Showing 87001 words to 90000 words out of 107296 words
dashi tana kallonsa
"Better half"yafadi hakan yana kallonta sannan yasa hannu yana murxa hannunta,
"Wai haryanxu su baban basu dawo ba?!"
"Ohh damn it,better half nikam meyasa baki trusting d'ina ba nace maki suna qatar wani aiki baba yake acan"
"Shikenan"tace dashi a takaice,
"How about a frozen yoghurt?!"
"I'm already drooling sweethrt"
"That's my gurl"
Juya kan mota yai yatasheta suka bar wajen,
___Akwana atashi kwanan su Ummi Aisha biyar da aure kullum jiya I yau,ba abinda yatab'a shiga tsakaninsu na auratayya,kullum de xataci kwaliyarta tagyara gidan tsaf,abinci kuwa kala kala mama ce keyi take aiko masu dashi,kodah Ummi Aisha tayi masu wani abin marmarin itadashi bayaci kullum cikin fad'in ya k'oshi yake,bawani hira dake shiga tsakaninsu,takanyi kuka tagayawa Allah buk'atunta kodah sunyi waya da amminta bata tab'a fad'a mata halin datake ciki ba,tun safe yake fita aiki dagacan yawuce school baxe dawo ba se gaf da magrib insabone harta saba,takuma tsaida k'arshen satin aranar daxata fad'a masa itama tanaso tai resuming school tunda ankusa fara exams,ranar lahadi da yamma tana xaune taji tana sha'awar tuwo don rabonta da tuwo tun kafin afara bikinta gashi tunda mama ke aiko da abinci bata tab'a aikowa da tuwo ba,da sauri ummi Aisha tashiga kitchen tad'ora ruwan shinkafar tuwonta,zafi taji garin dukkoda sanyin na'urar ac n dakeyi hakan be hanata jin zafi ba,da sauri tahau sama tashiga d'aki ta canxa Kaya cikin jeggings wando iya gwiwa tasaka vest kad'ai,sannan tad'akko hijabi tasakko dashi kodah taji muryar ashraf tai sauri tasaka,cikin awanni k'alilan tagama tuwon shinkafarta miyar kuka da manshanu dayake duksu Kuka da sauran kayan kad'in miya amminta tayo matasu,sedataci tai nak sannan tahau sama tayo brush tai sallah,xama tai a parlorn saman ta kunna channel na foreign policy tana kalla dayake suna saka updates na diplomatic issue/affairs Kuma field d'intane tunda international relations take,se bayan magrib da dad'ewa ashraf yadawo yai parking motarsa yashigo cikin gidan da sauri yaxaro handkerchief yatoshe hancinsa dashi yanabin parlorn dakallo dake cike da k'amshin kuka da manshanu,gashi babu warin abunda yatsana a duniya irin warin miyar kukan datasha daddawa gashi warin ya baibaye ko'ina na parlorn,
"Ummi Aisha"ashraf ya k'walla mata kira da k'arfi yanasake toshe hancinsa da handkerchief,
Ummi Aisha dake sama tana kallo tajiyo muryarsa ba kanta kenan tafadi hakan azuciyarta dayake ashraf d'in bame hayaniya bane,maganarsa bata futa sosai shiysa tayi mamaki k'warai dataji sunanta da k'arfi dayakira kamar a loudspeaker,da sauri ta rarumo hijabinta ta d'ora akan vest d'in jikinta gashi hijabin roba ne yana nanewa ajiki se asannan ta tuno vest ce kawai jikinta da sauri tai hanyar d'aki don saka abaya akai muryarsa ce ta tsaida ita daga shiga cikin d'akin,
"Ummi Aisha"yasake kiranta a karo na biyu,
"Na'am just a minute"tace hakan sannan tasaka hannunta cikin hijabin tad'agoshi tayadda baxe kwantar mata ajiki ba,tasauka k'asan da sauri........
•✨•
Wannan page d'in nakune masoya makaranta littafin Ummi Aisha,inasonku kuna raina a kodayaushe,Ina kuma fatan xa'a cigaba da hak'uri da 'yar mutan yerwa makaranta ta aure ni,Team#UMATM✨
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:59 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
85
©®MISS XOXO
👄
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
K'arasawa tai cikin parlorn tana sanye da hannunta tacikin hijab,ashraf yadubeta daga sama har k'asa sekuma yad'auke Kansa haryanxu hannunsa rik'e da handkerchief yana toshe da hancinsa..
"Warin me wannan?!"yace da Ita yana binta da kallo
"Wari Kuma?!"ta bashi amsa tana d'an bud'e hancinta don ita kam banda k'amshin kukar datasha daddawa da manshanu ba abinda takeji ,
"Tambayarki fa nake"
"Nide gaskia banajin warin komai"
"K'arya namaki kenan??" hakan yana watsa mata wani sihirtaccen kallo da manyan idanuwansa,
"Bance ba"tadauke kanta don baxata iya jure salon kallonsa ba
"To bani amsa na" yafadi hakan yana sake kafe ta da ido,
Tagane kallonta yake dukkoda kanta a k'asa yake a hankali tace
"Tuwo nayi shi nake marmari tunba yau ba"
"Amma ki rasa mexaki se
miyarnan me wari"
"Miyar kuka ce fa"
"To nikamde duk abinda natsana a duniya yabi bayan miyar kuka saboda haka kisan yadda xaki wannan warin yafita"yakarashe maganar yanabin Kayan jikinta da kallo wanda tafito d'as kamar barbie doll,
"To"kawai tace atakaice sannan tanufi kitchen d'in
Cikin k'ank'anin Lokaci ta d'ora gawayinta irin na sachet d'innan akan gas minti d'aya ya huru,cikin sauri ta janyo kwalbar turaren wuta dayake ta ajiyeta musanman saboda k'aurin abinci,bulala turaren wutar tai nandanan kitchen d'in ya fara tashin k'amshin turaren Wutar har cikin parlorn, ashraf dake cikin parlorn se asannan yacire handkerchief d'in hancinsa yana shak'ar k'amshin turaren Wutar dayake tashi,futowa Ummi Aisha tai daga cikin kitchen d'in d'auke da kaskon Wutar tana turare lungu da sak'o na parlorn haryanxu taki cire hannunta tacikin hijab d'in,kasan hijabin tasa tana kame da kaskon wutar,bayan tagama ta ajiye kaskon agefe k'amshin yacigaba da tashi,sannan tai hanyar bene xata koma sama,muryar ashraf ce ta tsaida ita.
"Ke" yace da Ita yana kauda Kansa gefe bayasan ta lura da kallon dayake mata,
Don sosai a idon ashraf xaka gane yana matuk'ar buk'atar matarsa,
Jiki sanyaye tadawo harga Allah ta tsani ke d'in dayake ce mata kamar wata y'ar aikinsa,
"Gani" tace dashi tana isa Inda yake,dagacan baya ta tsaya tana sauke da kanta k'asa tana wasa da faratanta da suka sha maroon nalle/lalle.
"Me zaki a saman da kike sauri haka??"
"Kal..kallon news nake na foreign affairs" tabashi amsa a d'an tsorace muryarta na rawa,
"To bansallameki ba,Kuma inasan kicire hijabin jikinki waye xe kalli wannan jikin naki ?!" Yakarashe maganar yana tab'e bakinsa had'e da d'auke kansa amma axahirin gaskia so yake yaganta ba hijabin don da hijabin ma tayi Kyau ballantana ta cire,
"Sanyi nakeji fa" tafadi hakan tana komawa bayan k'arfen benen,
"Kinsan Allah sekin cire awannan xafin xakice sanyi kikeji??"
K'in cirewa Ummi Aisha tai tana rik'e da hijabin nata kamar wanda xa'a k'wace,ganin baxata cire ba yasanya ashraf mik'ewa daga inda yake yana nufar wajenta,tana ja da baya yana binta har bango suka kai sannan yasa hannu d'aya yatokare ta ajikin bangon tareda sa d'ayan hannun ya xare jan hijabin nata,kasa aikata komai yai ganin abinda ke jikinta Lokaci k'alilan k'wak'walwarsa tafara ayyana masa abubuwa,tunda ga k'afarta yake kallonta har xuwa kanta da yadda tai parking shukunta na baya ga jelar gaban yala yala ta zubo a fuskarta,samin kansa yai dabin rigar jikinta da kallo yadda ta kamata ga rigar transparent ce sleeveless ana ganin komai na ciki don batada maraba da net na sauro gashi Ita kad'ai tasaka,ya jima yana bin jikinta da kallo itako idonta a rufe yake ta takure atsorace gani take duka xekai mata,da sauri yacire hannunsa daga jikin bangon yakoma kan kujerar dake facing inda take a tsaye yaxauna yana kallonta wadda da alama batasan yabar wajen ba sosai ta runtse idanuwanta tana tsakure,zuciyarsa ce tafara kawo masa abinda yaci alwashin baxe aikata ba ahankali yadafe kansa yana girgixa shi,yana taune da lips d'insa yana fezar da zazzafar iska daga bakinsa,seda Ummi Aisha taji alamar yabar wajen sannan ta bud'e idanuwanta a hankali taga baya wajen yana xaune kan kujera ya tsurawa tv ido kamar me kallo amma ba kallon yake ba yanayin da yasameta cikine yasashi wani tunanin na daban daya dad'e beyinba,ahankali taja sayyadar k'afafuwanta ta tsakure a kujera tanayi tana kallonsa gaba d'aya ta tsorata da shi,sallar isha'i ce ta ceci Ummi Aisha daga tsakuren datake ahankali ta mik'e tahau saman ko takanta bebiba,tana shiga d'akinta tai saurin fad'awa band'aki tayo wankanta had'e da d'auro alwala,kakkaurar atamfar daviva tasaka me style bubu sannan ta yane kanta da mayafin abaya bak'i dake akwai ratsin bak'i ajiki,sallah tayi had'e da tab'a karatun alqur'ani sannan ta xauna tana naxarin yadda xata b'ullowa ashraf yabarta takoma makaranta,
•
"Kasani zikiri ga Allah ta'ala ba k'aramin babbar kariya bace izuwa ga bil adama,ace de mutum kullum besan ya kamataba Ina karatun arabin ka yake?!bokon nan da kukafi bawa mahimmanci babu inda xata kaiku"Mahaifin muhannad ne keta wannan banbamin masifar yanayi yana kallon muhannad d'in da suka fito daga masallacin dake cikin gidan nasu,
"Baba nayi fa"
"K'arya namaka kenan ko angaya maka ba na lura dakai kullum haka kake"
Har cikin gidan suka shiga magana d'aya ce de suketa maimaita ta,ta inda uban yake shiga ba tanan yake fitaba,se haurawa yake yana saukewa muhannad d'in kwandon masifa da alama ransa yakai matuk'a a b'aci,
"Haba alhaji hayaniyar me kukeyine haka?!tundaga gate akejiyo muryoyinku lapia kuwa??"
Hajia sakeena mahaifiyar muhannad Ita ke fad'in hakan lokacin da ta amsa sallamarsu da suka shigo cikin parlorn xama mahaifin muhannad d'in yai akan doguwar kujerar dake parlorn yaxare hular kansa ya ajiye agefe,se huci yake shi kad'ai,seda ya nutsu sannan yakalli muhannad daya rakub'e agefen kujera daga k'asa yana sunkuyar da Kai kamar munafuki,siririn tsaki yasaki yamaida dubansa ga Hajia sakeena dake jiran yalabarta mata abinda yafaru,
"Wannan yaron da kike gani nibansan wane iri bane shi,acede kullum mutum kamar me k'wak'walwar kifi aita masa magana amma da ike yanuna shid'in d'an yaune seyasa k'afa yai shuri da abinda akace masa?!"
"Alhaji ni kasani cikin duhu Wai meyayine? "
"Wallahi inde mutum yace shi se boko kawai to Wlhy rayuwarsa baxata tab'a tafiya daidaiba,kwita ganin abubuwanku basa tafiya daidai duk wata sabuwar cuta tafito se mutum yayita saboda baya karatun alqur'ani baya lazumi baya azkhar naneman kariya daga ubangijinsa shiyasa ko sihiri akaima mutum ko kanbun baka da na ido ke saurin kama irinku,kullum ga k'anwarka nan cikin karatun qur'ani take da lazumi kala kala babu dare babu rana amma Kai kaine kullum cikin bawa aikin yahudu muhimmanci,gobe kaine kallon wasan barcelona jibi kaine wani had'add'en joint to kasani duk wasu moves d'inka ana kawominsu,Kuma shi karatun islama ba'a girma dashi komai girmanka ance kafita ka nemo ilimi,gashinan samarin unguwarnan harda Wanda suka fika suna had'uwa suna karatun qur'ani da littattafai da daddare,kaikuwa ina kai ai gani kake ka wuce ajinnan kana can kana xargawa karenka igiya se inda k'arfinka yak'are" yak'arashe maganar yanajan dogon tsaki
"Nima ina masa maganr hakan alhaji"
"Babban abin takaici liman na sallamewa xakiga ja'irin yaron nan ya mik'e yafita ko zikirin bayan an idar da sallah ne bayayi,ko addua yayi yashafa bayayi seda yai hanxarin dawowa gidah kulllum 24/7 rik'e da wayar hannunsa yana chatting yana murmushi sekace tab'abb'e bakiji kunyar danakeji ba inyai hakan.Don haka xakiga mutanen cikin masallacin sunbishi da kallo ,kowa yana jiran liman yashafa addua amma shi sauri yake yafuto yadawo gidah,Allah ya kyauta"
"Gaskia kam baya kyautawa tanan b'angaren,Wlhy alhaji namasa,namasa bayajine kawai"
"Ai kunnen k'ashi ne dashi,yadda kikasan shiya haifi kansa haka yake Kuma shi kad'ai ne halinsa yafita daban"
"Ayi hak'uri de alhaji,Kai muhannad kabawa mahaifanka hak'uri ka kuma yiwa kanka fad'a"
"Hak'urin me xebani?! aini beyi mun komai ba yasamu de yayiwa rayuwarsa karatun ta nutsu"
"Baba dan Allah kayi hak'uri kayafemin kuma Insha Allahu xan dingayi" muhannad yafad'i hakan muryarsa da alamar nadama donshi Kansa rabonda yad'auki qur'ani yakaranta ko yai adduar kariya baxe iya tuna yaushe bane,
"Niba kamin komai ba Allah ya yafemu gaba d'aya amiin"
Seda muhannad yatabbatar hankalin iyayen nasa ya kwanta sannan ya mik'e yashiga d'akinsa,
_____Ranar lahadi ranar Ummi Aisha tacika sati d'aya agidan mijinta ashraf,xaune take akan gado tagama waya kenan da amminta,tashi tai tana zagaye d'akin da alama naxarin wani abin take,da sauri ta d'auki mayafinta akan stool na mudubi kalar kayanta ta yafashi akanta tulin gashinta yafuto ta baya,sauka k'asan tai da sauri ganin ashraf yasanyata tafiya ahankali,tundaga saman datake sakkowa yake binta da ido sosai tamasa Kyau cikin shigar filtex blue and yellow datai Kayan ya amshi jikinta dukkoda ba kwalliya tai ba amma fuskarta tayi Kyau sosai,ganin tana kallonsa yasashi had'e rai yana cigaba da kallon jaridar weekly trust dake hannunsa yayi hakanne don karta gano kallonta yake,k'arasawa kujerar dake nesa dashi tai taxauna,ahankli tafara fad'in;
"Dan Allah inaso nai resuming school"tafad'i hakan cikin muryarta me dad'in sauraro,
Shiru ashraf yai bebi takanta ba sema sake bud'e wani shafin yai na jaridar yana cigaba da karantawa amma axahirin gaskia ba karantawar yake ba kallon k'asa yake mata yajima yana bin y'an yatsun k'afarta da kallo dake d'auke da nalle sosai sun burgeshi matuk'a yashagala da kallonsu muryar Ummi Aisha tasake masa reto a kunnensa,
"Kaji"tace dashi kamar xatai Kuka....
"Wai kaji?! ni d'ankine?! Nifa ba d'anki bane kullum maganar ki kenan ko kanajina?ko kaga...haba wannan wacce irin rayuwace? ko ni Idan xankiraki kinji nake ce maki?!sekace wani d'anki na fari" yakarashe maganar fuskarsa cike da takaici,
"Kayi hak'uri toh,inaso nai resuming school ne xa'afara exams pls ashraffff.....!"Yadda taja raffffff d'in har cikin k'wak'walwarsa,
Samin Kansa yai cikeda jin dad'in yadda takira sunansa duk duniya seyaji babu Wanda ya iya kiran sunan nasa kamar Ita,barin yadda tajashi takuma fitar da haruffan yadda suke har magudanar jininsa yaji dad'in hakan, da saurinsa kamar xa'arugashi yace;
"Shikenan ki shrya gobe Idan Allah yakymu xaki fara xuwa"yafad'i hakan yana binta da kallo
"Yeyh thank you so very much Allah yasaka da alkhairi amiin"tace hakan cikeda jin dad'i don bata xaci amsar daxe bataba kenan
"Ameen" yace atakaice har cikin zuciyarsa yaji dad'in abinda tace,shyasa take sake shiga ransa saboda akwaita da addua da Kuma yaba kyauta komai k'ank'antarta,
Haka suka xauna xaman kurame suka tsurawa tv ido suna kallon Indian film d'in 'prem rotan don payo' amma kowannensu da abinda yake sak'awa cikin zuciyarsa.Har shabiyu ta gota itade Ummi Aisha b'ingirewa tai tana bacci se ashraf ne yatasheta yace taje ta kwanta,
Washegari;da sassafe da yake lectures d'in 10 ne dasu da wuri Ummi Aisha tatashi tun asuba datai sallah take shirin sch don d'oki take tayi,tashiga kitchen ta soya chips and egg da ruwan tea,sannan takoma saman tai wanka kafin 8 harta gama kintsa ko'ina nagidan takuma shirya cikin abayar Lebanon ja ta yane kanta da mayafin abayar light makeup tai had'e da saka jambakinta na kiley 24hrs red se k'amshin strawberry yake ,mild turaruka tasaka,handbag d'inta ta rataya bak'a da covered show d'inta shima b'aki tasauka k'asan parlorn cikin hanxari taxuba chips and egg d'inta taci takora da ruwan tea tasake kuskure bakinta da mouth fresh,se gurin k'arfe tara saura ashraf yasakko sanye cikin manyan kaya riga da wando blue da hularsa xanna bukar light kalar xanen dake gaban rigar se k'amshi yake yayi Kyau abinsa,ya jima yana kallon Ummi Aisha sosai tamashi Kyau musanman dayake red abu yana fito da mace yana Kuma yiwa Ummi Aishan Kyau ga jambakin datasa yasake fito da d'an k'aramin bakinta yayi Kyau dashi,
"Ina kwana?!" Tace dashi tana kallonsa don shid'inma yamata Kyau ba kad'an ba,
"Yana kwano" yace da Ita yana shiga kitchen,
Ko kad'an bata damuba don inde arrogant halinsane tuni ta saba dashi , tun abin yana damunta harya dena,cikin mintina kad'an yafito da cup ahannunsa da alama coffee ne ciki don k'a idane kullum dashi yake karyawa Kuma shi yake had'a abinsa don bayacin abincin datai shiyasa koxatayi cikinta kad'ai take girkawa se megadi datake xubawa,seda yashanye tass sannan yaxuba mata idanuwa yana kallonta,murmushi yai dake k'ara masa kyau yana taune pink lips d'insa,itakwa banda kallon agogo ba abinda take Allah Allah take karsu makara don bataso malami yafara lectures bata class gashi mentor d'intane xe masu lectures d'in wato professor tajuddeen...
"Ina zaki jene?!" Yace da Ita yana murmushi,
Ware Ido tai tana kallonsa cikeda mamaki,ahankali tace
"Makaranta mana jia fa kace yau xanje"
" a hakan xakije?!"yace hakan yana nuna shigarta
Bin doguwar rigar abayar dake jikinta tai da kallo ko kad'an bataga makusaba,sosai abayar take a baje ko kamata batai ba ga mayafinta wadatacce,
"Ai rigan be kama ba"
"Ance maki matan aure na xuwa da kwalliya makarntane?!"
"Ba kwalliya nai ba fa, abaya ne fa"
"Ba dressing d'inki nake magana ba"yafad'i hakan tareda mik'ewa yanufi inda take,
Hannunsa yasa akan lips d'inta masu laushi,
"Is either ki goge wannan jambakin da kikasa koki xauna agidah abinki"
Tissue taxaro da sauri cikin jakarta tashiga goge jambakin,shaf ta manta 24 hrs ne baya goguwa Lokaci d'aya,
"Na goge" tace dashi ,
"I'm not kidding,kode ki goge shi konai tafiyata nabarki kidena b'atamin Lokaci"
Mudubin console d'in dake jikin bango ta duba fuskarta se asannan ta tuno 24hrs kiley jambaki tasa,
"24hrs ne baya fita yanxu kaji?!"tafadi hakan ahankali cikin shagwab'a
Siririn tsaki yasaki had'e da k'arasawa kusa da Ita yasa hannunsa ya jinginata ajikin bango ahankali yasaka bakinsa kan leb'anta seda ya lashe jambakin tatas gawani kamshin strawberry dasukeyi,sannan yafara kissing nata passionately harda sa hannu yatallab'o k'ugunta,sosai yake kissing d'inta romantically seda Ummi Aisha taji yana k'ok'arin sa hannunsa cikin rigarta tai saurin k'watar kanta takoma baya,se maida numfashi take har ashraf d'in dake gefenta maida numfashin yake Lokaci d'aya idonsa ya kad'a yai ja,da sauri yadedeta Kansa yafita waje binsa tai abaya tashiga motar,banda murmushin mugunta ba abinda ashraf yake itako Ummi Aisha se sunkuyar dakai take cike take da kunyarsa gefe d'aya Kuma tsoransa takeji,ganin yadda lips d'inta har d'an kumbura sukai,har suka isa makaranta babu Wanda yakewa wani magana cikinsu....!
•✨•
Ina mik'o gaisuwata ga masoya littafin Ummi Aisha,ina Kuma godia ga Wanda suka kirani da Wanda suka min messages na jin yaya lapia ta?! Alhmdlh inajin sauk'i Allah Kuma yasaka maku da mafificin alkhairinsa ameen....!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.......
[4/18, 11:59 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
86
©®MISS XOXO
👄
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
Suna xuwa yai parking a parking space dake department d'in,sannan ya sa hannu ya k'aro air conditioner na motar,Ummi Aisha kamar tasa kuka ganin goma harta wuce da minti goma gashi batasan afara lectures ba ita,duk abinda take ashraf na lura da Ita yaxuba mata manyan idanuwansa yana kallonta ta k'asa yana sane yak'i bud'e mata lock ta fita,
"Pls karfa prof yafara lectures kaji" Ummi Aisha taceda ashraf hakan,
Yi yai kmar beji metace ba yacigaba da bin taken wak'ar mad over you dake tashi ahankali cikin motar,
"Pls ashraf"tace dashi hakan finally with full confidence,
Lock