Showing 12001 words to 15000 words out of 107296 words
hafsat dinsa,yanzu idan magajiyan tashigo abinda xecigabada faruwa kenan ,lalle dole yakara dagewa da addu'a dan abinda su sadeeya suka aikata ba karami bane,
"Haka yadanne xuciarsa suka cigaba da hira sama sama dasu gwaggo ,dukkoda xuciarsa a kuntace take,Sarai saboda su surayya sunsan abinda suka aikata ko keyarsu beganiba tunda yaxo,'maganar Yaya sameer ce tadawo dashi daga duniar tunanin daya tafi,
"Adam inde yau xaka juya gwara kai haramar tafiya naga garin yau kam Alhamdlh antashi da hazo,
"Capt adam yace kwarai gaskia to barimuyi sallama ,Sannan yaduka kusada gwaggo ,yace gwaggo xamu tafi,"gwaggo tace toh Allah yakayku lapia ,Sannan tace to wannan yaron(Yaya sameer)jamu muyi addua ko?!
"Yaya sameer yace Toh gwaggo ,Sannan yafara jero du'ai,sunayi suma harya karkare da fatiha da salatin annabi Sannan suka Shafa,
"Capt Adam yaciro bandir na 1k guda biyu ya ajiye agefen gwaggo,'gashi gwaggo bayawa ayi hidimar biki,Sannan yadan Sosa keyarsa Yana mikewa daga sunkuyon dayi,naga kinyi lefe ma gwaggo toh Allah yasaka da alkhairi,kila natafi abuja ma gobe,inde tafiyar tayiwu to baxan dawo kaduna ba kuma Se Allah yakaymu ranar asabar din da safe ko jumaa da daddare,
"Gwaggo tace toh angode Allah yashi albarka,inde tafiyar bata yiwuba daka 'kokarta kaxo kunyi magana da magajiyan ko?!yanzu ma badan da hazo ba ai daka biya kun gaysa..
"Shide Capt Adam gaba yai Yana tafiya Yana magana,gwaggo yanxu da haxo gaskia mayi magana da ita ta Waya ba matsala ,
"Da sauri sauri Capt Adam yaiwa Yaya sameer sallama Sannan driver yajashi se kano tadabo tumbin giwa koda mekazo anfika,
KANO;
"Hafsat ce tarako sister dinta mjay xuwa parking space suna magana suna murmushi,
"Hafsat tace toh mjay sekuma yaushe?! koda yake ranar Saturday din xanxo gida insha Allah,
"Mjay tace toh Yaya Hafsat Allah yakawoki,ai ba ranar kikace daurin auren Yaya Adam ba?!
"Hafsat tadafe haba oh ni hafsatu ,mjay karfa kije kina broadcasting wannan zancen agidah Sarai nasan halinki,to wallahi xance yafito waje ba abinda yashafeni,xance bansan magana ba sede in mama(mahaifiyarsu)ce tasani agaba itama kuma Bana fatan tasani,
"Mjay tai daria ,Yaya hafsat to inba afadaba suwaye xasu tsaya sumaki DANNAN 'KIRJI?!(littafin mrs jh taredani MX)dukkoda nasan ba auren so da shakuwa bane xasuyi,Sannan tabude mota tashiga tana daria,
"Hafsat tasa gefen mayafinta ta kwadawa mjay a fuska da wasa,wato naxama abin tsokana kenan ko?!xakixo kisameni,kigayda su mama kafin inxo,Sannan sukai waving juna,ita takoma ciki,ita kuma taja mota ta tafi gidah..
•••••••
"Karfe biyar saura kwata su Capt Adam suka shigo garin Kano,harsun dau titin sardauna crescent,Capt adam "yace jirgi juya kan motarnan muje zoo road,yasunan shopping center dinnan dakuke yawan xuwa da Hajia ma?!!kaji sunan yabace mun kasan wurin shopping dinne sunyi yawa agarinnan gasunan lungu da sako'
"Jirgi yakada Kansa ayyo sahad stores kake nufi ko?!bare shi ance garuruwa dayawa akwai kantin nasa,,,,"capt Adam yace tabbas sahad stores ne,ai a abuja har biyu ne dashi,"jirgi yace kwarai kuwa oga anan dinma guda biyu ne,,sunata magana har suka isa sahad stores dake titin zoo road Kano ,parking jirgi yayi a parking space din da'aka tanadeshi dan motoci,
"Jirgi na parking Capt Adam yace fito harkai xamu shiga ciki ai,tare suka shiga cikin shopping center din,nan idanuwansa suka kai akwatinan dake jere nasayarwa kusada wurin biyan kudi na maza,tsayawa yai yana admiring kyan wani akwati me set 3 da kit,kirar company din Victoria secret sosai sunyi Kyau gasu kuwa best color din Hafsat dinne wato purple amma da ratsin black Se yabada unique style,
"Kusa dashi wasu dattijan mata ne har biyu suma suna kallon Wanda xasu dauka ,da alama lefe xasu hada dan ga carriage nan na stuffs cikeda kayan kwalliya da aramfofi a hannun daya daga cikinsu,
"Capt adam yadan matsa kusada su Yana kallon dayar dake neman akwatin daxasu dauka,'ahankali akuma nutse yadan gaishesu Sannan yace hajia Dan Allah wannan sets din sunyi Kyau kona dauka wasu?!
"Matar daya cewa hajia tai murmushi "wallahy sunyi Kyau sosai,yanxunnan nake cewa 'kanwata kinga sets din hannun bawan Allahn can sunyi Kyau sosai da da irin design din damun dauka wa faruk,kaninmune daxeyi aure,
"Capt adam shima murmushin yai,nagode Hajia ,Allah yasanya alkhairi nima lefen nakesan hadawa ayanxunnan,yanayi yanadan sosa kansa,
"Matar tai daria masha Allahu,to bari mutayaka kafin nan ankawo wasu designs din,dama yanxu sukecemana inba sauri mukeba ansauke Kaya yanxu mubari agama shryawa semu xaba Wanda mukeso,to dama faruk dinmuke jira xekawo mana sako ma,
"Capt adam yai godia Sannan suka shiga tayashi hada Kayan kamar wasu yan Uwa sosai yasake dasu dayake basuda dauke kai ko wulakanci,toh sudinma haka suka yaba da hankalinsa lokaci daya kuma yashiga cikin ransu,har faruk din yaxo shima yashiga tayasu,suka hadu suka hada komai har shima Capt Adam din yatsaya suka hada na faruk din,har akai sallar magrib,seda sukai sallah suka dawo Sannan suka karasa hada abinda babu aciki,
"Sosai Capt adam yamasu godia kusan rabin kayan dasuka siya shiya biya masu ,Sannan sukai exchanging digits din juna suna cewa sesunxo bikin juna,Shide capt adam daria yai kawai,
"Jirgi driver ya loda kaya a mota Sannan suka tafi gidah suna yaba karamci irin namutanen dasuka hadu dasu,ana kiraye kirayen sallar isha'i suka isa gidah,seda Capt adam yatsaya yai sallah a masallacin dake kofar gidan Sannan yashiga ciki,
"Dadda'dan kamshin turaren wutan da hafsat tasane yafara dukan hancinsa,yawani lumshe ido Sannan yabude har cikin ransa yakejin dadin tsaftar da hafsat keyi,ko'ina nacikin gidan tsaf kai kace duk seconds ake gyarawa,sallama yakarayi akaro nabiyu Sannan hafsat tafuto tana gayra daurin dankwalinta,
"Dagudu ta amsa sallamar sannan tai hugging mijinta tanajin sonsa,"sannu da xuwa hayatee I knw you are tired and exhausted,"Capt adam yai murmushi bayan yadagata cak yamata maxauni akan cinyarsa bayan yaxauna akan kujera,"I'm very tired my Hafsat ,but yanzu I'm okay tunda naga kyakkyawar fuskarki,wai meye sirinne naga Kullum bakya tsufa kaman sanda na auroki?!
"Hafsat tai murmushi hayatee kenan Ina godia ,babu wani sirri Allah ,naga ban tsufa ba kwata kwata nawa nake 38 fa,tanayi tana shagwabe fuska,captain adam yabata peck a kumatu toh nagodewa Allah akullum ganinki nake kamar time din Dana auroki kina 18 lokacin,"Hafsat tai daria,yo kaima aibaka tsufa hayatee,
"Capt adam yamike yana daria fada kike kawai ina,adam ba hadeje aiyakai gangara ,barinje in watsa ruwa my hafsat se inxo inci abinci dan your aroma is calling..."Hafsat tai daria toh seka fito barinyi arranging table kamar Kansa favourite dinka aka dafa,
"Capt adam yace wow,Ina godia dole abaki tukwici my Hafsat,"wanka yashiga yayi Sannan yafito suka ci abinci tai feeding din mijinta sosai,Sannan suka hau hira inda yake fada mata gwaggo tace magajiya xata xauna a kaduna,Sannan yakira jirgi kan yashigo da akwatinan,
"Ana shigo dasu Hajia hafsat tace wow sunyi Kyau Walhy ,yanxu yaushe xa'akai lefen gashi time Yana kurewa?!!!
"Capt Adam yai Daria bayan yasallami jirgi driver yatafi yadago yakalleta,ahankali yataso yadawo inda take Yana kallon kwayar idonta,"my hafsat bakayan lefe bane wannan ,wannan gwaggo tariga tayi har ankai,wannan nakine halak malak hayatee dinki yabaki,
"Hafsat ta ware Ido ,hayatee kana nufin Kayan fadar kishiya ne wannan?!aidabaka wahalar dakankaba,nida ka shawarceni wallahy dabaka siyo ba,seta fara hawaye amma tai sauri tai kasa da kanta danbataso yagani,murya narawa take fadin,duk yawanci sanda kafita kokai tafiya seka kawomin Kaya/sutura/clothings...wallahy sun isa haka hayatee..I do not know what I would do without you,you'hv been there for me thru it all you protect me with everything in you..
"Capt adam yai saurin katseta ssssh my hafsat,I am because of you,not you because of me,I love you pass my mind beyond my soul,,matata Ina matukar sonki,duk abinnan danake maki kadanne nadaga tarin farin cikin dakike sani,tabbas kece FARIN CIKINAH(littafin hafsart Rano)you are indeed my everything ,bar kuka my Hafsat Allah yabarmun ke,yabamu abinda muka dade muna addu'a akai,....
•✨•
Gaisuwa maitarin yawa ga masoya littafin UMMI_A'ISHA..inajin dadin yadda kuke 'karfafamin gwiwa Wlhy..baxan iya lissafokuba sede ince Allah yabar zumunci inasonku aduk inda kuke,Allah yabarmu tare..
nanahafsat.wordpress.com
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
12
©•MISS XOXO
👄
DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼
•✨•✨•✨•✨•✨•✨•
"Hafsat tai shiru tana ajiyar zucia,gawani dadi datakeji yana ratsa 'bargon jikinta nadaga abinda hayatee dinta yake fada, a shagwabance tace'I love you the most of everybody,inakuma alfahari dakai akoda yaushe,Allah yabarmana kai hayatee dina....
"Capt adam shima ajiyar zuciar yai ganin tadena kukan datake dan sosai yakejin kukan nata aransa,ahankali yashiga rada mata sanyayyun magana masu sanyaya xucia a acikin kunnenta Wanda Ita kadai tasan meyake nufi dasu,tunda iya su kadai sukasan mesuke cewa,ahankali yaxame ta daga jikinsa Sannan yashiga kiciniyar bude akwatinan,seda yabude su duka Sannan yasakko da'ita daga kan kujeran,oya duba abinda beyiba se'amayar,
"Ware Ido Hafsat tai tanabin kayan da kallo Wanda kowane gida akakai su amatsayin Kayan lefe xasu karbu,sosai suke shake da Kaya ,babu ce kawai babu aciki,hafsat tabi laces da materials din da kallo uwa uba takalma da jakankunan dake ciki designers su suka Kara sata ware Ido,sosai tajima tana kallon Kayan Wanda seta dau shekaru basu kare ba dan sunada yawa,
"Captain adam yai 'kasa da ido Yana kallon 'kwayar idonta ahankali yakai hannunsa yadora akan nata ganin yadda tai shiru da alama ta lula duniar tunani,my hafsat you liked it?!idan basuyiba yanxu ma lokaci bekureba semuje acanxo wasu akullum ina gaya maki your happiness matters most,feel free my hafsat....
"Hafsat tai murmushin da dimples dinta suka lotsa Wanda idan tayi Ita kanta tasan tagama da capt adam,"ware ido tai tadora akan nasa fararen idon dasuke mike dagashin ido zara_zara,hayatee wannan kayan ko lefen 'yar gata se haka,wallahy harcikin xuciata nakejin son kayan nan,shirun danai kuma wallahi mamakin yawon Kayan da kyansu nake,wallahi Kayan nan sunyi matuka kuma nagode wallahy bansan tayaya xannuna maka iyakar godiar nanba,Ina rokon Allah kada yakawo ranar daxan 'saba maka hayatee insha Allah bana tunanin akwai ranar daxataxo Wanda xaka kawo abu cikin gidannan nace beyiba ko banaso,wani ma baxan masa haka ba ballantana kai dakaikadaine acikin zuciata,ai wannan Kayan sun wuce beyond like,I really loved them..kalla yanda suke daukan ido,what amazes me most was the boxes ,,Hayatee favourite color dina kasamu,wannan de second lefe kamin,nagode Allah yakara daukakamin kai,yabarmu tare har abadan abidina,
"Capt adam ya washe fararen hakoransa Wanda suke jere ras acikin bakinsa,'Alhamdulillah ya rabb I feel beyond blessed,and I'm very glad that you loved them....ai my hafsat komai namaki banfadi 'kasa ba sede fatan Allah yabarmu tare,batin yawan Kaya kuma karki manta kedin 'YAR GATA CE(littafin miemee)'yar gatan adam,ko kin manta da wakar da marigayiya(deceased) baba laure ke mana?! "hafsat yar gata ce,'yar gatan adam captain.....
"Hafsat tai daria tana rufe baki,wai tsohon zance Kasan lokacin nan i was 17 fa,baxan manta ba ,,Kai Allah sarki baba laure Allah yajikan Wanda suka rigamu gidan gaskiya da rahama amin,
"Capt adam yace ameen ya rabbi ...kai baba laure akwai abin daria sosai...'Sannan yace my hafsat baki tambaye ya akai nahada wannan kayan ba...
"Hafsat tai daria wallahy inataso natambaya kuma namnta I'm all ears hayatee gist me,nasan kila jirgi ne yai haka dan sometimes i wonder yadda jirgi yasan womanly abubuwa haka,'
"Capt adam yadinga daria harda rike cikinsa sedayai kwala"my hafsat kinsawa jirgi ido fa,kimasa excuse kinsan shikadai ne namiji adakinsu acikin su 10,taran duk mata ne shikadai ne Allah yai blessing iyayensa dashi sekuma yaxo yasami mata data maidashi kawarta'kwanaki yanagayamin yana washe baki ,kinaji nakira shi nace yaxo yakaini unguwa seyaxo lokaci a kure,time din kinje gidah,wallahy Ina Gaya maki waidana tambayeshi meyasa haka kinsan meyacemin?!
"Hafsat tadinga daria dakyar tadago kanta tace a'a..
"Capt adam yace hmm secayaimin wai wallahy oga ,me 'daki nace ana mata 'kunshi shine tace nakular mata da abinci inyayi nasauke kada nafita ya 'kone,kinsan me ?!yanayi yana sosa keya yakecemin wallahy oga toh senadan sake dauraye kwanukan gidan ,dayake xamuyi baki kasan takusa sauka(haihuwa)...Capt Adam yakarashe xancen yana magana irinta jirgin... dan haushi my Hafsat ko kallonsa banyi ba nabude murfin mota nashiga,
"Hafsat tadinga daria tana 'kyakyatawa wallahy hayatee ka iya gwada maganar sa kuwa,amma jirgi ya iya abin daria,no wonder yake haka.. gaskia dole na masa excuse kam,amma ya iya zaben kaya dukda nasan hayatee dina shima ya iya daukar favourite choice...amikamin godia metarin yawa ga jirgin,
"Capt adam yace Wlhy kuwa ,amma bafa shikadai muka hada Kayan dashiba,nide nasan I partake in chosen your favourite colors tundaga sets na akwati se kuma jirgi daya temaka da su sets na bangles da necklaces da earrings(awawwaro,sarkoki dakuma dankunnaye)sena 'hadu dawasu manyan mata dattijai xasu girmeni ashekaru gaskia,wallahy a'dan kankanin lokaci muka saba dasu,suma sunxo hada Kayan brother dinsu wani faruk,sunada kirki beyond Wlhy,infact de sune suka hada maki kayannan karaf senida jirgi damuka tsinto wasu abun Se faruk tunda shi matashi ne auren farko shiya daukar mana latest designs da ake yayi awannan era(zamani)din...
"Hafsat tabaro inda take xaune takoma inda Capt Adam yake,sosai ta rungumeshi tana bashi wasu warming kisses dasuka dinga ratsa ita me sending din sakon dakuma shi dayake receiving din wannan zazzafn kisses,ahankali taxare jikinta daga nashi tana kallon kayan'thank you so much hayatee I love you endlessly ,"Capt adam yace ina godia sosai my Hafsat naji dadi dakike nuna soyayyarki akan duk abinda nabaki..."sannan yadan rage maganarsa ahankali yace dare yayi my hafsat gwara muje mu kwanta dan inaso da safe in Allah yakaymu xanfita munyi xamu hadu da imran,
"Hafsat tace gaskia ne hayatee but tayani zipping akwatunan semu tafi tare,'dukawa sukai atare suna rufe akwatinan suna ajiyewa agefe,harsun mike bayan sungama rufewa sun jera agefe wajan showglass dake cike da turaren wuta,hafsat tahango ledan da mjay takawo masu Kayan tsaraba aciki,
"Sauri tai tarike hannun Capt adam dayai gaba yana fadin my hafsat kinga traffic jam ahanyar kaduna yau?!dakya...
"Bekarasa ba hafsat ta tari numfashinsa"hayatee namnta shaf wallahy daxu mjay taxo Kasan tadawo hartake cemin kunyi magana ta whatsapp amma ta 'boye maka saboda wai suprise visit takeso tamaka,wallahy shine takawo mana tsarabaa hartaba haule ma dogon riga da kayanta kunce,nikuma kaga,
"Tasa hannu tabude kwalin tace 'tadaaa'(suprise)"capt Adam yace wow gaskia sunyi Kyau sosai kalla takalmin xema kafarnan taki kyau,"hafsat tai daria sosai ma kuwa akwai shigen design din a wancan Kayan sede shi machel kors ne(mk)Sannan taciro turaren tabashi,"gashi wannan tace abaka,
"Captain adam yace ohh mjay hadda wahala haka,haddani atsaraban?!ware ido yai bayan yaciro kwalin turaren Elizabeth aden fa,"Kai gaskia nagode sosai Wlhy Allah yasaka da alkhairi amin badan dare yayiba dana kirata nayi godia gaskia wannan tsaraba tamin dadi...Allah yabarsu tare da mu'azzam 'din nata,
"Hafsat tai daria bayan tasaka jakan cikin akwati,ainace mata kagode sosai,Don nasan yanzu mjay taje germany a bacci kasan kamar Wanda Tasha sleeping pills in dare saboda tsabar bacci,"Ina mu'azzam yanxu kam mjay tashure xancensa tace ita gaskia baxata iya da bakinsaba kaji itama kamar ba bakar bace,wai tayi wani acan capetown though masters dinsa yake yanzu ,wani namnta sunansa de wai Ita gaskia yanzu shi takeso saboda fari ne,tafison sudinga haifan ya'ya Fanta and coca cola(fari da baki)...
"Capt adam yai daria Kai mjay akwaita da childish stuff ,xa tadena ne yarinta ce,...
Haka suka 'danyi hirarsu Sannan suka nufi 'daki bawa bacci hakkinsa...
"Koda safe ma haka Capt adam yafita yadawo ,kullum zamansu cikin lumana da mutunta juna,sosai suke xaman lapia ga lokacin aurensa se matsowa yake,hafsat tayi tayi dashi yashirya yaje kaduna yaki yashure xancenta,ko abuja dinma yace yadau absence leave kullum suna tare kaman chewing gum,
"Aikwa ana'i jibi daurin aure ranar alhamis kenan,gwaggo takira Capt adam kan yaxo kaduna yanzu ko me yakeyi ya aje yaxo kaduna,batajira cewarsaba takashe waya,jiki ba karfi yamike yahada 'yan kayansa tareda temakon hafsat dinsa,sanin Kansa yasan dakyar in gwaggo xata barshi yadawo seta Allah kawai,da kalamai masu dadi hafsat tashrya shi tareda fadin itama ranar asabar xataje gidansu,addua sukai suka Shafa sannan ta rakashi har mota jirgi yaja se kaduna garin gwamna,
"Haka tadawo cikin gida jikinta Yayi sanyi na irin rayuwar daxata shiga idan magajiya taxama matar adam.....
•✨•
nanahafsat.wordpress.com
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👄
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
13
©•MISS XOXO
👄
•✨•✨•✨•✨•✨•✨•
Dedicated this page to my wonderful co writer humayra(MELODY)A.K.A(little mermaid)Allah yakara basira acigaba da mana NAMIJIN KENAN!
•✨•
"Da yamma lis jirgi yai parking a parking arena din dake gidansu na kaduna,tunda yataho a mota suke waya da hafsat dinsa,sede in ankirashi yakatse ya amsa Sannan yakira back,dan wayar da suke yi da hafsat din ta temaka matuka wurin rage masa makokon bakin cikin zuciarsa sosai raguwa,dakyar sukai sallama Sannan ya maida wayar cikin aljihunsa,ahankali yataka yashiga cikin gidan yaname addu'a na Allah ya kauda duk wani 'bacin ran daxe fuskanta acikin gidan nadaga gwaggo dakuma sharrin 'yan uwa surayya da sadeeya Wanda sanadiyaru ne wannan sabon al'amari yafaru dashi,
"Da sallamarsa yashiga cikin babban parlor din gidan Wanda daka shiga shi kake fara gani,babban parlor ne dake dauke da kujeru har set biyu ,sosai xeci mutane ba kadan ba ,dukkoda ginin da ne amma sosai ankara renovating dinsa Yayi kyau,gidane wadatacce sama da kasa,Kansa tsaye yanufi saman ganin bakowa a parlor din dake kasa,kwakwazon su surayya ne yatabbar masa cewar gwaggon na saman,sarai yagane yanxu sune suka harzuka' gwaggon tasashi tahowa dole,
"Bakinsa 'dauke da sallama yashiga cikin parlor din,ayatsine su sadeeya suka amsa sallaman Sannan suka cigaba da hiran da suke,'Capt adam yadauke kansa dan yasan saboda sunga gwaggo agurin ne yasa sukai haka,bebi takansu ba sema haura 'kafarsa dayai yakarasa wurin gwaggon wadda tacika tai fam kamar wadda xata fashe dan 'bacin rai,
"Ahankali yakarasa wurin gwaggon tareda xubewa kusada gwiwoyinta " gwaggo barka da yamma,nasameku lapia?!ayimin afuwa gwaggo abubuwane suka min yawa,wallhy aikine yasani agaba,Allah ya huci zuciarki gwaggo,
"Gwaggo tadauke kanta tana kallon gefe,adakile ta amsa gaisuwar,'dannan(capt adam)yanzu abinda kai yadace kenan?!yanxunnan ina gama kunhadu ahanya da Ita ,magajiya taxo nan tana kuka shabe' shabe' da majina cewar gashi daurin aure saura kwana biyu amma bata saka a idonta ba,tace 'kawayenta da sauran 'yan uwa sunata