Showing 12001 words to 15000 words out of 104242 words

Chapter 5 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16064

Baban Ama... Yace, ''ai kishi a jinin mata yake brother, babu mai iya rabasu dashi sai dai ALLAH kawai, kana daiji mi Saliha kefad'a yanzun, wai wazata auri tsoho? alhalin zan iyama d'aukar budurwa sa'ar Amatallah". Yak'are maganar da dariya.
Uncle M.A ma dariyar yakeyi, " kai brother, yanzu in ance ga budurwa sa'ar my daughter saika aura kuma?".
"Ah da guduma kuwa, kana ganin tamin kad'anne?".
" hhh kamata yawa dai brother, mumafa balaifi munja kwana a duniyarnan, kusan 47years fa".
"Ai brother rayuwa nabani tsoro wlhy, ALLAH dai ya gafarta mana, yau kake gobe sai labarinka, yanzu nan su kawu da mamana Khadija harsunyi 12years da rasuwafa kenan?".
" ajiyar zuciya uncle M.A ya sauke, yad'an shafa fuskarsa yayinda k'asan zuciyarsa yay rauni saboda Baban Ama... yata6o masa wani sashen rayuwarsa, cikin sanyin muryarsa yace, "hakane brother sunkai".
Yanda baba yaji muryar uncle M.A ta canja saiya canja hirar shima, ya d'akko hirar abinda yay sanadin kwanciyar Amatallah a asibiti.
Ahaka suka k'arasa gida, mamaki dukya cika Uncle M.A, cikin damuwa yace, " brother gaskiya ina wata shawara da zuciyata tun kusan 1year data wuce, akan wani rikici dayafaru, danake kallo a labarai sainaga duk matasane a wajen, sannan duksu akafi kashewa, hakan yatada hankalina wlhy, tun lokacin nake juya maganar araina, amma narasa dawa zan tattaunata, kasancewar nasan akwai fuskantar k'alubalen masu dafamin mu tallafi tafiyar.
Murmushi baban Ama... Yayi, kafin su zauna a kujerun seatroom d'in, uncle M.A yacire babbar rigarsa shima ya zauna, ruwanda Baban Ama...yazuba a cup yamik'o masa, kar6a yay yasha.
"Brother mikake rik'e a zuciya har kusan 1year? In dai ka yarda dani kafad'amin, insha ALLAH ina tare dakai 100%".
"Haba brother mikake tunani? ai duk duniya inka cire baba da innani babu Wanda yasanni sama dakai, kama fisu sanin wasu abubuwan akaina, dansu bakomai zan iya yi agabansuba kona fad'a musu, kaikam a sirrin rayuwata miye baka saniba brother?".
" tom naji, nayi kuskure, amin afuwa, yanzu fad'amin mike ranka to? Insha ALLAH ina tare dakai".
"Alhmdllh brother".......
Katseshi Baban Ama... yayi, bayan yagama zuba musu abincin, yace, "mufara cika tunbinmu, sai maganar tafi shiga to".
Dariya suka tuntsure dashi suduka, sannan Uncle M.A ya sakko.


______________________________

" Oga akwai fa matsala gaskiya".
Wani yaron zike ne ke magana cikin muryar maye.
Zike dake zaune kan dakalin sokawe Na toilet d'in primary school yana busa taba yad'ago jajayen idanunsa yana kallonsa, "matsalar mi manu!?".
" oga! Gagis fa bai wullaba wlhy, ance yana general hospital kwance, kaima kasan yana mik'ewa yak'ine kawai zai tashi, ALLAH wlhy".
Wata 'yar zabura zike yayi, yacire tabar dayake busawa daga bakinsa, kallon sauran yaransa yayi daduk suke a cake, wasuma kwance suke a k'asa, wasu kuma suna busa wiwi, wasu kuma rik'e suke da roban faro suna shan wani far in abu, ya maida kallonsa kan manu, ''kai waye yafad'a maka?".
"Oga ba d'azun ka aikeni gidan Oga Pam ba? natarar wannan shegen d'an koran nasa zasuje wai dubashi a asibiti, harda mai k'aton kannan da ido gulu-gulu kamar Na kasa jan goro a faranti".
Dariya duk suka bushe da ita, amma banda zike da hankalinsa ke a tashe, yasan wanene gagis sarai, tashinsa kuma bazai zama sauk'iba a garesu su dukansu, kallonsu yayi, duk suka tsaya da dariyar dasukeyi.
Yace, ''kai guys, dolenefa yau d'innan lahira tayi bak'on bawa, am telling you idan gagis yatashi sai kowa yabar jos, kuma kunsani".
Manu yamik'e yana tangad'i, " Oga shiyyasa nafad'a maka ai, yanzu hakafa yaransa nemanmu sukeyi, danma Oga Pam yayi gargad'in kar Wanda yayi wani abune, ammafa dayanzu anfara Caskale a garinnan, ALLAH wlhy". yay taga-taga zai fad'i, saikuma yarik'e bango.
"Yau Operation biyu garemu, dolane mu k'addamarma tsohon yarinyar can daya had'amu da kwalawa wlhy, sannan Na yayyaga uwarta a gabanta, itama haka, kafin Na wullasu gidan daba'a dawowa".
Dariya suka kuma bushewa da ita, yanzu kam harda zike.
Yacigaba da fad'in saikuma wancan sauran gawan gagis, har yaransa saina k'are musu tanadi,, yanzu kutashi muje lik'a posters d'in Oga, koba'aso dolene ayisa kokuma lahira tai bak'i wallayi".

(Duk cikin harshen turanci suke magana, Dan k'alilanne ma acikinsu kejin hausar, manu nema kad'ai bahaushe, saurankam kowanne dayarensa, kusandai yanda jos ta tara yarurruka iri-iri, wannan yasa aka cakud'e waje d'aya, baka isa cewa wannan yarene tsageraba a jihar, saboda matasansu a cakud'e suke, musamman ma irinsu zike marasa jin magana🙁).

Duk mik'ewa sukayi, kowannensu a buge yake, dan sunyi mank'as da kayan mayen da Oga Pam ya basu, wani buhu dake gefe suka d'auka, zike yabud'e yad'ebo posters yana raba musu, saida kowa yasamu sannan suka tafi, kowa yana rik'eda posters da gam na ruwa a hannu. Sai ihu suke suna kirari wa Oga Pam.
Jikin pols da bangon gidaje suke lik'a posters d'in, daduk inda yay musu, babu mai hanasu Dan ansan halin tsagerancinsu sarai. ihu suketa zabgawa.
"Wuyyyyyiiii huhuuuuuuuu!!!!!, sai Oga Pam ko jiki yay tsami, a za6esa dole ko wlhy uwar gayu tahaifi wani, wuuuuyii huhuuuuuu!!!!!!!.
Abinda suketa fad'a kenan, ba yaraba hatta manya gefe suka koma suna kallonsu. duk poster d'in da suka gani cireta sukeyi, inhar bata Mr Pam baceba.
Kad'an yarage fad'a ya kaure tsakaninsu da wasu matasan anguwar, wad'anda suka lik'a wasu posters da suke cirewa. amma wani dattijo yamusu magana. ALLAH yasa wad'ancan masu fahimtane, akwai sauran hankali a jikin, saisuka k'yalesu akan zasu had'une koba yauba.
Su zike kam filin nasune, haka sukaita bin anguwanni suna lik'e-lik'en fostar Mr Pam.☹
Wata anguwar a tanka musu, wani wajen kuma ayi kamarma ba'a gansuba. Saida suka gama tas sannan suka koma bayan Government primary school inda suka maida dan-dalin shaye-shayensu suka zauna maida numfashi, da hirar tsiyatakun dasukayi a yau d'in, wani suyi dariya. Wani suyi surutu da zage-zage.


_____________________________

Tunda suka fita Amattalah ta sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarta tayi tana tunanin rashin zuwan Sadeeq saurayinta dubata.
Kobaiji batada lfy bane? Kokuma yazo tana barci halan?.
Gashin wayartama tana gida balle ta kirashi, kuma tanajin kunyar tambayar Ammi koyazo...........✍🏻



*yawan comments, yawan kwazona fa🤔🤥.*


One luv my fans🥰🥰





*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu._*😭🙏🏻
[1/16, 1:05 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 7_*
____________________

*_WASHE GARI_*
🤔😭

Abin mamaki washe gari da safe sai ga labarin kisan gagis yafito, anje har cikin asibiti da daddare anmasa yankan rago.
Kai tsaye kowa su zike aka zarga, musamman da akasan tushen abinda ya kwantar da gagis asibitin.
Humm, amma abin tsoro da ALLAH wadai sai aka nemi su zike aka rasa a cikin jos, Ashe suna gidan Mr Pam yabasu mafaka, bayan sungama tsara masa k'arya da gaskiya akan su gagis sunason 6ata siyasarsane shiyyasa suka kasheshi.
Sosai Mr Pam ke hura hanci da banbamin masifa akan k'are Duk wani dayace zai kawoma siyasarsa togaciya dolene a 6addashi, koda kuwa abokan takararsane.
A daren ranar yadank'ama su zike makamai masu had'ari sosai, wai surik'e domin kare kansu. sunyi farin ciki sosai da wannan k'yauta, dan aganinsu k'arin k'arfin guwwane agaresu.


Nidai nace, "hummm".☹



____________________________

Tunda sassafe Baban Ama yay shirin tahowa asibitin, danya kar6i Ammi taje tai musu girki.
Alhmdllh yatadda jikin Amatallah da sauk'i, jiya kuma firgitar kad'an tayi, sai dai zazza6i mai zafi data kwana dashi, dukda Magani da akabata bai saukaba, haka taita sambatu da kiran sunan Ammi da babanta.
Lokacin da babanta yake fitowa saiya ci karo da uncle M.A, babu irin rok'onsa dabaiyiba akan yay kwanciyarsa yak'ara hutawa zuwa anjima amma yak'i, yace suje tare kawai asibitin su kar6i Ammi.
Haka suka taho badan baban Ama yasoba.
Sun iso Amatallah Na barci, saboda batayi barcin dareba, bayan sun gaisa da Ammi tawuce gida sukuma suka zauna hira.

Kusan 9:30 Ammi takirasu akan sutaho tagama.
Har lokacin Amatallah Na barci.
Ammi tataho sukuma suka tafi,
Suna kammala cin abinci suka tafi k'auyen da zasu kar6o maganin baba.
Basu dawoba sai misalin 2:38pm. kai tsaye asibitin suka nufo.
Amattalah na zaune a kan gadon datake jiyya, abinci takeci tana hawaye, ga likita tsaye agefenta yana kallonta yana murmushi shida wata Nurse, Ammi kuma Na a bakin gadon zaune tahad'e fuska tana fuskantar Amatallah, da Alama itace ta tsareta takeci abincin.
Cikin gur6atacciyar hausar likitan yace, "Ametala please mana, stop crying, baka sen kai babba baniba? amma kinama common injection kuka? randa zakaje labour room kuma fa iye?......"
Banza Amatallah tamasa, jitake kamarma ta bugeshi dan haushi, shigowar su baba yasaka doctor da Ammi kallonsu, duk suka amsa sallamarsu.
Uncle M.A yak'araso da d'an sauri yana tambayar lafiya? Amatallah ke kuka?".
Doctor ne yamasa bayani akan sunason mata allurane saboda zazza6i yak'i sakinta, to gashi bataci komaiba kuma, shine yace tad'anci abinci kafin sumata. tace tak'oshi, Ammi ta tsareta saitaci, wannan ne dalilin kukan nata.
Babantama dariya abin yabashi, dan haka yay dariya kad'an, can k'asan ransa kuma yanamai jin tausayin d'iyar tasa tilo, sai dai bai San daliliba, tunda safe dasukazo ya kalleta yaji kwalla sun cika idonsa, haka kawai yau yawayi gari da k'ulafucin tunaninta da tausayi.....
Ajiyar zuciya yasaki, yayinda ya tsinkayo muryar uncle M.A Na lallashinta.
Bai ce komaiba, saima gefen Ammi daya koma ya zauna yana kallonsu cikin wani yanayi, ita kanta Ammi kallonsu takeyi a wani iri.
Da lalashin uncle M.A akasamu Amatallah taci abinci aka mata allura. tun tana hawaye har barci ya d'auketa, suduka ajiyar zuciya suka saki, kafin su tashi su fita zuwa gida cin abinci, sukabar Ammi Na gadinta, lokaci-lokaci masu dubiya k'awayen Amattalah da makwafta da 'yan uwan Ammi Na zuwa.


____________________________

Gab da magriba Baban Ama yakira Ammi akan tazo gida tabashi wasu takardu daya bata ajiya.
Tayi d'an Jimm kafin tace, "to Baban Ama wazai zauna da ita? gani nake bai dace nabarta ita kad'aiba anan.
Ajiyar zuciya Baban Ama ya dauke, kawai saiyaji idonsa yacika da k'walla, zuciyarsa tayi rauni, a sanyaye yace, " karki damu, ga Brother nan yataho wajenta, idan kika d'akkomin saimu koma asibitin tare ni da ke".
Kanta ta jinjina tamkar tana a gabansa, tace, "to ganina zuwa".
Amatallah na kwance tanajin Ammin ta, jitayi bata k'aunar tafiyar Ammin, bayan Ammi ta yanke wayar Amatallah ta kalleta, hawaye taf da idonta tace, " Ammi ki kwatantama baba inda takardun suke saiya d'auka basai kinjeba". tak'are maganar da zubda kwalla.
Kallonta Ammi tayi, tana mamakin miye abin kuka anan? daga dai zuwa d'akko takardu tadawo.
Matsowa tayi jikin gadon, ta dafa kan Amatallah tana murmushi, "haba Khadija miye abin kuka to? yanzufa zanje na d'auka masa mudawo, kiringa hak'uri da rayuwa Khadija, wannan k'ulafucin namu dakikeyi ki ragesa, karfa ki manta akwai mutuwa, kuma ke d'iya mace ce, wataran aure zakiyi kibarmu dole, kizama mai hak'uri kinji, komi kike tunani, koya cutar dake, koya sakaki rud'ani, to kisaka *HAK'URI* agabansa, insha ALLAH zaki zama mai riba a duniyarki da lahira..........
Sallamar Uncle M.A ce takatse Ammi........, shiru tayi tareda janye hannunta daga kan Amatallah, ta amsa sallamarsa, ya tambayi jikin Amatallah, tace da sauk'i sannan tafita.
Har taje k'ofa tajuyo takuma kallon Amatallah dake binta da kallo itama, jiki a sanyaye tafice zuciyarta na k'una.

Kawai sai Amatallah ta fashe da kuka.
da sauri Uncle M.A yak'arasa inda take yana fad'in " subahanallahi, My Best miya faru da kuka kuma?".
Kasa bashi amsa tayi, tacigaba da raira kukanta.
Kusada k'afafunta ya zauna yana lallashinta, shikansa gabansa sai fad'uwa yakeyi, gawata matsananciyar fargaba da yakeji tunda safe, harma zuciyarsa tana raya masa ko jikin babane?.


________________________________

"Ka tabbatar kayi kamar yanda nace, karka bari asamu kuskure fa".
"Oga karka damu kanka, kasaka aranka kawai sun wulla, itakuma bab.. d'in tana hospital, hawan k'awara yakamata mumata da daddare".
" karka damu, kaje afara wannan aikin first."
"Okey sir, babu damuwa".


_______________________________

Cikin mintuna k'alilan Ammi ta iso gida, a k'ofar gida sukayi kici6is da baba zaitafi salla, tashiga shikuma yanufi massalaci.
Ramzaki dake la6e bayan wani kwano da aka zagaye bishiyar mangwaro yafito, da sauri yashige cikin gidan, babu Wanda ya lura dashi saboda duhun magriba daya fara, gakuma garin da alamun hadari ma.
Ko kad'an Ammi bataji motsin shigowaba, tayi alwala tashige ciki. duk Ramzaki Na la6e yana kallonta. sai da yaga tashiga falon sannan shima yashigo cikin gidan sosai.
Bayan kamar mintuna biyu ya tabbatar Ammi ta kabbara salla. Sad'af-sad'af yashiga cikin falon.
Tabbas Ammi taga shigowar sa cikin falon, amma taza6i cigaba da sallarta, dan duk tunaninta 6arawone, hartayi raka'a d'aya yana tsaye a kanta, kallo yake k'are mata sama da k'asa, duk da gefen zuciyar Ammi ya tsorata, amma ta daure batabama shaid'an damar cin galaba akantaba bare ta sallame sallar.
Ramzaki sai da yabari tayi sujidar k'arshe sannan yazaro wuk'arsa daga k'ugunsa, dai-dai lokacin dazata d'ago ya soka mata wuk'ar a gefen cikinta na haggu.😭
Babu shiri Ammi takoma Sujudar datayi niyyar d'agowa, maimakin tayi ihu saita fara ambatar "La'ila ha illallah, muhammadarrasulullah, hazbinallahu wa ni'imal wakil". Wannan shine abinda keta fitowa daga harshenta, har Ramzaki ya zare wuk'ar, yadawo d'ayan gefenta yakuma sokawa.
Hawayene masu zafin gaske suka fara kwarara a idon Ammi dake a sujuda har yanzun, Ramzaki nakuma zare wuk'ar saita zube kawai awajen, la66anta dake motsawa suna kalmar shahada har yanzu nake kallo.

*_Masu karatu nikaina ina cikin rud'ani, wannan rashin imani har INA.😭_*

Ramzaki Na tsaye akan Ammi har tagama shure-shure, numfashinta yakoma fita a hankali.....
Dai-dainan baba yashigo gidan, da sauri Ramzaki yakoma bayan labule ya 6oye.
Baba yashigo cikin tsokana yana ambatar " Uwargida ran gida! kina ina? Zokiga angon gobe........
Maganarsa ta mak'ale a mak'oshi saboda ganin jini Na mamalowa daga inda Ammi ke kwance, kasa motsawa yayi inda take, yabi jinin da kallo kafin ya maida kallonsa ga Ammi, takawa yayi a hankali har inda take kwance.
Da sauri Ramzaki ya kwantar da gallon d'in fetur d'in daya shigo dashi, sad'af-sad'af yafice a falon.
Fetur d'in yafara malale falon.
Durk'ushewa baba yayi a gaban Ammi, yakama hannunta na haggu data dafe gefen cikinta na dama dashi, a hankali yad'aga hannun, soyake ya tabbatar daga nannne jinin ke zuba ko kuwa?.
Idanunsa yazaro, Dan ganin yanda jini ke 6ul-6ula, muryarsa na rawa yashiga kiran Saliha! Saliha!!, ke Saliha!!..........maganarsa mak'alewa tayi saboda ganin hasken huta, yajuyo a sanyaye.
Kasa motsawa yayi, yay sagade yana kallon wutar dakeci afalon, tanabin duk inda fetur d'in ya ta6a. ko kad'an baiyi yunk'urin motsawaba, saima matsawa dayayi jikin gawar Ammi ya kwantar da kansa bisa fuskarta ya fashe da kuka.😭
A hankali wutar tafara k'arfi, dan har kujeru sun fara kamawa, duk da zafin wutar na dukan baba yakasa tashi, motsin kirkima yakasayi awajen, jiyake tamkar an d'auresa da igiya. Sannu a hankali wutar ta iso inda yake, tuni numfashinsa yafara sark'ewa saboda hayak'in wutar.

Hankalin 'yan anguwa yafara dawowa gidan baba, saboda ganin hayak'i tasaman zinc.
Wanine ALLAH ya nuna masa fitowar Ramzaki daga gidan.
Ihu yafara yana nuna Ramzaki.
Ramzaki naganin haka yakwasa da gudu, hakanne ya tabbatarma da mutane baida gaskiya. nanfa wasu matasa suka rufa masa baya domin kamashi. wasu kuma suka afka gidansu Amatallah dan ganin mike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login