Showing 93001 words to 96000 words out of 104242 words

Chapter 32 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16046

ngd da comments d'inku da addu'ar dakukema mahaifina, duk ina gani saidai babu damar amsawa, typing d'inma a wayar my Abdull nakeyinsa wani lokacin wlhy, dan wayata dana cika danne-danne saita k'ame🤣._*




🤩👎🏻
One luv my sweet fans









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻


[1/24, 2:15 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

____________________
*_Number 38_*
____________________

A wajen shan ruwanma bai nemi kowaccensu ba, harma mai girkin kanta, tareda yaransa sukaci daganan ya zauna sauraren shirmensu.
Aneesa tasan tanada laifi shiyyasa tak'i fitowa, Amatallah kam firarsu sukesha da Aysha hankali kwance, tasan ba itace da mijinba, abincima yana tafiya salla dama ta d'ebo musu, Fateema kam zamanta tayi itama ta sharesa.
Sauraren surutun yaran kawai yake, amma hankalinsa nakan matan nasa, yasaba ko yaushe indai yana a gida duk suna gefensa, yau kuma yalura sunma had'e masa kai sun barsa shida yaransa.....
Wayarsa dake wringing ta dawo dashi hayyacinsa, Innani yagani ajiki, da mamaki yad'aga dan saiya had'a watanni bata kirashiba inba shine ya kirataba.
A ladabce ya gaisheta, ta amsa tamkar yanda ta saba, ta d'ora da fad'in ya yaran.
"Lafiya lau suke Innani, ya baba?".
"Yayi barci, Aysha ce bata dawoba, shine abin yadameni nace bara na nemeka, danna kira warta bata zuwa".
''Kiyi hak'uri Innani, wlhy naje d'aukar Khadija saita biyomu akan idan nasha ruwa zanzo gidan saina maidota, tokuma saina iske Aneesa basu dawo daga gidan Shehu ba hankalinna yatafi can, amma yanzu zan maidota".
''Alhmdllh, dama ni damuwata kar wani Abu ya samarmin yarinya, amma tunda tanan shikenan dama kun bari saida safe kawai, tunda dare yayi har tara fa, yaushe kukazo ka koma, nifa banason yawon darennan".
" to shikenan ALLAH ya kaimu goben a gaida gwaggo".
"Zataji". ta fad'a tana yanke wayar.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yamik'e yanufi 6angaren Amatallah.
Tunkan yashigama yafara jiyo dariyarsu, yashiga falon da sallama, film ya iske suna kallo, da sauri Aysha tace, " sorry Uncle, nataso kagama?".
"A'a Innani tace ki kwana anan, amma ki kirata dantata kiranki wayar tak'i shiga".
" to Uncle".

Bedroom d'in Ama...... yashige, hakan yasata mik'ewa dole tabi bayansa, ta iskeshi a bakin gado zaune.
d'an nesa dashi ta zauna. ya kalleta fuska babu walwala, "saboda 'Yar uwarku tamin laifi kuka had'e kai kuna fushi dani?".
Ama.... ta d'an zaro ido waje, " Uncle fushi kuma?".
"Eh mana, bagashi kunbarni nida yaranaba kowacce ta dawo d'akinta".
" nidai Uncle wlhy bahaka baneba, kawaidai ganin karna bar Aysha ne ita kad'ai, amma kayi hak'uri".
Baice komaiba yamik'e ya fice, yaran yacema suje su kwanta gobe akwai school.
Duk suka amsa da to, samansa ya haye shima.
Shigowar Siddiqa da saifudden yasaka Aneesa tambayarsu ina Abbunsu?, Saifudden yace "momy yafi d'akinsa".
" umma fa?".
"Itama tana d'akinta".
Sakasu tayi suka kwanta, taima Abubakar shirin barci sannan ta d'an kuma fesa turare tafito, 6angaren Fateema taje, itama isketa tayi tanama yara shirin barci.
" Umman yara alfarma nazo nema, dan ALLAH bara naje nabama Abbunsu hak'uri, nasan lattinmu yajawomin laifi".
"Hakan yayi, dama yanzu zanje nace kozakije kibasa hak'uri, naga muduka ukun haushinmu yakeji, yatasa yaransa gaba ya share kowaccenmu".
" kuyi hak'uri, nasan nina jamuku".
"Wlhy kibarma zargin kanki, kinsan halinsa dai akan yara, kijedai naji sunce yatafi 6angarensa".
" okey ina zuwa".

A bedroom ta samesa yana shirin barci, sallamarta kawai ya amsa yacigaba da abinda yakeyi.
A bakin gadon ta zauna harya kammala sannan tace, "dear!".
" uyim". yace batareda ya kalletaba.
Tace, "dan ALLAH kayi hak'uri, nasan namaka laifi tunda nasa6a lokacin dakace mu dawo, wlhy Hanifa ce ta d'auki su Ummita suka fita, gashi tabar wayarta kuma babu Wanda yasan gidan".
Kallonta yayi cikeda takaici, " amma shine kika gagara kirana ki sanarmin? inda nasan Baku tahoba aizan biya na d'akkoku kamar yanda na kaiku, saboda tsabar kin rainani shine bakiyi hakanba ko?".
Shiru tayi tana kallonsa, tama rasa ta ina zata farane, danta kula yakai mak'ura a 6acin rai.
Matsawa tayi kusadashi sosai, ta marairaice murya tamkar mai kuka, "dan ALLAH kayi hak'uri dear, wlhy ba raini bane, naga kayi azumi ne karmu shiga hak'inka, ka yafemin hakan bazai sake faruwa ba wlhy, kuma nikad'ai namaka laifin banda 'yan Uwana".
" bandasu amma kuka had'emin kai?".
"Bahaka bane wlhy dear, maybe su Baka fahimcesu bane, kayi hak'uri to".
Tausayi tabashi yanda yaga dukta damu, harda guntun hawayenta.
" shikenan na hak'ura ki kiyaye gaba, karki kuma min irin haka, inhar hakan takuma faruwa ki kirani ki sanarmin, miye amfanin wayar, dan baki ta6amin hakanba kuma yasa na hak'uran".
Cikin farinciki ta rungumeshi tana godiya, saikuma tasakeshi da Sauri tace sorry".
Murmushi kawai yayi ya d'aga mata kai, takuma masa godiya tafita.
Ganin yanda tafito ya tabbatarma Fateema komai ya daidaita, dan haka tashiga itama, (dama tasan mijinsu yanada saurin sauka afushi inhar zaka nuna masa nadamarka) saikuma tad'anji haushi, kar Aneesa tagama rurrungume mata miji tana nan. (Abin dariya masu karatu🤣).
Itama dai saida yamasa k'orafin sun had'e masa kai, hak'uri tabashi tacigaba da tattalin mijinta, shima kuma yabada kai bori ya hau.

Amatallah kam tun fitarsa tabishi da kallo, a fili tace, "ALLAH ya huci zuciyarka Uncle". daga nan tafito suka cigaba da hirarsu da Aysha, dukda lamarin Uncle d'in na caccakar mata rai haka ta danne.


*********

Washe gari

Da safe sai Amatallah taga da d'an sauk'i kamar ya sauka, hakanne yasa tasaki jikinta kad'an, amma jiya da damuwar fushin Uncle ta kwana, tsaf yalura da yanda takeyi agabansa, shareta yayi danta bashi dariya.
Koda suka gama break fast bata yarda sun jirashi akan sufita tareba, da wuri tace sutafi itada Aysha.
Lokacin daya fitoma sun dad'e da tafiya.
ALLAH yasotama ranar Aneesa ce zata kar6i girkin.

Haka rayuwar gidan take tafiya musu cikin kwanciyar hankali da annashuwa, idan kuma wani damuwar ya gifta a fuskanceta a yanda tazo.
Wata safiyar laraba kuma Nazeefa tatashi da nak'uda, Uncle mijinta yafara kira, dan haka yatafi a rikice daga kasuwa.
Nazeefa tasha wahalar haihuwarnan kafin ALLAH ya sauketa kuma, dan harma sun fara shirin mata cs. tasami d'anta namiji k'ato mai kamada babansa.
A ranar daga makaranta Amatallah suka wuce itada Aysha, a can suka iskesu Fateema itada Aneesa. sunta santin baby kuwa, Amatallah harda kuka tayi a 6oye da addu'ar itama ALLAH yabata.
Uncle yazo kusan 5pm ya d'aukesu, dankar yara su dawo islamiyya basa nan, kallo d'aya yayama Ama.... yaji ajikinsa tayi kuka, dan ita koyaya tayi kuka sai manyan idanunta sun nuna. bai tambayetaba suka tafi, dama ranar girkintane, dan haka ta zauna a gaba, Aneesa da Fateema suna baya, mah-mah da Abubakar ma suna gaba wajen Amatallah.
Tausayinta yakuma kama Uncle d'in, ganin yanda taketa luguyguyta Abubakar da Mah-mah, koma saka baki a hirarsu batayi saboda yaran gaba d'aya sun d'auke hankalinta.
Suna zuwa gida mai napep d'in dake kai yara school yana isowa, ya d'akkosu daga islamiyya.
Tare suka shiga cikin gidan.

Da daddare bayan sun gama cin abinci da 'Yar hira yace yaran suje suyi shirin barci su kwanta.
Kafin yashige yaje yayma Aneesa saida safe yayma su saifufden addu'a kamar yanda yasaba yafito, itama Fateema yashiga yayma yaran addu'a.
Amatallah tagama tsaftace jikinta da baje ko wanne lungu da sak'o na jikinta da k'amshi, duk a sanyaye takeyin komai, dan rashin haihuwarnan tata na damunta, musamman yau dataga babyn Nazeefa ma. A sanyaye tashigo bedroom d'in nashi, haryama kwanta danya gaji da jiranta.
Hannu yamik'a mata alamar tazo gareshi ganin ta tsaya a bakin k'ofar.
Idonta harya cika da kwalla ta taka a hankali zuwa gaban gadon, shiya kamo hannunta yajawota tafad'o jikinsa.
Rungumeta yayi sosai, a cikin kunanenta yace, "my heartbest waya ta6amin kene?".
Ai tamkar yazugata saita rushe masa da kuka kawai.
Dama yasan za'a rina dan tund'azu batada walwala koda ana hirama.
Bai hanataba ya barta tayi kukan sosai yana shafa bayanta a hankali, alamar lallashi, saida tayi sosai sannan yad'ago kanta ya manne bakinsa kan nata kawai, yafara mata lalashin dazatafi gamsuwa dashi.
Saida hankalinsu yadawo jikinsu sannan yashiga mata kalamai masu sanyi da ratsa 6argo.
" haba my best fad'amin matsalarki please, nine Uncle nine baba nine Ammi nine miji kuma kinji?".
Kanta ta d'aga masa, murya a raunane tace, "uncle maganar haihuwarnan bata damunkane?".
Shiru yay danya rasa mima zaice mata, zuwa can yace ''ki kwantar da hankalinki khadeeja, insha ALLAH baki tare da kowacce matsala, Amma ranar Monday ki shirya saimuga doctor mana".
" Uncle inajin tsoro wlhy, inajin tsoron kar ace bazan ta6a haihuwaba........."
Da sauri yarufe bakinta, ''insha ALLAH zaki haihu, sainaga jinin brother d'ina da nawa cakud'e a waje d'aya da izinin ALLAH my best, ki d'auka komai akwai lokacinsa, watarana sai labari, kikama sani ko nayi ajiya wannan watan". yay maganar cikin tsokana yana shafa shafaffen cikinta.
Kanta takuma cusawa a k'irjinsa tana 'Yar dariya.
Yayi dariyar shima yana sumbatar Sumarta da fad'in kokefa, amma da anatamin rowar fara'arnan dake yalwata farincikina da annashuwata nima.
Kuma k'ank'amesa tayi tana fad'in kai Uncle".
"ALLAH kuwa my Dee....."


***** ******* *****

Ranar Asabar d'in week d'in Abulkhairi yashiga layin yara masu zana jarabawar fita daga primary, shima zai wuce secondary insha ALLAH A wannan year d'in, yaron yagirma, kamanninsa da Uncle suna kuma fitowa sosai, hakama Sahib shima yaron yayi girma, dan dakad'anma Abulkhairi zai fishi tsawo, yamafi Abulkhairi wayo.

A ranar Monday d'in kuwa Amatallah ta zabgama Uncle wayo dankar suje asibiti, dan itafa tsoro takeji taje ace akwai matsala.
Dukda yaganota haka ya k'yaleta, dama shimad'in bayason aje asibitin.


Agurguje please😫



Rayuwar tacigaba da tafiya ahaka, yau fari gobe tsumma, yau dad'i gobe hak'uri, ansha sunan yaron Nazeefa, (Sulaiman). su Amatullah kam anata karatu, dukda tanada damuwa azuciyarta bata bar hakan yazama silar raunanar karatunta ba, kullum Fa'iza da Aysha cikin kwantar mata da hankali suke da nuna mata muhimmancin hak'uri da yarda da k'addara.
Hakama 6angaren danginta su kawu hafizu, koda yaushe sukayi waya yakan k'ara kwantar mata da hankali.
Shikansa Uncle d'in duk abinda zai kwantar da hankalinta da kauda mata damuwar rashin haihuwar yanayi. ganin yanda duk suka damu sai itakuma tafara rage nuna tata damuwar, tama d'auke tunaninta daga wajen gaba d'aya, ta duk'ufa gayama ALLAH kukanta dayawan azumi, sadaka dadai sauransu.


To Ama..... ALLAH dai yasa mudace😢🙏🏻.



****** ****** ******

"Wai lafiyarki kuwa Ama......?"
"K'alau Fa'iza, mikika ganine?".
" kawai tun jiya nifa wani sukuku nake ganinki, tamkar wata mara lafiya".
Kanta ta kwantar jikin kafad'ar Aysha tana jan k'aramin tsaki, "kibari kawai, nifa jikin nawane ma duk babu wani dad'i, kuma babu inda yakemin ciwo wlhy".
Da sauri Fa'iza tace, " tin yaushe kika faraji?".
"Yanaga kin wani tsorata? bafa wani abu bane".
Cikin dariya Aysha tace, " aimu fatanmu yazama wani abun, nifa wani k'yauma naga kinayi kwanan nan hajiyata, miye sirrin?".
Duka Ama... takai mata, Aysha ta goce da sauri tana dariya.
"To miye na dukanta? ba gaskiya tafad'aba? baby ALLAH yasa abinda muke fatane dai, amma koni wlhy naga kin k'ara k'yau, maganace dai kawai banyiba".
" uhm kuma daina wahal da kanku, ni banida komai, kawai inaga malaria keson kamani dai".
Dariya suka mata, akadai bar maganar ahaka, kowa kuma ak'asan ransa yana addu'ar ALLAH yasa abinda suke fatane😊.


Kwana biyu dayin wannan maganar Ama.... ta tashi da zazza6i mai zafi, gashi ranarma Uncle ba d'akinta yakeba, yana wajen Aneesa.
Har zasu fara break fast babu Ama...., dayake weekend ne.
Uncle ya kallesu yana fad'in wai Khadija fa?".
Aneesa tace, "Wlhy nibanga tafitoba tun d'azun, Siddiqa ma tashiga tafito tace barci takeyi, tona d'auka ko gajiyace tahanata tashi da wuri".
Fateema ma tace, " ni wlhy kwana biyunnan ma sainaga kamar Auntyn yara batajin dad'i sosai".
"Nima nad'an zargi hakan, harma Na tambayeta amma tacemin babu abinda ke damunta, bara dai Na dubata kawai".
Sukace to.............





Manage please😎








One luv😻😻😻
[1/25, 12:25 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 39/40_*
____________________


Tundaga falo jikinsa yafara sanyi, dan babu alamar tayi gyara, da sallama yashiga bedroom d'in, babu amsa, ya kalli gadonta, tana k'udundune a bargo tarufe har kanta, da sauri ya k'arasa ya yaye bargon.
"Khadija lafiya kuwa? da uban zafinnan kika lullu6........"
Maganarsa ta tsaya a mak'oshi saboda yanayin daya ganta, ga jikinta zafi zauu, har wani huci ke fitowa.
"Ya salam my best!" yafad'a yana zama gefen gadon, hannu yakuma kaiwa a wuyanta ya ta6a, tarik'e hannun da sauri tana rawar sanyi, "Uncle please bar ta6ani, hannunka sanyi".
"dama bakida lafiya amma baki fad'aba Khadija? kuma har tadaki nazo nayi da asuba".
" Uncle sannan zazz6in ya saukane, banyi zaton zai dawoba da safe".
"Dashi kika kwanama kenan?".
Kanta tad'aga masa tana wani lumshe idanu dakuma dunk'ulewa waje d'aya saboda bargon daya cire mata.
Tashi yay yashiga bayinta, yahad'a ruwa maid'an zafi sannan yadawo, ya taimaka mata tasakko tanata rawar sanyi da fad'in "Uncle please kabarni Na kwanta, ina ganin jirine".
" Sorry my best! Bara namiki wanka kiji d'an k'arfi saimuje Asibiti".
Tirjewa tayi tana tura baki gaba, "nidai Uncle basai munje asibitiba, danasha parasitemol zan warke".
" to naji shagwa6a66iya, muje dai ayi wankan first ".
Da kansa yamata wankan, ya taimaka mata suka fito, a bakin gado ta zauna, ya d'akko Vaseline ya shafa mata, tanata langa6e masa itafa jiri take gani, hakadai ya lalla6ata yasaka mata doguwar riga bak'a.
Fita yayi itakuma takoma ta kwanta harda jan bargo takuma lullu6a, taji dad'in wankan, dan ciwon jikin saitaji yaragu harma da zafin.

Yana fitowa suka hau tambayar miya faru da Ama.... d'in?.
"Batada lafiya Ashe, zazzabi takeyi, Aneesa had'a mata break fast d'inta".
Sun nuna jimamainsu akai, Aneesa ta had'a break fast d'in ta d'auka da kanta domin kai mata, Fateema da Uncle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login