yar su Fa'iza suka lallashi Amatallah dake kuka, goodness tace, "ai hankali aka kiya miki, saiki tashi dan kamo mijinki, wazai kallesa yace matansa Uku bare yayi tunanin yakai shekarun dakika fad'a mana, wlhy sisi kardai kiyi sake.....
Sosai suka mata fad'a, bakamarma Fa'iza dakejin tamkar ta mangareta.
Koda aka tashi lecture d'in k'arshe wajen 2:30 bata nemesaba, dukda kuma yace idan tagama ta kirashi, tafiyarta tayi bayan tasha gargad'i wajen Fa'iza akan kartaje tamasa shirme tunda bashine yace zee tasoshiba, kuma tabata shawara akan abin sharruwa daya kamata ta had'a masa.
Tadai tafi tana zun6ure-zum6ure. (Ama...kishi lol😆)


_________

Uncle kam baisan wainar da'ake toyawabama shi, saidai idan yatuno yanda Amatallah ke satar kallonsa a aji yakanyi murmushi.
Yasamu ganawa da dukkan lecturers d'in, Yakuma kawo musu kudirinsa na kafa k'ungiyar matasa dakuma zawarcin abokan tafiya.
Wasu sun bada had'inkai, wasukam sunata 'yan kame-kame saboda sunji maganar hardata kud'i, duk Uncle ya lura dasu.
Ya tausasa harsher yana fad'in " karfa hakan ya dameku, bawai tilasne saika zuba kud'inkaba, inhar zuciyarka atsarkake take da nufin son a gyara tafiyar matasan zaka iya bada gudun mawarka, Dama munsaka maganar kud'inne saboda tallafama Matasan dabasu sami koda karatun secondary d'inba, sai Mike ganin Sana'a yafi dacewa su a tallafesu da ita, saikuma wad'anda karatun Nasu ya tsaya iya secondary d'in, sunada buk'ar mu taimakesu domin cigaban karatunsu, saboda wasu sun cancanta amma rashin tallafi yasakasu maida takardunsu kasan jakka sukoma maula ko dabar siyasa ko shaye-shaye, akwai kuma Matasan dasun kammala karatun amma babu aikinyi, bazai yuwu kowanne saiyazama ma'aikacin Gwamnati ba, Dan bazata iya d'aukar kowa aikiba, to kunga saimu tallafa musu da sana'oin hannu dazai rik'e rayuwarsu kodan rage musu rad'ad'i wajen tunzuruwarsu ga aikata ta'addanci, mukuma cire musu ak'idar nayi karatu dolene Nina naga kaina a office. Wad'annan hanyoyin zasu rage ma matasanmu yawan Shiga TARKUNAN 'yan siyasarmu masu gur6ata tunaninsu da kud'i harsuna haddasa mana rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI*, kudancinmu sunrigada sunyi nisa a irin wannan taimakon, zakiga mutum d'aya ya d'auki nauyin yara goma karatu, koma fiye dahaka, babu kuma abinda suka had'a, kawai k'auyensu d'ayane. Amma mufa 'yan arewa duk iri-iren wad'annan abubuwan bamayi, kullum burinmu mu Gina k'aton gida, musa tsala-tsalan mata da ma'aikata masu yimusu hidima, saika samu harabar gidan mutum d'aya da mota goma, har yaran gidan k'anana sunada motarsu da ake kaisu yawo, amma gawasu suna cikin wahalar rayuwa bama tausayinsu, idan munga idonsu ko kud'insu sai sun tsaya takarar kansila ko ciyaman ko d'an majalisa ko gwamnan jaha, to sannanne zasuna mana 6arin kud'i kamar basusan ciwonsuba, a wayonsu idan sun hau kujerar mulki sunsan zasu maida fiye da abinda suka watsa mana".
"Mun manta damaganar alk'awuran aiki dasukai masa, wannan tunanin namune ya Karya arewacinmu, akowane lamari mune koma baya, yanzu damuna taimakon matasanmu wasu azzalumai sun isa su sami damar haddasa mana tantin ta'addaci a yankinmu? Bakwajin ciwon yanda ake kashe mana matasa ana kama wasu acikinsu ana jinginasu da ta'addancin? Idan kana ganin babu d'anka aciki ko k'aninka, baka tunanin ta6ar6arewar komai har 'ya'yan naka su taso suma sugaza amfana da komai na k'asarsu? Shin bakwa tunanin ba ayanzun matsalar takeba sai zuwa nangaba mun rasa jagororin tallafin arewacinmu, sufa matasannan damuke zuba ido wajen kallon lalacewarsu koma jagorancin lalacewar tasu watarana sune zasu zamto rik'e da k'asar. Shin mikuke tunani akansu idan k'asar tazama a hannunsu? Kuna ganin 'ya'yanmu k'anana zasu shane? Kokuwa yankinmu damu kanmu zamusha? Kufayi tunani akan wannan lamarin, dan duk d'inmu iyayene, kuma yayyane, musan zafin damukeji yayinda mukaga d'aya acikin zuri'armu kangararre, shin bakwa tunanin ya sauran iyaye sukeji suma?. Akiraka mai kud'ine abin birgewa kokuwa ALLAH ya aminta da k'yawawan aiyukanka? Wannene za6inku?!!!".

Duk shiru sukayi tamkar ruwa yacisu, saikuma jikkunansu sukayi sanyi da dukkan furicinsa, sunsan tabbas gaskiya yake fad'a, nanfa k'ananun maganganu suka fara tashi k'asa-k'asa.
Cikin fusatar 6acin rai Uncle yakwashi takardunsa yafice daga d'akin taron, duk kiran da Alhaji Sabi'u da shugaban makarantar kemasa bai ko waigosuba.
Ajiyar zuciya Alhaji sabi'u ya sauke, ya kallesu da kulawa "kuyi hak'uri ransa yarigada ya 6aci sosai, Alhaji Muhammad labbo mutumne mai kishin k'asarsa da yankinsa, mai irin tunaninsane kawai zai fahimci zafi ko bak'incikin dayakeji akan ta6ar6arewar Arewacinmu. Ga form nan duk mai son kasancewa a tafiyar tamu saiya samu shugaban makaranta ya yanka ya cike, naira dubu d'yane kacal, bayan mun mammala samun abokan tafiya kuma saimu fuskanci tsare-tsare nagaba, Dan abin yazo mana a kure, za6e yagabato, somuke kuma mu nunama 'yan siyasar k'asarnan matasanmu sune *KASARMU* dolene kuma a dama dasu tako wane fanni."
Daga haka shima yamusu sallama yafice, yarage dagasu saisu.
Nan dai sukaita tattauna lamarin, wad'anda sukayi na'am atake suka yanki form d'in.
Wasu kuma dai basuce komaiba a kan lamarin.............✍🏻



_bara nabi Amarku sarkin kishi🚪🚶🏻‍♀_.


🤩👎🏻

One Luv my sweet fans🥰









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


_Gundumemiyar gaisuwa gareku da fatan alkairi *Hafsat Rano, Ummu Hanan (mamana) Mzzdaddy, Maryam wasagu, Aysha Manshat, Maman Shaheed, Ummu Affan (mamana) Bily s fari* na gaisheku nakuma Na gaisheku, inayinku over, ALLAH ya k'ara basira agareku writer's d'inmu🥰🥰🥰👍🏻😘_



____________________
*_Number 28_*
____________________


Tana cikin Napep kiran Fa'iza yakuma shigowa, d'agawa tayi batareda tayi maganaba.
Fa'iza tace, "wlhy Amatullah ina mai baki shawarar karkije gida kina kuka ko fushi, ki saki fuskarki, dama wai haka kike da kishi kema?".
" bazaku ganeba Fa'iza, nifa ba kishi baneba".
"Oooh to miye?".
" humm, mubar maganar kawai".
"Shikenan an barta, kiduba Na tura miki wani Abu, amma Dan ALLAH inamai rok'onki ko'a fuska karki bari mijinki da abokan zamanki suga fushi a fuskarki, sannan kinutsu sosai wajen shirya masa abincin shan ruwa, kikuma tanadi kalaman kare kanki a wajensa idan ya tambayeki dalilinki Na tahowa Baku nemesaba". Kitt Fa'iza ta yanke wayar batareda tajira mi Amatallah zata fad'aba.
Ajiyar zuya Amatallah ta sauke, ga wata k'aunar Fa'iza nashiga harcan k'asan ranta, tabbas k'awa tagari rahamace ga kowanne bawa, shigowar Fa'iza rayuwarta ALLAH ne kad'ai yasan nasarorin data kawo mata, takanji tamkar ciki d'aya suka fito da Fa'iza. Addu'a taitayi a zuciyarta hartaji abinda ya rik'e mata mak'oshinan ya koma, har sukaje k'ofar gida tana sakin ajiyar zuciya akai-akai, shidai mai napep yanata aikin tuk'insa da saurarenta, ALLAH ma ya taimaketa ba irin masu shegen surutunnan baneba da shiga abinda ba huruminsuba.
Kud'insa ta basa kafin ta shige ciki. Babu kowa a falon, sai dai yanata k'amshi mai dad'i. Harga ALLAH bazata 6oyeba tsaftar matan gidan Na birgeta, koyayane bazaka tadda falon a cikin dattiba, shirun gidan ya tabbatar mata yara sun tafi Islamiyya.
Bata shiga d'akiba, saita lek'a kitchen, dan tanata tunanin komi yara zasuci idan sun dawo? batayi zaton wani acikinsu zaimata girkin daya zama wajibi akantaba. Sai dai tashiga mamaki yayinda taci karo da kular abinci dakuma fleets alamun anci abinci, tabud'e kular (jallop d'in shinkafa Ce) maidawa tayi ta rufe tana mamakin waye yayi girkin to acikinsu? Koda wasa tamasan ba Aneesa bace.
Kasa hak'uri tayi dai, tashiga 6angarenta a gaggauce tayi wanka tai sallar la'asar data risketa a hanya, bak'ar doguwar riga jallabiya tasaka, hula tasa a maimakon d'ankwalin tanufi 6angaren Fateema dannan tafi zaton an taimaketa.
A falo ta isketa tanashan fanka, a girmame ta gaisheta, itakuma ta amsa cikin fara'a da k'ok'arin danne kishinta.
"Anty Fatee ngd sosai, nabarki da wahalar girki".
Fateema ta kalleta tana d'an murmushi, " ayya Amatallah momyn yarace tayi banibama wlhy, taga har yara sunkusa dawowa baki dawo bane".
Mamaki ya kama Amatallah, shiyyasa akeson ka k'yautata zato wa d'an uwanka, duk mugun halin mutun tawani 6angaren sai kaga mutumin kirkine, tabbas ita kanta tasani, inhar tacire maganar kishin tsiya Na Aneesa batada wata hujjar zaginta akan mugun hali. fita tayi tanamai jin nauyin zargin datama Aneesa.
6angarenta tashiga a sanyaye, a falon sai Siddiqa fake wasa kawai, tana ganinta tataho da gudu tana gwarancin su Na yara, Dan maganar tata babu dad'i sosai har yanzun, sama Amatallah ta d'agata tana cafewa suna dariya.
Ahaka Aneesa tafito daga bedroom ta samesu, (duk mai son d'anka dolene duk zafinsa dakakeji kaji sassauci), Dan haka Aneesa ta kallesu da murmushi a saman fuskarta, zama tayi abinta batareda ta tankaba. Amatallah ta sauke Siddiqa a cinyarta bayan ta zauna, gaisheda Aneesa tayi a girmame kafin tace, "Anty ngd fa da girki, nabarki da wahala ALLAH ya raya su Siddiqa".
Murmushi Aneesa tayi, " karki damu da wannan, taimakon juna tilasne agaremu komin kishin damukeji akan juna, kishi daban k'yautatawa daban".
"Gaskiyane Anty ngd". daga haka tataso tafito rik'eda Siddiqa.
Zamanta tayi a falonta bayan tazubo abinci, tanaci tanabama Siddiqa harsuka gama, daga nan taita biyema yarinyar suna shirme..

A wannan lokacinne kuma Uncle yashigo gidan, bai wani yimusu horn ba yafito dakansa yabud'e gate yashigo, wannan yasa babu wadda tajishi dukda kuma bama wutace ke akwaiba bare ace k'arar TV ta hana. hankalin sune kawai bai jeba, Aneesa ma waya takeyi da mutanen Ghana tun fitar Amatallah.
Fateema kuwa tanashan fankarta da ta samu isashshen charge tana karatun addu'in 40rabbana.
Itakuma Amatallah shirmensu da Siddiqa ya d'auke hankalinta gaba d'aya, tanason yara kodan tasowa datayi ita d'aya kwallin kwal agidansu, koda suna jos haka zatayita jajubo 'ya'yan jama'a Na makwafta, wani lokacin Ammi taita fad'a tamkar ta ari baki, sai dai Amatallah tabata hak'uri, ammafa gobe babu fashi saikin ganta dad'an wani ta yayibo.
Harya shigo falon babu wadda ta fito, shi mamakinema ya kamashi, wai duk matannan biyu babu wacce tasan da shigowarsa, (zatonsa Amatallah bata dawo school ba, shi saima yanzu yatuna ko tanacanma tana nemansa gashi yataho), Ramsa a 6ace yake shiyyasa yay shigewarsa samansa batareda yanemi kowacceba barema Amatallah daya bari a makaranta.
Ruwa kawai ya watsa ya saka k'ananun kaya wando dogo da k'aramar Riga, falonsa yadawo yad'an kwanta adoguwar kujera ya lumshe idanu badan barciba saidan son dai yasamu damar yin tunanin halayen mutanenmu masu ban haushi darashin Sanin darajar Kansu da mutuncin yankinsu. Ya jima a kwance yana tunani batareda yasan lokaci yajaba, hardai yafara jiyo hayaniyar yara sun dawo islamiyya.

A 6angaren su Amatallah da gaske babu wacce ALLAH yabata ikon sanin shigowar mai gidan, kusan 5:00pm Amatallah tashiga kitchen, lokacin Siddiaq tayi barci ta goyata. Da abincin gida ta fara, tuwon semo.... Miyar Ogbono tayi, Dan komai Na kalolin miya daba'a amfani dasu anan Kano saida Anty furera ta tanadar matashi, musamman miyoyin k'abilunnan da Amatallah duk ta iya mafi yawa aciki, Dan Ammi batayi wasa wajen tsayawa koyama Amatallah kalolin abinciba da aikin gida, wannan yasa batada Matsala akan kowanne fanni Na girki dakuma kulada muhalli (kamar Ammi tasan k'addarar d'iyar tata zama cikin kishiyoyi).
Batawani jimaba ta mammala had'a miyarta, sannan ta d'ora tuwo dakuma wani 6angare Na kayan shan ruwan Uncle. Dan danan k'amshi yafara baje gida (had INA had'iyar yawu Nima mai rahoto....lol😋😜) tsaf tagama komai ta kimtsa kitchen d'in, tana mopping yara suka dawo daga islamiyya.
Jin suna Neman Abbunsu yasata fitowa daga kitchen d'in, Dan duk iyayensu Na d'akunansu. hayaniyar yarance ma ta fiddo Aneesa.
Kusan tare suka fito da Amatallah.
Tuni yaran sun arta sama aguje, sunsan Abbunsu yana gida tunda ga motarsa a waje.
Aneesa da Amatallah suka kalli juna, Aneesa tace, "dama ya dawo?".
Har Amatallah zatace da bata saniba, saikuma taga ai abin kunyanema ita mai girki bata san miji yadawo ba, kuma alamar yaran ta nuna tabbas Abbunsu yadawo d'in. " eh Anty yadawo babu jimawa sosai, yad'an kwantane ya huta".
"To, ALLAH yasa lafiya dai, Dan dear baya barcin yamma gaskiya".
Cikin son kare kai Amatallah tace, " kansa ke ciwo".
''Ayya shiyyasa, ALLAH yakawo sauk'i. Wai yanzunan k'atuwarnan kika goya haka? bak'ya gudun ciwon k'irji?".
Murmushi Amatallah tayi, tagyara zaninta data Goya siddiqa dashi daga sama tana fad'in "lah Anty aibatada nauyi".
" lallai kam, sannu da k'ok'ari, aini bama zan iya aiki da yaro a bayaba, Umman yaracema da wannan k'ok'arin".
Murmushi kawai Amatallah tayi batace komaiba.
Aneesa ma tajuya d'aki abinta.
Amatallah kam tsaye tayi tana kallon matattakalar benan, kodai Uncle fushi yakeyi da ita danta taho?. Jitai kwalla tacika idonta, jiki a sanyaye tanufi saman, takula gabma ake da shan ruwa. Baya takoma tad'ibo dabino awani d'an kwano, tad'ora a tire da ruwa da cup, hakan duk yana cikin aikin fa'iza data koyar da ita, da kuma training d'in Ammi dabazata ta6a mantawaba, (kunsanfa duk abinda katashi kaga anayi agidanku mawuyacine kiga kaima Baka aikatashi a gidan mijiba, iyaye saiku kula wlhy saboda 'ya'yanmu masu tasowa).😊👍🏻.

A falo ta iskesu shida yaransa, duk suna a jikinsa kowa nabada labarin abinda aka koya musu, sallamarta tasakashi d'ago idanunsa ya kalleta. Koda suka had'a ido saita sakar masa murmushi, hakanne ya sanyaya zuciyarsa daga haushinsu dayakeji.
"Sannu da zuwa Uncle". tafad'a murya k'asa-k'asa.
Dukda surutun yaran hankalinsa Na kanta, kuma yaji mita fad'a. ya d'auke idonsa akanta yamaida kan Abulkhairi, "Abulkhairi kuje maza a canja Uniform ayi alwala nima ganinan sakkowa mutafi masallaci kunji".
Atare suka mik'e suna fad'in to Abbbunmu.
Daga shi har Amatallah da kallo suka raka yaran, kowa Na murmushi.
Ya maido kallonsa kanta, " my best kinyi k'yau da goyon kuwa".
Murmushi tayi kanta a k'asa tace, "ngd Uncle, kadawo lafiya".
Still murmushi shima yayi, ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kallonta, " ba godiya zakiminba tunda ba k'yautar Siddiqar nabakiba, kawai kema kidage ki haifomin naki".
taji kunyar maganarsa, Dan haka ta kauda kanta gefe tana murmushi.
Yasa hannu yakamo nata, cikin zolaya yace, ''kokuwa yau zamu samune ma kawai nayi shiri?".
Batasan sanda ta dubeshiba tana zaro ido waje, shima yayi yanda tayi, sai suka tuntsure da dariya kuma.
Tace, "kai Uncle".
Yace, "ALLAH my heartbeat ".
Murmushi kawai tayi, shikuma yashafi kumatunta, "Matsoraciya wasa nakeyi, sorry nataho Na barki a school ban nemekiba, 6atamin rai akayine".
'Dan kallonsa tayi da mamaki, har zatayi magana saikuma tayi shiru, gwarama kawai tabarsa a yarigata tahowar.
"Fad'i mana".
Yayi maganar idonsa akanta.
" a Uncle babu komai, gashi can ana kiran salla".
"Alhmdllh" yafad'a tareda mik'ewa yashiga bedroom d'insa, babu dad'ewa yafito, da alama alwala yayo da brosh. Zama yayi inda ya tashi, yaci dabino uku yasha ruwa kafin yamik'e yana shafar gefen kumatun Amatallah, "bara naje masallaci babyna".
"Adawo lafiya" Amatallah tafad'a a kunyace".

Itama sakkowa tayi danyin sallar, ta sauke Siddiqa agadonta tashiga bayi.
Su Uncle basu dawoba saida akayi isha'i, zuwa sannan tad'an gyara fuskarta da hoda da kwalli da d'an janbaki kamar yanda Anty maijidda da Nazeefa suka gargad'eta akan bakoda yaushe ake zuwa wajen miji fuska a kod'eba.

Ranar dai Uncle yaci girkin Amatallah yana mata Santi, itako sai dad'i takeji tana dariya, daga Fateema har Aneesa babu Wanda ya tanka, yara kuwa suna taya Abbunsune.
Yauma a d'akinta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login