Showing 48001 words to 51000 words out of 104242 words

Chapter 17 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16044

Tace, "ALLAH uncle inajin kunya".
" my best! to miye najin kunyar?, nifa Uncle d'inkine, ko yanzun an daina Uncle d'in dani sai mij......"
Bai kai k'arsheba ta waro manyan idanunta a kansa.
Shima saiya waro nasa kamar yanda tayi yana murmushi har hakwaransa Na bayyana a fili.
Yunk'urawa tayi zata tashi danta gudu ya rik'e hannunta yana fad'in kinga wasa nakeyi, muje kici abinci, kowa ya hallara babu ke, har Fateema Na tambayarki taga bakizo mata sannu da zuwaba".
"Uncle azumi nakeyi ai".
" azumin me my best? Yaufa Saturday?".
Rasa mizata cemasa tayi, dankuwa k'arya ta mullik'a babu wani azumi, tana dai jin kunyar fitane saboda kwalliyarta.
Hakanne yasa yagane k'arya take.
Mik'ewa yayi itama ya mik'ar da ita tsaye.
Ta marairaice masa fuska kamar zatayi kuka, "wayyo Uncle da gaskefa nakeyi".
Baima San tanayiba, dan kallonta yake daga sama har k'asa, bak'aramin zama kayan sukayi a jikintaba.....
Ganin hankalinsa bama kanta yakeba ta girgiza hannunsa dake rik'eda nasa.
Kallonta yayi da sauri, yace, " mikikace my best!?".
A shagwa6e tace, "kai Uncle kana nufin baka jiniba ma?".
Kasa amsata yayi, yaja hannunta dan yakula inhar suka kai wani lokacin a falonnan zai iya kauce hanya ya aikata abin kunya....
''Uncle please zanje da kaina, ALLAH zanma ci abinci". Amatallah tayi maganar da sauri dan ganin da gaske soyake ya kaita har falon yana rik'eda hannunta.
Baice mata komaiba ya saki hannunta, fitowa sukayi yana gaba tana bayansa, dan haka ta 6oye sosai a bayansa.
Fitowarsa yasaka Fateema da Aneesa d'agowa suna kallonsa, kowa da dalilinta na kallonsa da son suga Amatallah d'in.
Anty Maijidda tace, " a'a Yaya lafiya dai ko? ina Amatallah d'in to?".
Juyawa yay a zatonsa bata biyoshiba, sai ya ganta a bayansa, tana famar 6uya, matsawa yayi gefe yanda zasu ganta yana fad'in ''k'alau take, kunyarku takeji saboda tayi.....". Sai kuma yay shiru ya k'are maganar da 'Yar dariya yana zama a kujerar daya tashi wadda Aneesa da Fateema suka sakashi tsakkiya.
Amatallah jitai tamkar ta nurse k'asa dan kunya, Fateema da Aneesa duk sukad'an waro idanu kanta cikin mamaki da ganin k'yan datayi.
Aneesa Na mamakin yaushe Amatallah ta koma haka?, Fateema kuma Na mamakin canjawar Amatallah d'in a watanni hud'u.
Nazeefa kam cikin nuna kamar batasan da kwalliyar Amatallah d'in ba tace Woow!! Amatallah, wannan wanka yayi, kinfito a amaryarki".
Jabeer da Shehu da Anty Maijidda da Uncle duk dariya sukayi, yayinda wani kishi ya tokare mak'oshin Aneesa da Fateema.
Amatallah komawa tayi baya da sauri tashige bangarenta.
Nanfa duk aka saka mata dariya, harda yaran.
Nazeefa tashiga kwala mata kira, amma sai Uncle yace "barta Nazeefa, haka Khadija take da kunyar tsiya".
" Yaya ai bataci abincin bafa".
" 'Diba ki kai mata kawai, kowama yakamata yay saurin kammalawa yanzu zakuji magrib".
Duk da to suka amsa.
Nazeefa ta d'iba komai dai-dai misali Dan tasan Amatallah batada cin abinci sosai ta kaimata. Har Nazeefa tashiga ta fito Amatallah bata yarda sun had'a idoba, dariya Nazeefa tayi kawai tafito abinta.

Suna mammala cin abinci mazan suka wuce masallaci, Matan kuma sukayi agida.
Su Uncle basu dawoba sai da sukayi sallar isha'i.
Koda suka dawo basu zaunaba, shidasu shehu da Anty Maijidda suka tafi gidan iyayensu danya gaishesu, harda Nazeefa Dan tace bazata kuma kwanaba kuma, ba lallashin da Uncle bai mataba tace, a'a.
Anty Maijidda tace yabarta, gara ta tafi. Saboda yanayin zaman gidan nashi ba mace d'aya bace, idan ta nuna kusancinta da d'aya sai yazama abin magana, sukuma zaman lafiya mai d'orewa sukema gidansa fata.
Badan ya soba suka tafi gaba d'aya. Daga innani har baba sunyi farincikin ganinsa sosai, sai dai innani ta danne abinta a zuciya kamar yanda ta saba masa.
Sunsha hira, Dan saida baba yace yaje gida ya huta, gobe idan ALLAH ya kaimu yadawo suyi hiran. haka ya tafi badan hira da iyayensa da 'yan uwansa ta isheshiba.

Tunda suka fita Aneesa tashige 6angarenta, aka Shiga k'imtsa jiki.😜
Fateema ma 'ya'yanta taja suka shige Nata 6angaren, Dan k'anwarta zaliha tazo Tamata gyara tun jiya da safe.
Lokacin daya shigo gidan tsit kamar babu kowa, a tsakkiyar falon ya tsaya yana Mazarin INA yakamata yafara Shiga?, wajen Fateema, ko Aneesa, ko Amatallah?.πŸ˜‚πŸ€...........✍🏻





πŸ€©πŸ‘ŽπŸ»

One luvπŸ₯°


_Dan ALLAH idan mutum ya tambaya daga farko maishi yaringa tura mishi, ku Na tausayimin mana, kodan k'ok'arin muku typing danake kullum, abubuwan sunmin yawa, banason kuma masoyina yaga Na wulak'antasa wlhy ko kad'an, Duk masoyina Na gaskiya nasan zai taimakeni._😊🀝🏻








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*πŸ™πŸ»πŸ˜­

[1/16, 9:01 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*πŸ’‘
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ceπŸ€™πŸ»_*



*_Jiya maganar gaskiya naci dariyar Comments naku over, dan naga zanga-zanga kuka shirya yimin akan kwanan Amatallah jiyaπŸ˜‚, especially 'yan Group d'ina da Group d'in party, sai Kundin Haske da Group na Manshat , sai dai network yamin iya shege, amma ngd sosai walhy, ALLAH yabar zumunci, bilyn Abdull Na yinku irin Trillion's d'innan, I love you wujiga-wujiga._*πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ€πŸ»πŸ‘πŸ».


____________________
*_Number 21_*
____________________

Yadad'e tsaye yana canki canka, daga k'arshe dai yashiga 6angaren Amatallah, babu kowa a falon sai dai k'amshi mai dad'i dake tashi, tsayawa yay kallon falon, Dan d'azun ta rikitashi bai kalli komaiba, komai yayi k'yau yanda ya kamata, cikin yabama k'ok'arin k'annensa Na za6o abinda yay dai-dai da ra'yinsa shida Amatallah yashiga bedroom d'in. nanma babu kowa, amma ko ina tsaf yake kuma k'al, gadon yasha gyara, ga ta saka filolin a wani style mai k'yau, guntun murmushi yayi kafin yamaida kallonsa ga bathroom inda yake jiyo motsin ruwa alamar wanka takeyi.
Juyawa yayi yafita kafin tagama ya dawo.
Saiya shiga 6angaren Aneesa.
Tana zaune abakin gado cikin wata rigar barci jaa datayi masifar mata k'yau da haska farar fatarta, Siddiqa takema shirin barci, Saifudden Na kwance a gadon haryayi barci.
Tsayawa yay kwai yana kallonta danba k'aramin k'yau tamasa ba a rigar barcin, cikin wani salo ta d'ago idanunta tana kallonsa tareda d'an fari.
Murmushinsa mai k'ayatarwa yasaki, yataka a hankali zuwa gareta, dai-dai ta shinfid'e Siddiqa a gadon.
Ta baya ya rungumeta cikin kunnenta yace, "zaki kasheni da salonki my Neesa".
Dad'i ya kamata, ta juyo sosai suna fuskantar juna, sai kawai ta fad'a jikinsa suka rungume juna tsam, tace, " I miss u so much my Dear".
"Me too my Neesa". yafad'a yana d'ago kanta, bakinsu kawai ya had'e waje d'aya, yashiga mata wani salo mai rikitarwa.
Su duka sun haukace, kai kace yau suka fara ganin juna, sai da Uncle yaga abin zai zarta sannan yacire bakinsa a nata, ya kuma rungumeta da k'yau a jikinsa suna maida numfashi. kusan mintuna biyu sannan yace, " My Neesa kinsanfa yau niba naki baneba, Na Amaryane".
Idontane yacika da kwalla, yanzu kam ba zafin kishi bane kawai, harda tsananin buk'atuwar da take ciki, wata hud'u ba wasa baneba, takuma k'ank'amesa kamar mai gudun arabasu, (dukda tana buk'atarsa bazata ta6a cemasa karyaje wajen matarsa ba, duk zafin kishinta bata fatan shiga hak'k'in wata a abokan zamanta).
Jin laimar hawayenta a k'irjinsa saita bashi tausayi, yasan yanayin Aneesa sosai, wata hud'u ba wasa baneba kuma agareta, Dan baita6a nisan kiwo basa kusa dashiba kamar haka.
Jin yana k'ok'arin d'ago kanta saitayi saurin share hawayenta, koda tad'ago saita masa murmushi, murmushin shima yamata, yasa hannunsa biyu yakamo kumatunta, cikin kuma k'asa da muryarsa yace, "sorry my Neesa, ban fad'a Dan wulak'antaki ba, saidan kawai hak'intane Na sauka a wajenta, kuma namata kwanaki 7 kamar yanda yake a shari'a, amma karki damu zan nema mana mafita idan kin amince".
A sanyaye tace, " wace mafitace dear?".
Lumshe idanunsa yayi tareda kissing la66anta sannan yace, "zanje Na rok'i Khadija tabamu kwana d'ayannan kawai domin Na kwaranye miki k'ishinki".
Ajiyar zuciya tasaki sannan tagyara tsayuwarta tana fad'in " a'a dear, itama anshiga hak'inta kenan ai, nida ita duk Abu d'ayene a wajenka, maganar wadda kafiso wannan a zuciyarka yake, tsananin k'aunarka da kishinka danakeyi bazaisa na jagoranci abinda zaisa katashi ranar kiyama da shanyanyen jiki har Na kaika wuta ba, insha ALLAH zanyi hak'uri har tayi kwanakinta, amma kasani INA matuk'ar Sonka da kishinka, harma nakanji nafi kowacce mace Sonka da kishinka a duniya".
Tausayi tabashi, Dan haka Yakuma d'ora bakinsa kan nata batareda yayi maganaba, yashiga kuma nuna mata tsantsar soyayyarta dake cikin zuciyarshi shima. Sunja adadin wasu lokuta kafin Aneesa ta janye jikinta da k'yar, kan gado kawai ta haye ta kwanta tareda juya masa baya.
Yasan kuka takeyi, Dan haka baice mata komaiba yajuya yafita jiki a sanyaye. Samansa ya haye, yaje yay wanka da shirin barci. Babu dad'ewa ya sakko.
6angaren Fateema yashiga, takashe komai Na falon, sai fitilar wayarsa ya kunna, d'akin yaran yafara Shiga yaga babu kowa, hakan ya nuna masa suna tareda ita kenan, d'akintama fitilar a kashe take, data wayarsa ya haska ya hangosu a kan gado sun jeru suna barci, murmushi yayi ya k'arasa garesu yana ayyana soyayyar uwa da 'Yaya a zuciyarsa.
Duk saida yabisu d'ai-d'ai yama kowa kiss a goshi, Fateema kam harda d'an tsotsar la66anta sannan yama cikinta da wuyanta kisses yamusu addu'oi yafita dukda yasan Fateema tamusu suma yaran tasakasu sunyi.

Amatallah tunda tafito wanka taji kamar k'amshin turaren Uncle, gabantane ya fad'i, cikin sand'a ta lek'a falo azatonta yana can, ganin wayam babu kowa tasaki ajiyar zuciya sannan tadawo. Zani ta d'aura tasaka hijjab tayi shafa'i da wutiri, idarwarta kenan tacire hijjabin ta d'ora saman gado, tabud'e Waldrop danufin Neman kayan barci yay sallama, ba k'aramin tsorota tayiba da ganinsa, taja hijjab d'in data cire tasaka da Sauri duk da yama Rigada ya shigo d'in, Yakuma ganta a yanda bata son.
Murmushi kawai yayi, ya k'arasa bakin gadon ya zauna.
Kanta a k'asa tamasa sannu da zuwa.
Idonsa a kanta yace, "yauwa my best! Kin daina kukan tafiyarsu Nazeefa ne?".
Kwallace tacika idonta, ta d'ago kad'an ta kalleshi ta duk'ar da da kanta.
"Kukan dai kuma?".
Girgiza kai tayi da sauri.
Zamansa ya gyara yana nunu mata kusa dashi, " zoki zauna naji to".
Dukda tanajin kunya haka ta zauna amma d'an Nesa dashi. Idonsa akan yatsun hannunta dake d'aukar hankalinsa yace, "to, ya school?".
" Alhmdllh Uncle".
"Masha ALLAH, babu dai wata Matsala ko?".
Kanta ta girgiza masa da fad'in " eh uncle".
"Alhmdllh ai haka akeso, zuwa da safe Na duba Nagani idan da gaskene, yanzu alfarma nazo nema".
Cikeda mamaki ta kalleahi, " uncle! Alfarma kuma? a wajena?".
Kansa a jinjina mata fuskarsa d'aukeda guntun murmushi. "Alfarmar kwananki nake nemama Aneesa".
Ko kad'an Amatallah bata fuskanci inda maganarsa ta dosaba tace, Uncle ban ganeba ai".
Shiru yayi yana nazarin tayaya yakamata yamata bayani, sai kuma yamatso kusada ita sosai, hakanne yad'an sakata jin tsoro heartbeat d'inta Na k'ara gudu, kamar zatayi magana saikuma tayi shiru.
Duk da ya fuskanceta hakan bai hanashi kamo hannunta ba ya saka a nasa, " uhm INA nufin kibari yau Aneesa ta kwana d'akina".
"Wayyo Uncle, ni mizai sakani Na hana Anty Aneesa kwana d'a......."
Saikuma takasa k'arasawa saboda maganar Tamata nauyin fad'a.
'Dan murmushi yayi, aransa yace tunda kinsan ma'anar kwana d'akin nawa, a hankali abinda nake nufinma zaki gane ai. a fili kuma yace, "Nasani bazaki hanataba, amma hak'inkine ai".
Zuwa yanzun kam Amatallah tagama fuskantar Inda Uncle d'inta ya dosa, amma nauyin maganar bazaisa ta ta6a nuna masa ta ganeba, saima mamakinsa take a zuciyarta dukda shima azancen NASA akwai salon alkunya tunda bai fito kaitsaye ya nuna mata manufarba.......
Katseta yayi da fad'in "kinyi shiru Khadija".
" Uncle nidai dukda bansan miyasa kake son hakanba Na amince ta kwana wlhy". Tayi maganar a kunyace.
Murmushi yayi tareda sumbatar bayan hannunta, yace, "ALLAH yay mini albarka Khadija".
Shi duk zatonsa Amatallah da gaske bata gane Inda ya dosaba, Dan kallonsa k'aramar yarinya shataf yake mata.


Nidai nace, " hummm Uncle kenan, shekarar Amatallah 20 yanzu ace batasan miye aureba?, bayan yanzun yaramu sai dai addu'a, 'Yar shekara 15 saita baka labarin mi ake a gidan aure tsaf, in kayi wasa takuma fad'a maka komai dalla-dalla, ai wayaπŸ“± babu masifar dabata kawo manaba a wannan zamanin, sai dai kawai wad'anda ALLAH ya tsare, amma jeka Facebook kawai kaga ta6ar6arewar tarbiyyar yaranmu.😭
Kama godema ALLA daya baka Amatallah d'in mai kunya, yanda idanun 'yan matanmu ya bushe yanzu suka d'au kunya k'auyanci ai abin ba'a magana, ALLAH dai ka shiryamana zuri'a kawai.πŸ™πŸ»

Mik'ewa yayi yana fad'in "tom tashi ki kwanta namiki addu'ar barci".
Kanta a k'asa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta tace, " Uncle ai bansa Sleeping dress".
"Okay, to tashi kisa ka".
Shiru tayi kamar bazata tashiba sai kuma ta mik'e ta koma wajen Waldrop d'inta ta ida zaro kayan data fara d'auka d'azun. duk Uncle yana tsaye yana kallonta. toilet d'inta tashiga dan ta Sanka.
Murmushi yayi yana shafa gemunsa, a ransa yanajin k'aunar Amatallah da yanda take komanta a nutse, wani lokacin idan tayi Abu yakanga tamkar brother d'insa (to jini ba k'arya baneba aii Uncle).
Yana nan tsaye harta fito, kallonta yayi, dukda tasaka Riga da wando na barcin, hakan bai hanata sanyo hijjabin ba a sama.
Tsaye tayi a bakin k'ofar kanta a k'asa.
Yace, " zoki kwanta mana, ko zakiyi wani abunne kuma?".
Kanta ta jinjina masa alamar a'a.
"Ta kowa yayi a hankali har inda take, ya kama hannunta batareda yace komaiba, har gaban gadon sukaje sannan ya saki hannunta yana nuna mata gadon da yatsa.
Bata yarda ta kalleshiba ta hau gadon ta kwanta bayan ya gyara mata filon.
bargo yaja ya lullu6a mata zuwa k'irjinta sannan ya rankwafo saitin kanta daf. ita dai Amatallah kallon ikon rabbani takeyi, da girmanta an maidata baby.
Hannu yasa cikin bargon kad'an yafara tattara hijjabin jikinta, a hankali ya furta "d'aga my best a cire wannan hijjab d'in, babu k'yau kwanciya da hijjab, zai iya kawo matsala ga mai barci, kamar shak'e mutum da makamancin hakan".
Kanta ta jinjina masa a hankali, Dan yanda ya rank'wafo kanta saitaji kamar zai fad'o mata, har saukar numfashinsa tanaji, taimaka masa tayi yacire hijjabin, kafin ya ida cirewa tayi saurin Jan bargon ta rufe k'irjinta.
Yana kallonta, dan haka yay dariya a zuciyarsa kawai. yana gama cire mata hijjabin ya ajiye gefe ya zauna kusada ita a bakin gadon. addu'oi yamata kamar yanda yakema sauran matansa, ya tofa mata a hannu ta shafa itama da wanda tayi, mik'ewa yayi yasake rankwafowa ya gyara mata bargon, sannan yamatso da fuskarsa daf da tata, hakanne yasaka Amatallah saurin rintse ido dad'an k'ank'ame jikinta zuciyarta tana kuma bugawa da k'arfi saboda kusantowarsa garesa sosai.
Kiss ya manna mata a goshi da kumatu, sai kuma ya dakata yana kallon fuskarta da yanda take k'ara k'ank'ame ido, yanda tayin saita bashi dariya harya murmusa, yace, " bud'e idon mana my beat ki kalleni".
"Ya salam" tafad'a a zuciyarta tareda mamakin wannan lamari na Uncle, tana masa kallon salihi Ashe shima A ne na bugawa a jarida.......
Batakai k'arshe. Tunanin taba taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login