Showing 1 words to 3000 words out of 104242 words

Chapter 1 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16066

Compiled
By Aysha Galadima
Story and written by
D. Perfectionist
BILLYN ABDUL


[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_




*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*

*_HASKE WRITES ASSOCIATION_*
```{home of expert and perfect writer's} ```


( بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ )


Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.


*_ina mai farincikin sake had'uwa daku a sabon littafina akarona goma sha uku, ina rok'on ubangijin al'arshi yabani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar musulmai, yatsare harshena daga fad'ar abinda zai ruguzani nidaku😭🙏🏻._*


_ya ubangiji kakai rahama da gafara kabarin masoyina mahaifina, ALLAH ka gafarta masa ka yafe masa da dukkan 'yan uwa musulmai dasuka rigamu kwanta dama.😭🙏🏻_
*I love you so much my dear Abiena.*😭


*_wannan labari ba habaici baneba, bakuma gugar xana baneba, banyi domin kowaba saidan fad'akarwa da tunatarwa, ALLAH yasa afahimceni._*


_duk Wanda ya canjamin wani Abu aciki, komin k'ank'antarsa ban yafeba🙅‍♀._

_ALLAH katsareni daga cecekucen social Media🤕._

____________________
loading... *_Number 1_*
____________________


*_.......NIGERIA_* babbar k'asace katafariya dake yankin nahiyar Africa, itace k'asar datafi kowacce k'asa yawan al'umma da tarin arzik'i a Africa.
K'asace data k'unshi yawan k'abilu manya da k'anana. a nazarin masana, sun rairayo manyan k'abilun k'asar ta Nigeria da adadinsu ya haura 400+.
Gakuma Addinai daban-daban dasukeda mabiya, saidai Muslim's and Christian's sune sukafi rinjayen mabiya ak'asar.
Nageria k'asace dakeda 6angarori guda biyu, wato *_AREWACI DA KUDANCI_*, wannanne yakawo cakud'ewar k'abilunsu awaje d'aya, musamman awasu jihohi na kudancin k'asar da arewaci. saidai akwai wasu manyan k'abilu uku dasuka wawashi kaso mafi yawa nawasu jahohin k'asar.

*_"KABILAR HAUSA FULANI"_*

Suna da wasu manyan jihohin k'asar dazaka iya samun zallar wannan yare acikinsu, dukkuma girman k'abila tashiga yanki wad'annan jihohin yaren yakan had'iyeta, a wannan ga6arma zan iya cewa yaren Na Hausa Fulani, yacinye mafi yawan k'ananun k'abilu k'asar, Wanda ahalin yanzu sun daina yara yarensu sai dai Hausa, harshen Hausa har manyan k'abilun ma bai bariba, dan bak'aramin k'utse yayiba a yankunan k'asar ta NIGERIA, har wasu sunama iya kallon yaren amatsayin *General language* saboda mamaya dayayma k'asar Nigeria dawasu makwaftan k'asashen k'etare dake jingine da k'asar.

*Jihohin:- Kano, katsina, sokoto, gombe.*

Jihohine da ainahin yaran Hausa Fulani ke'a ciki.

*_KABILAR IGBO_*

Shima babban yarene dazai iya bugar k'irji a k'asar yakira kansa mai fad'a Aji, dukda ko Rabin yaren *Hausa fulani* bai kaiba, amma yarene dakeda d'unbin al'umma, saidai yafi k'arfine a yankin kudancin k'asar kawai, a kudancinma awani yanki, amma zaka iya samun wannan k'abila akowanne lungu da sak'o Na k'asar ta Nigeria, saboda yawan kutsa kai dasuke dashi a kowanne yanki na k'asar domin kasuwanci, harma dawasu k'asashen k'etare.

*Igbo sunada jihohin:- Anambra, Enugu, Abia, Imo, Ebonyi.*

*_K'ABILAR YORUBA_*

Yoruba babban yarene ak'asar ta Nigeria shima, Dan zamu iya cewa shima ya mamaye mafi yawan yankin kudancin k'asar, sannan wasu k'ananun yarurruka suna amfani da wannan yare, saboda kusantuwar k'abilunsu da yaren Yoruba, shima yarene mai d'aukeda yawan jama'a, suma babu laifi, sun k'utsa wasu yankuna Na k'asar ta NIGERIA, sannan sun wawashi wani babban yanki mai fad'a aji Na k'asar, Wanda yazama babban birni mai tarihi dasu Kansu yarabawan ke alfahari dashi, Dan k'asar ta Nageria kanta Na tink'aho dashi. *Lagos*

*Yoruba sunada jihohin:- kwara, Lagos, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ekiti, kogi.*

_________

Nasan a wannan ga6ar k'ila mai karatu zaiso jin wani d'an 6antare daga tarihin k'asar, hakanne zai bamu damar fahimtar mi labarin littafin *_"SIYASA KO KABILANCI!?"_* yazo mana dashi.
Karna jaku da nisa, ga bayani akan Nigeria mu a wani dogon k'arni, bisa ga bayanan masana Dana tattaro, Dan nasan mafiya yawan masu karatu, basuda jimirin bincike ta wannan fannin, alhalin abune mai muhimmanci da yakamata kowanne d'an k'asa yasani.


*_NIGERIA AWANI LOKACI._*


Turawan Portugal sune wad'anda suka fara harkar kasuwanci a Nigeria, a tashar ruwan dasuka baiwa suna Largo's data Calabar, a k'arni Na 17 zuwa Na 19.
Turawa sunringa shigowa da kayayyakin kasuwancinsu suna musayarsu da bayi a wannan lokacin, Wanda shuwagabannin wuraren ne kawai ke mu'amula dasu, kuma suke ribantuwa da kasuwancin nasu.
A shekarar 1807 burtaniya ta dakatar da cinikin bayin da akeyi a Nigeria, bayan biyowar yak'e-yak'en mallakar k'asashe, burtaniya takafa wata rindina a Africa ta yamma, a yunk'urin dakatar da cinikin bayi da k'asashen duniya keyi.
A shekarar 1884 zuwa 1885 aka gudanarda da wani babban taro a k'asar James, da ake kira da taron Berlin, inda aka kakkasa kasashen Africa zuwa yankuna daban-daban na mulkin mallaka.
Bayan taron. burtaniya tasamu yankuna da dama a yammacin Africa, Wanda Nigeriya naciki.
Har zuwa wannan lokacin, ikon turawa mulkin mallaka bai k'arasa Arewacin Nigeria ba, yawancin ikonsu ya karkata a kudancin k'asarne, da yankin iko da Legos.
A shekarar 1903 turawan sunsami nasarar mamaye Arewacin Nigeria, bayan tafka gumurzu tsakaninsu da sarkin musulmai Attahiru.
Turawan mulkin mallaka sun cafke sarakuna kamar sarkin Kano Alu, bayan dayak'i mik'a wuya, inda suka kulleshi a lakwaja.
Bayan wannanne kuma turawa suka samu mallakar yankunan biyu da yankin ikko.
Shekarar 1914 babban gwamnan jinar Frederick lugard ya had'a yankunan kudu da Arewa aka sakawa k'asar suna.
Sunan Nijeriya yasamo Asaline daga kogin neja bayan da a ranar 8 ga watan January Na shekarar 1897, wata 'Yar jarida wadda daga baya Frederick Lugard ya aura, dame flora Louisa Shaw, ta rubuta wata k'asida a jaridar *"The times"* ta England, kancewa yakamata asama k'asar suna Nigeria, wato *"Niger da Area "*, sabili da kogin Neja dayabi ta ta cikin k'asar.
Nigeria na makwaftaka da k'asar Benin, ta yammaci Chadi da Cameron, ta gabashi dakuma janhuriyar Nijar da arewaci.
Baki d'aya k'asashen da Nigeria ke makwataka dasu France ce ta mulkesu, inbanda arewacin Cameron da burtaniya ta mulka zuwa wani lokaci kafin France ta kar6a.
Tundaga wannan lokaci Burtaniya taringa gudanar da mulkin mallaka Wanda keda majalissar dokoki data k'unshi 'yan k'alilan daga cikin 'yan Nigeria.
Da tafiya tai tafiya an nad'a wad'ansu 'yan Nigeria dansu shugabanci wasu yankunan k'asar.
Wannan yak'ara basu ikon cin gashin kai, sai dai kuma hakan shine ummul aba'isin haifar da rikice-rikicen *ADDINI dana K'ABILANCI* a sassa daban-daban na k'asar ta Nigeria.
Bayanda turawa sukaga lamarin yak'ici yak'i cinyewa, sai sukai tunanin sake fasalta k'asar, inda suka kasata zuwa yankuna uku, *k'abilar Hausa fulani* Arewaci, sai *Yoruba* a yammaci, *Igbo* a gabashin k'asar.
Kodayake wannan tsarin yaraba 'yan k'asar, to amma kuma kowanne 6angare yasamu k'arfin fad'a aji a yankinsa.
Bayanda wad'annan manyan k'abilu uku na Nigeria suka sami karfin mulkar jama'arsu, dandanan sauran k'ananun k'abilun k'asarma suka fara Neman da abasu *'yancin su*, inda akaita rikice-rikice.
Domin asamu kwanciyar hankali a shekarar 1954 an cimma wata yarjejeniyar rarraba ikon tafiyarda ayyukan cigaban al'umma da cigaban k'asa, kamar kiwon lafiya, ilimi da dai sauransu, a tsakanin kabilun ko wanne yanki.
Itakuwa gwamnatin k'asa ke kulada harkokin tsaro da tattalin arzik'i.
Kodayake wannan baikawo k'arshen rikicin ba, har sai da aka kafa wata hukuma 1957 mai suna *Willink minorities commission*, Wanda ta duba k'orafe-k'ofen k'ananun k'abilu a wannan lokacin.
A shekarar 1953 Chief Anthony Enahoro ya gabatar da baiwa Nigeria 'yancin kai a shekarar 1957.
Sai dai kuma 'yan Arewacin Nigeria basu amince dahakanba, saboda k'arancin kwararrun dazasu tafiyar da harkokin mulki a yankin, dakuma gudun Cewar 'yan kudancin k'asar zasu mamaye harkokin gwamnati.
A wannan lokacinne akaita tura 'yan Arewa k'asashen turai musamman England domin yin kwasa-kwasai ta yanda zasu sami ayyukan kamar su akawu da akanta.
To domin samin zaman lafiya bisa wannan banbance-banbance ne aka amince da shekarar 1960 da za'a ba Nigeria 'yancin kai.
Bayan shafe shekara da shekaru 'yan kishin Nigeriya nata gwagwarmayar kwatowa k'asar 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya, a k'arshe hak'arsu ta cimma ruwa, inda ranar 1 ga watan October shekarar 1960 Sir Abubakar tafawa 6alewa yazamo prime minister Nigeria na farko ne yakar6i tutar 'yancin k'asar daga hannun governor general sir James Wilson Robertson, wada ya mulki Nigeria daga shekarar 1955-1960.
An gudanar da za6en farko a Nigeria, a shekarar 1959, koda yake, jam'iyyar NPC ta Arewa itace tafi samun k'uri'a a za6en, to amma yawan k'uri'ar data sami basu isa ta kafa gwamnati ba, abinda yasata kafa gwamnatin had'in gwuywa tareda jam'iyyar NCNC ta k'abilar Igbo.
Bayanda k'asar tasamu 'yancin kai a shekarar 1960 wad'annan jam'iyyu biyune suka kafa gwamnati, inda bisa tsari Sir Ahmadu bello sardaunan sokoto ya kamata ya zama prima minister, amma saiya marawa mataimakinsa baya wato Sir Abubakar tafawa 6alewa, Wanda ya zamo prime minister farko, shikuma Dr. Nmandi Azikwe governor general na farko a Nigeria.
A d'ayan 6angaren kuma jam'iyyar action group ko AG ta yarabawa wadda Abafemi Awolowo ya jagoranta ta kasance jam'iyyar adawa.
A kwai banbance-banbance addini da al'adu sosai tsakanin hausawan arewaci da Igbo a gabashi da Yoruba a kudancin k'asar.
Anyita samun rikice-rikice a gwamnatin had'in gwiwa, Wanda yakai ga rarrabuwar kai tsakanin wad'anda ke cikin gwamnatin.
Itama jam'iyyar adawa ta AG ta samu rarrabuwar kai a tsakanin 'ya'yanta inda a shekarar 1962 wani bangaren jam'iyyar *national Democratic party (NNDP)* wadda S.I Akintola ya jagoranta.
Rigingimun *SIYASA* sun mamaye gwamnatin wannan lokaci abinda yakai ga kafa yankin yamma ta tsakkiya, wato *Midwestern region* a shekarar 1963 daga cikin yankin yammacin k'asar.
Ranar d'aya ga watan October shekarar 1963 ne aka amince da kundin tsarin mulkin k'asar, kuma a wannan lokacinne Nigeria tazama member a k'ungiyar k'asashen renon England ko *Common wealth* kundin tsarin mulkin yasa Nigeria ta koma ga mulkin tarayya dake da shugaban k'asa da mataimakinsa, inda aka za6i Dr Nnamdi Azikiwe a matsayin shugaban tarayya.

A shekarar 1963 an gudanar da k'idayar jama'a wadda ya nuna yankin Arewa ne yafi kowanne yanki yawan jama'a a k'asar.
Sakamakon k'idayar ya janwo rikici tsakanin yankunan Nigeria, inda jam'iyyar NCNC take ganin anyi hakanne domin kawai aba yankin Arewa k'uri'a mafi yawa a majalissar dokokin k'asar.
Bayan da rigingimu sukak'ici sukak'i cinyewa sai sojoji sukayi juyin mulkin farko a ranar 15 ga watan Jenuary shekarar 1966.
Dr Nnamdi Azikiwe ; shugaban k'asar Nigeria na farko tsakanin 1963-1966.

Sir Abubakar tafawa 6alewa prime minister Nigeria na farko tsakanin 1912-1966.

Major general Johnson Thomas Uwunnakwe Aguliyi-ironsi. Shugaban sojan Nijeriya Na farko, ironsi ya kwashe tsawon kwanaki 194 yana k'aragar shugabancin k'asar.

General yakubu gawon.

General murtala ramat Muhammad.

Olusegun obasanjo yayi shugaban k'asar a mulkin soja tsak'anin 13 February 1976 zuwa 1 ga watan October 1979. Yasake zama shugaban k'asar a farar hula a 29 ga mey 1999 zuwa 29 may 2007.

Alhaji Shehu Usman Aliyu shagari turakin sokoto, shugaban Nigeria Na farko mai cikakken iko.

General Muhammad buhari ya mulki Nigeria daga 31 December 1983 zuwa 27 August 1985.

General Ibrahim badamasi babangida IBB, ya mulki Nigeria daga 27 August 1985 zuwa 27 August 1993.

Chief Earnest shoneko

General Sani abacha, yayi shugaban Nigeria a 1993-1998

General Abdussalam Abubakar, ya mulki k'asar a 9 ga June 1998 zuwa 5 ga may 1999.

Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa, yayi shugaban k'asar daga 29 may 2007 zuwa ranar 5 may 2010.

Goodluck ebele Azikiwe Jonathan 2010-2015.

Muhammad buhari a yau kuma a mulkin farar hula.

________________

Alhamdullah, wannan shine tarihin k'asarmu ta gado a tak'aice, Wanda keneman k'arin bayani, zai iya kwakwkwaran bincike ga masana, nidai iya abinda ALLAH yabani ikon tattarowa kenan a taskar masanan.😅

*yanzunne labarinmu zai fara kai tsaye*.

Plartoar state (jos)

Shima jihace data kasance a cikin yankin Arewa, sai dai tanada yawan k'abilu, sannan d'auke take da mabiya addinin Muslim's and Christian's.
Wannan yasaka yawan k'abilanci da rikice-rikice a yankin, mafiya yawan rikicin kuma *_SIYASA KO K'ABILANCI!_* ke haddasasu, amma bada wani nisaba saikiga yazama Fad'an *ADDINI*, shiyyasa al'umar wannan yanki ake yawan musu kutse wajen haddasa fad'ace-fad'ace.

Jos tana d'aukeda manyan k'abilu kamar haka.

Afizere, Afo, Alago, Anaguta, Amo, Ankwel, Bashiri (bashirawa), akwai kuma mafi yawan k'abilar Hausa fulani ma a jihar.

*Khadija Isma'il Uba (Amatallah)*

Itama tafitone daga wannan k'abila ta Hausa Fulani, wadda sanadin cirani ya tilasta musu maida jihar jos asalin jiharsu ta haihuwa, wadda zasu iya bugar k'irji su kirata k'asar kaka da kakanni.......✍🏻😅👍🏻





*_ALLAH ka gafarma iyayenmu🙏🏻😭_*
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡




*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 3_*
____________________


........Amatallah wai mikike tunani haka? tun d'azun kin saka abinci gaba kina jagwal-gwalasa kink'i kici?.
d'ago manyan idanunta tayi tana kallon Amminta, ta janye idanun nata saboda kwalla dasuka ciko, muryarta na rawa tace, "ALLAH Ammi na k'oshine".
" Amatallah banason shashanci fa wallahi, mikikaci dakika k'oshin? kofa abincin rana baki masa cin arzik'iba, lauma batafi hud'uba kika ajiyemin kika fita wai kina saurin islamiyya, shine yanzu zaki cemin kin k'oshi kuma........?".

"Miya farune kuma?". 'Baban Amatallah dake fitowa daga d'akinsa yay tambayar'.
Daga Amatallah har Amminta kallonsa sukayi. Ammin tace, ''abinda kasanine kullum dai, maganar cin abinci".
Guntuwar dariya yayi, yak'arasa cikin falon inda Amatallah ke zaune jikin kujera, a kujerar data jingina ya zauna, " haba mamana nikad'ai, ci abincin mana, babufa k'yau zama da yunwa, a haka kikeson zuwa hutun kano gidan Uncle d'in naki kuma?".
"Baba zanje, amma ALLAH na k'oshi". 'Tayi maganar tana matso hawayen datake mak'alewa tun d'azun'.
" subahanallah mamana, kuka kuma? kinga tashi ki maida abincin kitchen, kizo ga fura dana saya miki lokacin dazan dawo aiki".
Murmushi tayi tana share hawayenta, tamik'e da sauri tanufi kitchen da fleet d'in abincin.
Binta yayi da kallo yana murmushin shima.
Ammi kuma tace, "wallahi kaine ke saka yarinyarnan duk wata ta6arar datakeyi, nidai ina tuna muku halin rayuwa, kuma gidan wani zata". a k'ufule tayi maganar tana shigewa bedroom d'inta.
Baba yabita da kallo kawai yana girgiza kai, yasan gaskiya take fad'a masa, to amma bashida za6in daya wuce gatanta tilon d'iyar tasa, wadda tundaga kanta haihuwa tamusu adabo, shekara kusan 19 kenan amma ko 6ari matar tasa bata sake yiba. ajiyar zuciya ya sauke saboda motsin zaman Amatallah akusa dashi.
Tace, " baba nad'ako, nagode sosai, ALLAH yak'ara bud'i".
"Amin mamana, ALLAH yay miki albarka kinji".
''Amin baba".

Hirarsu suke d'anyi itada babanta, dama kullum haka sukeyi, sai dai yau hirar tasha banban data kullum, Dan yau duk akan abinda yafarune d'azun Amatallah take sake tisama baban nata labarin, muryarta kawai zata tabbatar maka har yanzu a tsorace take.
Ammi ma fitowa tayi tazauna, har kusan 10:30pm suna hira, kafin su tashi kowa yanufi d'aki yayi shirin barci.

Wata sabuwa Amatallah takasa barci, abinda yafaru d'azun yafara dawo mata dalla-dalla, saita ringa ganin su zike tsaye akanta da wuk'a, da sauri ta kunna fitilar d'aki, tashiga kalle-kalle, amma babu komai, duk da haka kasa barcin tayi, sai can cikin dare barci ya figeta.
A firgice ta farka ta kwalla wata razananniyar k'ara, saboda mafarkin datayi su zike sunzo har gida zasu kasheta.
K'arar tace ta farkar da iyayenta, arazane suka nufo d'akin, tana ganin su tafad'a jikin Amminta tana kuka, jikinta sai rawa yakeyi.
Abu kamar wasa k'aramar magana tazama babba, Amatallah takasa barci, takuma hana iyayenta, tun suna d'aukar lamarin wasa har ya fara basu tsoro, Dan Amatallah harda sumanta, kafin asuba kuma zazza6i yama jikinta rijif, maganarta ko fita da k'yau batayi.


__________________________

A gaggauce ta taimaka masa ya kimtsa cikin jallabiya Brown mai gajeren hannu, ya d'an fesa turarensa sannan suka sakko falon k'asa, yaran suna zaune suna kallon wani program na yara a wata tashar larabci, duksun maida hankalinsu sosai a tv n. dan har Abbun nasu yak'araso cikin falon basu saniba, jin jina kansa kawai yayi yana kallonsu da murmushi.
Matarsa ta ajiye k'aramin kwano mai d'auke da dabino a agabansa, sai ruwa a jug na glass.
Kallon dabinon yayi sannan ya kalleta, "no, nifa naci dabino a mota, bani ruwan dai".
Ruwan ta tsiyaya a k'aramin Kofi ta mik'a masa, ya kar6a yana mai fad'in " jazakallahu khairan my wify".

"Amin Nurrina".

Sai da ya shanye tas ya ajiye kofin, yana anbaton " Alhamdullah".
Tace, "saura abinci kuma".
" okey, had'amin, bara na duba jikin Saifuddeen".
Bai jira amsartaba yanufi 6angaran amaryarsa.

Tana zaune a falonta, nono take bama Siddiqa, gefenta kuma ga wani yaro zaune yana kuka da Kofi k'arami a hannu, da alama tsaresa tayi dole yake shan abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login