Showing 39001 words to 42000 words out of 104242 words
taso, harda kukanta kuwa.
Saita bashi tausayi, har yakai ga mata addu'ar ALLAH ya sassauta mata kishinnan nata.
Koda su Aneesa suka sauka Jabeer ne yaje ya d'akkota. tunda ta shigo gidan taketa faman ta6e baki, dan ganin fentin da gidan yasha, hakama dasuka shiga falon gidan taga an maido da k'ofar 6angaren bak'i ciki, taita baza ido don son ganin Amatallah, amma komai kama da ita bata ganiba, daga yara sai Nazeefa.
Bayan tahuta taci abincin da Amatallah ta girka kafin ta wuce school, saita hau gyaran 6angarenta, (India tsaftace badaga bayaba Matan Na Uncle, dan Aneesa ma tafi Fateema tsafta gsky, dukda itama Fateeman bawai k'azama baceba, sai dai Aneesa irin matannan ne dakomai sunfi sansa k'al-k'al).
Bata tambayi kowa Amatallah ba, har yara daketa bata labarin abinda antynsu ke musu, barema Saifudden dake nanik'e da ita. siddiqa ma nata yawo cikin 'yan uwanta danta fara tafiya.
Amatallah kam yau lectures d'in yammane da ita, shiyyasa saida tayi girki ta tafi school, basu fitoba sai around 6:pm, a gurguje tamasu Rita sallama tashiga napep d'in dasuka tare mata, dansu a hostel suke, yau kuma Fa'iza ma batazoba, maybe jikintane dan cikinta yafara tsufa.
Ana kiraye-kirayen sallar magriba Amatallah ta shigo gida, babu kowa a falon dan haka tashige 6angarenta kawai. hijjab kawai tacire ta tashiga toilet dan d'auro alwala.
Koda aka idar da sallar magriba bata fitoba, dan fargabar had'uwa da Aneesa, da akayi sallar isha'i sai kawai tashigama wanka, tana fitowa ta shafa mai kawai tasaka bak'ar jallabiya. Yunwa takeji sosai, bataci abincin ranaba tafita, harta kai k'ofar fita tadawo falonta kuma, tayi haka yafi sau uku kafin tayi ta maula ta fito.
Tana fitowa yara Na sakkowa daga sama suda Nazeefa, da gudu suka iso gareta suna mata oyoyo, duk rungumesu tayi tad'auki Siddiaqa da itama tashiga rubibin 'yan uwanta.
Sannu da zuwa Nazeefa Tamata, tace, ''badai sai yanzuba?".
"A'a Anty Nazeefa, tun magrib nadawo, kuna cikine shiyyasa. Ashe 'yan tafiya sun iso?".
" kina fita suna isowa, dan inaga daga kaiki ma ya Jabeer yawuce ya d'akkosu".
''Ayya bara Na shiga Na gaisheta to".
"Okey, kishiga tana ciki".
Cikeda fargaba Amatallah ta nufi 6angaren Aneesa d'aukeda Siddiqa, d'ayan hannunta kuma tarik'e Ummita.
Muryarta nad'an rawa tayi sallama, Aneesa dake zaune a falo tana fiddoma Siddiqa kayanta ta amsa.
Shigowa Amatallah tayi, Aneesa ta d'ago ta kalleta, sukaima juna kallon ido cikin ido, kowannensu saida yaji fad'uwar gaba, amma Amatallah saitamata murmushi.
Yayinda Aneesa ta kauda idonta, fuskarta kadaran kadahan, ba ad'aureba bakuma a sakeba kamar ta Amatallah.
" bismillah ki zauna". Aneesa tafad'a tana zuge zip d'in jakkar kayan Siddiqa.
Zama Amatallah tayi a d'ofane saman kujerar kusada ita, ta d'ora Siddiqa a cinyarta, yayinda Umminta ta ra6u da jikinta itama, cikin dauriya tace, "ina yini, kundawo lafiya".
" lafiya lau, yamuka sameku?".
"Lafiya lau Aunty".
Daga nan kuma falon yay tsit, sai dariyar Siddiqa da Ummita kema wasa.
Kusan mintuna uku babu Wanda yasake cewa komai, sai kuma Aneesa ta katse shirun da fad'in " ya karatu?".
Amatallah tace, "Alhmdllh Anty".
''Masha ALLAH".
daga nan kuma suka sake yin shiru, kowa da abinda yake kissimawa a zuciyarsa kan d'an uwansa.
Mik'ewa Amatallah tayi tace, " bara mu barku Ku huta ". Bata jira cewar Aneesa ba ta fice.
Aneesa tabita da kallo tanamai jin wani irin kishi a k'asan ranta, dukda tafi Amatallah haske da hanci Dan Aneeaa farace, koma nace k'yau, hakan bai hanata jin zafintaba da fargabar had'a miji da ita.
Amatallah kam babu komai a ranta, sai dai ta kula halin Aneesa ya banbanta sosai da Fateema, a ranta tace ALLAH yabani ikon zama da kowannenku lafiya nidai.
Nace, " amin Amatallah".
A canma Fateema ta isa Dubai lafiya, sun rungume juna ita da mijinta cikin kewar junansu, tun a mota yake nuna mata yayi matuk'ar missing d'inta, sai shafa cikinta yake yana kissing wuyanta.
Itadai murmushi kawai takeyi da mamakinsa, saikace ba yau wata matar tabar wajensaba.
Koda suka isa gida dakansa yamata wanka, yakuma ciyar da ita abinci, daga nan kuma aka koma soyayya🤭,
su Uncle fa babu dama, dole matanka suyita tsula kishi a kanka🤥.
🚶🏻♀
_____________________________
Abubuwa suncigaba da faruwa, wasu masu dad'i wasu marasa dad'i.
Zaman Aneesa da Amatallah dai sai a hankali, babu wani kulawa babu kuma gallazama juna, dan ba gargad'in wasa Uncle yayma Aneesa ba akan zaman lafiyar gidan, yakuma tabbatar mata inhar yaji wani Abu daban ita zai hukunta, tunda itace babba.
Itama Amatallah bai k'yaletaba, yamata gargad'i sosai.
To Alhmdllh babu dai wani gagarimin Abu daya faru, dan kowaccensu na gudun 6acin rai, kuma ma ga Nazeefa, duk abinda yafaru a gidan takan sanarma yayanta.
Rashin zamanma da Amatallah ke samu a gidan saboda makaranta saiya kuma sauk'ak'a wasu abubuwan.
Duk ranar asabar kuma suka had'u suduka sutafi gidansu Innani su yini a can.
Jikin babama Alhmdllh, dukda ciyone Na tsufa dai.
Masha ALLAH zuwa yanzun kam su Alhaji Muhammad baifi sauran 1month su dawo Nigeria ba, kuma Alhmdllh yasamu nasarori sosai akan abinda yaje nema.
Yanzu haka kam shirye-shiryen dawowar suketayi.
Tunda kwanakin dawowar Uncle M.A yazama 10days Anty maijidda tazo gidan, wasu kayan gyaran fata masu k'yau dana gashi ta kawoma Amatallah, ta nuna mata yanda zatayi kullum indan zata kwanta, sai wasu turarurruka masu masifar k'amshin tsiya, Na wanka dana gashi, ga mayuka masu k'yau da k'amshin tsiya,
Sosai tama Amatallah gargad'i akan tadage karta saka wasa a amfani dasu, sannan tace taringa shan fruits kullum safe da yamma, ga Nono shanu mai k'yau dana rak'umi tace tasaka a fright tanasha shima safe da yamma, sai kuma had'in Zuma da kayan k'amshi da mazar kwaila, shikuma da yamma kawai tanashan 3spoon.
Godiya sosai Amatallah tamata, dukda bata fahimci dalilin Anty maijiddar Na bata wad'annan kayanba, bakuma tasan ma'anarsu bama, tadai d'auka Na gyaran fatane dakuma murjewar jiki.
Duk yanda Anty maijidda tamata bayani haka ta dage sosai. aifa dandanan Amatallah tafara sauyawa, fatarta harwani shek'i takeyi, dama ga bak'inta mai k'yaune, k'amshi kam ba'a magana aii, ko da ga nesa ta giftaka saika jishi, su Goodness k'awayenta kullum cikin tambayar miya canjata haka sukeyi?.
Itadai sai dai kawai tamusu dariya bata cewa komai, dan har lokacin basu ta6a sanin tanada aureba, duk zatonsu Uncle datake yawan ambata shike rik'onta dai, Fa'iza cema taso ta d'an d'agota amma saita doje.
Fa'izan tace aibabu damuwa, inma tanada auren ai zasu sanine watarana.
Aneesa ba wani ganin Amatallah takeba sosai, shiyyasa bata kulada canjawar datayiba, sai dai k'amshin datakeyi kwanan nan yana d'aukar hankalin Aneesa, harma take mamakin ina Amatallah tasamo wannan k'amshin haka?.
Sai dai batada mai bata amsa, dodele tai gum da bakinta.🤐
____________________________
*_RANA BATA K'ARYA_*
yauce ta kama ranar dawowar su Uncle k'asarsu ta haihuwa, tunda asubahi Aneesa aka tashi tafara gyaran 6angarensa, saida taga komai yad'au haske da shek'i, hakama tadawo babban falon gidan, 6angarentama haka, Nazeefa dai nata kallon ikon ALLAH, Amatallah ma batasan hidimar da akeyiba, tunda tayi salla takoma barci, sai wajen 7:30 ta tashi tayi wanka, ta shirya kamar yanda Anty maijidda takira ta Umarceta.
Bata dade da kammalawa ba Jabeer ya kirata akan tafito yazo d'aukarta.
Mamakine ya kamata, dan tasan yaudai babu school, dan Asabar ce.
Tana cikin mamakin saiga Nazeefa ta shigo itama cikin shiri. Kallonta Amatallah tayi tace, "Anty Nazeefa tare zamu fitane?".
''Eh".
Cewar Nazeefa.
" ina zamuje to, ko wajensu innani?".
"A'a, kedai kiyi sauri ki shirya, dansu Ya Muhammad k'arfe 5pm zasu sauka, somuke kafin 3 mu dawo kuma.
Amatallah batace komaiba tak'arasa shiri ta fito. shiru taji falon, dan haka ta tambayi ina yara?".
Jikin motar suka k'arasa Nazeefa tana fad'a mata suna gidansu wajen innani, Aneesa kuma tafita itama.
Mota suka shiga Amatallah Na mamakin wannan Abu, ina kuma duk zasuje abar gida shiru haka?, amma koba komai tayi murna, dama batason Uncle ya iskota agidan..................✍🏻
Nace, "humm, Amatallah kenan, zakiyi bayani dalla-dalla-dalla da bakinki😂😜.
🤩👎🏻
One Luv my sweet fan's🥰
*_ALLAH ka gafartama iyayenmh😭🙏🏻_*
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
____________________
*_Number 17_*
____________________
Uncle M.A bai baro gidan Alhaji Sabi'u ba sai da suka tsara abubuwan masu yawan gaske, harda mutanen daya dace su tuntu6a domin samun had'in kansu a tafiyar.
Bayan sun kammala tsare-tsarensu Alhaji Muhammad yaymusu sallama yataho bayan ya ajiyema yara kud'in shan Chocolate's.
Daga gidan Alhaji Sabi'u gidansu yawuce ya gaida iyayensa, nanma yad'an dad'e sannan yataho da burin zai koma da daddare.
Harya tada mortar ya kashe, waya ya d'auka yafara laluben Number Amatallah yana murmushi.
Rabonsa da ita tunda yaje jos, kullum yakira saiyaji wayar a kashe, idan kuma sunyi waya da kawunta kunya yakeji yace yahad'ashi da ita.
Cikin sai'a kuwa yau sai Number tashiga.
Amatallah na zaune a tsakar gida itada Anty Sadiya da wata yarinyar makwaftansu Asiya tana mata kitso, Anty furera kuma nata kai kawo a tsakar gida tana girkin rana.
Game Amatallah keyi a waya hankalinta kwance, jefi-jefi takan saka baki a hirar Asiya da Anty Sadiya.
Kirane ya shigo wayar, wannan ne kuma karo na farko da aka kirata, dan ita mantawama take da wayar, tunda Uncle yabata suka gama gani ta kasheta. Bata kuma kunnawaba sai yanzu dataga games a wayar Asiya ta d'akko ta tura da films.
Number babu suna, shiyyasa ko kad'an batayi zaton Uncle baneba.
d'agawa tayi tareda manna wayar a kunnenta tace, "hello".
d'an lumshe idanunsa yayi ya gyara zama sosai da kwantar da kansa a jikin kujerar motar. Amatallah takuma fad'in " hello wanene?". cikin Nutsuwarta tayi maganar.
d'an murmusawa yayi sannan yamata sallama cikin sassanyar muryarsa datake matuk'ar so.
Bata buk'atar k'arin bayani kam, danta ganesa. saita samu kanta da fargabar amsawa.
Sai da Yakuma maimaita sallamar da cewa "My Best! Bak'ya jinane?".
" inaji Uncle, ina yini".
"Bazan amsaba, dan kinmin babban laifi my best, Wanda kuma kika cancanci hukunci mai girma da tsauri".
Amatallah ta marairaice murya kamar zatayi kuka, " wayyo ALLAH na, minayi Uncle?".
Daga Anty Sadiya har Asiya baki suka sake suna kallonta da mamaki, su gani sukeyi tana sane takeyi, saboda sungane Uncle d'in tane na Kano, kuma Mijinta a yanzu.
Itakam kokad'an ba haka bane, babu wata manufa aranta, sai dai saboda shagwa6ar datakema babanta abayane kawai, saikuma take ganin Uncle d'in kamar shine Baban ayanzun, shiyyasa takan masa Abu tamkar yanda takema babanta, dan ita tama manta dawani batun aurensa dake kanta.
Ba k'aramin canja tunaninsa shagwa6ar Amatallah tayiba, saiya samu kansa dakuma narke mata shima, ya manta matsayinta na d'iyar Isma'il brother d'insa, yarinyar da aka Haifa a tafin hannunsa harya rad'a mata Suna.
"Uncle please, kafad'amin laifin dan ALLAH?".
" Ajiyar zuciya ya sauke, yakuma k'asa da muryarsa sannan yace, "miyasa kika kashemin waya? tunfa dana tafi bakiko nemeniba my best".
" kayi hak'uri Uncle. ALLAH mantawa ma nayi da wayan, sai d'azun natuna dazan tura games aciki".
"Uyim an manta da Uncle, amma ba'a manta da tura games da Films ba ko? zan ramane ai nima".
" wayyo Uncle bazan sakeba ALLAH insha ALLHU, kaji Dan ALLAH".
"Shikenan, amma idan kin sake zan hukun taki, kin amince?".
Kanta ta d'aga masa kamar yana gabanta, tace, " to Uncle, sai kuma tace uncle katafine? ".
"A'a ban tafiba dai tukunna, amma insha ALLAH gobe k'arfe 3pm zan wuce".
"Ayya, ALLAH ya kaimu lafiya Uncle, yasa kaje a sa'a kadawo da Nasara".
" amin my best daughter, ALLAH yamiki albarka kinji, ya gafartama su brother ".
Murya a raunane ta amsa da amin.
Sallama sukayi akan zai kuma kiranta anjima Dan yaji muryarta tafara canjawa, bayason jin kukanta ko kad'an.
Tana ajiye wayar Asiya ta tuntsure da dariya harda rik'e ciki.
Kallonta Amatallah tatsaya yi da mamaki tareda k'ok'arin had'iye kwallan data cika mata idanu.
" Asiya lafiyarki kuwa?".
"Ah, k'alau nake kuwa, Amatallah irin wannan lobayya haka".
" lobayya kuma Asiya? Uncle d'inanefa".
"Uhm ai Nasan Uncle d'in nakine nima, ALLAH dai ya kaimu Kano kawai musha kallo, ALLAH da nacema Abba banson karatu a Kano, amma yanzu kodan ke can zanje".
Baki Amatallah ta ta6e, tace, " k'yadai ji dashi".
Anty Sadiya dai batace komaiba, sai 'Yar dariya datakiyi itada Anty furera.
Amatallah bata fahimci duk inda suka dosaba, tacigaba da game d'inta, sai dai k'asan zuciyarta tana mamakin a salon da Uncle ya amsa mata waya yau, sai kuma narke murya yake k'asa sosai, dukda tasanshi shid'in dama k'arshe ne awajen golden voice.
Shiru Uncle M.A yayi yanabin wayar da kallo, kai kace acikine zaiga Amatallah ta 6ullo, gemunsa yashafa a fili ya furta " Muhammad mike damunka hakane? d'iyar Isma'il cefa, wadda a tafin hannunka aka haifeta". Ya k'are maganar da fad'in "ya salam!" tareda furzo iska daga bakinsa.
Ya dad'e yana sak'awa da kwancewa Kafin yatada motar yanufi gida.
*_Washe gari_*
Misalin 2pm yasamu rakkiyar matansa da k'annen sa zuwa airport, yara sunsha kuka har saida yamusu wayo sannan. kafin jirginsu yatashi saida yay k'ok'arin kiran Amatallah amma wayarta a kashe, ya kira kawunta kuma yace baya gida wlhy. baiji dad'in rashin samuntaba, haka dai yashiga jirgi suka shilla.
Jabeer ya maidasu Fateema gida da yara.
Anty Maijiddah da Shehu da Nazeefa suka shiga keke napep suma suka tafi, dama anan sukazo.
___________________________
Tunda Uncle M.A yabar k'asar rayuwa gidansa ta canja salo, sunkoma rayuwar babu ruwan wani da wani, ko wacce harkar gabanta takeyi, idan an had'une dai za'a gaisa kowacce takama tsaginta.
Tafiyarsa da kwana biyu Nazeefa ta had'o kayanta tadawo gidan, wani d'aki dake can sama kusada nasa ta gyara.
Hakan kam bak'aramin haushi yabama Anresa da Fateema ba, amma babu yanda suka iya, Dan Nazeefa bata raga musu, shiyyasa duk suke shakkarta, ko Fateema dake 'Yar uwarta bata d'agama k'afa.
Kullum Jabeer zaizo da safe yaga lafiyarsu, da yammama idan yadawo aikima yakan zo, shima shehu randa 'yan arzik'in ke kansa yana lek'owa, wadda kuma tamasa kallon banza a cikinsu kotak'i basa abinci yamata wankin babban bargo yay tafiyarsa. Anty Maijiddah ma takan lek'o ganinsu.
Alhmdllhi jikin baba ma babu laifi, yasamu sauk'i, dukda lokaci-lokaci ciwon kan motsa masa.
Kullum ta ALLAH Alhaji Muhammad yakanyi k'ok'arin kiran kowa yaji lafiyarsa, dakuma k'ara nuna soyayyarsa ga matansa, shiyyasa kowacce kejin kanta On top, tamkar ma mijin yafi kulawa da ita da yawan kiranta.
Basusan inhar yakira d'aya dasun gama waya zai kira d'ayarba. Harma Amatallah dabawani sakewa take suyi hiraba, bare akai ga zancen soyayya, yakan daiji lafiyarta sukumayi hira kad'an.
Hakanne kuma yafara tasirantar da shak'uwa a tsakaninsu, koyaya takan d'an saki jiki dashi, yayinda shikuma kanyi mamakin kansa a yanda yake gaza controlling d'in tunaninsa akan Khadija d'iyar Amininsa,