Showing 27001 words to 30000 words out of 104242 words
Aneesa ta zaro idanu waje, " mubar matafa kace?".
"Eh mana". 'Yay maganar cikin d'age gira'.
Bakinta ta ta6e, cikin matuk'ar hasala tace, " ai wlhy ba haifi d'iyar dazan banmata kaiba, raba dai-dan kama danekiyi tsoron azabar ALLAH ne kawai yasani hak'uri, nifa wlhy harma mamaki nakeyi yanda kayarda da auren d'iyar cikinka, shin baka tunanin kamata tsufane?".
Wani abune ya soke zuciyar Uncle M.A, ya kafe Aneesa da idanu ko k'yaftawa bayayi. tabbas maganarta ta mugun shigarsa. bai ce mata komaiba ya d'auki wayarsa da key yafice.
Bayansa Aneesa ta raka da harara, yau ko shiga su gaisa da Fateema bai yiba. Sai tashin motarsa kawai taji.
Da kansa yabud'e gate ya fice, sannan yafito daga motar ya yarufe, tafiya yake amma maganar Aneesa nakuma tasiri a zuciyarsa, shikansa tunda aka d'aura aurenan abinda ke damunsa kenan, sai yaga kamar an cutar da Amatallah, duk da shikam garas yake jin kansa da lafiya, bai San miyasa maganar Aneesa tamasa zafiba da yawa, bayan shima yasan gaskiya tafad'a.
Hannunsa yakai yashafo ma dai-daicin gemunsa, kafin ya furzar da iskar bakinsa yana kuma dafe sitiyari.
Ya d'anja lokaci a hanya kafin ya isa gidansu, saboda 'yan makaranta.
Babu kowa a tsakar gidan, sai dai yaji kamar alamar mutum a Ketchin.
Yasan maybe Nazeefa ce, Dan haka saiya wuce d'akin baba. Sai da yayi sallama, aka bashi izinin Shiga sannan ya shiga.
Innani ya tadda gefen baba tana gyara masa rawani bisa kansa data yafa masa, da alama wanka tamasa, kullum da sassafe take masa wanka ta shiryasa, shiyyasa saika taddashi tsaf.
Tunda yashigo baba da innani suke binsa da kallo, Dan tabbas sun gano alamun damuwa a fuskarsa, duk da sunsan damuwar rashin isma'il har yanzu bata barshiba, hakan bai hana baba fad'in "Muhammadu lafiya kuwa?."
Duk girman d'a agaban iyayensa yarone😊.
Dan haka sai Uncle M.A yakuma jin zuciyarsa tayi rauni, zama yayi ya gaida iyayen nasa, da tambayar ya jikin baba?.
Tambayar baba yasake mai maita masa. Innani dai batace komaiba, tama kauda kanta daga garesu, tanata ninke kayan baba daya cire, sai dai dukkan hankalinta Na kansu.
Yay k'asa da kansa, cikin sanyin muryarsa yace, "baba akan maganar auren nanne, sai nake ganin kamar an cutar da yarinyarnan, musamman idan akayi dubi da shekarunta da nawa".
Murmushi baba yayi tareda gyara rawanimsa dayake rufe masa fuska, yace, " miyasa kake wannan tunanin Muhammadu?, ai ba haramun baneba idan mai shekarunka ya auri kamar Khadija, sai dai malamai sukance yin zai iya zama cutarwa ga ita yarinyar zuwa gaba, Dan sanda zaka kai wasu shekarun tsufa ita kuma sannan take tashen k'uruciyarta, kaga zata iya cutuwa saboda kai k'arfinka ya ragu, amma zakaga wani kuma idan ALLAH yabashi lafiya babu abinda bazai iyaba alokacin, (anta6a ma sheaik jafar Mahmud Adam tambayar nan, irin wannan amsar naji kuma yabada) amma ALLAH bai haramtaba, saboda masalahar gudun yad'uwar zinace-zinace yasa malamai sharhantawa".
" kai kumama ai shekarunka basukai adamun ba har irin haka".
A raunane uncle M.A yace, ''baba shekara 47 fa".
Da sauri Innani ta juyo ta kalleshi, baba kuma yay guntuwar dariya.
"Muhammadu kai yanzu shekarunka 47?".
"eh mana baba, koma nafine?". 'Yaya maganar a raunane'.
Yanzun kam ba baba ka d'aiba, har Innani sai da ta murmusa.
"Lallai Muhammadu, to ai ko auren namu baima kai 45 ba sai a watan jibi, kuma awatan da aka kawo zainabu gidannan a watan tasamu cikinka, wannan lissafin kane dai kawai".
" to Amma baba a takardar haihuwata ai hakane".
"Yo Muhammadu takardar haihuwa ba kaine kaima kankaba lokacin dazaka sakandire, koka mantane?. lokacin da aka haifeka zainabu a rogo ta haihu, Dan ana goyon ciki a lokacin, tun cikinka Na wata bakwai akazo aka tafi da ita can, sanda tadawo min nan kanada wata biyu da kwana 26 a duniya, sannan ana arba'in biyu idan mace ta haihu tana wankan jego.
"Na dai manta taka mai-mai miya faru karon haihuwarka, amma an haifeka da shekara 1 aka kifar da gwamnatin gawon, Murtala ya hau mulki, sai dai bana mantawa abinda nake ganin zan iya k'iyastashi da haihuwarka lokacin dai an cireka a mama da kwanaki 6 obasanjo yazama shugaban k'asa a mulkin soja ko zainabu?, da wannan kawai zan iya k'iyastawa gaskiya, saika bincika shekarun kagani".
Innani tad'an gyara tsayuwarta a jikin bango, batareda ta kalli Uncle M.A ba tace, " hakane Malam dan bazan mantaba har shi ubasanjo ya sauka ba'a dawomana dashiba, har sai da iya ta rasu, dan munma fidda rai akan zai dawo wajenmu, nama haifi maijiddah har da cikin Barirah".
"Wannan gaskiyane zainabu, dan haka saika lissafa kaga shekara nawa ya kama, ka had'a da shekaru biyu kafin mulkin shi Ubasanjo d'in".
Waya Uncle M.A yaciro a aljihun gabar rigarsa, Dan yau ba babbar riga yasakaba, ya d'anyi danne-danne sannan ya d'ago yana kallon baba, yace, " baba 44 fa kenan".
"To shekarunka kenan Muhammadu, kaga kuwa ba kai tsufan daza ace kagagara auren Khadija ba, kumama duk muture maganar shekaru, ai mahaifinta yasan daliln cewa kaine kadace ka aureta, kodan nagartarka, dukda yasan yawan shekarun naka ko. kuma koda shi baiyi hakanba ni zan aura maka ita da kaina, kaine kafi kowa sanin ciwonta, da yadda zaka kula da ita domin kwaranyewar damuwarta, ko Jabeeru ban yarda dashiba akan hakan, sai ka kwantar da hankalinka wajen kula da amanar da Sama'ila yabar maka, ALLAH yay muku albarka".
"amin baba".
Nasiha baba yamasa sosai, itama Innani tayi tata, sanan yamusu sallama yafito.
'Dakin Nazeefa ya nufa, saboda yasan Amatallah tana can...............✍🏻
🤩👎🏻
*_k'ashin. Mindirik'inku saiya kwanta, kunji baba yace Uncle baikai 47 ba, 44 yake,😂, ammafa kusani d'an 60years ma yana auren 'Yar 17, kuma auren lobayya😜🤣._*
Wataranma sainayi novel da d'an shekara 70😏🥴.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[1/16, 1:29 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*
*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_
*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
____________________
*_Number 14 & 15_*
____________________
Sosai ransa ya 6aci daganin gungun matasan dake gefen titi, sai ihuce-ihuce sukeyi, daga mai sanda saima wuk'a da katako, kallo d'aya zaka musu kasan mafi yawansu ba'a cikin hankalinsu sukeba, huci ya furzo daga bakinsa kafin Yakuma maida kallonsa Kansu, sai lik'-lik'en poster's d'in wani d'an siyasa sukeyi, kansa kawai ya maida jikin kujerar ya kwantar, hannunsa d'aya dafeda sitiyari, kallonsu yakeyi daki-daki, kai kace TV yasamu.
Babu abinda k'asan ransa keyi sai suya da k'una akan halinda wasu MATASANMU suka tsinci Kansu aciki, sun mance matsayinsu a cikin al'umma, basa tunanin gobensu da jibinsa, jiyansu da yau ne kawai agabansu, 'yan siyasa sun maidasu karnikan farautarsu, dakuma sun d'are kujerun mulki sai su ringa kiransu da suna *'yan ta'adda*, bayan kuma sune sanadin wargaza rayuwar Mafi yawan matasan, sun haddasa bak'in ciki a zukatan iyayensu da al'ummar k'asar baki d'aya.
Jiyay kewar brother d'insa ta dawo masa sabuwa fil, tamkar yanzune yabar duniya, kwallar data taru masa a ido yasa d'an yatsa d'aya ya d'auketa, har zuwa yanzu yarasa wazai tunkara domin samun goyon bayan kafa k'ungiyar matasa kamar yanda Baban Ama yace suyi.
Karaf tunaninsa yafad'a akan abokinsu Sabi'u m Ali, tabbas yasan Sabi'u shima mutumne mai jure gwagwarmaya, kuma tabbas yasan baisan Isma'il ya rasuba.
d'an murmushi yayi saboda samun abokin tafiya Na biyu bayan brother d'insa.
Bai sake kallon matasan nanba yatada mota yabar titin.
Kusan Horn uku yayi sannan Aneesa tazo ta bud'e masa gate.
Koda ta rufe gate d'in saita nufo motar, duk da zuciyarta tana cikeda fargabar tarbar dazata samu a gareshi, saboda yanda suka rabu da safe.
Motar yabud'e ya fito, ganin yanda take a d'arare dashine yabashi dariya, amma saiya danne baiyiba. yad'an kalli k'ofar falon yaga babu mai tahowa, saiya matsa kusada ita kawai ya rungumeta da manna mata kiss a kumatunta, cikin kunnenta yace, "kinyi k'yau my Nessa".
Duk da taji dad'in kalaminsa, hakan baisata daina fargabarba, Dan tasan halinsa akan share Abu yayi tamkar bai 6ata ransaba, saika manta ya hukuntaka akansa.
Yatsu biyu yasa ya d'ago ha6arta yana kallon fuskarta sosai, cikin k'asa da murya yace, ''koba'a murna da dawowata gidan da wurine?".
Murmushin k'arfin hali Aneesa yayi, ta girgiza masa kai, "a'a wlhy my Dear, abinda nayi makane da safe yake matuk'ar damuna".
Murmushin gefen baki yayi kawai yakama hannunta yana fad'in "yarafa?".
Tace, " basu dawo islamiyyaba ai".
"Okay, to muje ciki, yunwa nakeji sosai, jinake kamarma zan iya cinye abincin gidannan duka yau".
Babu shiri Aneesa ta tuntsure da dariya, " kai Dear amma wasa kakeyi ko?".
"Hh, ba wasaba fa My Nessa, tunda Na fita drink kawai nasha awajen meeting....."
Yakai k'arshen maganar suna shiga falon.
Aneesa batasamu bashi amsaba, saboda Fateema data fito daga nata 6angaren cikin kwalliyar d'aukar hankali.
Kallonta kawai Uncle M.A yatsaya yi, saboda babu k'arya kwalliyar tata tayi masa k'yau, amma dukda haka yayi hakanne danya bama Aneesa haushi, itama taji bak'in cikin dayaji d'azu da safe.
A hankali yasaki hannun Aneesa da mamaki yahanata koda motsi, Dan bahaka sukayi da Fateeman ba, sunyi shiri akan sun daina masa duk wani Abu dazai faranta ransa, amma danta d'auketa sakarai shine taci uban kwalliya ta fito.
Uncle M.A daya k'arasa inda Fateema take sai kawai ya rungumeta yana fad'in "woow! my tee.., kinganki kuwa? saikace wata 'yar 22?. d'agota yayi daga jikinsa ya manna mata kiss a bakinta da yasha jan janbaki, harya d'ebo tsaraba shima😉.
Kutt, zuciyar Aneesa tamkar ta fashe, ai ko ita dakeda girki bai yaba kwalliyarta haka ba, sannan ma a kumatu yamata kiss, amma Fateema a baki, wannan wane irin wulak'ancine?.
Da sauri tabar wajen tashige 6angarenta.
Yana ganin ta shige yasaki Fateema yanufi samansa.
Binsa da kallon Fateema tayi tana gumtse dariya, sai da taga ya shige sannan tayi dariyar mai isarta, halin Muhammad nak'ara mata sonsa matuk'a, shi mutumne da in matarsa tamasa Abu bazai ta6a 6ata lokacin wajen mata ihu ba, sai dai yabi wata hanyar ya bak'anta miki rai, bata raba d'ayan biyu abinda Aneesa tamasane da safe yarama. ta gallama 6angaren Aneesa harara tana fad'in "'Yar rainin sense, da kin d'aukeni wata sakaraine ko?, azatonki na mince mun had'a kai ko? to Fateema garas take kallonki, bar ganin shekarunmu d'aya, sabodama kin rainamin hankali nun Yanke shawara babu Wanda zaiyi kwalliya shine kika koma d'aki kikayi ko? A nufinki kinbar sakarai anan, haba matarnan tas nake kallonki, shiyyasama naci kwalliyar dataci uban taki, mtsoww, sakarai wadda bata iya danne kishinta ba".
Tana gama fad'a ta shige nata side d'in itama.
Nace, "lallai Fateema kin burgeni wlhy, mata sai kuma Ku gyara😊".
Shikam yana shiga nasa d'akin dariya yayi shima, sannan yashiga k'ok'arin cire kayan jikinsa.
Harya fito wanka babu labarin Aneesa, bai damuba Dan yasan yanzu tahau sama. Farar jallabiya yasaka, yad'an fesa turare sannan yadawo falonsa, zamansa yayi dai-dai da shigowar yaransa da gudu su hud'u.
Duk kansa auka fad'a suna fad'in "oyoyo Abbunmu".
Shima rungumesu yayi cikin farincikin ganinsu, yace, " my Children's oyoyo, andawo islamiyyar?".
Atare sukace "eh abbunmu".
" masha ALLAH manyan gobe, ALLAH yayi muku albarka kunji, mi'aka koya yau?".
Rige-rigen fad'a masa suka farayi, barema Ummita da take bisa cinyarsa.
"Kunga afad'a d'ai-d'aya, kungafa banason hayaniya nagaji sosai". yafad'a a kalar tausayi.
Suma duk sai suka marairaice suna "sorry Abbunmu".
Murmushi yayi, yabi dukkan kumatunsu ya sumbata, sannan suka shiga fad'a masa d'ai-d'ai.
Ana haka Aneesa tashigo d'aukeda tire, fuskarta kawai ya kalla yasan tayi kuka, (sai dai a k'asan ransa rayuwarta tana burgeshi, ko kad'an Aneesa batada rik'o, in har zaka 6ata mata rai dazaran tayi kuka kota amayar da maganar to shikenan kuma ta huce).
Kallon yaran tayi tace, " kunga, kowa yaje yacire Uniform ko, abar Abbu yaci abunci".
Atare sukace to momy. Duk suka fita.
Sai da ta tabbatar sun sauka daga benen sannan ta tako a hankali inda Uncle M.A ke zaune yana kallonta.
Saman cinyarsa kawai ta zauna, batareda tace komaiba ta had'e bakinsu waje d'aya.
Bashida za6in daya wuce kar6arta hannu biyu.
🚶🏻♀bara na koma falon k'asa, idan sun dai-daita saina dawo😏.
Kusan mintuna 5 sannan Na koma, tararwa nayi tana zuba masa abinci suna dariya.
Na rik'e ha6a ina fad'in lallai (mata da mini said ALLAH), kuma gaskiyar Nazeefa, zaman gidannan Sai mai wayo, Dan rayuwa akeyi ta kissa da kishin masu Ilimi, masoyan Amatallah saiku mik'e sosai, dan saikun mata training akan zaman wanga gida da ake kishin 'yan bar.....🤭ban dai Ce komaiba
Ba ruwana bara Na tsuke bakina kar masoyan Aneesa da Fateema su caskalani🤐
Da kanta tabashi abincin suna hira cikin so da k'auna, sai da yagama tsaf sannan yay alwala suka sakko k'asa tare, ya tasa 'ya'yansa maza gaba suka tafi masallaci sallan magrib.
Saidai sukayi sallar Isha'i sannan yaturo yaran gida, shikuma yatare Napep sai gidansu dukda garin yafara canjawa kamar hadari zai had'u.
Nazeefa da Amatallah suna zaune a d'aki tareda Innani, Tuwo sukeci suna hira kad'an-kad'an domin d'aukema Amatallah kewa.
Sallamarsa kawai suka jiyo a tsakar gida, Nazeefa ta amsa dad'an k'arfi yanda zai jiyosu.
Sai da ya lek'a d'akin baba yaga barci yakeyi sannan yadawo d'akin Innani dayajiyo muryar Nazeefa, nanma sai da yay sallamar aka amsa dabashi izinin shiga sannan yashiga.
Idonsa Akan Amatallah yafara sauka, wadda tunda taji sallamarsa gabanta yashiga fad'uwa, sai ma taji tuwon yafita kanta, koda yashiga bata d'aga ido ta kalleshiba.
Kusada Innani yaje ya durk'usa yana gaisheta da tambayar jikin baba.
Ta amsa tana kauda kai gefe kamar yanda ta saba masa. sunama gama gaisawar tamik'e tafita daga falon.
Nazeefa ya kalla dake gaisheshi, bayan ya amsa yace, "Jabeer da shehu fa?".
''Yaya basu shigoba tukunna".
" Okay".
Cikin d'an rawar murya Amatallah ta gaidashi itama, idanu kawai ya zuba mata batareda ya amsaba.
Takuma maimaita gaisuwar a karo Na biyu.
Yanzunma bai Amsaba, sai cewa da yay "my best! alk'awarin kenan? tunkan muyi nisa harkin karya?.
Cikin dabara Nazeefa tazare jikinta ta fice tabarsu.
Cikin muryar kuka tace, " kayi hak'uri Uncle ban karyaba".
d'an murmushi yayi tareda girgiza kansa.
Sai kuma yataso yadawo inda Nazeefa ta tatashi yana lek'a kwanon tuwon da sukeci.
"Uhm my best babu tayine?".
d'an murmusawa tayi tace, "a'a to bismillah".
gyara zamansa yayi, cikin dai-daita murya dan soyake ta saki jikinta dashi.
Yace, "Sai da Na rok'a my best!?".
"to kayi hak'uri, bara nakawo maka wani wannan ya k'are".
"A'a ngd".
Kallonsa tayi, a shagwa6e tace, " uncle fushi kayi ko?". 'Tak'are maganar tamkar zatayi kuka'.
Yanda tayi maganar a shagwa6e sai yaji wani iri daban, bak'aramin birgesa tayiba, jiyay zuciyarsa Na kissima masa wani Abu daban, yay saurin fad'in ya salam, kai zuciya ta, mikikeyi hakane? Amatallah d'iya tace.
"Kaji Uncle, please mana"....
Maganarta ta kuma saukar masa bisa kunne.
tsintar kansa kawai yayi da mairairaice murya shima, harda langa6e kai gefe kamar yanda tayi.
"Ni dai gaskiya na k'oshi my best".
Dariya sosai Amatallah takeyi, shikuma ya kafeta da ido yana kallonta da murmushi. sai da tayi sosai sannan ta daina.