Showing 90001 words to 93000 words out of 104242 words

Chapter 31 - SIYASA KO KABILANCI COMPLETE HAUSA NOVEL

04 Oct 2024

16055

ankarar dasune akan sushiga hankalinsu, inba hakaba kuma su antayoka k'asa daga kujerar taka.


A gurguje please😎.


*_3 years ago_*...............✍🏻
🤭🙆🏻😂


Karfa kuyi magana🤐🥴



🤩👎🏻

One luv my sweet fans.






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
[1/21, 6:14 PM] Aysha Galadima: *_Typing✍🏻_*


*_HASKE WRITER'S ASSO..._*💡
_{home of expert and perfect writer's}_





*_SIYASA KO K'ABILANCI_* ⁉
_(Hattara matasa)_



*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


____________________
*_Number 37_*
____________________

Duniya mai gudu da sauri. da dare yayi saikiga gari yawaye, sai marece, duniya nata zabga gudu tamkar iskar guguwa.
Abubuwa da dama sun faru acikin shekara ukunnan, ciki harda auren su Nazeefa, yanzu haka Asiya matar ya Jabeer ta haihu d'anta Namiji Ahmad suna kiransa da sunan (Farhan) itama matar Shehu Zaliha ta haihu d'iya mace Hafsat, Nazeefa ce dai ALLAH bai kawo dawuriba, saima yanzu takeda cikin.

*_Gidan Uban gayya kuwa Uncle_* abubuwan sai sanbarka, dukda ansamu marasa dad'i damasu dad'inma, sunan sunata kishinsu kamar yanda suka saba, tattalin mijinsu kam sai abinda yay gaba, haka shima soyayya yake nuna musu tamkar babu gobe, Aneesa ma tasake haihuwar d'anta Namiji Abubakar Sadiq, harma yayi wayo abinsa.
Amatallah dai har yanzu babu labari, tunma abin baya damunta harya d'an fara damunta, badan tana samun hantara daga mijin ko abokan zamanta ba, a'a tana burindai itama taga jinintane, tananan tanata karatunta, saidai yanzu kam daga ita sai Fa'iza da Goodness wadda sanadin zama dasu Amatallah d'in takar6i musulinci awata ranar juma'a data gabata, shekara d'aya kenan, tace d'abi'un su Amatallah Na matuk'ar burgeta, tunda suke tare basu ta6a nuna k'yama agaresuba, sun d'aukesu tamkar 'yan uwa Na jini, gasu sunyi aurensu suna gidajensu kuma suna karatu, hakan na matuk'ar birgeta (Dan Fa'iza ma takuma haihuwar d'a Namiji Salim) tunranda Goodness (Aysha) takar6i musulinci Rita tafara jabaya dasu, daga k'arshema tadaina shiga cikinsu kwata-kwata, wai karsu mata tsafin dasukama Goodness itama tazama Musulma, sunta jawota ajiki da nuna mata sufa basu tilasta Goodness tabi addininsuba, kuma ba tsafi sukai mataba, ALLAH ne kad'ai ya k'addara tanada rabon hakan, amma Sam Rita tak'i fahimtarsu, bilhak'k'i tana a kan bakanta Na asirine yasa Goodness komawa addinin musulunci, (wa'izubbillah).
Lokacin dasukaje level 4 aka rarrabasu fannoni daban-daban na karatun likitanci, sai Rita takuma nisantarsuma gaba d'aya, da Amatallah da Fa'iza da Aysha (Goodness) fanni d'aya suka d'auka, sun zarce medicine 6angaren mata (Gynecologists), Rita kuwa saita koma 6angaren ido (optometry).
A yanzu haka su Amatallah suna cikin asibitin AMINU KANO TEACHING HOSPITAL suna cigaba da karatunsu, tsakaninsu da Rita hello hii ne, shima saita gadamar amsa musu, tamafi jin zafin Aysha (Goodness).
Itakam ko'a kwalar rigarta, harkokinta takeyi, dukda ta fuskanci matsaloli sosai ga danginta saboda musulinta datayi, daga k'arshedai wasu daga ciki suka fahimceta, amma sunce dolene tabar family d'insu, tundaga nan tadawo Kano ta sanarma su Amatallah, Amatallah tasamu Uncle ta sanar masa komai, dakansa ya buk'aci ganin Goodness, bayan yakumajin tabakinta yace ta tattaro kayanta tadawo wajen innani, bayan yama iyayensa bayanin komai gameda ita, baba yace tadawo nan gidan dazama tunda dama su kad'aine yanzu a gidan, sai gwaggo rakiya data dawo tana d'ebe musu kewa, (dama mijinta yarasu tuni, yaranta mata kuma biyu duk sunyi aure).
Wannan shine silar dawowar Aysha (Goodness) gidansu Uncle, Innani tarik'eta tamkar 'Yar cikinta, duk wata hidima kuma Uncle namata tamkar su Nazeefa, dukda haka takanje Kaduna ta gaida danginta, kuma wasu basa sakar mata fuska har yanzun, bata damuwa kokad'an, saima addu'a datake musu ALLAH ya ganar dasu suma, dan Islamiyya Uncle yasamar mata take zuwa, agida kuma innani Na kuma tunasar da ita, gakuma su Amatallah agefe suma suna bada tasu gudunmawa, sosai hankalin Goodness ya kwanta taketa karatunta dakuma rik'e addininta Na islama, Dan batada matsalar dangi tunda gasu Uncle sun kwaranye mata wannan bak'in cikin.

A 6angaren k'ungiyar su Uncle kam saidai muce Alhamdullahi, Dan tazama gawurtacciyar k'ungiya datake gogayya da manyan k'ungiyoyin duniya, sunyi k'arfi a arewa fiyeda zaton mai tunani, ayyukansu sunshiga lunguna da sak'o Na birni da k'auyika, hakama kudancin, dukda suna fuskantar ra'ayin rik'au Na *SIYASA KO K'ABILANCI* hakan baisa sun nuna gajiyawarsu da kiranye ga matasanba, sunkuma cigaba da tallafama matasan sosai.
Zuwa yanzu Kungiyar ta wawashi wasu manyan masu fad'a aji nak'asar, tundaga kan malamai har zuwa attajirai da wasu k'usoshin gwamnati, dukda haryau suna kan ak'idarsu ta suba 'YAN SIYASA baneba, dan komin k'arfin mulkinka Baka Isa kazo musu ta fuskar SIYASA su kar6ekaba, SARAKUNAN GARGAJIYA ma ba'a barsu abayaba, dama sune sukafi cancanta suzamto a tafiyar k'ungiyar, Dan ta hanyoyinsune za'a iya gamsuwa da zak'ulo matasan da tallafa musu.
Nasarorin k'ungiyar sunkuma ha6akane ta dalilin wani tsari da Uncle yazo dashi Na kowanne matashi daya samu tallafi daga KUNGIYAR ya taimaki matasa uku dabasu sami tallafinba, koda ta silar masa hanyane nasamun tallafin k'ungiyar, idan kuma kai k'arfinka yakai ka taimakeshi da aljihunka.
Wannanfa takuma kawo haske da dakuma tallafawa lamarin matasan, shaye-shaye da dabar siyasa sunfara zama labari (dama mafi yawa talauci ke sanyasu aikatawa), ga islamiyoyi Na addini da Matasan suketa sauke alkur'ani da fahimtar wasu littatafai, harma abin ya ha6ak'a, kungiyar suna fidda matasan zuwa k'ashen SAUDI ARABIA domin k'arin fad'ad'a ilimin addinin, (to wani abun dayawa jahilci nakawoshi, musamman matasan Na yanzu da ilimin boko yafi tasirantuwa a ransu fiyeda Na addinin) to Alhamdullh, sanadin wannan taimako Na bud'e islamiyoyi saiga abubuwa dayawan gaske sun canja salo, tarbiyyar matasan da kulada tarbiyyar k'annensu, biyayyarsu ga iyayensu dama dattijai Na sama dasu, (lallai ilimin addini haskene, kuma shima daza'a tsayama Matasan k'asarnan saimun samu sauk'i wasu abubuwan Dakuma gyararrakin gidajen aurenmu dasuke da rauni yanzu).


😂Baku tambayeni labarin zee ba?.
Tunda tasami Number sa tafara addabarsa da yawan message, yana gani amma baita6a maida hankalinsa ba, yasha kuma shiga bayaro tazo ta gaisheshi, bawani sakar mata fuska yakeba, amma hakan baisa tagaji da bibiyarsaba.
Dayake wahala bata ishi zee ba kusan shekara uku kenan tanata k'ok'arin yad'a manufarta, dukda tanada d'unbin samari masu sonta, amma ita zuciyarta Uncle takeso. zuwa yanzu kuma yakan d'aga waya idan ta kirashi, shiba k'aramin yaro baneba, shiyyasa bai ta6a hantarartaba kocin mutuncinta, da wannan damar zee take amfani tana kuma cusa kanta gareshi.
Duk abinan dake faruwa Amatallah bata ta6a ritsasuba balle kuma su Aneesa dake gida, zuwa kuma lokacin Zee tasan Amatallah matar Uncle ce, harma yanada wasu matan, amma dukda haka bataji sonsa yaragu a rantaba ko kad'an.


Nidai nace humm.😎


******* **** ******

Yau takama Alhamis, girkin Fateema ne kuma, kusan 5pm Uncle yakira Amatallah tana Asibiti.
Cikin kwantar da murya tamasa sallama, ya amsa cikeda shauk'i.
Ta marairaice murya tamkar zatayi misa kuka "Uncle ALLAH yau nayi ti6is saboda gajiya".
"ayya my heartbeat sorry kinji, gashi banida damar miki tausa yau, saboda nimai tsadane a gareki".
Kukan shagwa6a tasaka masa tana bubbuga k'afa da fad'in "hakama zakace ko? shikenan munyima fad'a babu ruwana dakai daga yau, kuma wlhy nima namaka tsada yau harma sati biyu".
Aysha da Fa'iza suka tsaya kallon ikon ALLAH, itakam tama manta dasu a wajen.
Daga can Uncle yace, " rufamin Asiri my best, wasafa nake miki, nimai arhane koda yaushe agareki, sati biyu, aikafin kigama fushin natafasa Na k'one a tunkunya".
"Garama ka tafasan, ni karma ka sake kirana sai anjima".
" please my best na tuba, barama Nazo da kaina na d'aukeki idan kin gama".
"Aini ko kazo bazan bikaba, Aysha zanbi wajen Innani zan kwana ma".
" wayyo babie na, kinaso namiki kuka kenan? koda yake nima saina kwana tsohon d'akin jabeer nima".
"Anty fateen fa?".
" sainace mata kece kika jani".
Dariya Amatallah ta k'yalk'yace dashi, tace "ALLAH ya shiryeka Uncle, nidai babu ruwana wlhy".
"Nima ai babu ruwana d'in. yanzu kin gama nazo mu wuce? dan ina kusada asibitinku".
" wai da gaske".
"Eh mana, nazo wajen wanine".
" to saika zo, ina jiranka".
"Okay babyna saina zo".
Daga haka suka yanke wayar.

Aysha da Fa'iza suka saki baki suna kallonta, suka ce " lallai baby kina wutafa, lamarin naku yana bada citta walhy".
Far tayi da idanu tace "ya ranku babies?".
" fari tas". cewar Aysha.
Fa'iza tace, "ni wlhy shekara hud'u daya wuce akacemin Amatallah zata zama haka zan k'aryata fa, ni yanzuma malamar taki kinfini gogewa a harkar".
Amatallah da Aysha suka saka dariya, Aysha tace, " muma dai ALLAH kabamu mijinnan mushiga daga ciki".
"Amin baby, amma wlhy kibama doctor Yazeed dama, gayennan yana sonki over amma kinata yankwanashi".
''Ba haka bane Ama....., wlhy inajin tsoron kishiyane, kuma matarsa ance batada kirki".
" ke 'yammata kar rashin kirkinta yadameki wlhy, kibada kai bori ya hau kawai, zamu bida itane tayi mubaya'ar zaman lafiyar dole, bakiga Anty Aneesar gidanmu yanzu tayi sanyi ba, ai yau da gobe tawuce wasa".
''Wlhy gaskiyarki Amatallah, Amaryarmu tunda taji mijinmu na Neman ta hud'u takama kanta, Uwargida kam aidama tayi sanyi tuni wlhy, ai yanzun an daina yayin kishin HAUKA, kowa tata ta fisheta akeyi".
"To shikenan, kubari dai zanma Innani maganar da Uncle, yanda sukace saimu k'ara tattaunawa, Ama... Kid'an farama Uncle maganar".
"Okay ALLAH ya tabbatar mana da alkairi to".
Atare suka amsa da amin.
Suna 'yar hirarsu har Uncle ya iso.
Bayan sunje sun gaida shi Ama.. tamusu sallama tashiga mota, Uncle yace "Aysha keba gida zakijebane?".
" gida zanje Uncle, zamu samu Napep yanzu insha ALLAH".
"Ku shigo to na kaiku bakin asibitin, Dan time d'in shan ruwa yakusa, sai anjima zan shigo gidan, idan kuma zakibimu to?".
Da sauri Amatallah ta k'yafta mata ido wai tace eh".
Murmushi Ayshan tayi tace " to Uncle".

Baya suka shiga, a wajen asibiti Fa'iza tashiga napep yabiya kud'in sannan yanufi gida dasu Ama.....
Motar tayi shiru, Uncle nata tuk'insa, Amatallah da Aysha suna d'an hira jefi-jefi akan aikin yau d'in, Uncle najinsu amma baice komaiba har suka Isa gida ana kiraye-kirayen magriba.
Fateema tafito cikin kwalliya da d'okin tarbar mijinta, amma saitaci karo dasu Ama... nafitowa a motar itada Aysha.
Kallonsu kawai tayi batace komaiba, amma taji zafi a zuciyarta. Shikansa Uncle yakula bataji dad'iba Dan fuskarta ta nuna hakan.
Su Amatallah kam ko a kwalar rigarsu, gaisheta sukai suka shige ciki abinsu suka barta da mijinta.
Cikin fara'a ya tarbeta, yafito yana fad'in "yarafa my tee!".
"Basu dawoba suda momynsu".
Fara'arsa yarage yana kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, " mtsoww nifa banason irin wannan rayuwar, shiyyasa banson wani birthday d'in banzan nan, ankira magriba amma suna gidan mutane?".
"Kayi hak'uri, wlhy nasan itama hankalinta na gida".
Baice komaiba yamik'a mata wayoyinsa, " bara naje nayi salla ni".
Tace, "adawo lafiya".

Ciki takoma abinta, bataji motsin su Amatallah ba tashige 6angarenta, dan gaskiya taji haushin ganin Amatallah da Uncle tare, ga yarinyarnan data fara zargin kodai mijinsu sonta yakeyi? yo haka kawai dan yarinya ta musulinta sai a maidata tamkar wata jininsu, (nace hummm, kardai kishi ya rufe miki ido fateema).
Su Amatallah ma basusan tanayiba, Dan suna shiga Aysha tashiga wanka, Amatallah tazauna tana sauke numfashi dajiran fitowarta itama tasamu tayi, dan tanama fashin salla ne, shiyyasa Aysha tafara shiga danta sami damar yin salla akan lokaci.

Har Uncle yadawo sallar magrib Aneesa da yara basu dawoba, ransafa yafara 6aci, bayason shirme irin wannan, yanzumma anfi k'arfinsane, wai d'iyar su shehu ce ke birthday d'in cika shekara biyu, shine Aneesa ta kaisu dan Amatallah batanan, itakuma yakamata taje d'in tunda itace k'arama kuma kamarma za'a iya cewa k'awar Zalihance.
A falon k'asa ya zauna yakira Number Aneesa amma tak'i shiga, itadai Fateema tanata had'a masa kayan bud'a baki a d'arare, dukda abin na damunta a rai, tun bayan tafiyarsa masallaci kuma itama take kiran Number Aneesa network ya hanashi wucewa.
Tsaki yaja yad'auki ruwa yanasha.
Da wayo Fateema tanufi 6angaren Amatallah. fitowarta wanka kenan itakuma tashigo, Aysha kuna na zaune inda tayi salla tana karatun alkur'ani.
"Antyn yara munga idi".
" kamarya Anty?".
"Wlhy momy naketa kira awaya tak'i shiga, kuma Abbunsu yafara fad'an rashin dawowarsu, shima yagwada wayarta tak'i shiga, narasa misuka tsayayi har dare haka?".
Amatallah tace, " mun banu, Anty Aneesa ta manta da yandama yayarda suje Birthday d'inan? bara nima na gwada kiranta to".
Amatallah ma takira tak'i shiga, tace, "bara nakira zaliha to".
''Yauwa, ni wlhy tunanin nanma bai zominba, yo dukna rud'e kirata muji........"
Maganar Fateema tamak'ale saboda sallama da Amatallah tayi alamun Zaliha ta d'aga. bayan sun gaisa taimata Happy Birthday d'in Hafsa d'in dabata hak'urin rashin zuwanta sannan tace Su Anty Aneesa fa? basu taho bane?".
"Yanzu suka taho Anty Ama..... wlhy Haneefa ce yarinyar Anty Mariya ta d'auki su Ummita da Siddiqa wai suka tafi gidan k'awarta can k'asan layinmu, gashi tabar wayarta agida, munrasa yanda za'a kirata tadawo dasu, kuma babu wanda yasan gidan. ALLAH yasa Yaya baiyi fad'aba dai?".
"A'a baiyiba, tunda dai suntaho shikenan, ALLAH yakawosu lafiya".
"Eh sun taho, ya shehu mane yarakosu saboda yaran sunmata yawa gashi ba motar gidaba".
" wlhy kuwa, shikenan a gaidamin hafsa, sainazo cin cake".
Dariya zaliha tayi suka yanke wayar.
Ta fad'ama Fateema duk yanda sukayi, hamdala Fateema tayi, tace, "ALLAH ni tsoronma fita nakeyi, ran Abbunsu a 6ace yake, shirya mu tafi tare".
Ido Amatallah tazaro waje, " Anty Fatee ke kina tsoronsa bareni kuma?".
Karki damu saka kaya kedai, idan mu biyune k'ila ya sassauta.
Aysha najinsu, tayi murmushi cikeda sha'awar wannan family, ita kanta a d'azun taga fuskar Fateema ta nuna rashinjin dad'in ganin Uncle ya kawosu, amma gashi yanzu sun had'u suna magance matsalar data shafi kishiyarsu, rayuwarsu na birgeta.
Doguwar riga tasaka kawai tad'an shafa fauda tasaka turare suka fito, yana zaune inda fateema tabarsa, yad'ago ya kallesu, ransa a 6ace yake amma kwarjininsa ya shanyeshi, duk sai tsoro yakama Amatallah, ta la6e bayan Fateema tana satar kallonsa.
Kauda idonsa yayi daga kansu kawai, a d'arare Fateema tace, "kozakayi wanka tunda gasunan tahowam......"
Wata harara ya jefeta dashi wadda tasakata kame bakinta ta maida kanta k'asa.
Hakan yakuma bama Amatallah tsoro, dama Uncle ya iya fushi haka? lallai takuma yarda bayason abinda zai ta6a 'ya'yan nan nasa.......
Tunaninta ya katse saboda shigowar yara da gudu, daga Amatallah har Fateema ajiyar zuciya suka sauke, kowa yafurta alhmdllh a hankali.
Dukansu jikin Abbunsu suka fad'a suna masa oyoyo, abin mamaki sai Amatallah taga yaware yana musu dariya, Aneesa tashigo a d'an tsorace, Dan tunda taga motarsa a harabar gidan jikinta yay sanyi k'alau.
Su Amatallah duk sukai mata barka da dawowa, ta amsa tana nuna musu Uncle da ido, da hannu Fateema tamata alamar itadai tayi shiru.
Barka da gida tamasa, ya amsa kamar bata masa komaiba, (itama tasan bazaice mata komanba agabansu Ama....., saiya ke6e dagashi sai itane zataga 6ancin ransa).
Shehu yashigo d'aukeda Abubakar, zama yayi ya gaida yayansa dasu fateema, kamar babu komai sukad'an ta6a hira sannan yamusu sallama yatafi.
Shima sallar isha'i suka fito da yaran.
Baidai sha ruwaba sai bayan isha'i daya dawo yay wanka............✍🏻



*_wayata tagajine, iskanci takemin, ALLAH dai yasa nasamu na k'arasa buk d'inan, shiyyasama nabar chart d'in dannayi manage,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login