Showing 9001 words to 12000 words out of 104242 words

Chapter 4 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16035

ba.
A baya basu nuna kishin Amatallah d'in, amma tun zuwan dayayi jos sati 4 daya wuce kar6o maganin baba, saiya d'auki pictures d'in Amatallah a wayar babanta (abokinsa), shikam harga ALLAH bada wata manufa yayi hakanba, shiyyasa daya dawo yanuna musu hoton dansuga yanda tak'ara girma, shima kusan 3years bai gantaba, suna ganin hotunan suka canja fuska. tundaga lokacin ko maganarta yayi saisun nuna jin haushinsu, yarasa miyasa suke hakan shikam?.......
Ta6asa datayine yasashi dawowa hayyacinsa, har yanzu bata saki fuskaba tace, ''gasu Na had'a".
Mik'ewa yayi yana fad'in ''to sannu da k'ok'ari, ya d'auki sauran abin dazai buk'ata da tsarabar daya yoma Amatallah yasaka a madaidaiciyar bag d'in data had'a masa kayan.
Jakar ya d'auka, yad'ago yana kallonta, tsaye take jikin mirror, tayi kicin-kicin da face, ahankali yatako gabanta, yad'an murmusa kafin ya rungumeta a jikinsa, acikin kunne yaymata rad'a, sannan ya sumbaci la66anta da goshinta yana fad'in "saina dawo".
Duk da maganarsa tasaka zuciyarta yin sanyi, amma saita gimtse, batace komaiba tabiyo bayansa, jakar takar6a suka sakko k'asa tare.
Babu kowa a falon, yara duk suntafi school.
Kallonta yayi yace, ''bara nayi sallama da Fateema".
Kauda kanta tayi daga kallonsa, batace komaiba.
Gaba yay abinsa, zuciyarsa Na mamakin kishi irin na mata. komin k'ank'antar Abu sai sun nuna kishi akansa, musamman Aneesa tafi fatima kishi.

A Falo ya tadda Uwargidan tashi zaune tana kallo, tamasa sannu da zuwa.
Amsawa yayi yana zama kusada ita, idonsa akan TV yana kallon film d'in datake kallon. sai kuma ya maida kallonsa kanta.
" Fateema zanje Jos ne".
"Jos kuma Nurri? Da ranarnan? Ko jikin babane ya motsa?".
" a'a, ba jikin baba bane, zan dai kuma amso masa maganin nan ne, daganan naduba jikin Amatallah batada lafiya, sunama Asibiti an kwantar da ita".
Dukda maganarsa ta soki zuciyarta amma saita danne, tace, "ayya ALLAH yabata lafiya? Mike damunta haka?".
" Uhm to, bandai saniba, d'azu nake waya da Brother shine yake sanarmin."
Azuciyarta tace shine kake sauri katafi tunda ga 'Yar Goal. afili kuma tace, "ALLAH yabata lafiya to, a gaida mana dasu".
"okey zasuji".
Harya mik'e yakoma ya zauna, yakula da yanda itama yanayinta ya canja, amma dayake tafi Aneesa hankali tayi k'ok'arin danne kishinta, yay murmushi yana fad'in "koma abinda zan tuna baza'a baniba?".
Kamar zatace bagashi zakaje inda za'a makaba. saikuma ta danne tace, ''to mikake so?".
Girarsa d'aya yad'age yace, " komima?".
Kumatunsa ta sumbata.
Shima haka ya sumbaci nata, sannan suka fito.
Aneesa Na falo tsaye, tagama cika fam da haushi, koda suka fito bata kallesuba tayi gaba abinta, binta kawai yayi da kallo, itakam Fateema saita ta6e baki tana Harar bayan Aneesa.
Har jikin motarsa suka rakashi, Aneesa tasaka masa bag d'in a gefensa, bayan yatada motar yamik'o musu hannunsa Na dama, d'aya bayan d'aya sukayi musabaha🤝🏻, sannan yace, "abama yara hak'uri nayi tafiya basu saniba, sannan dan ALLAH karna dawo naji abinda zai 6ata raina, Ku kama kanku, insha ALLAH 2days kawai zanyi nadawo".
Atare sukace insha ALLAH bazakaji komaiba, ALLAH ya tsare.
Yace, " amin to my Sweet wife's". dan son tsokanar su yace, " Amma bakuce na gaida Amaryaba".
Kowacce kauda kanta tayi gefe basuce komaiba, dan bak'aramin dukan zukatansu maganar tayiba, ashedai hasashensu gaskiyane?.
Da sauri Aneesa tashige ciki tana hawaye.😹

Jiyayi kamar ya kwashe da dariya, amma saiya gimtse, ya kalli Fateema dake tsaye har yanzu yace, "my tee... bud'emin gate to, tunda bazakuce Na gaishetanba, saina dawo".
Kanta kawai ta d'aga masa, tanufi gate tabud'e masa, harya fice yana d'aga mata hannu, tamaida tarufe sannan takoma cikin gida zuciyarta Na k'una, dajin tsanar Amatallah.


Nikam bilynku Nace, "wannan fa shine gudu a duhu masu karatu🤣🥴".


Yana tuk'i yana dariyar abinda matan nasa sukayi, a fili yace, " dama kun kwantar da hankalinku my wife's, Muhammad bashida burin k'ara aure, koma zanyi babu yanda za'ayi Na auri 'yar cikina, Amatallah she is my daughter ".
Da wannan tunani yak'araso gidansu mahaifarsa.
A k'ofar wani gida yay parking motar, gidane irin ginin da, sai dai ko ina mulmule yake da siminti, tundaga k'ofar gidan har zuwa bangon gidan.
Yatura murfin yashiga soron gidan da sallama, karo sukaci da wani saurayi dabai wuce 30years ba.
"A ya Muhammad barka da zuwa".
" yauwa Jabeer, daga ina haka kuma? bakaje aiki bane?".
"Wlhy naje yaya, mantuwa nayi nadawo d'auka, ina yarana? duk suna lafiya dasu Aunty's?".
" lafiyarsu k'alau, ya jikin baba?".
"A alhmdllhi wlhy, yanzu haka nabaro innani nabashi kunu dayasa a dama masa".
" masha ALLAH, jiki yafara sauk'i, bara to nashiga, dan zanje Jos ne".
"Amma yaya Muhammad tafiyar yamma?".
" to yaza'ayi Jabeer, ai ranar dole sai dole, bara nashiga dai".
"To shikenan, ALLAH ya tsare hanya, a gaida mana su Yaya Ismail da iyalansa".
" insha ALLAH zasuji".
Musabaha sukayi🤝🏻, shi ya shiga, shikuma yafita.

Tsakar gidan babu kowa, sai dai a share yake tas, sai kuma k'amshin girki dake fitowa daga kichin d'in tsakar gidan.
Kai tsaye d'akin baba ya nufa, tunda jabeer yace innani tanacan.
Sallama yayi a k'ofar d'akin, sai da aka bashi izinin shiga sannan yashiga da sallama.
Mahaifinsu na zaune a saman k'atuwar katifar da yake jiyya, ya jingina da filuluwan da innani ta saka masa a jikin bangon, yatsufa sosai gaskiya, duk da hadda alamun rashin lafiya data kuma fiddo tsufan nasa, danma 'ya'yansa tsaye suke Kansa wajen kulawa dashi, musamman ma Alhaji Muhammad d'in. Sai dattijuwa itakuma tana zaune a kujera 'Yar tsugunno kusadashi, itama dai babu laifi ta manyanta sosai gaskiya, sai dai jikinta yafi Na baba k'arfi, saboda lafiya da ALLAH yabata, hannunta rik'eda ludayi zata saka a kwanon shan ruwa, da alama tagama bashi kunun.
Tunda yashigo tamasa kallo d'aya saita kauda kanta gefe. baba kam murmushi yayi, idonsa akan sa..
Ya tartare malun-malun d'insa ya zauna a k'asa kusada babansa shima yana murmushi, "sannu baba, ina yini?".
Ahankali baba yace, " lafiya lau Muhammadu, ya iyalanka?".
"Lafiyarsu lau baba, ya k'arfin jiki?, duk da dai yauma naga Alhamdulillahi".
Murmushi baban yak'arayi, yace, " gaskiya ne Muhammadu, jiki kam sai dai mucigaba da godema ALLAH".
"to Alhmdllh baba, ai mu haka mukeso, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana masu amfani".
Baba ya amsa da ''amin Muhammadu".
Kallonsa ya maida ga innani data kauda kanta gefe tun d'azun, yace, " Innani ina yini".
Kuma kauda kanta tayi sannan ta amsa masa. ta tambayi iyalansa.
Shima kansa a k'asa yace duk suna lafiya.
Batace komaiba tafara yunk'urin tashi.
Da sauri yace, "innani dama zan koma jos ne wajen maganin baba, dan naga yanajin dad'insa, daganan kuma zan duba d'iyar Isma'il batada lafiya, har an kwantar da ita a asibiti ma".
Yanzu kam sosai ta kalleshi, tace, " subahanallah, badai Khadija ba?".
"Eh innani ita".
" miya sameta?".
"Wlhy nima ban san dai miyake damuntaba, sai dai naje tukunna".
Daga innani har baba addu'a suka mata, sannan baba ahankali yace, " amma Muhammadu zakayi tafiyar dare ai".
Kallon agogon hannunsa yayi, "baba insha ALLAH kumin addu'a zan Isa da wuri, yanzu dana fita salla kawai zanyi Na d'auki hanya".
" to shikenan ALLAH ya tsareka, yakaika lafiya kaji".
Amin baba, ALLAH ya k'ara lafiya".
Sukace amin.
ya fiddo kud'i a aljihun babbar rigarsa, saman katifar ya d'ora, "innani ga wannan kowani Abu zai taso bana nan, insha ALLAH jibi zan dawo".
Batareda ta kalleahiba tace, " da kama bar kud'inka, dan Wanda kabada jiyama ko ta6asu ba'ayiba, munada komai agidannan, d'azuma jabeer yayo cefane mai yawa dazaiyi iya kaimu sati".
"Duk da haka a ajiye innani, ina Nazeefa da Shehu? Banji motsin suba".
"Nazeefa ta tafi gidan maijiddah, zata tayata aiki abokiyar zamantace ta haihu jiya, Shehu kam wai yatafi makaranta yace"..
"ALLAH sarki, to ALLAH ya raya, shikuma ALLAH yasa gaskiyane, tunda nasan halinsa. bara naje lokaci Na k'ara tafiya".
"Katsaya kaci abinci, naga Ramatu takusa gamawa".
Agogonsa Yakuma kalla, ya d'an kwantar da murya, " kiyi hak'uri Innani, gara naje karnayi dare, naci abincima babu dad'ewar nan."
"addu'a duk suka masa, yafita yana amsawa, zuciyarsa nak'ara masa dad'i, dajin k'aunar mahaifan nasa. salla kawai yayi ya d'auki hanya.



_______________________________

Koda d'an siyasar nan Mr Pam da jama'arsa sukaje police station sai suka nemi ganin d.p.o
Bayan ankaisu office d'insa, suka gaisa cikin mutunci, sannan ya mik'a buk'atarsa ga d.p.o nason asaki su zike, da farko d.p.o yaso ya tirje.
Amma tunda Mr Pam ya fiddo 'yan dubu-dubu bugun Abuja sai d.p.o ya waske. Mr Pam yay murmushi ganin yanda d.p.o yayi.
Ya ajiye kud'in agabansa yana fad'in "Yaya za'a banisu yalla6ai?".
" wata 'yar dariya d.p.o ya d'anyi, yasa hannu kan kud'inda Mr Pam ya ajiye, sannan yace, "yanzun kuwa".
Daga Mr Pam har yaransa biyu dake tare dashi dariya sukayi.

Duk wani ciku-ciku daya dace Mr Pam yayi, yasamu nasarar fiddo su zike.
Wad'anda tunda aka bada belinsu suka fito da k'udirin d'aukar mataki akan Amatallah da ahalinta.
Su duk zatonsu babantane yamusu shunen 'yan sanda suka kamasu.
Shiyyasa suka k'udirci ramawa..........✍🏻


_(wannanfa Shine halin mafi yawan jami'an tsaron k'asar tamu. Shin tayaya za'a samu gyara? bayan masu gyaran suma suna buk'atar a gyarasu, *CIN HANCI DA RASHAWA* yazama abokin kowa a k'asarmu, kuma duk a dalilin *SIYASA KO K'ABILANCI*, zakiga d'an siyasa yayi duk wani shigi da fici wajen samun yanda yakeso, koda bai cancantaba. Zakiga ankama mai laifi awani waje, amma saboda bad'an yankin bane, ba d'an k'abilar bane sai a masa mummunan hukunci, amma idan k'abilarsa ne babba awajen, da 'yan uwansa sunzo sun mik'a sai a fiddashi, komai girman laifinsa, shiyyasa zakuga idan mutum k'abilarsa nada wani babban muk'ami awaje bayajin tsoron shiga kowanne tarko, saboda alfarmar dayake da ita, shin yaya zamu kira matsalolin k'asarnan?, *SIYASA KO K'ABILANCI!?* ne ke jagorancin lalacewarmu🤷🏽‍♀?.)_





*_ya ALLAH ka gafarta ma iyayenmu🙏🏻😭_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



*_Happy Birthday Abba gana, ALLAH yak'aro shekaru masu al'barka da amfani a duniya da lahira👯🏻🔪🎂🍾🍹_*



____________________
*_Number 5_*
____________________

Kusan 5pm ya isa garin jos, damma ba gudu yakeba, yakuma tsaya a garin Mr Ali yayi sallar la'asar, dan yana ganin kafin yashigo gari time ya shige sosai.

Baban Ama... da Ammi duk suna a asibitin, Amatallah na kwance, idonta biyu, amma tarufesu, su Aminta ne kawai ked'an hira duk akan ciwonta.
Wayar baba tayi ringing, cikin fara'a ya d'auka yana fad'in "inaga brother ya iso kam".
" Assalamu alaika brother, halan harka shigo".
"Ai ganima a k'ofar asibitin".
Cikin zaro ido Baban Ama... Yace, " maimakon kaje gida kawai? dama isowarka nake jira natafi gidan, nazata can zaka wuce?".
"Ai bazan iyaba, sainaga jikin my best D.. first brother".
" humm, kai da d'iyar taka ba'asan gwaniba ai, bara nazo to nashigo dakai".
"Baban Ama... Ya iso kenan?". Cewar Ammi.
" eh wlhy, wai gashima a gate d'in asibitin".
"Ikon ALLAH, nazatama zai wuce gidane ai".
"kinsan halin brother, bara mushigo dai".
"To".

Duk abinda ake Amatallah na jinsu, amma batace komaiba, saima luf data sake yi a kwance, haka kawai taji gabanta ya tsananta fad'uwa, duk da dama yau Throughout haka ta wuni gabanta na fad'uwa, jitake kamar wani gagarumin abu zai faru da ita, shiyyasa dukta tsangwami kanta......😢
tun kafin su shigo k'amshin turarensa yayo gaba, Amatallah ta shak'a tareda kuma matse idanunta, still zuciyarta nacigaba da bugawa da sauri-sauri. Addu'a tafara karantowa, dan batasan dalilin wannan gudun da zuciyarta keyiba?, kuma tun ganinta Na farko da *_Uncle M.A_* a wancan zuwan hakance tafaru, harya tafi wancan time d'in idan suna waje d'aya koya shigo sai heartbeat d'inta taringayi kamar zata fito, kuma itakam a shekarun baya tana yarinya batajin hakan akansa, komiyasa yanzu kuma?...........

Sansanyar muryarsa ce ta katse tunaninta. bayan sun gama gaisawa da Ammi yamatso gaban gadon saitin face d'inta.
Yace, "My best daughter! barci kikeyine?".
Ya sallam!, tafad'a a zuciyarta. batasan ya zata musalta yanda cool voice d'in uncle M.A ke razana zuciyarta da dukkan magudanar jininta ba, jitake kaf duniya yafi kowa dad'in murya.
Babantane ya ta6a k'afarta tareda d'an bubbugawa.
Ta bud'e ido ahankali tamkar mai barcin gaskiya, da uncle M.A tafara tozali, yana tsaye agaban gadon kusada fuskarta, sanye yeke cikin Cyan color d'in tattausan boyal, Wanda yasha d'inkin babbar riga, ya kafa hular zanna bukar black akansa da ratsin cyan kad'an, sai bak'in agogo da bak'in takalmi heir cover. Waro ido tayi cikin acting like tana mamaki ganinsa.
Tattausan murmushi ya sakar mata.
Ta yunk'ura a hankali tatashi zaune tana "lah Uncle yaushe kazo".
Still murmushin yakuma yi, kafin yace, " my best daughter yanzunnan nazo kina barci, ya jikin naki?".
"Da sauk'i uncle, ya hanya? Yasu Saifudden da jikin baba?".
"Everything Alhmdllh my best D..., amma gaskiyafa kin rame sosai, anya kinacin abinci my best?".
K'asa tayi da kanta tana murmushi, saikuma tad'an jinjina kai, tamkar wata k'adan garuwa. Tana fad'in ''inaci uncle, katanbayi baba da Ammi ma".
Murmushi yayi, sannan ya maida kansa ga babanta, " brother wai miya faru da my Daughter hakane?".
"Humm ai Brother inaga muje gida, sai muyi maganar a can, dan yinta anana zai iya zama danger gaskiya".
"okey, amma anbata sallamane?".
"No basu sallamemuba, inga dai k'ilan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan kaganta yanzudai normal, sai dare yayi jikin ya rikice, taita firgita, kullum akanta muke kwana babu barci wlhy".
" ya salam, abin yayi tsamari haka Dama?".
"Brother Amatallah dama haka take da rik'e Abu, shiyyasa kullum nake cikin fargabar irin mijin da ALLAH zai iya had'ata dashi, ba kowane zai iya d'aukar wannan rayuwan tataba gaskiya, so ina tausaya mata".
" karkace haka brother, muyi mata addu'a kawai, insha ALLAHU ALLAH zai bata miji nagari ma".
"To ALLAH yasa brother".
dahaka suka k'arasa motar sa.
Har sun shiga motar Baban Ama... Ya hango Ammi Na tahowa da sauri.
Kallon Uncle M.A yayi dake k'ok'arin jan motar yace, ''d'an dakata ga Ammin tanan, inaga munyi mantuwar keys d'in gid......
Bai k'arasaba Ammi tak'araso, keys d'in tamik'a masa kuwa tana fad'in "kun manta keys d'in ai. abinci nannan a seatroom Na shirya".
Murmushi Baban Ama... Yayi yana fad'in " jazakallahu khairan uwargidana".
Hararan wasa tamasa tace, "kuma amarya ba".
Duk su biyun dariya sukayi shida uncle M.A, Baban Ama... Yace, " ai nima aure zan k'ara, bakiga brother ma 2 Star ne ba? kilama yana shirin zama 3 ban saniba, gara nadage nayi nima Amatallah tasamu abokan shawara itama".
Juyawa Ammi tayi tana fad'in " wace zata auri tsoho?".
Dariya suka kumayi, sai da suka fita daga asibitin Uncle M.A yace, "brother mata basa girma akan kishi, wani lokacin har mamakinsu nake, komin k'ank'antar Abu sai yazama Na kishi a wajensu fa".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login