Showing 99001 words to 102000 words out of 104242 words

Chapter 34 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16045

da hanakan, muna muku barka da zuwa wannan taro, da godiya ta musamman ga amsa wannan kira namu, MATASANMU!! abin alfaharinmu, kune k'asar, inhar babu Ku babu k'asa, kun AMINCE da hakan?!!!".
Cikin Ihu sukace " Eh!!!!!!!!".
"Kun Amince kune K'ASARMU?!!!".
" Eh!!!!!!".
"Kun Amince zaku had'a hannu wajen rik'eta dakawo zaman lafiya!!?".
" Eh mun amince!!!!".
"To Alhmdllh, muna godiya da wannan goyon baya, bara nabama shugaba kuma Uban jagoran wannan tafiya da jajircewar ganin munzama ababen Alfaharin, wato *_Alhaji Muhammad Ahmad Labbo!!!"._*
Gaba d'aya suka hau ihu da sowa, duksun d'okantu dason ganinsa.
Uncle yatako cikin nutsuwarsa zuwa gaban Munbarin, nanfa ihu yak'aru, suka shiga d'aga masa hannu da raira wak'ar girmamawa agareshi.
Shima d'aga musu hannayensa duk biyu yakeyi, fuskarsa Na fidda Annurin murmushi da tsantsar farinciki ganin matasan nan.
Da k'yar aka samu suka lafa da ihun dasukeyi, Uncle yay gyaran murya yana kuma daidaita tsayuwarsa da gyara zaman babbar rigarsa ta farar shadda akan kafad'a.
Cikin sassanyar muryarnan tasa yaymusu sallama.
Suka amsa.
Saikuma yay shiru yana binsu da kallo, dandanan hawayen suka kuma cika masa ido, yasaka handkerchief yana goge guntayen hawayen dasuka fara k'ok'arin zubo masa a kumatu, nanfa gurin yay tsit idanunsu duk suna kansa, jikinsu yayi sanyi ganin yana sharar ido alamar kuka kenan, ahankali muryarsa tafara ratsa sifikan, " Nagode muku, nagode sosai, bansanma yanda zan nuna muku farincikina ba, amma tabbas ko ayanzu nabar duniya NACIKA BURINA, tabbas wannan shine CIKAR BURINA, KUN CIKA MINI BURINA na tsawon shekara da shekaru, banida abinda zan biyaku dashi, banidashi........
yakasa k'arasa maganar saboda kuka daya tokare mak'oshinsa (nace jama'a dama maza Na kuka irin haka😨?).
Kukan Uncle yasaka matasan dayawa kuka, Dan aganinsu sune yadace suyi kuka bashiba, kodan ceto rayukansu dayayi a mafi yawan had'ararruka, ya canja musu gur6atattun ayyukansu da zaman banzan dasukeyi.
Dak'yar Uncle yasamu ya daidaita kansa ganin yakarya zukatan matasan, yagoge fuskarsa yana murmushi. yagyara zaman Microphone's d'in da'aka jera kala-kala, Na 'yan jaridu.
Yace, "kun shirya!!!!".
Cikin matsanancin d'okamtuwa suka amsa da " eh!!!!!".
Yakuma fad'in "da gaske MATSAN K'ASARMU sun shirya canja KANSU DA K'ASARSU!!!!?.
" nanma suka amsa cikin matsanancin ihu".
Uncle dasu Alhaji sabi'u suka tuntsure da dariya.
_"Shin MATASANMU zaku yarda acigaba da amfani daku wajen BANGAR SIYASA!!!?"_

"A'a bazamu aminceba!!!!!!!!".

_"MATASANMU Zaku kuma yarda abaku KAYAN MAYE domin Baku KU'DI kuyi bangar SIYASA ko wani TA'ADDANCI!!!!!!!!!?."_

" A'a bazamu aminceba!!!!!".

_"MATASANMU zaku kuma yarda acigaba da Amafani daku wajen haddasa rikice-rikicen SIYASA KO K'ABILANCI ko fad'an ADDINI ko 'BANGARANCI!!!!!!?._

"A'a bazamu amince ba!!!!!".

_" MATASANMU zaku kuma yarda ku ringa keta HADDIN abokan jinsinmu MATA ta hanyar yimusu FYA'DE ko zama KIDNAPPER'S ko FASHI da MAKAMI ko asakaku CIN ZARAFIN wani saboda KU'DI!!!!?"._

Nanma suka Amsa da bazasu aminceba.

_"Inhar dagaske MATASANMU sunyi alk'awarin daina wad'annan gur6atattun ayukan dake ruguza K'ASARMU to ina buk'atar Ku tabbatar min da hakan a ZA'BEN dake tunkaromu, yakamata amatsayinku Na 'yan ADAM kuyi nazari akan yanda rayuwar talakan K'ASARMU ke tafiya. Nigeria babbar k'asace maifad'a aji a yankin Africa, k'asace mai tarin K'ABILU da ADDINAI, haka Ubangiji yaso ganinmu, wani bayajin yaren wani, amma kuma saiya dunk'ulemu a k'asa d'aya. Shin munfi ubangijin sanin dai-daine da mukeson rarraba kammu??, Ku koma Ku bibiyi ASALIN TARIHIN k'asarmu Nigeria, kuga yanda magabatanmu sukasha wahalar gwagwarmaya wajen kafa k'asar da kwato mana 'yancinmu, amma maimakon hakan abin bak'in cikin sai muka bari wannan wahalar tasu tatafi abanza, SIYASA taraba kawunanmu, nuna 'BANGARANCI da K'ABILANCI yahanamu zama tsintsiya mad'aurinki d'aya, WAY!!!!? kowa K'ABILARSA kawai yake kallo da gashin arzik'i, miyasa mukema juna kallon hadarin kaji?, manyan K'ABILUN K'ASARNAN sune HAUSA FULANI, YORUBA, IGBO, amma zakaga babu wata gagarumar jituwa atsakanin wad'annan k'abilun, kowanne jiyake shine agaba kuma dolene abisa, ko dolane yazama wani ginshik'in k'asar, amma kumafa bazamu iya had'e kai waje d'aya domin gyaran k'asarba, shin tayaya sauran k'ananun k'abilun zasuyi koyi damune?"._

"Shin kunsan miyasa hakan ya gagara tunma farko?".

Suka Amsa da A'a.

Tsayuwa Uncle yagyara yana share gumin fuskarsa, yacigaba da fad'in.....
_"bakomai baneba face tsabar son MULKI da son tara dukiya, wlhy wlhy da wannane manyan k'asarmu suka rarraba kawunanmu, kowa buk'atarsa yazama SHUGABA, sannan idan yasami shugabancin bawaifa mu TALAKAWANNE agabansuba, ALJIHUNSU shine agabansu, damuwarsu shine su HADDASA MANA BALA'I su tattare IYALANSU subar K'ASAR da k'ud'inmu, yanzu inason namuku wata tambaya, tsakaninku da ALLAH kuma nakeson kubani amsa, nasan kashi 90 Na MATASANMU dake wajannan Government Schools mukayi karatu ai!!?"._

Suka shiga amsawa da eh hakane hakane.

_" Shin kunta6a ganin wani d'an Governor ko Minister ko d'an Majalissan jiha kona datta6ai ko wani hamshak'in k'usar gwamnati a MAKARNTARKU ne ta gwamnati?"._

Gabad'a gurin ya kaure da ihun cecekuce.
Saida akayi magana suka tsagaita.

Uncle yacigaba da fad'in....

_"BANGAR SIYASA dasuke sakaku akwai 'ya'yansu? ko'a wajen Campaign baka ganin 'ya'yansu, wanima saiya gama shugabancin bakaga d'ansa ko d'ayaba, to basa k'asar, sunacan k'asashen TURAI suna karatu, idan sundawo k'asar kuma saidai ka hangesu A manyan motoci suna wucewa kan titi, shin wai mu 'ya'yan TALAKAWA bamusan kammu bane ko bamusan muhimmancin rayuwa baneba!!? idan Su badamuwarsu matasolinmuba mizai hana mu toshe duk wata hanyar dazasu sami Damar shugabantar tamune_."

"Shin zamu iyane?".

Suka amsa da sosaima kuwa.!!!!!!!!!.


_"Alhmdllhi, kusanifa komai sukazama mune sila, dan haka awannan karon MATASANMU mu tabbatar musu da mune k'asar, mu tabbatar musu da lokacin amfani damu yawuce, mu tabbatar musu da yanzu munsan ciwon kanmu, mu tabbatar musu da dolene adama damu. ta hanya d'ayace hakan zata faru shine daina yarda ana amfani damu wajen aikata ta addanci, mutashi mu nemu Na kanmu, mudaina zama dogaro da gwamnati, akwai sana'oi k'ananu dayakamata MATASANMU sunayi domin kare mutuncin Kansu, kwad'ayin aiki da burin sainayi kud'ine ke ruguzamu, dashine suke samun galaba a kanmu, idanfa munyi haratu bashine ke nufin dole samun sami aiki a k'aton office's ba, shi karatu anayinsane domin k'ara nemawa kai martaba da kima aduk inda katsinci kanka, mudaina Shaye-Shaye, dan shima yana ruguzamu da tasirantuwa wajen maidamu baya, MATASANMU dan ALLAH muringa fad'ama kanmu gaskiya kafin wani yafad'a mana, mu gyara kafin a gyara mana, mu canja kafin a canjamu, mu yima kammu hisabi kafin ayi mana, mu tsaftace kammu kafin a tsaftacemu, rayuwarmu tamuce, idan ta lalace mune mukayi asara, wlhy duk sonmu da gwamnati ta gyara sai muma mun gyara d'in, duk Wanda kaji ankira da suna WANE to wlhy badaga kwance ya tsinto sunanba, saida yasha wahalhalun rayuwa, SHUWAGABANNINMU fa suna zuwa dai-dai da halayenmu ne, to Ashe samun tsaftataccen shugabanci da dawwamammen zaman lafiya dayake a hannunmu, idan muka gyara kammu shugabannin kansu tsoron 6atamana zasu dingaji, dansai kazama nagarine zamu za6eka mu kaika inda kake kwad'ayin, Ku gyara dan aza6e nagaba sonake naga MATASANMU ne governor's, kune Senate's president, kune house of Rives kune Minister's kune kune kune........!!!!".πŸ™‹πŸ»β€β™‚πŸ˜_

Gaba d'aya wajen yarud'e da ihun sowa, fad'i suke "ALLAH yaja zamaninka, yak'ara maka lafiya da yawancin kwana.......".
Saikuma suka koma wak'ar girmamawa agaresa (Ku saurara zan reromuku wak'ar kujiπŸ˜‚πŸ˜œπŸšΆπŸ»β€β™€).

'Daga musu hannu kawai Uncle yakeyi, bakinsa yakasa rufuwa saboda jindad'i da farincikin ganin wannan rana mai tarin tarihi a history nashiπŸ˜πŸ˜πŸ˜βœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœ‹πŸ».

Da k'yar sukayi shiru Alhaji Sabi'u shima yay nasa jawabin cikin girmamawa, dukdai gargad'ine akan karsu bari ayi amfani dasu wajen haddasa rikice-rikicen za6e, kowa yaza6i za6insa cikin lumana, kuma suza6i mutumin kirki bawanda zaiyi amfani da mulkiba ya ruguzasu suda k'asar baki d'aya, suyi amfani da shawarwarin shugaban wannan k'ungiya Alhjai Muhammad Ahmad Labbo, kada subari kud'i su rud'esu, dansu kwana kad'an zasu k'are, mutuncinsu dana k'asarsu kam yacigaba da sauka kenan harta koma babu abin moruwa, suduba gobensu da jibinsu bawai yau d'insuba, shima yagudanar da nasiha mai ratsa jiki, wadda tasaka matasan jinjinama k'ok'arinsa da yin na'am da wannan nasiha.
d'aya bayan d'aya shugabannin sukaita jawabi da nasiha ga matasan.
Taro yatashi lafiya Alhmdllh, su Uncle dole suka kwana Abuja dan sun kuma gudanar da taro isu-isu Na manyan k'ungiyar Na jihohin Nigeria baki d'aya.

Su Amatullah duk a NTA suka kalla live. kafin kacemi taron yazagaye kafafen yad'a labaran social media dana redio's television's, Jaridu, bawai a Nigeria kawaiba harma da k'asashen k'etare.
Dayawan 'yan SIYASA kam lamarin ya tsoratasu, tabbas matasan da gaske sukeyi gyara suke buk'ata 100%, gakuma sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci sunbama wannan k'ungiya goyon baya 100%................✍🏻



πŸ€©πŸ‘ŽπŸ»





One luvπŸ˜»πŸ˜»πŸ˜»πŸ˜»βœ‹πŸ»
[1/25, 5:58 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*πŸ’‘
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*


____________________
*_Number 46/50_*
____________________


Alhmdllh wannan lamari yakuma k'ara fiddo kimar Uncle a idanun duniya, nanfa wasu manyan k'ungiyoyin duniya na matasa suka fara gayyatarsa domin zama Na musamman, harma dawasu shuwagabannin k'asashe.
Uncle yazama babban gwaska, tauraro abin alfarin MATASANMU da k'asarmu, kowa burinsa yayi mu'amulla dashi, dolensa ya ajiye aikin dayakeyi a bayaro, dan nauyi yamasa yawa sosai, ga iyali ga aikin al'umma.
Dukda wad'annan nauye-nauyen hakan bai hanashi cigaba da tattalin iyalansaba, saima abinda yay gaba, suma kuma suna tattalinsa dabashi kulawa, kowacce tana kishinsa da k'ok'arin kafa babbar fada a zuciyarsa.
Duk d'insu yana yabama k'ok'arinsu da jinjinama halin dattakonsu, dan kishinsu shine yakamata asamu akowanne gidan aure, saidai yasan wani zafin kishin yakan had'a da zalincin wasu mazanπŸ™πŸ™„.

ALLAH dai ya shiryesu Uncle.



**************

Ana gab da za6e sukasha binkin Aysha da Dr yazeed, Wanda Uncle ne komai a bikin, duk wata hidima daya kamata iyaye suyi shine yayma Aysha, kuma baigazaba wajen zuwa takanas ya fad'ama danginta komai, harma da rok'onsu wasu sushiga lamarin auren, koba komai dai d'iyarsuce, kimarsa da halin dattako yasakasu nad'o gari zuwa bikin, tabbas jikinsu yayi sanyi daganin Goodness (Aysha) bata rasa komai Na rayuwaba, saima d'aukaka da ALLAH yak'ara mata, ga miji ga karatunta mai yankeba, Wanda fatansu tasha wahala sabida rashin tallafinsu, a haukarsu hakan zaisa tadawo addininsu, shiyyasa suka koreta, to Ashe Na kwarai basa k'arewa, saigashi ALLAH yaymata nasibi da samun wasu dagin masu k'aunarta.
Bata nuna musu komaiba, saima kar6arsu da nuna musu har yanzu sunada muhimmanci a rayuwarta, dan ba'a canjama tuwo suna.
Su Ama.... Sune amarori k'irjin biki.
Ahakadai taro yatashi lafiya, amarya tatare gidan mijinta, Innani harda hawayenta Na rabuwa da Aysha, dan harga ALLAH tana k'aunar yarinyar har cikin ranta.

To shatu ALLAH yabada zaman lafiya da zuria d'ayyiba.😻🀝🏻


************

Za6e yagudana cikin lumana da kwanciyar hankali kamar yanda su Uncle sukayi fata, Alhmdllh kuma ansamu biyan buk'ata daga matasan wajen za6en shugabanni Na gari masu kishin k'asar dason cigabanta.
Sannan matsan dayawa sunsami wasu fannoni Na madafun ikon k'asar , kamadaga ministers, Commissioners, da wasu fannoni daban-daban Na muk'amaiπŸ˜πŸ‘πŸ».


Saimuce ALLAH yatayaku rik'o😻.


******* ****** *******

Yau takasance Juma'a, tunda Uncle yadawo sallar juma'a shida yara bai sake fitaba, sukayi Lunch gaba d'aya kamar yanda yazama doka yanzu agidan, duk weekend tare sukecin abinci suda yaransu.
Sallar La'asar tasaka taron firar watsewa, Uncle da yara suka tafi masallaci su Aneesa kuma kowa tashige d'akinta.

Da sauri Amatullah tak'arasa gaban gadon ganin Raihana dake barci Na neman sakkowa, tatashi tuni, kasancewar yarinyar tanada matuk'ar hak'uri ko kuka batayiba, tagaji da wasa agadon shine tafara k'ok'arin sakkowa, ALLAH ma yakawo Ama... d'in datasha k'asa.
Dungure mata kai Ama... tayi tana fad'in "mamana dakin fad'o Aida kinjamin masifa wajen Uncle nasan bawai zai ragamin baneba".
Kamar Raihana taji mi Ama... ke fad'a saita ta6e Baki tana niyyar yin kuka, rawa Ama... tafara mata tana rera mata wak'a kamar yanda take musu itada Rayyan idan suna rigima.
Tuni Raihana tayi shiru takoma 6alle Baki tana dariya, Ama..... ta sauketa tana dariyar itama, yauwa Ammi Uwa mai dad'i, zauna kiyi wasa nayi salla kafin Rayyan yatashi shima, yau inada Shiga kitchen".

Idar da sallarta babu dad'ewa tajiyo kamar ana magana sama-sama daga babban falo, kuma tamkar muryar Aneesa.
Cire hijjab tayi ta d'auki Raihana dake wasa a k'asa tafita (dan tuni yaran sunama rarrafe).

" momyn yara lafiy......."
Maganar Ama... takatse lokacinda idonta ya sauka akan zee-zee dake zaune itada Rita dawasu 'yammata biyu Wanda duk Amatullah ta sansu amma ta manta sunansu.

Aneesa ta katseta da fad'in "kokin sansune Auntyn yara?".
Sosaima kuwa, aiduk school mate d'inane, ''amma lafiya kuwa Rita?".
Yatsine fuska Rita tayi tana wani taunar cingom, a yangance ta nuna zee.
Ama.... Ta maida kallonta ga zee d'in, ''Zainab lafiya?".
Saida Zee tamata wani kallon sama da k'asa sannan tace, "maigidan nazo nema".
Fateema dake fitowa tace, " maigidan kuma? shikam Nurri miya had'ashi da wad'annan masu kamada kilakin?".
Daga zee har muk'arabanta babu wacce ta tanka, saima taunar Cingom sukeyi, jikake k'ass! k'ass!! k'ak'as!!!.
Saida suka gama shan k'amshinsu sannan d'aya daga cikin 'yanmatan biyu tace, "Amaryarku ce tazo gaisheku ".
Kallon juna Aneesa da Fateema da Amatullah sukayi, Aneesa sarkin rashin hak'uri tafara lailayo musu zagi.
K'in tankawa sukayi, saima cigaba da iya shegensu sukayi.
Ana haka maigidan yadawo, kallon matan nasa dasuka tsareshi da idanun tun shigowarsa yayi, " lafiya kuma kukam?".
Aneesa Ce ta nuna masa su zee tana k'ara kumbura baki.
Gabansa yafad'i, azuciyarsa yace yarinyarnanfa ta gundureni, yanzu abin yakai harma gidana..........?
Fateema ta k'atse tunaninsa, "Nurri waisu waye sune?".
Kallonta Uncle yayi, sannan ya kalli yaransa dake tsaye cirko-cirko suna kallon iyayensu da wad'annan bak'i dabasu san kosu wayeba.
" Abulkhairi ja k'annenka kuje tsakar gida kuyi wasa, kar Wanda yadawo sai an kirasa".
"To Abbu".

Suna fita Uncle ya kalli su Zee.
" miya kawoku gidana Zainab?".
Kanta ta sunkuyar k'asa tana wani murmushi, "nagane kusan 2weeks baka picking calls d'ina shiyyasa nace bara nazo naga lafiya".
Tsayuwarsa yagyara sosai, hannayensa zube cikin aljihun blue d'in jallabiyarsa, ya fiddo d'aya yashafa gemunsa sannan ya maida, cikin sauke numfashi yace, " k'alau nake, kawai ayyukane sukamin yawa, ngd".
Yana gama fad'a yanufi samansa batareda yakuma kallon kowacce acikinsuba, harsu Amatullah d'inma.

Wani mayataccen kallo zee tabishi dashi, yanda ma yake taka steps d'in benen kawai abin birgewane, harya kai k'arshe kuma bai juyo ya kallesuba.
Su Aneesa suncika sunyi FAM, shin me mijin nasu yake nufine? Budurwar tasace kenan da gaske?.
Ai bak'inciki hana Amatullah maganama yayi, saita juya 6angarenta kawai.
Aneesa ce tafara masifa, "to gayyar tsiya arna a idi sai a tashi abar mana gida ko, tunda bana gado baneba".
Su Rita zasuyi magana Zee ta hanasu, tamik'e tsaye tana fad'in " kutashi muje, karku wani damu kanku, kwana nawane nazama matar gidan nima, kowacce shegiya acikinsu saita bar gidan da k'afafunta, dan nikad'ai nakeson kasancewa da abin sona, duk d'unsu basukai matsayin Na had'a kishi da sub.......
Dukan da Aneesa takaima bakinta yasakata yin shirun dole, tadafe baki "kai kai nikika dakarma baki?"....
" andaki bakin naki, Ku kama gabanku ma kafin mu jigataku a falonnan''. Cewar Fateema.
Kwafa su Zee sukayi suka fice.

Fasifa k'awayen nata suka hau yi bayan sun fita, akan miyasa bata bari sun koyama matannan hankaliba.
Tace, "kubarsu, lokacinsune, daga sanda nashigo gidan babu mai sake yin tari acikinsu, kudai kusaka ido kusha kallo."
Dariya suka shek'e da ita damata jinjina.

Koda su Zee suka fita sai Aneesa da Fateema suka nufi saman Uncle, a zaune suka iskeshi hankali kwance yana searching tasha a TV, sallamarsu kawai ya amsa batareda ya kallesuba, dan yasanma miya kawosu.
Fateema tace "wai yanzu nan Nurri wannan kuma wacece?".
Kallonta kawai yayi ya kauda kansa,
Aneesa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login