Showing 45001 words to 48000 words out of 104242 words

Chapter 16 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16051

tafiya cikin Nasarori da jarabawa, yau kwanakin Amatallah hud'u agidan Uncle d'inta.
Kullum da safe takanje har d'aki ta gaida Fateema, ta taya Nazeefa aikin gidan tana k'ara nuna mata komai yanda zatayi, Dan Fateema bata iya aikin saboda laulayin datake fama dashi, dama ita haka take fama a farkon kowanne ciki.
Ita Nazeefa ma hakan dad'i yamata, Dan koba komai Amatallah zata kuma koyon abubuwan dasuka dace sosai takuma kware da wahalaryi kafin mijin nasu ya dawo.
Yaran kuwa sun maida 6angaren Amatallah nanne wajen zamansu, itakam jansu takeyi ajikinta sosai, Dan tana kallonsu tamkar k'annenta, kuma hakan Na sakata Nishad'i sosai, saboda ta tashi ita kad'ai kwallin kwal a gidansu, babu Yaya babu k'ani, su Ammine komai nata, shiyyasa shak'uwa tashiga tsakaninsu sosai wadda taketa wahal da ita har yanzun.
Uncle kam yana kira a wayar Nazeefa yace abata, wani lokacin dataga Nazeefa da wayar saita shige toilet d'in k'arya, har sai yagaji ya kashe, sai idan Nazeefa ta rutsatane sanan take amsar wayar.
Ganin kamar yana takura mata saiya rage kiran, koya kira Nazeefa baya cewa abata.

Aneesa kam bayan tagama fushinta ta sakko Dan kanta batareda ya kula da lamarintaba, danshi tausayi da dariya take bashi..


*_one Week ago_*

Sati d'aya cif da tarewar Amatallah tafara zuwa school, Jabeer dakansa yakaita a motar Uncle.

Sanye take cikin shigar mutunci, dantasha gargad'i wajen Uncle sosai. Atanface siket da riga porpul mai haske da ratsin pink kad'an da bak'i, saita saka pink d'in hijjabi mai hannu iya gwiwa, ta saka d'an abubuwan dabaza'a rasaba a cikin pink d'in lady's bag, takalman tama flat pink, duk da bawata kwalliya tayiba tayi k'yau sosai, sai k'amshin turarenta marar k'arfi dake fita k'ad'an, inba ma kusada ita kakeba bazakajiba kam.
Gaba ta bud'e zata shiga Jabeer yace, "a'a shiga baya abinki Amatallah".
Kunyace ta kamata, ta duk'ar dakai tana murmushi, a hankali tace, " a'a Yaya Jabeer, kabari Na zauna a gaban kawai, kaiba driver d'ina bane".
Murmushi kawai yayi shima, yabud'e mata murfin motar tashiga gaban sanan yatada motar suka fice daga gidan.

Motar tayi tsit, babu mai magana acikinsu, Jabeer yamaida hankalinsa ga tuk'i, itakam Amatallah kalle-kalle kawai takeyi tana sauraren redio daya kunna har suka shiga cikin BUK.
Tunda suka shigo take addu'oin Neman nasara a rayuwar wannan makaranta dazatayi.
Guri Jabeer yasamu yay parking, har Amatallah zata fita yace, "ki kunna wayarki Ya Muhammad yace zai kiraki".
Kanta ta jinjina masa batareda ta juyoba.
Atare suka fito, Amatallah nata kallon mutane dake kai kawo, wasu 'yan mata da samari wasu kuma samari zalla, wasu 'yan mata zallah, kowa dai da abinda yakeyi. wasu kuma daga cikinsu duksun zuboma su Amatallah idanu, hakanne yasaka Amatallah duk'ar dakai, Dan ita irin mutanen nanne da basu cika son taron jama'a ba.
Jabeer ya kalleta yace, " muje".
gaba yay tabishi abaya har zuwa wani Office. sai da yayi Knocking aka bashi izinin shiga sannan yashiga Amatallah Na binsa abaya.
Mutumin dake zaune a office d'in wanda da alama shine mamallakin office d'in koda ba'a fad'aba, ya fad'ad'a murmushinsa da fad'in "Jabeer kun iso?".
Jabeer ya amsashi da " eh yaya Lawan".
Ta gefen ido Amatallah ta kalleshi, shima dai zai iya kaiwa sa'an Uncle d'inta. sai dai yafi Uncle k'iba sosai, Dan zaima iya ninkashi biyu.....
Maganarsace ta katse mata tunani, ta kalleshi da Sauri saikuma ta kauda kanta, zama tayi kujerar dayake nuna mata. bayan zamanta ta gaidashi a ladabce. Shikuma ya amsa cikin fara'a.
Sun tattauna da Jabeer, aka bata wasu takardu tasaka hannu sannan suka masa sallama suka fito.
Har department d'insu Jabeer ya rakata, ya d'an mata bayani sannan yamata sallama yatafi bayan yabata 1k, yace bayan sun gama takirashi.
Kanta ta jinjina masa tayi godiya.
Tafiyar Jabeer babu dad'ewa wayarta tafara wringing, Jakarta tabud'e ta lalubo phone d'in, ganin sunan Uncle saida gabanta yafad'i, d'an wawwaigawa tayi Dan Neman inda zata zauna. A dakalin barandar wajen taje ta zauna, dan taga wajen yanada tsafta, ta d'aga wayar tasa a kunne.
Sassanyar muryarsace tamata sallama.
Itama a sanyayen tace, "wa'alaikassalam, Uncle ina kwana".
" lafiya lau my best, amma mu munshiga yini nan, ya Ku isa makarantar?".
"Eh Uncle, harma Yaya Jabeer yatafi".
"okay, to babu wata dai matsala ko?".
" eh Uncle, komai normal".
"To Alhmdllh, saikuma a dage, banda wasa da k'awayen banza please my best! Kinji, banda biyema samari dan ke matar aurece kin sani".
Idontane yacika da kwalla, itafa kokad'an batason atuna mata wai tanada wani aure, aurenma Na Uncle d'inta.........
" kuka kikeyi ko my best!? ".
Da sauri ta share hawayenta, tace, " a'a Uncle ina jinka".
''Imyiim, bagashi naji muryarki Na rawaba".
"Uncle murace kawai keson kamani".
" kokuma Uncle akeson yima wayo ba, anyway koma dai Yaya kiringa tuna alk'awarin da kikamin na kin daina kuka".
Kuma share hawayen tayi, sannan tace "to Uncle, insha ALLAH bazaka sake jiba".
" haka kullum kike fad'amin ai, amma kin kasa cika alk'awari".
"To kayi hak'uri Uncle, zan kiyaye yanzu. yasu Anty da siddiqa?".
" suna gida lfy lau, ni ina school ne".
"Uncle inka koma ka gaida minsu".
" zasuji insha ALLAHU, yanzu ki samu wata a wajen saiki tambayeta inkunada Lecture by this time kinji".
"To Uncle sai anjima".
''Ok bey bey my heartbeat".
Da sauri tace, " Uncle!".
''Yace uyim, yayane? kobaki yarda ke heartbeat d'ina bace?". A wani salo yay maganar.
Da sauri ta yanke wayar, shikuma ya tuntsure da dariya daga can.


Nima dai Na tayaka Uncle🤣, nasan Fans ma zasu tayamu🤩👎🏻.

Amatallah tana yanke wayar ta rik'e ha6a tana fad'in "o ni Khadija, dama haka Uncle yake?".

Amatallah kad'anma kika gani indai Uncle ne😂.

Mik'ewa tayi tana cigaba da juya lamarin Uncle d'inta a zuciya, harta k'arasa wajen wata dake zaune can gefe itama cikin shiga ta kamala, aganinta ita kad'ai ta dace tama tambayar da Uncle yace tayi, dan tun tana waya taga wucewarta har zamanta awajen.................✍🏻



🤩👎🏻


One Luv my sweet Fan's🥰








*_ALLAH yajik'an iyayenmu._*😭🙏🏻
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



_masoyanmu Amanna afuwa dajin *YAR SARKI CE* shiru, wasu 'yan dalilaine suka kawo hakan, amma insha ALLAH zata cigaba🥰🥰._


____________________
*_Number 20_*
____________________

Wani Saloon Ya Jabeer yakai su Amatallah, a can suka iske Anty maijiddah, itadai Amatallah sai mamaki take a k'asan ranta.
Babu 6ata lokaci wata farar mata tajata wata k'ofa, Ashe cikin gidane, koda suka shiga saita kaita wani d'aki, zani tabata tace tacire kayanta tana zuwa.
Amatallah dai mamaki dukya kasheta, amma duk abinda aka sakata babu musu takeyi, tasan Anty maijidda dai bazata cutar da ita ba.
Tana gama cirewa babu dad'ewa matar tadawo da kwa6a66en Abu a boket k'arami.
Mik'a mata boket d'in tayi, tace, "dan ALLAH karki cutar da kanki, ki tabbatar ko ina Na jikinki yasamu, bayan kin gama murje jikinki saiki shafa wannan shikad'ai a fuskarki wannan kuma bayan kin gama zanzo nasaka miki a gashi. daganan kishiga nan cikin, ta nuna mata wani k'aton bambu da aka saka wani Leda.
Kai Amatallah ta jinjina mata.

Duk yanda matar nan tasakata haka tayi, abun sai wani masifar k'amshi yakeyi, haka dai tagama murje ko ina najikinta tashiga banbun kamar yanda matar tace, kusan mintuna biyar da kammalawarta matar tayi Knocking k'ofa da tambayarta ta kammala.
Amatallah ta amsa mata da eh.
Shigowa tayi, taga Amatallah tayi yanda duk tace, taji dad'i, dan haka tafara shafa mata d'ayan abun a gashinta, tana gamawa tasaka bak'ar Leda ta d'aure mata kan, tafice ta barta.
Sai da Amatallah tayi kusan awa biyu sannan matar ta shigo tahad'a mata ruwan d'umi da k'amshi, sai wani sabulu tabata tace tayi wanka.

Indai tak'aice muku sosai Amatallah tasha gyara a d'akinnan, kusan awa 3 sannan suka dawo ainahin wajen saloon d'in, su Anaty maijidda sai yaba k'yan da tayi sukeyi, Nazeefa harda tatta6ata.
Itadai Amatallah murmushi taitayi, ita kanta tanajin canji Na musamman a jikinta.
An kuma wanke mata kai aka gyara matashi, sanan aka mata kunshin Jan lallale da bak'i.
Dole ka ganta kasan Amaryace, tahad'u sosai abin harma ba'a magana, ga wani sirrin k'amshi Na musamman.
Basubar saloon d'inanba saida aka yima Amatallah simple makeup mai burgewa, ba'a cikashi d'inanba yanda zai canja mata kamanni, amma tayi k'yau masha ALLAH.
bayan matar nan ta had'ama Amatallah wasu kayan gyaran jikin dazata ringayi a gida suka tafi.
Anty maijidda gidansu ta wuce, Jabeer kuma ya maida Amatallah da Nazeefa gida.
Kusan k'arfe 3:26pm lokacin, kuma ALLAH yasosu Aneesa bata dawoba.

Dawowarsu babu dad'ewa sukaji dawowar Aneesa, itama gyaran jiki taje, takumayi k'yau sosai wlhy, sai shek'i da walk'iya takeyi kamar amaryar itama.
Batawani 6ata lokaciba tashiga ketchin, dama kafin ta fita ta tanaji komanta, had'awa kawai zatayi.
Nazeefa Ce tafito ta tayata komai, danta hana Amatallah fitowa. Tace baza'a ganta ba a waje sai su Uncle sun shigo gidan.
Rashin ganin Amatallah yasa Aneesa d'aukar koma bata gidan, bakuma ta tambayi Nazeefa ba.
K'arfe hud'u suka gama komai, suka kuma gyara gidan da bazama kowanne lungu da sak'o k'amshi mai dad'in gaske.
Aneesa ta shigo 6angarenta dan tsara kwalliyar tarbar mai gida.

Amatallah tana idarda sallar la'asar saiga Nazeefa ta shigo, itace ta zaunar da ita ta gyara mata kwalliyarta datayi alwala wasu guraren suka d'an 6aci.
Wani material pink colour da akaima d'inkin sket da Riga Nazeefa tabata,
d'inkin yayi 'yau over, gashi yafitar da ainahin Shep d'inta, sannan colour d'in ya haska bak'ar fatarta. Nazeefa tamata d'auri mai k'yau, itadai Amatallah kallon ta kawai takeyi cikeda mamaki, amma takasa cewa komai, ita damuwartama yanda zata had'u da Uncle d'in nata, dan kunyarshi takeji sosai, musamman ma idan ta tuna da yanda yake mata a waya yanzun.
Bayan Nazeefa ta gama mata komai hardasu sark'a da abin hannu, ta fesheta da turarurruka masu k'amshin tsiya da shiga zuciyar mai shak'arsu.

Hummm, masu karatu, yaufa Amatallah d'inku ba'a magana, ni tsorona ma karta haukatar mana da Uncle fa🙆🏻.

Aneesa ma tanacan tana tsara nata gayun, itamafa babu sauk'i, dan wanka iya wanka tayi, ta bulbule lungu da sak'o Na jikinta da k'amshi, dama harda Siddiqa aka tafi gidansu innani.

A can kuwa 4:30 nayi su Anty maijidda da yara suka tafi tarbo su Uncle a airport.
5:8pm jirgimsu ya sauka.
Uhhm nafad'a lokacinda naga Fateema Na sakkowa jirgi da k'yar, cikinta ya tsufa, tak'ara k'yau da haske ga k'iba, Alhaji Muhammad Na bayanta shimafa ba'a magana, ya murje dakuma kwarjini, sajennan da gemunsa sunkuma yin bak'i sid'ik, sai furfura d'ai-d'ai data k'awata gemun nasa, wadda bazamuce ta tsufa bace sai dai baiwarta da ALLAH yamasa.
Da gudu yara sukaje suka tarosu suna ihun Kiran Abbunsu da Ummansu.
Alhaji Muhammad duk yahad'asu ya rungume harda yaran Anty maijidda guda uku, bayason su Ce zasu rungume Fateema dantayi nauyi.
Tsaye tayima tana kallinsu da murmushi jin dad'in ganinsu.
Anty maijidda ta k'araso tana mata sannu da zuwa da tsokanarta uwar biyu.
Duk dariya sukayi, aka shiga gaishe-gaishe kafin su k'arasa mota, dole saida suka had'a da taxi dan motar tamusu kad'an.

Duk hayaniyar da akeyi a gidan Amatallah Na jiyowa daga d'aki, gabanta sai kuma fad'uwa yake, heartbeat d'inta nak'ara k'arfi, amma takasa fitowa Dan kunya takeji.
Uncle kam tunda Aneesa tafito idonshi akanta, bak'aramin k'yau kwalliyarta tamasaba, gadan-gadan shi ta nufa zata rungume amma saiya doje ya d'auki Siddiqa da Umminta, Dan bazai iya abin kunyarnan gaban k'annensa da yaransaba.
Lamarin yabama Fateema dariya sosai, danta lura tsaf da nufin Aneesar dakuma abinda mijin Nasu yayi Na gujema manufarta.
Nazeefa ma ta lura, ta juya fuska tana dariya.
Duk da abinda yamata ya 6ata mata rai, amma saita danne, ta k'araso daf dashi tana masa sannu da zuwa, cikeda fara'a ya amsa mata da kanne mata ido d'aya. ta sakar masa da wani sihirtaccen murmushi kuwa da d'age masa gira.
Kallo d'aya tama Fateema tace sannunki.
Ran Fateema ya 6aci da rainin wagon Aneesar, ya gida kawai tace itama tayi gaba abinta.
Har suka k'arasa ciki yana baza idon son ganin Amatallah amma babu ko k'urarta. Anty Maijidda Na lura dashi, sai kawai tayi murmushi, a zuciyarta tace ya Muhammad Amatallah tawuce arhar ka ganta kai tsaye, saika bita har d'akinta.
Dukda daular abincin da Aneesa ta had'a musu bata d'auke hankalin Uncle ba, gaba d'aya hankalinsa nakan son ganin Amatallah, soyake kawai yaga halin datake ciki.
Suna cikin cin abinci Fateema ta kalli Nazeefa tana fad'in "Nazeefa wai Amatallah fa?".
Da hannu Nazeefa ta nuna 6angaren Amatallah d'in.
Uncle datun da suka fara maganar ya d'ago ido yana kallonsu yace, " lafiya dai ko bata fitoba?".
Nazeefa tace, "Yaya ban saniba nima, tundai d'azun tana ciki"..
Ajiye spoon d'in hannunsa yayi ya mik'e yana fad'in "bara Na dubata to".
duk binsa da kallo sukayi, wani haushi yakama Aneesa. Fateema kuma tayi murmushin mugunta, dama danta rama abinda Aneesa tamata ta tambayi Amatallah d'in, Dan tasan dole mijinsu yayi wani Abu akai.
Anty Maijidda kam da Nazeefa sai dariya sukeyi a zukatansu.

Amatallah da har suka shigo cikin falon tana jiyosu, tana kwance a doguwar kujerar falonta tana game a waya, dukda zuciyarta sai harbawa take da fargaba. game d'in kawai takeyi, amma bawai yana mata dad'i baneba, Rabin hankalinta nakan su Uncle d'in.
A hankali yaturo k'ofar falon ya shigo.
Ko kad'an Amatallah bataji shigowar saba, sai k'amshin turarensa saboda ta juyama k'ofa baya, kuma a la66ansa yayi sallama yanda bazai yuwu tajiba.
Shiru tayi tana hasashe, a zatonta ko tun daga waje k'amshin ke shigo mata.
Uncle kam al'ajabine ya kamashi, shiyyasa yakasa motsawa, tunda yake bai ta6a ganin Amatallah da kwalliyaba sai yau.
Jin kamar mutum tsaye akanta yasata juyowa cikeda fargaba. da Sauri ta mik'e tana fad'in "Uncle sannu da zuwa, ALLAH banasan ka shi..go..ba ne".
Murmushi yayi, ganin yanda jikinta har rawa yake, kai kace taga wani ojuju ne, takawa yayi a hankali har inda take batareda yace komaiba, daga zaune Amatallah tad'an matsa baya kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta, a kujerar ya zauna shima kusada ita, ai saitaji kamar tatashi ta tsilla a guje.
Hannunsa ya d'ora kan yatsun hannunta datake wasa dasu, yanda Jan lallen yay rad'am ne ya burgesa, murza yatsun yayi, hakanne yasaka Amatallah d'agowa tad'an kallesa.
Komi ya tuna kuma saiya saki hannun, cikin sassanyar muryarsa yace, " haba my best! Babu fad'a miya kawo gabane? Laifin mi mukayi aka k'i fitowa tarbarmune, ko ba'a murna da dawowarmu mu koma Inda muka fito?".
Hannu tasa ta rufe fuskarta dantaji kunya sosai tace, "Sorry Uncle, ALLAH ba haka bane fa, kawai dai".
Murmushi yayi mai k'ayatarwa, yasa yatsun hannunsa biyu ya d'ago ha6arta tareda saka d'ayan hannun ya janye hannayenta data rufe fuska, saita rumtse idanunta.
"bud'e idon to, kifad'amin kawai dai me? kokuma nayi wani Abu".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login