Showing 54001 words to 57000 words out of 104242 words
Dariya tayi, shima yafita yana dariyar dajin k'arin k'aunarta har k'asan ransa.
Tunkan ya fito Aneesa tajiyo dariyarsa, da sauri tashige 6angarenta zuciyarta na suya.
Koda tafito saiya Nufi 6angaren Amatallah............βπ»
π€©ππ»
One luv my sweet Fan'sπ₯°
*_Ya Rabbi ka kai rahama da gafara kabarin iyayenmu_*πππ»
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingβπ»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*π‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
Comments naku na k'yatar dani ainun.
*_Ummu Ameer, Nana yakaku, maman khalifa, Ummu Ramlat, Layla, Xeecul, mom yasna, m@imun@tu, Maman iman, Jamila fika_*
_π¨ALLAH ya albarkaceku da yawafa, aradu kozan cika page d'inan bani gama zanoku, ko 'yan group d'ina kad'ai sa cikashi.π₯° inayinku irin Trillion's d'innan wlhy, ALLAH yabar k'auna.π₯°π₯°β€ππ»ππ»._
ππ»ππ»Aneesa ma fa akwai farin blood
*_Maimuna ado, and xaujatu_*
basa barin a ta6a musu itaπππ»π₯°π₯°π₯°β€ina yinku kumaππ».
____________________
*_Number 22_*
____________________
Kamar yanda yasaba da asubahi yabisu duk ya tada kowacce dantayi salla, yatasa yaransa gaba suka tafi masallaci.
Koda suka dawo saiya haye samansa yay kwanciyarsa.
Aneesa ma da barcin ta koma abinta, komi tagani kuma saita tashi tafita kitchen had'a break fast. tafara babu dad'ewa Amatallah ta shigo kitchen d'in itama, kallon juna sukayi, Amatallah tace, "ina kwana Anty".
Cikeda yanga Aneesa ta amsa mata.
Amatallah bataji komai a rantaba, dan har zuwa yanzun bata gama Sanin ma'anar kishinba, tarayu gidansu Amminta ita kad'aice, shiyyasa bata ta6ajin zafi ko haushin wani Abu da Aneesar keyiba, tanama d'aukar hakan kawai a tunanin halin Aneesar ne.
Kauda tunaninta tayi gefe, tai murmushi da matsawa kusada Aneesa tana fad'in " Anty mizan tayaki dashine?".
Yanzunma a d'age Aneesa tad'an kalli Amatallah, saikuma tacigaba da abinda takeyi, "no kije abinki, sonake yau na had'ama my Dear special breakfast da kaina, kodan na nuna masa godiyata na dad'in daya jiyar dani jiya, ai ba ayi mai miji da banba mai girki daban kingani ".
Dukda Amatallah taji duk maganar Aneesa tsaf, sai dai bata iya fassara magana ko d'aya ba a ciki, amma ta fahimci maganace cikin magana tamata. d'an murmushi kawai tamata tace, " OK bara naje to nayi shirin school, dama inada lectures d'in safe". bata jira amsar Aneesa ba tafice abinta.
Aneesa taraka bayan Amatallah da harara tana ta6e baki.
Nidai nace, " hummmm".
*********
A 6angaren Fateema tunda maigidan ya tadasu da asuba taga Saifuddin a d'akinta saitaji wani haushi, wato ita Dan an raina mata hankali shine aka d'akko yaro aka kawo mata dansu su samu su warwasa yanda sukeso. To aii idanma gaskiyane yau d'akin Amatallah yakamata ya kwana ko, kenan Aneesa tayi wani makircin?, ai ko sai tayi mata abinda zata bak'anta ranta yau d'innan basai gobeba.
Tayi wata 'Yar dariyar mugunta.
Tofa Uwargida ran gida, mikike k'ullama Aneesar kuma?.π
**********
Tunda Amatallah tabar kitchen d'in takasa manta maganganun Aneesa, datayi k'ok'arin mantawa sai maganar tadawo mata a rai, sai takejin wani gefen zuciyarta yanajin kamar d'acin maganar, haka tagama shiryawa sukuku.
Tayi k'yau cikin zani da riga Na shadda oxblood color, zani Rafa sket, saiya fita tamkar sket d'in, hakama rigar Tamata d'as, batawani yi kwalliyaba, fauda kawai ta shafa da kwalli sai lipstick data saka, d'an kwalinma normal d'auri tayi, tana tsaka da kimtsa abinda zata buk'ata a handbag yay sallama.
Amsawa tayi a sanyaye, sannan ta rissina ta gaidashi.
Tsura mata idanu yayi ganin yanda takeyi komai a sanyaye, tamkar mai tunanin wani abu. "Khadeeja!".
Yakira sunanta yana zama kan stool d'in madubinta datayi shafa.
Kanta a k'asa tace, "Na'am Uncle".
" bakida lafiyane?".
Yanzunkam sai da ta kallesa, idonta yad'an Tara kwalla, saboda haka kawai maganar Aneesa har yanzu cin zuciyarta takeyi, tanason tasan ma'anar maganar, Dan yanayin da Aneesa Tamata maganar kawai ya tabbatar mata bamai dad'i baceba.........
"Khadeeja!". Yakuma kiranta dad'an k'arfi Dan ganin tatafi wani tunanin, hakan kuma ya tabbatar masa akwai abinda ke damunta d'in.
Da Sauri tace, " na'am Uncle, INA jinka".
"Kina jina ko kina tunani dai my best, kinga please fad'amin damuwarki, karki 6oyemin khadeeja, yanzu nine Brother, nine Ammi, nine Uncle, kuma nine Miji, duk abinda yadameki nizaki tunkara Na share hawayenki kona kare mutuncinki nakuma kwato miki hak'k'inki kinaji ko".
Kanta ta jinjina masa tana had'iye kukan dayazo mata.
"Yauwa my Best! to fad'amin kinji, ki d'auka yanzu Nid'in Ammice, nasan dai bazaki iya 6oyemata damuwar kiba ko?".
Muryarta Na rawa tace, " ALLAH babu komai Uncle".
"Khadeeja ban yardaba, Bahaka muka rabuba jiya da daddare". yayi maganar yana tasowa zuwa gareta.
Handout d'in hannunta da bag d'in ya amsa ya ajiye akan gadon, ya d'ora hannayensa duk biyu a kafad'arta, idonsa Na kallon fuskarta.
Ita kuma ta duk'ar da idonta tana kallon k'afarsa.
Cikin sassanyar muryarsa wadda takuma komawa slowly yace, " waye ya 6ata miki rai a gidanan? Fateema!".
Ta girgiza kanta.
Yace, "Aneesa!".
Shiru tayi.
Hakanne yasashi fahimtar Aneesa Ce.
Iskar bakinsa ya furzar sannan yakuma cewa ''Aneesa Ce ko? mita miki?".
Hawayen datake mak'alewa ne suka zubo a kumatunta, murya Na rawa tace "babu abinda fa tamin Uncle, kawai naje tayata girkine tace nabarsa zatayi, shine naji babu dad'i, gani nake ko wani Abu namatane, tunda kaga da bakanan kullum tare mukeyi da Anty Nazeefa , wani lokacin kuma da ita Anty Aneesar, shiyyasa yanzu datace Na barsa sainakejin babu dad'i kamar wani laifi namata".
Iska Yakuma furzowa a bakinsa, kafin yamatso da ita jikinsa ya rungumeta yana shafa bayanta alamar lallashi. Sunkai kusan Minti 3 a haka sannan ya d'agota, hannunsa yasa ya goge mata hawayen kafin yakai bakinsa ya sumbaci goshinta. " ki daina damun kanji Indai akan hakanne kinji my heartbeat, badan kin mata laifi bane, kawai inaga Dan taga zakije school ne, amma zan mata magana, daga yau karki kuma zubarmin da hawayennan masu tsada akan wata a gidannan, kema matar gidace kamar kowaccensu, zankuma tabbatar musu da hakan kinji ko?".
Kanta ta d'aga masa alamar to.
Yace, ''yauwa my babyna, yimin murmushi mana konaji sanyi". 'Yay maganar yanajan kumatunta'.
Hakanne yasata sakin murmushi mai k'ayatarwa.
Sumbatar goshinta da kumatunta yakumayi yana fad'in "yauwa kokefa my best".
Kunya dukta kama Amatallah itadai.
" kinada lectures d'in safene?".
"Eh Uncle".
" Okay, to k'arasa shirin ki sameni a falo mutafi, idan Na ajiye yara a School saina k'arasa dake".
Kanta ta d'aga masa alamar to. shikuma ya juya yafita.
Afalo ya iske yara angama shiryasu, zama yayi duk suka zauna kusada shi suna gaidashi, ya amsa yana sumbatarsu d'ai-d'ai a kumatu.
Babu dad'ewa Fateema tafito cikin kwalliya, (a raina nace Uwargida kina fama da kankinma bazaki hutabaπ€).
Tunda ta fito idon Alhaji Muhammad Na a kanta, sai murmushi suke sakarma juna, mik'ewa yayi ya taimaka mata ta zauna, yanason yad'an sumbaceta amma ga yara, Dan haka yamata magana rad'a-rad'a, "sorry my tee.. My children's na kallonmu".
Murmushi tamasa, Dan tasan miyake nufi, yanason sumbatarta ga yara, tasan bazai iyaba.
Gaidashi tayi da tsokanarsa ango kasha k'amshi, duk angwancinne yasa aka manta damune?".
Wata 'yar dariya yayi, yakuma k'asa da murya Dan kar yara su jisu, " my tee... Nazama abin tsokana kuma? ai na shiga kina wanka, su Abulkhairi basu sanar miki bane?".
Itama dariyar tayi, tace, "wasa nakeni Nurrina, ya gajiyar hanya".
"Alhmdllh my tee.., ammafa akwai, gashi yau dolene nad'anyi wasu yawo wlhy a cikin gari".
" amma dai daka hak'ura kad'an huta yinin yau a gida, zuwa gobe saikayi duk abinda kakeso".
"Ai fitar tanada muhimmanci my tee..., Alhaji Sabi'u a matse yake dason ganina, nima kuma dai hankalina na kansa, za6e yakuma gabatomu gab, dolene muyi wani motsi da gaggawa kinga".
Kallonsa take cikeda so da k'auna, jin mijinsu take harcan k'asan ranta saboda k'yawawan halayensa...
Ahaka Aneesa tafito daga 6angarenta cikin kwalliya ta samesu. ganin yanda suke kallon junansu sai kishi ya kamata, harara ta balla musu.
Sarai Fateema ta ganta, amma shi bai gantaba saboda yabata baya kad'an.
Dariya Fateema tayi a ranta, da fad'in bakiga komaiba 'yan mata, saima anjima ma kin shiga tarkon dazan d'ana miki.
Fitowar Amatallah yasaka Fateema janye idonta daga kansa, ta maida kan Amatallah tana murmushi, " Amatallah kin tashi?". tafad'a cikeda fara'a.
Itama Amatallah d'in murmushin tayi, kafin tabata amsa yaran duka sukayo kanta suna fad'in "Antynmu ina kwana!". Kowa na 'Yar rige-rigen fad'a da shigewa jikinta.
Duk had'asu tayi ta rungume, ta amsa musu da tambayar sun tashi lafiya?.
A tare sukace " lafiya lau antynmu".
Daga Uncle har Fateema kallonsu suke suna murmushi, zuciyoyinsu najin dad'in yanda Amatallah keson 'ya'yansu, (masu iya magana kance mai d'a wawa) wannan yasaka Fateema kanji sassaucin kishin Amatallah tunkan ta tafi Dubai,, dan duk wada yaga yanda Amatallah kema yaran yasan har zuciyartane.
Guntun tsaki Aneesa tayi tashige kitchen. tana jiyo yanda Amatallah ke gaida Fateema cikin girmamawa, itakuma Fateeman tana amsawa tamkar da biyu. jitai duk tak'ara tsanarsu suduka.
Uncle kam dad'ine sosai yakuma kamashi, Dan ganin yanda Fateema take bama Amatallah kulawa, sai yaji takuma girma da kima a idonsa.
Yarane kawai sukayi break fast d'in, Amatallah ma tea kawai tasha, danji tayi bazata iya cim ko lauma d'aya daga abinda Aneesa ta girkaba, saitaji ma'anar maganganunta sannan.
Uncle baice mata komaiba, danya fahimci haushin Aneesa takeji, kuma tabbas ta 6oye masa ainahin abinda Aneesar ta mata.
Aikam ganin shine zaikai Amatallah school ko rakkiya Aneesa bata masaba, baibi ta kantaba shima ya fice abinsa, amma yanason saiya san ainahin abinda taima Amatallah d'in.
Amota ma Amatallah tayi shiru, sai shine keta hira da yaransa dake bashi labarin abuwan da akayi bayanan.
Wani yayi magana wani kuma yayi murmushi kawai, ahaka har sukaje school d'in yaran.
Yaran duk suka fita, shikuma yajuyo yana kallon Amatallah, "my best d'an bani 5minutes naga headmaster d'insu, ai bazaki makaraba ko?".
Kanta ta d'aga masa. da fad'in " eh Uncle".
Fita yayi yana murmushin miskilancin Amatallah, yadad'e da sanin dama Amatallah miskilace ta bugawa a jarida.
Kusan mintuna bakwai saigashi ya dawo suka tafi. motar tayi shiru, shi yana tuk'i yana kallon jama'ar gari da nazarin wasu abubuwa gameda yanayin matasan daketa kaikawo, ko zaiga wani canji dasuka samu a 11month's d'in d'aya d'auka baya k'ar, sai dai baiga wani canjin ba koda k'aramine.
Amatallah kuma tayi shirune tana kallon mutane dakuma cigaba da juya maganganun Aneesa, (kusan dai Amatallah wajen rik'e Abu arai).
Har gaban department d'insu ya kaita, amma yace bazai fitaba, Dan bada shirin shigowa yazoba.
Har zata fita yarik'o hannunta.
Juyowa tai ta kallesa, yawani langa6e kai "my best! dama haka ake sallama da miji?".
K'asa tayi da kanta tana murmushi. ya murza hannunta. dag'owa tayi tad'an kallesa, shikuma ya d'aga mata gira.
da sauri ta juyar da fuska tana fad'in ''kai Uncle". a shagwa6e tayi maganar.
"Lallai yarinya, ashe zamu kwana a motarnan kenan? dan yau babu wani Uncle anan".
Juyowa tayi tace, " uncle kwanafa!?".
"Sa wasa kiga aiki kuwa yau".
" wayyo Uncle, ALLAH munkusa shiga lecture, kagama su Goodness can da alama nisuke jira".
''Laifin waye to?".
Amatallah tace nashiga tara, wai Uncle ya manta matsayinsa ne agareni. a zuciyarta tayi maganar.
Kamar yasan mitake fad'a kuwa yakuma ruk'o hannunta da k'yau, "my best kifa rage kunyarnan, lokaci yayi dazaki fara d'aukar Uncle d'inki a matsayin miji ba Uncle kawaiba, koda yake niyakamata na canja wannan matsayin nawa a gareki". yak'are maganar da sumbatar hannunta.
Idonta ta rimtse a zuciyarta tace ya salam.
Yana sakinta ta fice da sauri.
Dariya kawai yayi yana girgiza kai, ya tada motar ya tafi yanamai jin farincikin yanda Amatallah tafara sakin jiki dashi, yana ganin zuwa yanzu lokaci kad'an zai k'ara mata komai ya dai-daita, ayanda yake gani itama takamu da sonsa kamar yanda ya koyar da ita.
Tunda ta fito a motar wasu daga d'aliban suka saka mata idanu, hardasu Fa'iza.
K'arasowarta yasaka Rita fad'in "baby ke da waye yau? muntafi tarbanki mukaga ba ya Jabeer bane".
Da sauri Amatallah tace, " uncle d'inane".
Fa'iza dake zaune da tsohon cikinta tayi dariya, danta kuma gaskata Amatallah nada aure yanzun..... Kafin tayi magana Goodness tace, "Amatallah anya Uncle d'inan ba mijinki baneba?".
Harararta Amatallah tayi batareda tace komaiba.
Aiko suka saka mata dariya, Fa'iza ta yunk'ura ta tashi dagyar tana kallon Amatallah, " to 'yammata ai yanzu munsan komai, sai a daina raina mana wayo, aini wlhy tundaga yanda kike amsa masa waya nasan yawuce Uncle kawai, yaukuma munga zahiri, dan yanda yarik'e hannunki yana miki wani kallo kad'ai yabamu ams........"
Amatallah bata bari ta k'arasaba tarufe mata baki. Rita da goodness suka shek'e da dariya.
Sai kawai Amatallah ta fashe musu da kuka, dama ga abinda Aneesa ta mata yanata caccakar ranta. shiru sukayi, saikuma jikinsu yayi sanyi, nan suka shiga lallashinta, suna bata hak'uri.
Share hawayenta tayi tace, "kubar bani hak'uri, nifa bakune kuka sakani kukaba, kawai dai yanda auren namu ya kasance da Uncle na tuna.
Tabasu tausayi sosai. ganin time d'in lecture d'insu yayai tace Subari su fito zata basu labari.
A sanyaye suka jinjina mata kansu, sanan suka nufi lecture................βπ»
π€©ππ»
One luv my sweet Fan'sπ₯°
*_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu_*πππ»
[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typingβπ»_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*π‘
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* β
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ceπ€π»_*
_Na gaisheku Aminan arzik'i, *Miss Xoxo and Ayusher Muh'd* kud'in na da banne a zuciyar Bilyn Abdull_
_i love you so much masoyan kwaraiππ₯°ππ»_
____________________
*_Number 26_*
____________________
Dariya ce takusan kufcema Amatallah amma tayi k'ok'arin dannewa, dariyar tata tazone kam saboda ganin yanda Aneesa take sakkowa daga benen tamkar wadda aka biyo. tayi k'ok'arin kauda kanta gefe tana cigaba da jere kulolin abincin bisa tiren data d'akko.
Sai da Aneesa taimata wani kallo sannan ta shige 6angarenta tana murmushin muguntar data shiryama Amatallah itama.
Sarai Amatallah taga mugun kallon da Aneesa tamata, amma bai dametaba, tadai nemi tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciya, Dan tasan tabbas wannan kallon bazai zamto Na alkairi bane.
gyara mayafinta tayi sannan ta d'auki tiren abincin tayi sama, komai cikeda dauriya takeyinsa, amma k'asan ranta ita kad'ai tasan a fargabar datake. Sallama tayi a k'ofar falon batareda ta shigaba.
Uncle dake kishingid'e har yanzun inda suka barsa ya amsa yana kallon k'ofar, "shigo mana". Yafad'a yana maida kallonsa ga TV.
Sai da tad'a sauke ajiyar zuciya kafin ta tura labulen da tiren tashigo.
Batareda ya kalletaba yace, " lafiya naga kin dad'e?".
Kanta ta kad'a masa kawai tana ajiye tiren bisa santa table d'in dake tsakkiyar falon.
Hakanne yasakashi