Showing 18001 words to 21000 words out of 107296 words

Chapter 7 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7693

tinda ba kunya ce ta isheta ba ..

Seda yafara biyawa wani dan kiosk yasiyo drinks sannan yatsaya dede wani gurin siyarda nama,zoka kara suya spot ke rubuce boldly ajikin rumfar me naman,mesaida naman na ganin zungureriyar mota yataso yanufa inda capt adam yai parking tareda saka kansa tacikin glass din motar yana magana"Alhaji nama xaka siyane kaza ko tsire ko balangu ko Kilishi ko...

Bekarasa ba capt adam yakatse shi"gasamin kaji kwara uku,

"Toh alhaji angama yanxu kuwa,sannan yanufi wurin kajin tareda ciro dakwale guda uku yasasu a tukubar yana kara 'dumamasu don suyi xafi,sannan yacire su yagyara tareda yankasu yasaka a foiled paper hade da xuba coleslaw agefe da duk wani abinda yadace Sannan ya nannade' yasaka aleda yakaiwa Capt adam"gashi alhaji angama,

Capt adam yai murmushi "aikinka yayi kyau,dajin kamshinnan ansan naman nan ya amsa sunansa Gaskia dole inxo in Kara kamar yadda nagani arubuce,toh nawa kudinka?!

Mai naman yai daria yana fadin"Dubu uku da dari biyar ne Alhaji,

Capt adam yasa hannu a aljihu yaciro kudin yamika masa Sannan sukai sallama,yafigi mota yai hanyar gidansa,yana xuwa yadanna horn megadi yataso aguje yawangale gate Capt adam yashiga,

Magajiya najin horn din mota tamike tanufi dressing mirror din dakin tafara gwagwada powder da jambaki,sannan takoma kan gado taxauna tareda sa mayafi tarufe fuskar ta wai Ita amarya,

Yana hawa stairs din dakunan yabi yana dubawa kusan duk dakunan biyar din cike suke da Kaya ,Yayi mamaki kwarai naganin yadda aka cike gidan da Kaya Yayi Kyau ba lefi dukkoda yasan gwaggo ce tai ruwa tai tsaki hakan ta faru,dakin karshe dake corridor yashiga nan yahango magajiyan xaune akan gado lullube fuskarta take da mayafi,daria yai naganin yadda tai din kamar wadda bata taba aure ba ,sallama yai sannan yashiga cikin dakin ,

Magajiya ta wani rage volume din muryarta tareda lankwasheta sannan ta amsa sallamar,capt adam yanufi gefen gadon ya sunkuya ya ajiye ledan kajin dakuma drinks sannan yamike yana fadin "akwai maganin sauro inxaki fesa acikin separate ledan gefan,Allah yatashemu lapia sannan yasa hannu yakullo mata kofan,

Dakin 'kasa yasauka ya ajiye kayansa tareda murxa key ,sannan yajanyo wayarsa yashiga kiran layin hafsat,amma kassh beyi sa'a ba wayar tata a kashe take,yasan kuma Sarai tayi hakanne saboda taga andaura masa aure bataso tashiga hakkin magajiyan,siririn tsaki yaja sannan yajanyo system dinsa yana duba sabbin email messages dasuke shigowa,



•✨•
18

Dedicated this page to my adoring co writer waliyya(walissco)Allah yabarmin ke tawan!

•✨•✨•✨•✨•✨•

Magajiya na ganin Capt adam yafice tamike tana zagaye dakin,tareda sa hannu akai kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa,

"oh ni magajiya duk uban kayan dana dirkawa cikina da jikina yatashi a tutar babu kenan?!dan wulakanci ko kallo ma ban isheshi ba gaskia baxan yarda ba wallahi.Wannan hafsat ko 'yar iska tashiga tafita tacireni aransa wallahy sena koya mata hankali xatasan dawa tasaka kafar wando daya" ,

A fusace tajanyo ledojin tana dubawa ,sosai kamshin da'kwalen kajin suka daki hancinta gakuma sanyayyan yoghurts da lemuka,se katon gwangwanin maganin sauron motein har guda biyu ,tsaki taja sannan tamike tashiga bandaki ta watsa ruwa tareda saka saukakkar rigar bacci sannan tahau cin naman tana korawa da yoghurt din sedataci tai dam ta gyatse sannan tabude dan karamin freedge din dake dakin tasaka leftover na kajin dakuma sauran lemon aciki,seda taci uban mitarta ita kadai tanayi tana tsaki sannan tabi lapiar gado takwanta,agadon ma batabar mitarba kamar wata mahaukaciya tanayi tanajan tsaki dakyar bacci yadauketa cikeda tarin irin mission din daxata hada'wa hafsat din,

Da safe ma haka capt adam yai wankansa sannan yasa jirgi yai ordering abinci anan hamdalah palace,kofar dakinta ya aje mata nata package din sannan yaci nasa Kansa tsaye yai ficewarsa unguwa kotakanta bebiba ,itakwa magajiya bata tashiba se wajen shadaya saura da hamma tamike ko salati babu se asannan tashiga bandaki tadauro alwalar asubah tai sallar da ko karatun sallar batayi ta sallame,sannan tasake komawa bandaki tayo wanka tareda mummulka turaruka dukde nadau kar hankalin Capt adam sannan tashafe rabin awa tana kwalliya harda girar da akeyi yanxu ta concealing.Wani material tasa doguwar riga 'kirar bubu sannan tai dauri indimi style,tasa hannu tabude dakin karaf idanuwanta suka sauka kan ledar dake ajiye agefen kofar ,

Hannu tasa tadauka tareda budewa 'lafceciyar wainar kwai ce agefe tareda soyayyan dankali da doya se kuma sauce na kayan ciki ,tsaki taja takoma cikin dakinta tana magana"yanxu bancancanci yashigo yaga yana tashi ba ,bankai kuma yamin magana nadau abincinba sede ya ajiye abakin kofa Allah ya kyauta",

Koda captain adam yafita gidan Yaya sameer yanufa,Yana xuwa kansa tsaye yanufi sashen yaya sameer din cike yakeda 'yan gidan Se hira akeyi,Capt adam yai sallama yashiga,bayan sun amsa,yaya sameer yadaga kansa yana duban capt adam din,

"Yanzunnan muke xancenka nida namesake dinka gashinan yanzu yadawo daga school yaketa wai shi nasa driver yakaishi wajenka",

Capt adam yai murmushi yana kallon yaron yaya sameer din wanda aka sawa sunanshi amma akece mashi ARFAAN yarone baxe wuce shekara 8 kuma yana yanayi da Capt adam din sosai,

"Zo my boy,my namesake"

yanayi yana mika masa hannu"oya xomu gaysa mana ARFAAN" ,

Dagudu ARFAAN din yanufi inda capt adam din yake tareda mika masa hannu"Baffa ina yini?"

"Lapia qlau ARFAAN ya school ya studies hope kana maida kai de ko?!danaxo last week bangankaba akace mamee tasa ankaika boarding school,kayi kokari akwai present babba inka fito da first ,second or third position kaji?"

ARFAAN yai fada'da murmushin dayake jin an ambaci present ,gashi dama keke yaketa San abbanshi yasiya mashi,sosai yasan capt Adam din xe siya mai tinda yasaba yimasu kyauta haka kawai ma,"ehh mamee ce tasa aka kaini turkish boarding sch amma da akwai dadi school din baffa every morning akwai sandwich da milkshake for free da ake bamu,xanyi kokari naxo haka Baffa xaka siyamin keke ko?"

Capt adam yai daria "karka damu ARFAAN insha Allah bayan keke harda wani abun ma xansiya maka,oya gimme a hug",

Da sauri ARFAAN yasa hannuwa yarungume Capt adam,nan sauran yaranma suka taso aguje suka makalkale Capt adam din suna wasa ajikinsa,

Haka Capt adam yaxauna ya bararraje suna wasa shida yaran gidan suka gama suka hau game din whot aka dawo nintendo,wiii ,sannan sukahau wasan hide and seek ,Shide ransa yanasan yaran dansunada shiga rai uwa uba kuma bashida yara shysa ,amma yaya sameer yayi kan Capt adam din yadau ARFAAN ko MUS'AB amma yace a'a ganin shidinma bawani yaranne dashi dayawa ba dan matan nasa nayawan haihuwa amma sede asamu akasin kobasuxo da rai ba kokuma insun dan girma kadan su mutu,seya kasance ARFAAN dinne babba Wanda aka sawa sunan Capt adam!

Sosai suka sha wasa da yaran Sannan Yaya sameer yai gyaran murya"Toh aje ayi wasan awaje kuma Baffa adam din yagaji haka kwadawo anjima",

Hira suka shi gayi shi dan uwansa inda yabashi shawarwari kan yarda xe rike matan nasa tsakani da Allah wato magajiya dakuma hafsat,sosai yadade agidan har gabannin sallar la'asar don ananma yaci abincin rana,Sannan yaiwa Yaya sameer din sallama yatafi,


Days passed,bayan kwana bakwai cif captain adam yahada kayansa Sannan yahau saman kamar kullum tana dakinta azaune donshi harmantawa yake da ita ma tunda babu abinda yataba shiga tsakaninsu,da sallamarsa yashiga dakin fuskarsa a'dan sake ,hannu yasa acikin aljihu yaciro bandir na 1k ya 'aje a gefen magajiyan da batako kallonsa bayan ta amsa sallamar wai Ita irin fushin nan,

"Gashinan koxaki sayi wani abin nixan koma aiki,absence leave din dana dauka yakare",

Magajiya tawani shagwabe fuska "yanzu my hubby tafiya xakai bayan bakawani da'de ba ninaxata ai sati biyu xakai ko fiye da haka"

Capt adam yaware Ido naganin yadda magajiya ke shagwaba dakuma Jin yadda takirashi wai my hubby,murmushi yai sannan yakadar da xancen yana fadin"idan katin wuta yakare akwai wani acikin locker drawer din jikin tv,nina tafi se Allah yakymu kuma",

Magajiya tamike tana wani chest out "Allah yakayka lapia my hubby yadawo dakai lapia I will mss you badly Gaskia,barin rakaka"

Tasa hannu xata cire igiyar jakar hannunsa yai saurin dakatar da ita"no thanks base kinfitaba nagode"

Magajiya tabata rai "meyasa my hubby?!"

Capt adam yai shiru yana kwakwalo abinda xe cemata tayadda dan bayaso yajera da ita ,can yakada kansa yace"Kinga akwai maxa yan aiki Wanda ba muharramankiba ko?!"

Magajiya tafara wani blushing taxata har zuci yafadi haka sewani fada take axuciarta yafara kishinta kenan tunda har bayasan maxan waje suganta,murmushi tai tana wani fari da Ido"okay my hubby safe trip",

Capt adam yafice yana fadin"okay thanks",
Doguwar ajiyar zuciya yai bayan yafita waje yashiga cikin mota dan dakyar yake iya magana da ita dauriyace kawai,mirza key yai sannan yanufi gidansu dake malali ,yana xuwa yai parking tareda bawa jirgi driver mukullin.
"Kadan wanke ta kafin naiwa gwaggo sallama yanxu xamu juya Kano dayardar Allah",

Cikin gidan yashiga dauke da sallamarsa se Murmushi yake duk dan gwaggo karta dakko wata maganar daban,dukkoda tarin bakin cikin dake xuciarsa yafi afadeshi ,sosai yatsani yatashi yaga fuskar magajiya a matsayin matarsa,sallama yai bakowa a parlor din sefa yar dattijuwar dake kula da gwaggon ,gaisawa sukai Sannan tamike tana fadin
"Bari ingayawa gwaggon kazo yanxu itama tashiga daki tadade anan zaune".




nanahafsat.wordpress.com


WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
19

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼

•✨•✨•✨•✨•✨•

Seda gwaggo tadan jima kafin tafito sannan daga baya tafito jikinta sake da babban hijabi har 'kasa da alama sanyi takeji bayanta kuma me aikintace harira dauke da kaskon wuta cike da garwashi jajir dashi,gwaggo tadan gyaran murya tana fadin"harira sa garwashin acan gefen parlorn yafi turaruwa gaba daya"

Bayan harira tayi yadda gwaggon tace fita tai tabasu wuri,shikuma Capt adam dasaurinsa yabar inda yake yakoma kusada gwaggon,

"Gwaggo barka da safiya antashi lapia?!"

"Lapia qalau 'dannan,ya magajiyan tananan qalau?!"

"Komai lapia Alhmdlh gwaggo tana gaisheku ma"

Gwaggo tai murmushi jin ya ambaci magajiyan tana gaisheta kenan suna xaman lapia da sauri tafada'da murmushin fuskarta "ina amsawa dakyau"

Capt adam yai 'kasa da murya yana fadin"gwaggo nixan koma bakin aiki hutun dana dauka yakare dama kwana gomane kwata kwata ,dakyar ma sukabani"

"Toh Allah yakiyaye hanya yakaiku lapia ,gashican bushasshen kifi kadau kwali daya katafi dashi dayan na wannon yaron ne shaf namanta mutan hadejia suka kawoshi"

"Gwaggo godia nake Allah yasaka da alkhairi,ina matukar son kifin nan sosai yake dadi a dafaduka dakuma miyar kuka,nagode kwarai xankirasu nayi godia insha Allah"

Sannan yadan sake dukawa "gwaggo nixan wuce"

Gwaggo tajasu addu'a Sannan suka shafa,sosai sukeyin hakan kullum idan ya'yan xasuyi tafiya ko idan sunaneman wani abun,tunda adduar iyaye dabance,

Sallama yaiwa gwaggon wadda tarakoshi har bakin kofa tana daga hannu sannan jirgi yaja mota Se kano,acikin mota capt adam yakira hafsat dinsa danya shaida mata yanakan hanyar dawowarsa ,ringing na farko tadauka, yasauke nannauyar ajiyar zuciya,da sauri muryarta kamar ana busa sarewa tadaki dodon kunnensa take ya lumshe ido,ahankali takara cewa,

"Slm alykm hayatee kana jina?!"

"Wa alykm salam my hafsat ,gaskia banjikiba kinsan inde ina magana dake i totally lost it"

"Hayatee kenan Allah yabarmin kai,ya kaduna da yan cikin kaduna hope Komi lapia?!"

"Lapia qlau my hafsat,yanzu haka I'm enroute to kano namatsu nai tozali da matata nayi missing dinta beyond words..

"I missed you beyond your expectations hayatee,and I'm so so very happy,Allah yadawomin dakai lapia,mekakeso nadafa maka?!"

"Banda zabi my hafst duk abinda kika dafa zanci,Allah yamaki albarka sena karaso"

"Okay hayatee yanxu kuwa"

kodah suka gama waya da Capt adam dinta sauri tai tashiga kitchen tafara hada aroma din abinci,cikin lokaci 'kan'kani tagama tafarfasa kazarta da Kayan kamshi tareda shiryta cikin jar miya dataji tafarnuwa,tuni kitchen din yafara kamshi,Sannan tadora ruwan farar shinkafa data tanadi su carrots agefe da green beans suma duk ciki xata sasu,da sauri taciro catfish cikin freezer tafara shirin gasashi(grilled fish),sedata gama shrya komi sannan tasashi kan grill yafara gasuwa,gefe daya kuma haule ce dake shrya ha'dad'dan salad hardasu dafaffen 'Kwai agefe...sauri tai tashiga daki tafada bandaki tayo wankan sabulu dana madarar turaren wanka se tashin kamshi take,sakeyin brush tai hade da kuskure bakin da mouthfresh na strawberry ,gaban mudubi tanufa tafara Shafa mai da turaruka da madarar turare,gefe daya kuma kayantane kan kambasa dake turarar kamshi,

Kafin captain adam yakaraso har angama jere abincin kan dinning hade da lemonade dayasha madara da ayaba,gidan se tashin kamshin du'aul jannah yake da hafsat tasa,

Karfe 2;00 dede jirgi yai horn aguje hannafi megadi yabude gate din suka shigo da motar ,sosai suka tari ogan nasu suna murnar ganinsa,Kai tsaye yashiga gidah bayan ya sallami jirgi yace shima yaje wajen iyalinsa,

Yana shiga as usual kamshi yafara dukan hancinsa abinda yafara missing kenan Dan magajiya bata taba saka turaren wuta ba kwana goman dayai agidan,bakinsa dauke da sallama yakara cusa Kansa cikin parlor din yana kasaitaccen murmushinsa Wanda yake kara masa Kyau dashiga ran duk Wanda yai toxali dashi,

Da sauri hafsat tafito tana murmushi medauke da fara'a sanye take cikin atamfa yellow and blue riga da skirt dinkin ya amsheta ba kadan ba,tayi dagwas da ita kamar yammata,"afuwan hayatee nadanyi nesa da parlor ne kayi hakuri pls"sannan yasa hannu takarba jakar hannunsa tareda doriyar"barka da dawowa"bayan tayi hugging dinsa tsam ajikinta,

Hugging dinta shima yai sun jima ahaka kafin yadago fuskarta Yana kallo "my Hafsat kin'kara Kyau kullum kara Kyau kike Wlhy"

Hafsat tai daria bayan ta cusa kanta cikin kirjinsa "hayatee kaine ka kara Kyau koda yake kai angone to nima inajin abin ya"....

Bata Karasaba captain adam yai saurin sa hannunsa kan bakinta"sshhh my hafsat talk no more pls kyaleni daxancen aurennan ,tunda natafi wallahy bansamu farin cikiba seda nadawo nagaya maki ni bandauketa amatsayin matata ba sede yar'uwa ta saboda haka kiyi shiru kawai kokinaso raina yaba'ci ?'"

Hafsat tai saurin girgixa kanta"uhm uhm hayatee baxan sake maganarba"

"That's my Hafsat oya xoki feeding dina da wannan dadda'dan abincin naki pls"

Dinning suka nufa sosai taxage tadinga bashi kamar kullum,har kifin seta tacire 'kayar sannan ta samashi abakinsa,..,kodah dare ma haka tai special abinci tai feeding dinshi ,ko gurin kwanciya ma Hafsat ta tabbatar ita kadaice azuciar captain adam danyayi missing dinta ba kadan ba toh itadinma hakan yake,

Lokaci yaja watanni sun shu'de amma xaman captain adam da magajiya yananan yadda yake jiya'i yau yana bata kulawa kamar kanwarsa haka yadauketa amma haryau yaki' karbarta amatsayin matar aure,bayan yataho daga gun magajiyan daga Kaduna danyana kwatanta adalci atsakani dukkoda xuciarsa tafi karkata ga Hafsat dinsa,yanxu kowanne gidah kwana uku uku yakeyi..yakira hafsat yace mata yana hanya,

Da sauri tamike dukkoda tarin gajiya dake jikinta,kwanakin nan gaba daya batajin dadi tasha pain reliever yafi akirga amma jikin meyakwn yai sauki karuwa yake gashi batasan tayarwa da hayatee dinta hankali,

Sassau'kar jollof rice tai da sphagetti dayasha kifi se soup din kaxa kawai datai masa,dakyar tayi donma haule na'dan temaka mata,

Kodah yadawo ma daurewa tai taresa tadanne kanta kamar ba abinda ke damunta danbatasan daga dawowarsa tadaga mashi hankali,sosai tafaranta masa rai,har kwanakin dayai suka kare aranar daxe tafi dasafe yakalleta lokaci daya dukta fita hayyacinta ta rame se fari data kara,nufa inda take yai da sauri yana dubanta
"My Hafsat bakida lapia ne naga kaman bakijin dadi?!"

"Lapia Lou hayatee kaina ne ke ciwo xedena fa karka damu hayatee".

"No tashi muje asibiti pls kila malaria ne kwana biyu bakya flirting hala?!"

"Yasss hayatee inaga malaria dan nayi amai ma, xanba haule tasiyo min anti malaria yanzu"

"Tashi pls my hafst muje asibiti barin kira dr NAUFAAL"

Bayadda Hafsat Ta iya adole tamike jikinta yadau xafi rau dashi,hijabi kawao taxura taje parlor taxauna Tana jiransa yafuto,da sauri yafito duk arude yake da Waya ahannunsa yasa a kunne,

"Hello dr NAUFAAL ya kana asibiti ne ko gidah wallahy madam Dina ba lapia?!,,,kana asibitin?!no barshi kawai baseka xoba I can't wait any longer barimuxo kawai is urgent Kasan yau xankoma kd"

Haka yashiga mota shida Hafsat din,hannu daya Yana tuki daya kuma Yana taba fuskarta datadau xafi,yafadi sorry my Hafsat yafi a kirga,

Mintina kadan suka Isa asibitin dr NAUFAAL,Wanda yamata yan tambayoyinsu na likitoci Sannan yace "Gaskia akwai malaria amma ungo kwalbannan ga bandaki can ciki kikawo urine dinki xamuyi test"

Shiga tai tayi Sannan takawo masa,yakarba yanufi lab dinsu ,mintina kamar 20 yadawo Yana murmushi tareda Bawa captain Adam hannu sukai shaking "congatulations captain you are now a father ,nayi Ma madam dinka test nagano tanada ciki na tsahon sati 14(wata uku da sati biyu kenan).."

Capt adam yaware Ido tuni hawayen farin ciki suka fara gangara afuskarsa"kana ..kana nufin MY HAFSAT TANADA CIKI?!"

•✨•
...nikwa miss xoxo nace Alhmdlh ya Allah for such a blessing! YA RABB those that haven't conceived bless them with a child MAI YAWAN ALBARKA,beautify their homes with beautiful children and make them the coolness of thier eyes,,,



nanahafsat.wordpress.com



WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/18, 11:57 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
20

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO
UMMI A'ISHA👌🏼

•✨•✨•✨•✨•✨•

Dr NAUFAAL yai murmushi 'hade da xaro tissue acikin aljihunsa yasa a idonsa Yana goge hawayen dake zubomai shima nafarin ciki,Dan sosai yasan yadda abokin nasa kesan yara shekara 20 kenan ,danshi har ya 'aurar da 'yar sama,Se yanxu Allah yabawa matarsa ciki xata haihu,Allah kenan mabuwayine kuma gagara misali,ahankli yasa hannu Yana daga kafa'dar capt adam din dake kuka,
"Tabbas matarka nadauke da ciki na tsahon sati goma shahudu(wata uku da sati biyu kenan,semuyiwa Allah godia da wannan babban rabo"

Hafsat dake gefe itama kukan tasa tana me kallon Capt adam,shidinma ita yake kallo,

Dr NAUFAAL yakallesu yadda suka shagala suna kallon junansu daria yai sanann yanufi hanyar fita daga consulting room din yana fadin"love birds inkun gama kallon junannaku ni ina scanning room xanmaki scanning muga lafiyan babyn dayadda xa'abaki shawarwari"

Yana fita captain adam yadawo kusa da Hafsat dinsa 'hade da janyota jikinsa yasa hannu yana goge mata hawaye 'hade da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login