Showing 96001 words to 99000 words out of 104242 words

Chapter 33 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16047

sukabi bayanta.
Da k'yar tatashi tasha kunun bayan su Fateema sunmata yaya jiki, ta amsa dak'yar tana tambayar ya yara suka kwana.
Uncle yayi yayi tatashi suje koda camix ne tunda yau babu aiki amma tak'i, itadai yabata perasetimol tasha kawai.
" nifa bazan baki maganiba kai tsaye, nasani ko ALLAH ya share kukanmu ne, kokuwa salon nama kaina ganganci".
Baki ta turo masa tana matso hawaye, "amma Uncle kofa masu tsohon ciki sunasha, kuma babu abinda yake musu, tunda a asibiti muna badawa aii".
Shiru kawai yayi yana kallonta, yama rasa mizai cemata, daga k'arshe dai saishi ya hak'uran, yabata tasha takoma ta kwanta.

Zazza6i dai yak'i sauka, saidai jikin ya huce yakuma dawo, ba Uncle ba hatta su Aneesa duksun damu, dan tasaba ranar weekend sunta shagalinsu da yaran agida kafin su tafi islamiyya, su Kansu yaran duk sunyi sukuki.
Da daddare dai abinda batason dole akayi, Uncle yakira doctor Shu'aibu yadubata, gudun karya bata Magani suyi 6arna yace tayi gwajin tsinke.
gwajin farko ya nuna mumsami baby💃🏻😀.
Murna wajen Uncle ba'a magana, babu kunya ya rungumeta a gaban Doctor Shu:aibu, Ama..... kam hawaye kawai takeyi, dukda tad'an dad'e tana zargin cikine dama, soboda aikintane, (dan kunsan doctor Ce fannin mata insha ALLAH anan gaba kad'an zata zama kwararriya💃🏻).
Su Fateema Kansu dai murna sukeyi, kodan k'aunarda Ama....kema 'ya'yansu dolene su tayata farincikin samun NATA itama, kuma ko kad'an basuji kishin farin cikin da mijinsu ke nunawa akan cikinba.
Doctor Shu'aibu yace, "dama nasan itama tasan tanada, kawai dai ta 6oye mukune".
" Uncle ya kalli Ama..... yace, "wai haka my best!?".
Kanta ta 6oye cikin bargo tana murmushi.
Duk sai sukayi dariya, Uncle yaraka Doctor sannan yadawo suka cigaba da farimcikinsu.
Ranar dai dole Aneesa tayi sadaukarwa na kwananta ga Ama....., Uncle yakwana a wajenta saboda jikinta. (Anee kin biyamu kwannamu😂😜).

Hummm kafin kacemi maganar cikin Ama....Yazagaye dangi makusantansu, har 'yan jos an gwargwad'a musu, murna dai ba'a magana, 'yan dubiya su Anty maijidda dasu Asiya su Nazeefa mai jego, ita Ama... Kunyarsuma takeji, duk kuma d'okin son samun cikin saiya 6uya yanzu da'aka samu d'in.
Babama yayi murna, hakama innani, dukda bata fito ta nuna a filiba, amma takanas shehu yakawota tazo ta duba Ama.....

Amatullah nashan wahalar cikinnan, dan laulayi takeyi sosai, dolene kaganta Tabaka tausayi, dukta rame sai uban haske data k'ara, dukda kasancewarta bak'a.
Girki dai su Fateema sun sauke mata, saidai ta kwana da miji, wataranma idan abin yay tsanani hakura suke da kwanan Nasu ya kwana a d'akinta, tanashan k'arin ruwa kam tamkar wata gallon🤭, kullun cikin zirara mata akeyi.


To Ama...ALLAH yaraba lafiya.



***********

Kwanci tashi babu wahala wajen Ubangiji, ga Ama.... cikinta yashiga wata na 7, yafito d'as kuma yamata k'yau, tanata karatunta hankali kwance, dan Alhmdllh tunda cikin yashiga wata na 5 tasamu sauk'in laulayin, saidai abinda ba'a rasaba, harma taje jos tayo sati biyu acikin d'an hutun dasuka samu, tazaga dangi sosai dukda ba wannane zuwanta Na farkoba, har anguwarsu taje ta gaida makwafta dasuke mutunci dasu kafin rasuwar su baba, dukda ma wasunsu sun rasa rayukansu a lokacin wancan rikicin, wasu kuma sunbar garin gaba d'aya, har kuka tayi dataga kufan gidansu, Dan tuni Uncle yanemi shawarrata akan ayi masallaci ko islamiyya awajen, domin ladan yadinga kaiwa ga iyayenta, takuwa amince, yasa akayima wajen gyara bayan an rushe, masallaci akayi k'arami da islamiyya mai aji hud'u k'anane amam, sai Bohol da akayi mutanen anguwar NATA d'ibar ruwa, dama basudashi. Wani son Uncle Yakuma ratsa ruhinta saboda wannan hidima dayay ga mahaifanta, (kowa yasan anason sadaka mai gudana ga mamaci). a zuwanne takejin labarin d'aure Ramzaki da akayi, saboda kashe wani da Mr Pam yasa sukayi, kuma aka kamasu, koda sukace shine yasakasu aka kirashi saiyace shibaima ta6a ganinsuba ballantana ya sansu, k'arya suke masa, hakanne yasa aka kaisu Court, hukuncin shekaru 25 aka yanke musu a prison. Amatullah dai jitayima INA itace alk'alin , da ratayesu zata sakama ayi take anna, amma hakanma tayi farinciki koba komai zai d'and'ani azabobi kafin yaje waken ALLAH kuma. Satinta biyu tadawo Kano ta koma school aka cigaba da bugawa.

Rayuwar gidansu nanan yanda take, saidai 'yan canje-canje daba'a rasaba, amma sunan akan tattalin mijinsu da kishinsa, kuma hakan bai hanasu k'yautatama junaba.
Haka shima mijinsu mai gajiya da basu soyayya mai tsaftaba, kowacce gwargwadon iko yana nuna mata tattali da soyayya, yana k'ok'arin adalci a tsakaninsu, wadda yafi so kuma yabarma zuciyarsa.
Maganar K'UNGIYARSU kam saimuce Alhmdllh, yanzu haka suna k'ok'arin had'a wani gagarumin taro na k'asa, domin wayarma matasa dakai a kan za6en dake tunkaro k'asar, Wanda bai wuce saura kwanaki k'alilanba a gudanar dashi.
Sai dai kuma a wannan tsakaninne wani Abu Mara dad'i yafaru😢, shine Rasuwar baba, adaren juma'a ranar alhamis kenan jikinsa yay tsanani, hankali tashe Innani takira Uncle kusan 1pm, harma ya kwanta, dan ranar a d'akin Amatallah yake, suna tsaka da barci tana kwance a jikinsa, yayinda hannunsa ke rungume da cikinta, da k'yar ya iya lalubar wayar a k'ark'ashin filo, batareda yaga mai kiranba yad'aga dafad'in "please wanene?".
Muryar data daki kunnensa tasashi wartsakewa babu shiri, innani yajiyo tana fad'in " maza kazo gida Muhammadu jikin babanku ya rikice".
A firgice ya wuntsilo daga gadon, haryana bigema Ama.... cikinta, Wanda zafinne yasata farkawar dole tana fad'in "wayyo ALLAHNA".
ina Uncle bai sauraretaba, sorry kawai yace mata yafice da sauri.
Dukda azabar da Ama... keji haka ta tashi zaune da k'yar, mamaki yacikata, tabbas babu lafiya, dan ko juyi zatayi cikin barci saiya farka, kuma zai taimaka mata ta juya cikin lalla6awa, amma yanzu ji yanda ya maujeta bai kulaba, sakkowa tayi tafito tana d'an cije baki, dan har yanzu inda ya bigeta bai daina zafiba, yaran cikinta sai motsawa yakeyi alamar shima yaji zafin maybe (😂lol).
Tana fitowa falon yana fita shikuma a rikice, ya canja kayan barcinsa zuwa farar jallabiya, hakan yakuma rud'ar da Ama... ta tada su Fateema duk ta sanar musu.
Jigum-jigum sukayi, kowa yana sak'e-sak'e da tunanin mike faruwa? dukda wani 6angaren tunaninsu yana kan babane k'ila, saboda jiya jikin nasa yad'an motsa har sukaje suma suka gaidashi.

Kasancewar titi babu motoci sai tsilli-tsilli yabama Uncle damar zabga gudu, lokacin dayaje gidan lamari ya 6aci kam, danba baba ba hattada Innani tafita hayyacinta, Aysha sai kuka takeyi, hakama gwaggo Rakiya.
Dole adaren suka tafi asibiti, sai daifa babu tsumi babu dabara, kafin asubahi rai yayi halinsa😭, ALLAH ya d'auke kayansa.
Mutuwar data zamema Uncle ta uku dabazai ta6a mantawa da itaba, duk yanda yaso ya daure ya rarrashi su Innani yakasa, shima kansa yakifa akan gawar yafashe da kuka😭.

😭hakanne nima yasani kukan, danna tuna da rasuwar nawa mahaifin😭, ALLAH ka gafarta musu, ka yafe musu, muda suka bari ALLAH ka d'auki ranmu muna a masu imani da tsonka ya rabbi, ya ALLAH ka k'ara mana soyayyar manzon ka tsaftatacciya a rihinmu😭.
Marayu ALLAH yabamu hak'uri kunji, inayinku a duk inda kuke.😭🤝🏻.

To anyita ta k'are, baba yatafi ya barsu Uncle, yanzu shine babban wa, shine kuma Uba.
Washe gari misalin 10am akayi jana'izarsa wadda ta tara d'unbin Al'umma, kodan d'ansa yatara, dan matasa dama dattijan sunta tururuwar halattar wannan jana'iza domin nuna hallaci ga Alhaji Muhammad Ahmad Labbo.
A kwana Ukun data gabata ba'a cewa komai, dolene kaga Uncle dasu Ya Jabeer subaka tausayi, barema su Nazeefa da Shehu da Anty maijidda, hakama su Amatullah duksun jigatu, amma Yaya za'ayi da ikon rabbi, saidai hak'uri.
ALLAH sarki Innani, mace mai hak'uri da k'ok'ari, tasha jiyya harta tsawon shekaru kusan 7, ALLAH yabata ladan jiyyar datayi ta adalin mijinta dattijon kirki mai yakana da dattako.



******* ******* *******

Tun bayan rasuwar baba abubuwa sukaima Uncle cak, Yakoma sai a hankali, kasuwama yadaina waiwayarta, wajen aiki kam danya zame masa tilasne, sauk'in sama ba kullum baneba, K'UNGIYA kanta tasan jagoranta yazama abin tausayi, dole sai Alhaji Sabi'u ne yacigaba da tafiyarda shugabancin kafin komai ya daidaita.
Su Kansu matsansa saidai Addu'a suke binsa dashi, amma komai nasa yayi sanyi.
Ahaka dai yauda gobe har zuciya tafara sanyi da hak'un dangana, yafara komawa kan harkokinsa dakuma jan 'yan k'annensa a jiki, yakuma ninka kulawarsa ga mahaifiyarsu Innani, wadda ayanzu itace Uwa Uba kuma, itama kanta dukta fita hayyacinta, ga girma na tsufa.


Cikin Amatallah yashiga watanni na tara kenan, haihuwa yau ko gobe, dolene kaganta tabaka tausayi, gawata kumbura datakeyi, Uncle dukya d'aga hankalinsa, koda yaushe cikin kiranta yake a waya, a d'an tsakanin dole tad'an jinkirta dazuwa Asibitima, tasamu Hutu harsai ta haihu.
Idan tana zaune haka zaita mammatsa mata k'afafu, idan kuma bayanan Aneesa ko Fateema zasuyita matsa mata, saikuma in yara sundawo makaranta, Amatallah tazama 'Yar gata, ai babu abinda zatacema ALLAH sai godiya, itadai ana gudun KISHIYA ita k'aunar nata takeyi, da godema ALLAH dayasa sune abokan rayuwarta, idanma taji mace nafad'in batason KISHIYA saitace amma bakida wayo wlhy, ai KISHIYA abar soce, ta 6angarori masu yawan gaske, mai dogon nazari da hangen nesane kawai zai fahimci hakan, musamman idan ALLAH yabaka mai hankali da sananin yakamata, amma inka samu mai burin korarka aika Shiga tara (🙁 ALLAH karabamu da irinsu to).

Ranar wata talata da rana kusan 1pm Amatallah tana kwance barci yad'an figeta wani azababben ciwon Mara ya tasheta kuwa, aiko a firgice tatashi tana kuka dakiran Ammi da baba.
Fateema na kicin tajiyo kukanta, a rikice tazo 6angarenta, halin data isketane ya tada hankalinta, tashiga rambad'ama Aneesa kira, itama a guje tazo.
Basu wani 6ata likaciba suka memo taxi sai asibiti.
Suna isa aka shiga bama Ama.... taimakon gaggawa.
Ganin anshiga da ita suka sami damar kiran Uncle suka Sanar masa, mintuna k'alilan saigashi ya iso shida Shehu, isowarsu kuma babu dad'ewa ALLAH ya sauki Ama..... lafiya, ta sunkuto baby girl d'inta, saikuma ga baby boy babu zato.
Nanfa murna da farinciki mara misaltuwa ya kaure, kafin kace mi labari ya karad'e dangi makusanta.
Ganin ta sauka lafiya zuwa yamma aka sallesu suka tafi gida tareda dangi dasukazo tayasu murnar wannan haihuwa.
Uncle baki yak'i rufuwa dan dad'i.😃.............✍🏻


Uncle nima bara na tayaka to😁😁, nasan masu karatuma zaru tayamu.💃🏻














One luv😻😻.



[1/25, 4:04 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 41/45_*
____________________


Uncle bai samu damar ke6ewa da Ama... ba sai dare, yashigo d'akin da sallama, gwaggo Rakiya tana zaune a falo tagama sakama macen kayan sanyi dan shirin barci, ya gaisheta tamasa barka, dan d'azun bata samu damaba saboda su Nazeefa Asiya Fa'iza Aysha zaliha dawasu dangi na familyn su Uncle duk suna a d'akin, sai yanzu daduk suka tafi, yarama da k'yar aka lalla6asu suka kwanta, amma da suka nanik'e da baby's.
Bayan zun gaisa ya d'auki babyn daketa barcinta, kallonta yake farinciki nakuma ratsashi dan copy d'in Amatallah ce awajen, sosai yarinyar ke kamada Uwarta, bedroom d'in yashiga inda ya tadda Ama... Na waya da 'yan jos, zama yay a bakin gadon ya d'auki Namijin yahad'a duk ya rungume a jikinsa, yanamaijin k'aunarsu tana kuma ratsashi dashiga 6argomsa tamkar sauran 'ya'yansa.
Bayan ta kashe wayar tace, "sannu Uncle".
Fuska d'auke da murmushi yace, " kece da sannu my heartbest, ALLAH yaymiki albarka".
A kunyace Amatallah tace "amin Uncle".
Tasowa yay yadawo kusada ita bayan ya kwantar da yaran, ya rungume ta yana bata zafafan kisses, tareda kuma sanya mata albarka.
Ita harma yabata kunya, tace, " Uncle jegofa mukeyi".
Murmushi yayi yana kuma sumbatar wuyanta, "nima ai jegon nakeyi my besty".
" Uncle kaid'inan ko! Hummm".
Yaja kumatunta kad'an, "nid'in minayi?".
" a'a babu komai, ai abin bana fad'a baneba".
Dariya yayi yana fad'in "idan lokacin fad'ar yayi zaki fad'ane, wane suna kikeson nasama yarana?".
Ta murmusa tana kuma lafewa a jikinsa tace, " duk Wanda yamaka yamin nima Uncle".
"Shikenan my best, Brother kawai da Ammi".
Ta kalleshi da sauri, " Uncle har sau biyu? Sahib ai ya isa, kar kuma abin yay yawa".
"Tab lallai yarinya, ko duk yaran gidannan zasu zama sunan brother bazasumin yawaba wlhy, kinsan kuwa yanda sunan keda daraja agurina, nama saka nagama, barama namusu hud'uba kawai".
Kasa cewa komai tayi, sai binsa kawai takeyi da kallo tana hawayen farinciki dak'arin jin k'aunarsa a ruhinta da 6argo, itakam mizatama Uncle tabiyashi da wannan d'unbin k'auna dayakema mahaifinta, ai saidai taita K'AUNARSA har k'arshen numfashinta itama kawai.😢

A kwanaki 7 d'inan ansha abubuwa, 'yan barka kullum cikin cika gida suke, su Nazeefa Asiya Zaliha Fa'iza Aysha kullum suna gidan, Innani ma tazo taga jarirai. Ranar suna kam mun rak'ashe mun kwalle abunmu, munci rangam iyakar k'arfinnmu, kad'an yarage Cikin Xoxo yafashe🤭, saida na 6oye kular abinci ta tsagaita, amma su o e sai aka 6oye a bayan murfin k'ofa dankar in ganta nahanata😜, yara sunci sunan Ammi da baba, *ISMA'IL & SALIHA* za ana cemusu *RAYYAN & RAIHANA* to ALLAH ya raya 'yan duguy-duguy iyalan baba.
Washe garin suna 'yan jos sukaso wucewa da Ama.... Saidai babu Dama saboda karatunta, daga k'arshedai gidan Innani takoma kamar yanda Innani tabuk'ata, Uncle dukda baisoba haka ya hak'ura, dan bashida damar jayayya da mafaifiyarsa.
A can Amatallah tacigaba da jego, ga kulawa ta musamman tana samu wajen Innani da gwaggo Rakiya, hakama Anty maijidda tasaka k'aimi wajen gyarata, acewarsu batada maimata saisu, hakama 'yan Jos ba'a barsu abayaba, kullum suna mak'ale da waya akunne.
Su Fateema kam duk k'arshen Sati agidan suke yini, hakadai sukaita wankan hankalinsu a kwance.
Watanta d'aya dawasu kwanaki Uncle ya ta'azzara dole suka tarkatota suka maido masa.
Hummm fad'a muku yanda Uncle ya ragargaji soyayya 6ata lokacine, ammafa anshata tamkar babu gobe, yaransa sunata k'ara wayo, Ama.... bata wani shan wahalar raino, sanda tana gidan Innani da zama tsakaninta dasu sai bada nono, idan zasuje makaranta ta d'auki d'aya Aysha ta d'auki d'aya, yanzu kam tunda suka dawo gida Fateema da Aneesa da yara sune 'ya. Raino, tsakaninta dasu sai idan sunyi kukan yunwa kozasu kwanta barci.
Ahaka aka shiga rugumniyar za6e.
Kwanakin taron su Uncle kuma yarage kwana Uku kacal. zasuyine a Abuja dan matasan K'ASAR na 6angarori biyu suke son gani.
Tun ana saura kwana biyu taron matasa suka fara turutwar tafiya birnin tarayya Abuja, kowa burinsa kar ayi babushi.😃🤝🏻.
Ana gobe taron kam ai Abuja da'd'im tayi da matasa, abubuwa dayawa saida suka tsaya na harkar kasuwanci dawasu abubuwan.
Washe garin taron kam hummmm, ai d'an adam ba'a cewa komai, saima ka d'auka duniyar suka tara a wajen kawai saboda yanda MATASAN KUDANCI DA AREWACI suka amsa wannan kira.
Su Uncle sai aranar suka isa abujar da sassafe kuwa.
Zuwa k'arfe 10 na safe taron yafara gudana.🤩👎🏻

Tunda su Uncle suka hau munbarin taron yake bin matasan da kallo, kawai saiyaji kwalla sun cika masa idanu, shin dama zaiga wannan ranar a rayuwarsa? ko a mafarki baita6a tunanin zai tara matasan dasuka haura hamsinba, amma ga sama da dubunnai a gabansa, hawayen dasuka cika idonsa suka fara gangarowa saman kumatunsa.
Alhaji Sani dake kusadashi yad'an bubbuga kafad'arsa yana murmushi. juyowa Uncle yayi yana kallonsa, shima fuskarsa d'aukeda murmushin, yasa handkerchief yana goge hawayen......
Maganar Husain Abubakar d'aya daga cikin matasan masu fad'a aji a k'ungiyar ya d'auki hankalinsu. cikin harshen turanci yake maganar. (Amma ni zan fassara muku da hausa😜).

"MATASANMU!!!".

suka amsa da ihu.

Yakuma fad'in " MATASANMU!! MATASANMU!!!!".
tamkar zasu fasa birinin Abuja haka suka amsa wannan kira cikin d'aga hannu da kuwwar ihu.
"Lallai Mun yarda MATASANMU suna buk'atar gyara a k'asarmu, amsa kiranku kawai ya tabbatar mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login