Showing 78001 words to 81000 words out of 104242 words

Chapter 27 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16048

d'iba suka ajiye, zuwa sannan gidan kam ya d'inke da jama'a.
Su Amatallah duk aka canja kaya, komai tanayinshine kawai, amma jikinta duk babu dad'i, saidai Alhmdllh tana k'ok'arin daidaita tafiyarta, kasancewar dama ita mutumce mai sanyi, komai NATA a nutsuwa takeyinsa, su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa takasa ta tsare. Sai 6angaren Amatallah yazama Na yaran mata, su Nazeefa da k'annen Fateema, dadai yara-yaran matan danginsu, suna falon Ama sunata shan shargallensu ana barkwanci da tsokanar juna.
Saigasu Fa'iza Goodness Rita dawasu k'awayensu Na makaranta da'ake gaisawa.
Nanfa fili yakuma kacamewa da hira, kokad'an babu Wanda yanuna k'yama gasu goodness kasancewarsu ba addininsu d'ayaba, suma tun suna d'ari-d'ari har suka saki jiki anata hira da dariya.
"Amatallah ta kalli Fa'iza cikin tsokana tace, " sannu uwar uku, ALLAH nazatafa bazaki iya zuwaba?".
Hararta Fa'iza tayi cikin wasa tace, "a'a uwar 12 ba ukuba, kenifa garau nakejina ko reren gudu saimuyi ehe".
" tab dawa zakiyi reren? Aiko zan barki a taku biyu harnaje Na dawo baki motsaba".
"Hawaba yarinya, badan karnama Uncle d'inmu asarar sabon babyba danace muyi".
" sabon baby a ina?".
"A cikinki". cewar Safina wata cousin d'in su Uncle.
Aiko nan tsokana tadawo kan Amatallah, ta dage tana kare kanta, nandai Ramla da Bilkisu suka shiga kare mata suma.
Sun kacame da surutu wayar Amatallah nata ringing bata saniba.
Anty maijidda tashigo tana magana da k'arfi yanda zasuji.
" oh ni Hauwa'u, anya kuwa wani najin maganar wani a cikinku? Kunjikuwa yanda kuka cika mana kunnuwa? Amatallah mijinki nata kiranki a wayama baki saniba kenan?".
Da sauri Amatallah ta kalli wayar, gata a gefenta amma batajiba, dayake wayar a silent take, kuma ta kifeta, mik'ewa tayi tana fad'in "ALLAH banjiba Anty".
" yazakiji kuna wannan zuba tamkar rediyoyi, kizo to".
Tsallakowa tayi tafito, Fa'iza da goodness da Rita suka kalli juna suna murmushin jin dad'i, dansunga sauyi ga aminiyar tasu, atunaninsu bazata mik'eba kai tsaye hakaba saita nuna jin kunya, (amma sai sukaga babu kowani alamar hakan tare da ita) basusan dauriya Amatallah tayiba kar ai mata dariya😂, (Dan tak'aru da hirar yaran matan da tund'azun akan gidan aure dama aketa surutun).
A waje ta iskeshi shida Aneesa tsaye suna magana, kishi da haushi suka kamata, (ya ita da miji wata dafara zuwa wajensa😏) (Ama... An fara kishi kenan....lol 🤣).
Danne zuciyarta tayi ta k'arasa, sannu dazuwa tamasa, ya amsa idonsa akan kwalliyarta data tafi dashi, maganar dasukeyi da Aneesa ya maimaita mata.
"Abokainane gasunan kusan su goma, kokad'an banyi zaton zuwan nasuba, saida nafitane Alhaji Sabi'u ke sanarmin sunce zasuzo ganin baby, naji dad'in k'ok'arinku, ALLAH yaymuku albarka kunji my wife's".
Atare sukace Ameen, kowa kishi nacinta a zuciyarta, amma a fuska bazaka ganeba, (Aneesa ma anfara k'ok'arin dannewa🤭😜).
" yauwa to yanzu saikuma Fateema magana, idan mun kammala cin abincin saikuzo Ku gaisa kenan, akawo Aminatun. Sai daifa bahaka zakuzoba k'attin banza su ganeminku, asawo hijjabai".
Daga Aneesa har Amatallah dariya sukai masa.
"To ai gaskiyane, danma karsuce, ALLAH da har nik'af zance kusa, kunsan inada kishi, khadeeja Ce kawai bata gama saninaba, amma ahankali zaki fahimci hakan kema"., yay maganar da kanne mata ido d'aya.
Murmushi tayi ta kauda idonta akansa.
Sarai Aneesa ta gansu, kuma taji zafi sosai, harma saida fuskarta tad'an nuna, amma tayi k'ok'arin waskewa dafad'in ''ALLAH nagaji over".
" sorry my neesa". Uncle yafad'a cikin tausayawa, ya kalli Amatallah ma yace sorry my best, nabaku wahala ko?".
"Lah babufa komai Uncle, ai alsunan babynmuce, damunyi barci gajiyar zata ware ko Anty?".
Murmushin yake Aneesa tayi, ta kad'an kanta kawai, amma mamakin Amatallah takeyi, dama tana magana haka? Dan tuni ta lura Amatallah miskilace.
Ciki suka koma, uncle kuma yakoma wajen bak'insa.

Kamar bayan 1hour yakirasu duk awaya akan suzo sun gama, kowacce cikin hijjabi tafito, Amatallah ta kar6i jaririyar daga hannun Fateema suka jera abin sha'awa suka nufi falon.
Sallama sukayi ak'ofa, saida aka amsa musu sannan suka shiga.
A mutunce suka gaisa, Uncle ya amshi Ameenatu a hannun Amatallah yabasu, fita sukayi suka bar musu ita tunda barcima takeyi.
Duk saida suka gama ganinta suka saka mata albarka da addu'oi sannan aka maidota da alkairi mai yawa daga garesu.

Alhmdllh taro yatashi lafiya, (Fan's barkanku da gajiyafa, lallai kunyima Uncle kara, irin wannan tururuwa haka, harfa gaza lissafoku nayi saboda yawa, to ALLAH yabar zuminci sai, kowa tasha kanwa saboda ciye-ciye damukayi, kar atashi da 2go da safe🤭😆, dansu o e naga har guzurin extra akayi a viva leda😜. Ba ruwana ban dad'i sunaba dai.🤫🤐🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀🏃‍♀.


To gida yayi lafiya, daga masu gidan sai Nazeefa da zaliha, sai anty maijidda da Anty badiyya yayar fateema itama Dan ba'a nan Kano take aureba, a jigawa, (yau tazo da safe, sikuma zuwa jibi ta koma. saikuma Anty Sadiya da Anty Furera da Asiya 'yan jos, saikuma inna Nafe.
Kowa yayi laushi, da k'yar suka tak'ark'ara sukad'an share falo akayi morphing, wanke-wanke kan ko kallon arzik'i bai samuba, a babban kitchen suka killace kwanukan kawai,
Yarama dakansu sukai wanka, suka kwanta, Dan suma sunyi laushin.
Da k'yar Amatallah ta tak'ark'ara tadafama Uncle cus-cus, Dan bazata ita bashi sauran jagwalgwalon mutaneba.
Dama su Anty Sadiya suna 6angaren Aneesa, tace annan zasu kwana, Anty maijiddah kuma da Anty badiyya zasu kwana 6angaren Fateema sai inna Nafi.
Nazeefa Asiya zaliha suna 6angaren Amatallah.
Abincin ta kinkima takai falonsa, da k'yar take taka step d'in saboda jikinta yak'ara tsami, harwani zazza6i takeji, ga bakinta d'aci yake mata, Uncle baikai ga shigowaba, Dan ba'a dad'e dayinma isha'iba, sukansu gajiyace tasaka kowa Neman makwanci bayan yayi salla. Duk abinda yake buk'ata ta ajiye masa danufin shikenan bazata dawoba, a 6angarenta zata kwana wajensu Nazeefa.
Takuma tako step d'in dak'yar tadawo, wanka tashiga tayi da ruwa mai zafi sosai, tagasa jikinta da k'yau kozataji sassauci.
Su Nazeefa duk suna baje a gado, Asiya Na waya da saurayinta, Zaliha da Nazeefa kuma charting sukeyi.
Bawani dogon shiri tayiba, komai bata shafaba tasaka wando da Riga masu kauri, tad'an saka tirare. gadon tanufo tana fad'in "hajiyoyi a matsamin".
Da mamaki Nazeefa da Zaliha suka kalleta, zaliha tace, " Anty Ama....ina kenan (dukda zasuyi sa'anni da zaliha Anty take cema Amatallah).
"Nan mana..."
Amatallah ta nuna gadon.
Cikin zaro ido zaliha takuma fad'in ''yayanfa?".
Hararta Amatallah tayi, "ni malama Ku matsa Na kwanta, ALLAH barci nakeji".
" hhhh aikuwa badai a gadonnanba".
Cewar Nazeefa tana k'ara bajewa sosai yanda Amatallah bazata samu wajeba.
Asiya data katse wayar saboda mahawarar tasu itama tace, "lallaima Amatallah, ke in ance ki kwanta anan saiki kwanta? Shikuma bawan ALLAH fa......"
Har Amatallah zatayi magana wayarta dake saman madubi tashiga 'Yar tsuwwa alamar kira. Juyawa tayi ta d'auka, ganin Uncle ne ta tunzuro baki gaba.
Hakanne yasakasu Nazeefa kwashewa da dariya.
"sai'a tattara atafi kiran boss".
Cewar Asiya.
Hararta Amatallah tayi kafin tad'aga kiran tasaka a kunne.
" wai ba'asan nadawo bane? Kokuwa ba'a yayinane?". Uncle yay maganar cikin sassanyar muryarsa wadda taratsa 6argo da jinin Amatallah".
Bubbuga k'afa Amatallah tashigayi ak'asa, cikin shagwa6a tace, "kai Uncle da bak'ifa".
"ayaaa kina nufin saboda bak'i bazakizo ki tarairayeniba? Nifa bazan iya barci nikad'aiba my best, a tausayama bawan ALLAH mana".
Yanda yay maganar a mariraice saiya bata dariya, ta to she baki tanayi k'asa-k'asa.
"Oh dariyama kikemin ko?".
Da sauri tace, " ALLAH uncle a'a, ammafa su anty furare fa........
"Karkimin k'arya, nasan suna 6angaren Aneesa, aina lek'o d'akin naji nagasu Nazeefa ne kwance akan gado, Dan haka nabaki 10minute's, kokizo da arzik'i konazo dakaina wlhy agabansu Na cicci6eki babu ruwana".... d'iff ya kashe wayar.
Tamkar Amatallah ta FASA ihu haka taji.
Tana zin6ure-zin6ure tasaka hijjabi yatafi, su Nazeefa suna mata dariyar wai dole a amsa kiran boss ko jiki yay tsami.
Fita tayi tana balla musu Harara, tabugo musu k'ofar da k'arfi.
Aiko suka kwashe da dariya, har tafara taka step tana jiyosu sunayi.

Nimafa bara nayi kad'an Ama.....🤣, fans kuma kuyi 'Yar kad'an😂 Dan kar musa Ama..... Ta fashe, naga tacika fam🤭😂😜)................✍🏻





🤩👎🏻








*_ALLAH kajik'an iyayenmu_*😭🙏🏻
[1/19, 8:33 AM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 33_*
____________________

Da sallama ciki-ciki tashigo falon nasa, baya nanma, tasan yana bedroom maybe.
Zamanta tayi afalon tana tura baki gaba, kusan 2minutes bai fitoba tayi kwanciyarta a doguwar kujerar, agajiye take over, dan haka barci yad'an fara figarta.
K'amshin turarensa daya cika mata hanci yasata bud'e idanun kad'an ta sauke akan fuskarsa, bud'e idon tayi sosai tana kallonsa.
Ya sakar mata murmushi yana zama gefen kujerar datake kwance, "anya kuwa amaryarnan tawa ba raguwa baceba?". yay maganar yana shafa fuskarta da hannunsa na dama, na haggun kuma yad'orashi akan hannayenta dake saman cikinta.
Tad'an lumshe idanun takuma bud'esu a kansa tana turo baki.
" shagwa6a namiki k'yau my best. yanzu dai ya kikejin jikinki?".
"Kwalkwal tayi da ido tana niyyar masa kuka, " ALLAH Uncle duk babu dad'i, bakinama d'aci yakemin".
"Ayya sorry my best duk na girmane, inji yaya d'acin bakin yake". Yay maganar yana manne bakimsa kan nata. (Humm, Uncle wayo kenan🤪).
Kusan mintuna 3 yana k..... nata, tuntana d'an dojewa hardai ta barsa yayi yanda yakeso, yad'ago yana kallonta da murmushi, " nimafa naji d'acin bakinnan my best, kodai muje muga doctor Shu'aibu? Amma bara nakumaji kad'an". Yamatso zaikuma had'e bakin nasu.
da sauri ta yunk'ura ta tashi "Uncle wannanfa wayone wlhy".
Ya tuntsure da dariya yana sakkowa k'asa kan carpet, itama murmushi takeyi tana zuba masa abinci.
" my best! My best!! Wato kin gane wayo nake miki kenan?".
"ALLAH kuwa Uncle ai na ganoka". ta tura masa abincin gabansa.
" shikenan my best tunda kin ganoni, matso muci abincin".
"No Uncle Na k'oshi, barci nakeji wlhy, nagaji".
Yanda tayi maganar saita sakashi narkewa, ya jinjina mata kai kawai danya kasa magana.
Tace, " Uncle naje Na kwanta?".
Kai ya d'aga mata yanamai lumshe idanunsa da shafa gemunsa.
Mik'ewa tayi tana neman k'ofar fita, da sauri yace, "my Best wai ina kike nufin zuwa?".
" k'asa mana Uncle".
Shiru yay kawai yana kallonta da hango zallar rashin wayonta, kusadashi ya nuna mata yace, "dawo ki zauna nabaki magani kisha kafin ki tafin".
Batayi musuba tadawo ta zauna, azatonta maganin zai bata da gaske. shiru babu mai magana acikinsu, har yagama cin abincin, kwanikan yamatsar gefe yana fad'in Alhmdllh, ya kalli Amatallah dake gyangyad'i.
Ya murmusa tareda jin tausayinta a zuciyarsa, yasan harga ALLAH tagaji d'in. TV ya kashe daduk kayan wutar, ya haska fitilar wayarsa ya sauka k'asa, Generator yaje ya kashe, ya maida NEPA dukda babu wutar, amma in case koda an kawo suna barci basai yatashiba.
Amatallah da barci ya d'auka batama san ya fitaba, ya tadata tareda kama hannunta suka tafi bedroom d'insa, batace masa komaiba saboda barcin dake idonta, ya zaunar da ita abakin gado yabata magani tasha tana yamutse fuska, kafinma ya ajiye ruwan hannunsa hartayi kwanciyarta, gyara mata kwanciyar yayi yafara mata tausa ahankali, wani barci mai dad'i ya d'auke Amatallah saboda dad'in tausar datakeji. Saida ya tabbatar yamata yanda zataji dad'in barci sannan yabarta, yaymusu addu'ar barci ya rungume kayarsa.



Nima akorikurar k'afafuna najawo zuwa wajen nawa boss d'in🤫.


_washe gari_ koda Uncle yafita masallaci itama Ama... Saita sakko k'asa abinta, taredasu Nazeefa tayi salla, babu Wanda yace mata k'ala, bata koma barciba tanufi kichin Dan neman abincin Karin kumallo.
Bata dad'eba Anty maijidda tashigo ta taimaka mata. Lokacin dasu Uncle suka dawo masallaci shida yara yaji motsi a kitchen amma baiyi zaton Amatallah bace, Dan haka yawuce samansa, wayam yagani alamun ta gudu, yay guntun murmushi kawai.
Su Nazeefa suka fito suma suka fidda wanke-wanke, Anty badiyya da Aneesa kuma suka fara k'ok'arin tsaftace gidan, ganin haka su Anty furera kuma suka hau yimasu Sahib wanka. kasan Cewar aikin kowa Yakama saiya yimusu sauri, Dan danan suka kammala, gidan ya dai-daita.
Bayan sun kusa kammala girkin, Dan kad'an ya rage Anty maijidda ta kalli Amatallah tana fad'in "yauwa maza kije kiyi wanka, kafin kidawo na had'ama mijinki saiki kaimasa daganan ki gyara masa 6angarensa, karnaga k'afarki a k'asa sai idan ya sakko zai fita".
Amatallah tace " to Anty".
Harga ALLAH tana kallon Anty maijidda ne tamkar Ammi agabanta, Dan ko'a shekaruma zasuzo d'aya da Ammi, ita kanta Anty maijiddan Dan d'anta nafari namijine kuma yarasu, Na biyunma namijine, amma da macece k'ilama tana shirin aurarwa kam.
Duk yanda ta umarceta hakan tayi, dama yau tanason zuwa makaranta, tayi kwalliyarta cikin gown d'in atanfa, d'inkin Yamata k'yau, simple kwalliyarta tayi tamkar yanda ta saba, tad'an fesa turare sannan tafito.
A falo ta iske su Anty maijidda tana zubama yara abinci, su Nazeefa ma suna zaune suna karyawa, gajiya tahanasu cin abincin dare, shiyyasa suka tashi da yunwa.
Kitchen tashiga ta d'akko tiren abincin da Anty maijidda ta had'a mata, yaukam saitaji batajin kunyar kowa yaganta Dan zataje wajen mijnta. A hankali take taka step d'in tamkar bataso, tayi sallama a k'ofar falon kafin tashiga dukda ba'a amsa mataba, falonma babu kowa, ta ajiye tiren, falon tahau gyarawa batareda tashiga bedroom d'inba.
Duk Uncle najiyo motsinta daga ciki, yana wankane.

Tana shiga bedroom d'in yana fitowa, juyawa tayi da niyyar fita tabashi waje ya shirya yace, ''hii".
Cak ta tsaya amma bata juyoba, k'arasowa yay gabanta yana kallon yanda rigar ta zauna ajikinta d'as, "my best shirinafa? Wazai mini?".
Kad'an ta kallesa ta janye idonta dan ganin dagashi sai towel, murmushi tayi tana d'an Susar wuyanta alamar kame-kame, " Uncle ina kwana".
Amsawa yayi yana murmushi, ya kama hannunta suka k'arasa bakin gadon, dolenta ta ajiye kunya gefe ta taimaka masa kamar yanda ya buk'ata, yay gayunsa cikin lemon green d'in boyal, yauma itace tamasa karin hula ta saka masa akansa, ya rungumeta yana fad'in "Thanks my heartbeat".
Itama ahankali tace, "I... love... you my Uncle". Da d'ai-d'ai tafad'a tamkar mai koyan magana.
Da sauri yad'ago kanta yana kallon fuskarta, "my best really!?".
Tana murmushi ta d'aga masa kanta.
Kuma rungumeta yayi yana fad'in Thanks you so much my heartbeat, I love you more". yakuma d'ago fuskarta yana bata tagwayen sumbata, yaukam Amatallah taga ikon ALLAH itadai, tana kallon Uncle d'in nata nadabanne acikin maza.

Bayan sun kammala breakfast tace masa yau zataje makaranta.
Yace ta hak'ura tunda dai su Anty Sadiya basu tafiba sai yamma. Baikuma dace tafita ta barsuba ai, gobe saitaje idan ALLAH ya kaimu da rai.
Hakan dole ta hak'ura, aikam yini guda sukasha hirarsu, sai k'arfe biyu sukayi shirin tafiya, tabasu alkairin da Uncle yabata, itama tahad'a da nata, Fateema ma ta had'a musu kayan suna, Aneesama ba'a barta abayaba, tare suka fita dasu Anty maijidda, sukaje suka gaida su Ammi sannan Nazeefa tarakasu tasha suka hau mota.
Gida kam yazama dagasu sai su, su Anty badiyya ma da inna Nafi suna kammala suyar Nama suka tafi.
Amatallah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login