Showing 51001 words to 54000 words out of 104242 words

Chapter 18 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16049

saukar la66ansa akan nata.
A zuciyarta tace na shiga tara ni Khadija, Uncle zaka kasheni da kunyarka wlhy.
Saida ya sumbaci la66anta sau biyu sannan yamik'e tsaye sosai yana murmushi idonsa a kanta face d'inta.
"Sai da safe my Heartbeat! ko kawai nashigo bargon mu kwanta abinmu, mu warware sadaukar da kwanan?".
Bargon taja da sauri tarufe har kanta gaba d'aya.
K'aramar dariya yayi yamatso kamar zai bud'e mata bargon, murya k'asa-k'asa cikin rad'a kamar mai tsoron ajisu yace, " Ina matuk'ar Sonki keda Salonki my best Darling. goodnight, zan kwana da mafarkinki".
Bai jira cewar taba yakama hanyar fita, yamasan bazata ceba d'in, fitilar d'akin ya kashe ya fice, bayan ya kunna fitilar wayarsa.
6angaren Aneesa ya komai, tana nan kwance yanda ya barta, tayi kuka harta godema ALLAH, bai mata maganaba ya d'auki Saifudden ya fita, wajen Fateema ya kaisa, dukda barci takeyi abinta hankali kwance itada yara, haka ya shinfid'eshi kusada 'yan uwansa yamasa addu'a sannan ya koma wajen Aneesa. yanzuma yanda yabarta haka ya isketa, ya d'auke Siddiqa daga gabanta ya gyara mata kwanciya gefe saboda gadon babbane ba laifi.
Duk abinda yakeyi Aneesa na jinsa, tun shigowarsa ta farko har d'aukar Saifudden ya fita dashi, ko kad'an batayi zaton Amatallah zata yarda ya dawo wajen taba, anya idan itace zata iya kuwa? sai taji Amatallah ta birgeta.....
Ajiyar zuciya ta saki yayinda taji ya rungumeta.


Hummm, nayi nan, Dan yau Uncle da neesarsa babu sauk'i.🤐
🚶🏻‍♀

Tumda Uncle yafita Amatallah ta sauke ajiyar zuciya a fili tace, ''kai Namijima sai abarsa, duk yanda kake kallonta a nesa ba haka bane, saika zauna dashi kake gane Natural colour d'insa, wlhy a baya idan wani yacemin haka Uncle Muhammad yake saina k'aryatashi, humm Ashe ya wuce tsammanina ma".
Hannu takai ta shafa bakinta, saikuma taja bargo da sauri takuma rufe fuskarta tana rintse ido da fad'in ''wayyo Uncle Muhammad ka kasheni wlhy, yanzu tayaya zan iya kallonka da safe?, shikenan na mutu ni Amatallahin Ammi da baba".
Haka taita sambatunta ita kad'ai, hardai barci yazo mata, takuma 'yan addu'oi ta gyara kwanciya.............✍🏻


Ni dai mai d'aukar rahoto nayo waje ina dariya wa shirmen Amatallahin ku😂👍🏻.



_Nasan saboda yawan page d'in nan yau har saikun kai jibi kuna karantawa🤭, kusan Read more 7 fa🤣😜, asha karatu lfylfy._
🏃‍♀



🤩👎🏻

One Luv my sweet fan's🥰👍🏻.







*_ya ALLAH ka gafartama mahaifina._*😭🙏🏻
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_Hummm, jiyakam ai magana gagarata tayi a kowanne groups, dan jiya kad'an garage nasha Suburbud'a hannunta masoyan Amatallah😆😆, Aneesa zata jamin jaza'i, nibada laifiba😂🙆🏻._*
Haba masoyan Ama..., karku damu zaku fanshe ne🥰👍🏻.



____________________
*_Number 23_*
____________________


Koda Uncle ya koma gida ya taradda Fateema kawai a falo, Aneesa kam tana 6angarenta.
Gaban Fateema ya k'arasa ya sumbaci Goshinta da cikinta, d'agowa yayi yana dariya da fad'in nabiya bashi my tee...
Itama dariyar tayi tana fad'in kafita koba sabulu".
zama yayi inda Aneesa ta had'a break fast, batareda ya nemetaba yazauna yaci kad'an kamar yanda ya saba. Fateema kam dad'ine ya kamata, tasan cin abincinnan dayayi bai nemi Aneesa ba saitayi tamkar ta fashe dan haushi.
Yana hayewa samansa itama ta tashi tashige 6angarenta, dama da biyu ta zauna falon.😆


*********

Amatallah bayan sun fito lecture suka nemi waje can gefe suka zauna suna sauraren ta.
A nutse tabasu labari tana kuka, suma sunayi, aka rasa mai lallashin wani cikinsu, saida sukayi mai isarsu sannan sukayi shiru suna bama Amatallah hak'uri, sosai suka tausaya mata.
Itama Rita tace zata basu labarinta gobe.
Duk suka amsa da ALLAH ya kaimu.
Amatallah tanason tambayarsu maganar da Aneesa ta mata da safe, amma tana ganin kamar suma bazasu fahimtaba, musammanma su Goodness, dan haka tayi shiru da nufin zata tambayi Fa'iza ita kad'ai.

Suna fitowa lecture ta k'arshe Goodness da Rita suka nufi hostel, yau basu musu rakkiya ba saboda kowa yagaji.
Da wannan damar Amatallah tayi amfani ta sanarma Fa'iza abinda yafaru tsakaninta da Aneesa, dakuma tambayar da Uncle yamata ta 6oye masa.
Kallon mamaki sosai Fa'iza kema Amatallah, tace, "dama bakida wayo haka Amatallah?. Wace mace ke sadaukarma kishiya kwananta? Sai dai haihuwa ko lalura wlhy, Lallai bakisan miye kishiba Ashe. Wlhy duk da kike ganina k'aramarnan bana bari kishiya tasamu lagona, bazanyi kishin haukaba kuma bazan raga mata ba".
" ban ganeba Fa'iza, kema kinada kishiyane?".
Dariya Fa'iza ta mata, "lallaima Amatallah, koda yake duk yandafa muke dake d'inan babu Wanda yasan gidan wani, toni rana d'aya aka d'aura aurena da kishiyata, ni da safe ita da rana, kuma yanada wata matar, saidai tana gidansu, sa6anin dasuka samune yayo auren huce haushi damu mu biyu, yanzu kuma shirin dawowa take an sasantasu".
Ba k'aramin mamaki da al'ajabi bane yakama Amatallah, a ranta tace halin maza sai abarsu. a fili kuma tace "amma Fa'iza kunsan da haka kuma kuka aureshi?".
" to yazamuyi Amatallah, auren zumincine, da mamana da babansa uwa d'aya uba d'aya, waccan kuma budurwarsace dama, saboda itanema suka rabu da matarsa akan yace zai Aurota ta tada hankalin kowa a families d'in, harya kai gamata saki d'aya saboda sakko iyayensa datayi a haukarta, mamansa kuma tanada zuciya, hakan yasa tace bayan auren dayakeson k'arawa yahad'a dani mu zama biyu, saitaga yanda uwargidansa zatayi d'in, shinefa dalilin dayasa aka d'aura aurenmu rana d'aya, ni da safe ita da azhur, kusan shekara biyu kenan, uwargidan bata kuma wani aurenba, bakiga yanzu duk yanda tafita hayyacintaba, kullum cikin bibiyarsa take tana bashi hak'uri da rok'on ya maidata, dan suna matuk'ar son juna, to shine manya dai suka shiga aka sasanta, yanzuma jibi zata dawo".
"Tabb, lallai wasu matan basuda hankali, nifa banga mafitaba ga macen da zata rud'ar da kanta wai dan miji zai sake aure, raini yake kawowa wlhy, kowa yanamaka kallon shashasha, kinga yanzu ta jama kanta daga d'aya anmata biyu, kuma mijin bazai kalleta da darajaba kamar da can?".
" wlhy kuwa hakane Amatallah, ALLAH dai ya sassauta mana kishinan, wasu Matan sun Gaza gane kishi cikin SIYASA tafi kawo zaman lfy da daraja wajen miji, kamazo kana hauka kan Namiji baisan kanayiba".
"Tokin gani, kuma wlhy kishiyarma indai kina nuna mata komai ba komaiba a fiska koda kina kishinta a rankin saikinga tana shakkarki da tsoron takaki, dan baki bata wata k'ofar dazata rainakiba, kuma mijin bazai ta6a aminta ta raina kiba, kinga ai kin nemama kanji daraja har wajen dangin mijin. yanzu wlhy Uwargidanmu inkikaga yanda take kishinta saita burgeki, amma Aneesa ba a magana, harma mamaki take bani".
''Karki damu Amatallah, zan koya miki wasu abubuwan, dukda shi zama da kishiya basai ankoyama mace shiba, wahalama na sakata ta koya, kamardai yanda ni wahalarce tasani koyon".
"Kai dan ALLAH?".
dariya Fa'iza tayi, " ALLAH kauwa Amata, ke idan INA Baki labarin gidanmu ALLAH saikice k'arya nake, ai garaku na fahimci kishin masu Ilimi akeyi a gidanku, mu Amaryarmu tafi uban kowa zafin kishi, ga uwargidan itama babu sauk'ice".
"To ALLAH ya k'yauta".
Nandai suka d'an tattauna, Fa'iza ta ankarar da Amatallah abinda Aneesa ke nufi da maganarta.
" kinga daga yanzu kema sauk'i shirya aii, amma dan ALLAH inason tambayarki, kumafa ki fad'amin gaskiya inhar kin yarda dani".
"Na yarda dake wlhy Fa'iza, shiyyasama nafad'a miki sirrina ai".
Murmushi Fa'iza tayi, sanan taja hannunta suka zauna kan wata baranda, dan dama basukai ga fita gate ba.
Kafad'arta ta dafa, " Amatallah shin kinason Uncle d'inki kuwa?".
Dariya Amatallah tayi, sannan tace, "gaskiya kikace na fad'a miki kuma zan fad'a miki Fa'iza. lokacin da akai aurenmu dai bana masa son aure, dan kallon uba nake masa, lokacin ga rud'anin rashinsu Ammi, amma tunda na fahimci yanason cikar burina akan karatu, da k'aunar dayakema mahaifina sainaji nafara masa SO irinna aure, Ahankali kuma yaytamin abubuwan dasukaja ra'ayina ta waya, da kuma taimakon shawarwari da k'anwarsa Nazeefa taita bani, saina kuma gane babu Wanda yasan muhimmancina da kuma zaiji tausayina kamarsa, nasan kuma wannan babana ya kalla harya k'ulla wanan auren, Wlhy Fa'iza ina son Uncle har cikin raina, saidai ina masifar jin kunyarsa, musamman idan na tuna alak'arsa da mahaifina".
👍🏻Jinjina Fa'iza tama Amatallah, " ammafa kin birgeni, dan kar6ar k'addarar ki dakikayi shine Abu mafi muhimmanci, na tabbata kuma k'addarar alkairice, dawatace saita bijire tace yamata tsufa. Maganar kunyarsa kuma karki damu, daga randa kuka kasance k'ark'ashin inuwa d'aya zaki rage da kanki wlhy, nima nayi wannan kunyar Akan ya Usman, amma yanzun hummm".
Dariya sukayi gaba d'aya harda tafawa.
Fa'iza tacigaba da fad'in ''yanzu Amatallah akan abokan zamanki zan baki shawara, saifa kin mik'e sosai, inba hakaba su maidaki sakarai har mijinma yacigaba da d'aukarki haka. Ki kama mijinki ram ki rik'e dan yanda kike bani labari nakula mijinku d'anson soyayyane da kulawa da mace, kiyi k'ok'ari kema ki samu rabonki kafin su tsufar dashi kinan kunya na tsutarki. inhar yau yabuk'aci ki kar6i kwananki wlhy ki kar6a, kuma ya buk'aceki karki bijire masa, yanda yanzu ake yayin mutuwarnan".
''Kai Fa'iza ALLAH kinban kunyafa".
"A'a ah yarinya zauna kallon ruwa kwad'o yamiki k'afa, yanzu maza tsada sukeyi shiyyasa kowacce mace ke tattali idan tasamu, karki bari kunya tasaki zama bora a gidan mijinki. kuma kin burgeni dabaki fad'amai ainahin abinda Aneesa tamikiba, dan da kanki yakamata ki rama, karki raga mata, intaga keda uwargidan halinku mai k'yaune itama zata fara gyarawa, kinga kun jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan, Ku k'ara daraja da soyayyarku wajen miji, kun kuma gyara halayyar abokiyar zamanku yanda zaku samu zaman lafiya sosai".
" gaskiyane Fa'iza, shikenan zanyi amfani da shawarar ki, Aneesa kuma zan nuna mata ainahin Natural colour d'ina, dan nakula kallon shashasha takeminne, batasan Amatallah bata d'aukar rainiba, halin rayuwane kawai ya maidani haka, bana fad'a amma kuma nasan yanda zan zauna dakowanne irin mutum".
"ALLAH ko kwanan dakike gani na barmata yahad'a da inajin kunyarsane, kuma itama ina son na gwadata, shiyyasama naje tayata girkin da safe, dannaga yanda zata kar6eni, hakan duk yana cikin dabarun da Anty maijidah ta koyaminne".
👏🏻Tafa mata Fa'iza tashigayi tana dariya, " da k'yau Amatallah, Ashe kemad'in A ce ban saniba".
"ALLAH Fa'iza ba wai haka baneba fa, kawai dai bana son rainine ALLAH kuwa, ina son idan na nuna maka girmanka kajashi".
" gaskiyane Amatallah, ALLAH yabamu zaman lafiya dai, nima jibi uwargida zata dawo, bansan kuma wane zama zamuyiba da ita".
"To ai yanzu kece Uwargida kenan".
Dariya Fa'iza tayi sosai, takama k'arfe ta mik'e da k'yar tana fad'in "su Uwargida anji jiki".
Amatallah ma mik'ewa tayi tana dariya, "babufa wani aniji jiki, karkima yarda akawo miki raini, kece Uwargida".
Haka dai suka tafi suna tsokanar juna, kowa tasamu Napep tashiga.
Shawarwarin Fa'iza sunyi tasiri sosai a zuciyar Amatallah, Hakanne kuma yasata d'aukar aniyar ramawa ta cikin ruwan sanyi, a ranta tanajin itama zata shiga a dama da ita, dan tana son Uncle d'inta, tunda tasan zama dashi babu cangi har Abadan saidai mutuwa, to mizaisa tacigaba da cutar kanta Aneesa na kallonta a banza, itafa ta tsani tana ganin mutuncin mutum yanemi zubda darajarsa a gurinta, dama ai bawai batasan kanta bane, kawai kunyar Uncle da kallon uba datake masane yasata komawa gefe, amma yanzu shawarwarin Fa'iza sun maidota hanya d'od'ar, kuma zatayi amfani dasu.


" hummm, su Amatallah anji jiki Anfara dawowa hanya🤣, haka masoyanki sukeson ganinki, musamman ma Tawan (miss Xoxo)😂👍🏻


___________________________
Sanda Amatallah ta dawo gidan ta tarar Uncle bayanan yafita, Fateema kawai ta tarar a falo zaune, yarama suna Islamiyya.
Sannu da zuwa Fateema tamata, ta amsa cikin fara'a tana mata barka da gida.
Jin maganganinsu ne yasaka Aneesa dake kitchen lek'owa a zatonta Uncle ne ya dawo, dukda cike take da haushin abinda yamata da safe, dan tana ciki har yayi break fast yay wanka yafice bai nemetaba, har yanzu kuma bai dawoba, amma dukda hakan tafitone yanzun tarbarsa danta bama Fateema haushi, sai kuma taga Ashe Amatallah ce.
Daga Fateema har Amatallah kallonta sukayi, Amatallah ta d'auke idonta tareda mik'ewa ta kwashi takardunta, saida taje k'ofar 6angarenta sanan tace Anty Aneesa sannu da girki fa". bata jira amsartaba tashige abinta.
Ba Aneesa ba kawai harta da Fateema saida ta kalli Amatallah d'in, dan awani salo daban tayi maganar, kuma cikin sanyinta kamar yanda ta saba, inma Baka saniba bazaka ta6a cewa itace tayi maganar ba.
Fateema tayi dariya a zuciyarta tana fad'in yanzun za'a fara wasan kenan.
Aneesa kam wani k'ududun bak'in cikine ya tokare mata mak'oshi, tama rasa yanda zata fasaara rainin hankalin Amatallah d'in.

Koda Amatallah ta shiga d'akinta alwala tafarayi tai salla, danta risketa tana hanya ne.
Ko da ta idar bata nemi abinciba, chin-chin d'in dasuka saya a makaranta taci tasha ruwa, sannan tashiga wanka, tadad'e a toilet d'in kafin ta fito, data fito batayi kwalliyaba, d'akinta tasama key dan bata buk'atar ko Uncle ya dawo ya shigo mata yanzun.
Game taita bugawa a waya abinta har saida aka kira sallar Magrib, tana jiyo hayaniyar dawowar yara tun 6pm, amma dai bataji alamar Uncle ya dawoba, hakan yamata dad'i kuwa.
Alwalar magrib tayo tazo tayi salla, tsakanin magrib da isha'i tayi karatun alkur'ani da azkar d'in yamma, daga nan gaban mirror takoma ta zauna, tanutsu wajen yin simple makeup, takuwayi k'yau d'as. Wasu Pakistan ta saka, rigar sky blue ce, wandon kuma na jins dark blue tayi k'yau sosai, ta taje kamta takuma gyarawa, dama batayi kitsoba, dukda gashinma bawani na kirki baneba, tamkar na (Fatee d'ayyabu Tyw😜) d'an siririn gyalenta shima sky blue tasaka, inba kallon Tsaf kamataba bazaka ta6a d'auka kwalliya tayiba, komai Simple tayishi, sai masifaffen k'amshi datake ta zubawa, wanda sirrin Anty maijiddane da k'awarta mai gyaran jiki😉.


Uncle kam yanacan wajen Alhaji Sabi'u m Ali suna tsare-tsarenasu, saida sukayi sallar isha'i sannan yabaro gidansa, daga nan gidansu yaje, bai wani zaunaba suka gaisa a tsaitsaye saboda yaje da safe daya fita kafin yaje gidan Alhaji Sabi'u, daga nan gidansa ya zarto.
Horn yayi kusan sau 3 sanan su Abulkhairi suka jiyoshi, da gudu suka fito suka bud'e masa ya shigo.
Hayaniyarsu Ce ta fiddo Aneesa, cikin kwalliya take kuwa kamar ka saceta ka gudu, tanata k'amshi abinta. fitowarta tayi dai-dai ta fitowar Uncle daga mota.
Yaransa duk suka rungumeshi, tarbarsu yayi cikin jin dad'i, yabisu d'ai-d'ai yana sumbatar kumatunsu, suma duk suka sumbaci nashi.
Aneesa dake tsaye gefe yayi kamar bai gantaba saita kuma cika fam, amma dukda haka ta danne fushinta tamasa sannu da zuwa.
Kallonta yayi ya sakar mata murmushin dake kasheta.
Babu shiri itama tayi murmushin, Siddiqa dake hannunta ya kar6a, tafara masa gwarancinta yana dariya shida sauran yaran, ahaka suka k'araso babban falon.
kujera ya nuna musu yace su zauna nan su jirasa yadawo, ya zaunar da Siddiqa itama, Aneesa na tsaye yawuceta ya shiga 6angaren Fateema.
A falo ya isketa zaune tayi rashe-rashe da k'afafu ta bud'ema kanta fanka, fuskarsa d'auke da murmushi yak'araso gareta.
"O my tee... Irin wanan bajewa haka? halan babynane yasaki jin zafi?".
"Kabari kawai wlhy Nurri zufa nakeji sosai kamar nayi wanka a ruwa".
Kusada ita ya zauna, yad'an rungumeta jikinsa yana manna mata kisses a wuya da la66anta, " my tee hakan ya nunamin babyna yakusa zuwa duniya, ai da kin fara zufarnan nasan haihuwarki ta gabato, ALLAH ya saukeminke lafiya Uwargidana".
"Amin Nurrina". Itama ta sumbaci kuncinsa".
" thanks my tee".
Murmushi tayi batace komaiba.
''Yauwa my tee bara naga Amatallah itama naje nayi wanka, yau ina son zama daku Ku duka".
" okey boss sai munji kira".
Rankwashi yad'an kaimata, tunkan hannunsa ya sauka a kanta ta tare tana fad'in "wayyo Nurrina sorry please".
Dariya yayi batareda ya rankwashe tanba, yace, " matsoraciya kawai, ga tsoro gajan fad'a".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login