Showing 36001 words to 39000 words out of 104242 words

Chapter 13 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16041

ne".
"A lallai na yarda munada laifi sosai a wajenka, yanzu nan har kadawo da iyalinka Kano amma babu labari balle a k'ulla zuminci?".
" to nima nayi laifi amin hak'uri, bama su dad'eba, 3month's kenan da dawowar, kaina bisa wuya".
Still dariya Uncle M.A yayi, yace, "shikenan to, indai ban takuraka ba zuwa 4:pm insha ALLAH zan shigo, Dan gobe zan bar k'asar ne".
" mutumina ina kuma zaka fad'a haka? Halan kaida Isma'il ne?".
"A'a, nasan namaka laifi gaskiya, amma Isma'il ALLAH yamasa rasuwa kusan 6month's ago". yak'are maganar hawaye na cika idonsa.
A can kuwa Sabi'u ya masifar rikicewa, sai sallalami yakeyi, dole Uncle M.A ya yanke wayar, dan k'ara karya zuciyarsa yakeyi. kusan mintuna goma sannan Sabi'u yasake kira, yamasa ta'aziyya sosai sannan yace babu damuwa yazo su had'u a gida, zai turo masa address d'in inda suke yanzun.
Uncle M.A yamasa godiya sukayi salama. Jin gina yayi da kujera ya furzar da huci, a hankali ya furta ALLAH yajik'anku brother, I miss you so Much wlhy.

Har Fateema tashigo ta shirya masa abincin Karin kumallo a k'asan carpet bai saniba, ya Lula sosai a duniyar tuna rayuwarsa da Brother d'insa.
Ganin shirun yayi yawa Fateema ta k'arasa kusadashi ta zauna. Sai da ta ta6a kafad'arsar sannan ya juyo yad'an kalleta.
" haba Nurri tunanin mikake hakane?".
"Kansa kawai ya girgiza mata baice komaiba".
Shuru tai tana Kallonsa kawai, amma fuskarta ta nuna alamun shiga damuwa.
Hannunta yakamo yana murzawa a hankali, cikin sassanyar muryarsa yace, " my Tee... ina tuna brother ne".
Tausayi yabata sosai, tasan har Abadan mijinsu bazai ta6a manta Baban Ama ba, Dan ubangijine kad'ai yasan irin k'aunar dasukema junansu. hannu tasa tad'an shafi k'asumbarsa zuwa gemu, sorry Nurrina, kacigaba damasa addu'a, muma duk ita muke jira, ALLAH ya gafarta musu sukuma".
"Amin ya rabbi".
" please abinci to, karya huce".
'Dan murmushi yayi ya sauka yana fad'in "wayo dai za'amin. yara fa?".
" taf ai wad'an nan tuni suka karya tun kana barci".
"Tofa lallai, yau kuma ba'a jira Abbu ba?".
" hhh aiko dai basu jirakaba, harma mai lesson d'insu yazo".
"OK, bara nima kiga na karya, fita zanyi naje nadawo da wuri, sonake yau na yini a gida ina kallonku kawai".
" kai Nurri, saikace wad'anda zasu mutu?".
"Mutuwarma ai bamuda tabbas d'in rashin zuwanta my tee".
"hakane kuma Nurrina".


Bayan ya kammala break fast yay wanka, gayu sosai yaci cikin shadda galila brown color mai duhu, yayi k'yau sosai, ya d'ora hular zanna bukar itama brown. Fateema dake fesa masa turare sai k'od'a k'yan dayayi take.
Murmushi yayi yana kashe mata ido d'aya, " my tee fesamin turarennan sosai, wata k'ilma nasamo ta hud'u".
Daina fosa turaren tayi, ta wani had'e fuska ta juya masa baya.
Dariya sosai yayi, har hakwaransa na bayyana, ya rungumeta ta baya yana mata magana a kunne, "my tee... bakwason ta hud'un ne?".
Juyawa tayi suna kallon juna, ta d'ora d'an yatsanta saitin zuciyarsa, idonta akan face d'insa, shima kallonta yakeyi yana murmushi, " Nurrina indai ina cikin nan ❤ ban damuba, kayi in dai amaryace, ai kowa da halinsa zai zauna."
Rungumeta yayi yana murmushi, "my tee... Karyi kokwanto kinji, kinacan k'asan-k'asan zuciyar Muhammad, babu kuma wata mace dazata iya tureki ko wacece ita kin gane".
Dad'ine sosai yakama Fateema, takuma rungumeshi tsam ajikinta tanaji kamar tashige kawai ciki, a hankali tace, " I love you more my Nurri".
Shima a hankalin kamar mai tsoron ajisu yashiga jero mata kalamai masu kwantar da hankali, kai kace itaka d'aice matarsa babu wasu.
Hakan da Alhaji Muhammad kema matansa yakesa kowacce d'aukar kanta itace mowa, Dan duk matar data kasance tana tare dashi, yakan nuna mata soyayya tamkar ita kad'ai gareshi, shiyyasa suke masifar kishi da juna, kowacce d'auka take anfi sonta da k'aunarta.
Shikam yanayin hakane danya saka kwanciyar hankali da farinciki a tsakaninsu, kuma Alhmdllh yaci nasara da salonsa😊.

Tare suka sakko falon k'asa, ya shiga 6angaren Aneesa.
A falo ya isketa tanama Siddiqa kwalliya, idonta a k'ofa harya shigo dan tunkan ya shigo k'amshinsa yayo gaba, ba k'aramin d'aukar hankalinta kwalliyarsa tayiba.
Ta sakar masa murmushi, shima ya maida mata murtani yana zama kusada ita.
"Dear irin wannan d'aukar wanka haka? ina zuwa?".
" zanje Jos ne wajen amarya".
Baki tad'an ta6e badai tace komaiba.
"Ko bak'yason najene?". 'yay maganar yana d'aukar Siddiqa dake cinyarta'.
"ni a suwa dazan hanaka zuwa wajen matarka?".
Kusada ita yamatsa sosai, yasa hannu d'aya ya sak'alo k'ugunta dashi tareda kuma mannata da jikinsa, "ke a matata wadda nake tsananin so mana my Neesa".
Kallonsa tayi tana wata dariya ban yardaba.
Goshinta da la6annta ya sumbata yana kuma mannata jikinsa da fad'in " kobaki yardaba ne my Neesa?".
"Humm dear kenan, zaka wajen wata kuma kanamin dad'in baki, da dai a baya dai na yarda, amma yanzu kam ganganne".
Siddiqa ya gyarama kwanciya a cinyarsa yana dariya, " My Neesa kice yanzu ni kinbar yarda dani Ashe?".
"Ya zance nabar yarda dakai kuwa, na yarda dakai mana, akan wannan maganar daine kam sai a hankali".
" lallai naga ta kaina, to maida wuk'ar, babu inda Muhammad d'inki zaije my lover, zanje cikin garine wajen wani abokina, insha ALLAH yanzu zanje na dawo, sonake yau na kasance daku Ku kad'ai, fitarma danta zama dolene da banyiba".
Murmushi tamasa, harda masa kiss a kumatu.
"Ya mik'e da Siddiqa a kafad'a, " humm my Neesa kishi".
Itama mik'ewa tayi tana dariyar, "yo kaga laifina ne dear?, Kasan kuwa yanda nake jinka kuwa? ba k'aramin danne zuciyata nakeba idan naga wata mace ta ra6u da kai, amma babu yanda zanyi, haka ALLAH ya k'addaramin raba dai-dai d'inka da wasu mata". ta k'are maganar kamar zatayi kuka.
Tausayi tabashi, dan shi kansa yasan Aneesa na matuk'ar k'aunarsa fiyeda tunanin mai tunani, shiyyasa shima yake mata uzuri akan wasu abubuwan, murya a sanyaye yana kallon kwayar idonta yace, " I love you so much my Neesa".
jikinsa ta fad'a, tahad'ashi shida Siddiqa ta rungume itama tace, "I love you Abadan my Heartbest".
Sosai yakuma mannata da jikinsa, yana sakar mata tagwayen kisses a wuya.


🤣ho Uncle Muhammad kazama na......., uhm babu ruwana dai🤭.


Lokacin dasuka fito falo tuni Fateema ta shak'i haushi, amma kokad'an bata nuna a fuskaba, saima wani salon kallo datake masa, hakan kuma saiya hasala zuciyar Aneesa, ta kar6i Siddiqa a hannunsa takoma batareda tamasa rakkiyarba. Fateema kuwa taji dad'in hakan sosai, ita kad'ai tarakashi, saida suka gaisa da mai ma yara lesson sannan yayma yara saiya dawo Fateema tabud'e masa gate yatafi.


Duk yanda Sabi'u yabashi Address d'in haka yabi.
Tarba aka masa ta girma, sai kace Wanda yadad'e da fad'an zaizo.
Iyalansa duk sukazo suka gaisa, shima matansa biyu da yara 7, d'ansa namiji na fari harya zama d'an saurayi.
Sabi'u yakuma yimasa ta'aziyyar Isma'il, da kuma jimamin wannan rasuwa, dan Alhaji Muhammad sai da yasanar masa duk yanda lamarin ya afku. sosai Alhaji Sabi'u yay ALLAH wadai da wanan hali irinnan 'yan siyasar k'asarmu da matasa, yakuma nuna fushinsa akan yanda irin wad'annan rikice-rikicen kan faru musamman lokacin gabatowar za6e, da an kad'a tambarin siyasa shikenan kowa yana cikin d'ar-d'ar na tsoron afkuwar tashe-tashen hankula na rikicin *SIYASA KO K'ABILANCI* dakan taso a irin lokacin.
Da wanan damar Alhaji Muhammad yay amfani wajen sanar masa manufarsa shida Brother d'insa, sai dai mutuwa tai musu gaggawa.
100% Alhaji Sabi'u yabada goyon baya, da alk'awarin shima zai shiga a dama dashi a tafiyar.
Alhaji Muhammad yaji dad'i da karamcin abokin Nasu, nan dai suka tattauna abubuwa da dama dasuka shafi k'asarnan kuma suke damunmu, musamman ma yankin AREWACIN NIGERIA.
Abubuwan tamkar an shiryasune daga plan A zuwa Z.
Rikicin boko haram kamar bazai k'areba, ALLAH dai yakawo mana iyakarshi, bayan kisan gilla da akaima al'ummar arewacinmu, sannan kuma sune ake kira da 'yan ta'addar, sai dai muna murnar samun sauk'in bomb's sai kuma na satar shanu ya shigo, shima abin mamaki a arewaci kawai yake faruwa kuma jama'ar yankin ke amsa sunan 'yan Ta'addar. Zaune bata k'areba fa bayan dak'ile Satar shanu sai kuma Kidnapper's da ayanzu sune ke addabar yankin na arewacin kasar again.
Shin wannan lamarin bazai Baku mamakiba kuwa? bakwa ganin abubuwan kamar dama angama tsarasune daki-daki, idan wannan bai tasiriba sai a koma wancan?.
Miyasa komai baya faruwa sai'a arewacin k'asar kawai? alhalin bushewar idanun matasanmu batakai ga aikata irin wad'annan manyan ta'addacinba.

Ba wai dan ina 'yar arewa nake maganar nanba wlhy, sai sai kawai lamarin kan bani mamaki, yanda kowanne bala'i sun k'are a Arewacinmu. nasan kuma banima kad'ai ba, duk mai hankali yayi wannan tunanin.
Shin a ina matsalar takene?.


Manyanmu ne?.
Talakawa ne?.
'Yan siyasa ne?.
Matasanmu ne?.
Kokuwa k'ulla mana akeyi dan a ruguzamu😭?".


🙏🏻ya rabbi kayi gaggawar ruguza duk mai son ruguzamu, kamana maganinsa kafin shi yayi namu, kahanashi zaman lafiya kafin shi ya hanamu, kahanashi farinciki kafin shi ya hanamu, kamasa abinda yadace da zalincinsa kafin shi yaci nasarar zalintarmu😭🙏🏻.
Ubangiji gareka muke, kuma gareka muke Neman taimako, ya ALLAH karkamana hukunci da halayen wasu wawayen dake cikinmu masu busashshiyar zuciya wajen aikata sa6onka. ALLAH ka zaunar da k'asarmu lafiya, kabamu shuwagabbanni nagari masu k'aunarmu dason cigabanmu.🙏🏻









*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*🙏🏻😭
[1/16, 1:30 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 19_*
____________________

"Assalamu alaiki". 'Amatallah tafad'a yayinda ta k'arasa ga matsiyar budurwar.
Cikin d'an murmushi ta amsa mata, tareda bata hannu alamar suyi musabaha.
Itama Amatallah saita mik'amata sunama juna murmushi😊🤝🏻😊.
Bayan sun gaisa Amatallah ta tanbayeta kotana a department d'in sune?.
" eh". ta amsa mata da kulawa.
''Yauwa sister dan ALLAH ko akwai lecture yanzun?".
"Yes sister, nanda 15minutes insha ALLAH".
" ok ngd sosai".
Budurwar ta jinjina mata kai tana murmushi.
Har Amatallah ta juya zatabar wajen budurwar tace "amma ke sabuwar zuwace?".
Juyowa Amatallah tayi tana gyad'a mata kai.
Budurwar tace, "Nasamu friend kenan? sunana Fa'iza Abdul-hakeem Gwarzo".
" Nice name dear, nikuma Khadija Isma'il Uba (Amatallah)".
"Woow Nice name, sunan mamana kenan".
Murmushi kawai Amatallah ta mata.
Gurinda Fa'iza ta nunama Amatallah kusada ita ta zauna, nan suka d'an fara hira kad'an-kad'an, dukma Fa'iza ce k'arfin hirar. har dai 15minute's suka cika suka mik'e domin shiga lecture.
Farin cikin da Amatallah ta tsinci kanta a ciki 6ata lokacine wajen bayyanashi ma.

Tundaga wannan ranar sabo mai k'arfi yashiga tsakanin Amatallah da Fa'iza, itama Fa'iza Ashe matar aurece, harma takusa shekara da d'an k'aramin cikinta ma.
Sosai suke maida hankali a karatunsu babu maganar wasa.
Yanzu group d'in nasu sunzama su hud'u, Amatallah, Fa'iza, Rita, Goodness, idan ka gansu abin birgewa, duk kuma kusan shekarunsu d'ayane, Rita 'yar Taraba state ce, Goodness kuma 'yar Kaduna ce, amma duk sunajin hausa, barema Goodness, garama Rita kad'an-kad'an takeji, bakowacce kalmar Hausa take ganewa da k'yauba.
Komai nasu tare sukeyi, bazaka ta6a tunanin mabanbanta k'abilu baneba, babu raini bare k'yamar juna, idan lokacin Salla yayi su Amatallah sukanje tareda su Rita, saisu sami waje su zauna a wajen masallaci harsuyi su fito.


Rayuwar gidan Uncle kam agareta Alhamdllh, bata fuskantar matsalar komai, dan Nazeefa tsaye take a kanta.
Itama kuma batasa wasaba wajen kulada abubuwan dasuka shafi gidan. tsakaninta da yaran kam sosai shak'uwa tashiga. Ko waya sukayi da babansu saisun bashi labarin Antynsu, da sweets datake siya musu kullum.
Sosai yakejin dad'in hakan, dan yanason maison 'ya'yansa.


_______________________________

Akwana a tashi babu wahala wajen ubangijin al'arshi, yau ga Aneesa da watanni hud'u a Dubai, ta murje tayi k'yau abinta, dolene kaganta ta birgeka😜.
Yau bayan Alhaji Muhammad yadawo gidan a gajiye, ta taimaka masa yay wanka sannan ya zauna yin bud'a baki, (kasancewar alhamis ne). dukda bawani Cin abincine dashi sosaiba hakan bai hanata had'a masa 'yan abubuwaba wad'anda bazasu zama almabazaranci ba.
Yana shan shayi suna hira kad'an-kad'an, acikin hirar tasune yake fad'in "my Nessa kifa fara shiri".
Kallonsa tayi cikeda kulawa, " Dear! shirin me kenan?".
'Dan murmushi yayai, dan yasan yanzu zai tsokaloma Kansa rikicinta, ya kur6i shayin yana d'aukar remote dan rage k'aran TV, "my Nessa komawa Nigeria mana".
" Dear Nigeria kuma? to saboda mi? kona maka laifine?".
Yanda take jero masa tambayoyin saita bashi dariya, amma saiya gimtse baiyiba, ya ajiye mug d'in yajawota jikinsa, a hankali yake mata wani salon da yasata narkewa jikinsa, "my Nessa kinsan dai bake kad'ai bace dani, inada wasu matan ai, kuma sunada hak'k'i a kaina, yazama tilas Na saukeshi kuma, kiyi hak'uri zaki koma ita kuma Fateema saita zo".
Wani k'ududun bak'in cikine yahana Aneesa magana, ta danne kukan da yazo mata.
Jin tayi shiru ya lek'a fuskarta, " my Neesa!".
Idanunta tad'ago ta kalleshi.
yace, "miya faru?".
Yunk'urawa tayi tatashi daga jikinsa, ranta a 6ace tace, " amma ai Fateemar ba lafiyane da itaba, itakuma d'ayar ai naga makaranta kace tanayi ko".
Guntun murmushi yayi yana girgiza kansa, wato Amatallah Ce d'ayar, batada matsayin daza'a fad'i sunanta ita.
Hannayenta yakamo ya rumtse cikin nasa yana murzawa a hankali, "hakane My Neesa, saidaifa kin sani Na Sani wanan ba hujja baceba dazan kare kaina a wajen ubangiji, abindama yasa kikaga babu Amatallah a tafiyar saboda haryanzun bata gama sabawa daniba, saboda yanda Auren namu yazo, tana buk'atar nagama koya mata yanda zata saba dani a matsayin miji kafin tasan hakan a aikace, rashin lafiyar Fateema bazai hana tazo gareniba kingane".
Hannunta kawai ta zare daga NASA, ta tashi tabar masa wajen.
Binta yayi da kallo harta shige bedroom d'insu.
Iskar bakinsa ya furzar, ya girgiza kai tareda cigaba da bud'a bakinsa


****

Tundaga ranar bai sake ma Aneesa maganar tafiyaba, yanata mata dai shirye-shirye da had'a mata tsaraba.
Fateema ma anan tanata shirye-shirye, dan bazataje da yaro ko d'ayaba, Ummita ma anasata a school.
Randa Aneesa zata taho ranar Fateema zata tafi.
Koda Amatallah taji batun tafiyar bataji komai arantaba, saima tunanin yanda zasu zauna da Aneesa ita kuma, tanata Addu'ar ALLAH yasa itama Tamaka kamar Fateema, sauk'in tama akwai Nazeefa a gidan.
Komai Na tafiyar Aneesa ya kammala, ana gobe zata tafi Alhaji Muhammad yasha rikicinta, hakadai ya shareta yanata lallashi.

Washe gari su Amatallah sukama Fateema rakkiya har airport, basu baroba saida sukaga tashin jirginsu. yara basu damuba, tunda ga Anty Nazeefa gakuma Amatallah, garama Ummita tad'anyi kuka kad'an dataga Ummanta tashiga jirgi ta barta, saida Shehu yace mata allura Umma zataje sannan tayi shiru.
Daga canma Alhaji Muhammad yayima Aneesa rakkiya, baibar airport d'inba saida yaga sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login