Showing 93001 words to 96000 words out of 107296 words
mata magana k'asa k'asa;
"I'm such a 'can I have a kiss ?' Every 5 seconds kind of a person,kuma everybody has an addiction mine just happens to be a kiss,sannan giving you a kiss shine purnishment d'inki,insaki abu ki k'iyi kiga,da wani cute lips d'inki awajen common jeki aikin gabanki kixo ki saka hijab akan kayanki nabaki minti 10"sannan yafice yana mata dariar mugunta,yana futa Ummi Aisha tagoge kwallar dake shatata a idonta tana magana Ita kad'ai;
"Mutum sekace arne sekace film,wallahi banyafeba,Allah seya sakamin wallahi" Ummi Aisha tace hakan tana cigaba da goge k'wallar dake tsiyaya daga idon nata,
Cikin sauri tai reheating Indomie da k'wan acikin micro wave,tasaka akan plate had'e da saka fork tafita parlor ta janyo center table ta d'orawa jay akai,
"Duk ni kad'ai our wife?karfa nakasa driving kaina naje gidah"
"Habade d'an indomie k'wara biyun?!ai batada wani nauyi aciki"
"To nagode our wife,I'm already drooling gaskia yau ina cin dad'i"
Daria Ummi Aisha tai,tak'i had'a ido da ashraf tai saurin hawa sama abinta,tana zuwa ta baje akan gado had'e da dakko wayarta tana dannawa aikwa tafara ringing 'ya hajja' shine sunan dake yawo akan screen d'in,d'auka tayi tana murmushi,
"Salam alykm ya hajjata..na'am!ina ciki wallahy,a'a don manzon Allah?! Banishi maxa,hello haba haba isuhu yaya tace fa kyaleta tashigo don baka tab'a ganinta ba shine xaku hanata shigowa?!babu komai yawuce,to ya hajja sekin shigo"
Ajiye wayartai agefe tana murmushi,murna fal cikinta jin itama y'ar uwarta ya hajja y'ar wan maman ammin tace dake aure a abuja taxo mata da alama tazo garinne,cikin sauri tajanyo mayafinta kalar kayan ta d'ora akai ta sauka k'asa,tana sauka suka had'u da ya hajjan suna yanayi da amminta sosai sede ita batakai hasken ammin ba,tare take da wata kyakkyawar yarta baxata wuce shekara d'aya da watanni ba b'ul b'ul da'ita se b'angala daria take,gaisawa ya hajjan tai dasu ashraf da jay sannan suka hau saman itada Ummi Aisha suka bud'e sabon shafin hira ba wata babba bace ya hajjan befi tad'ara Ummi Aishan da shekara d'aya xuwa biyu ba,
"Naga se wani fari kike kode da akwai k'unshin ajiyar ashraf a gefen marar kine?!"ya hajjan tace haka tana kallon ummi Aisha,
"Rufamin asiri ya hajjata nida bamu tab'a wani.."sekuma tai shiru tanasa hannunta kan bakinta da alama sub'utar baki tai,
Ware ido ya hajjan tai tana kallon ummi Aisha,tana salati tana tafa hannuwa,
"Garin yaya?!ya akai haka tafaru ?aure kusan kwana 8 dayinsa amma ace haryanxu shiru"
"Nifa ba abinda nake nufi ba kenan ina.."bata gama ba Ya hajjan ta katseta,
"Wallahi haka kike nufi,to Allah ya kyauta maki nasan Kuma lefin kine ba nasa ba,kisani de duk macen dake tauye hakk'in mijinta mala'ikun Allah natsine mata idan Kuma tsinuwar kikeso sekici gaba da yi Allah ya temakeki"
"Ba lefina bane ya hajja"
"Ke ba mace bace?! Bakisan yadda xaki ki karkato hankalinsa xuwa garekiba sekace wadda kika rako mata,ina kikabar title d'in kanurin naki da akace juya maxa muke kamar tandin waina??"
"Kai ya hajja"
"to nide yakolon yerwa ta aiko mana da sak'o ga naki Kuma don ko wajen aunty hafsan banjeba se anjima,yakolon tace da naxo nafara kawo maki hannuna da naki kafin natafi xanmiki bayaninsa sauran yadda akai xanji a waya ki kirata ki mata godia"tak'arashe xancen tana mik'o mata wata leda cike da jarka da wasu abu a leda bak'ak'e.
"To nagode Allah yasaka da alkhairi"Ummi Aisha tace da ya hajjan hakan tareda mik'ewa tasaka ledar cikin drawer dnta
"Ba canai ki kwalliya da ledar ba amfani xaki fara yi dasu"
"Xanyi Insha Allah"
Hira sukaitayi na yan uwan juna sannan suka sauka k'asan don d'ora girkin rana,jay ne da ashraf keta xubar hira se 'chu chu' sunan da ake kiran ihsan y'ar ya hajjan kenan dake xaune kan cinyar ashraf,
"Me kakeso adafa maka?!"Ummi Aisha ke tambayar jay
"Oh nide yau our wife kin maidani d'an gata,I have no choice,kome kika dafa xanci"
"Kafad'a de pls"
"Jollof rice ma ya isa nagode sosai"
"My favourite kenan ai"
"Mine too"jay yace hakan
Cikin awanni k'alilan Ummi Aisha da ya hajja suka shiga kitchen suka dafa had'addiyar vegetable jollof rice(ni mss xoxo nace Allah yasadamu da jollof rice a aljanna amiin)datasha hanta se sauce na Kayan ciki da salad,harda grilled fish da soup d'in kaza,gefe d'aya Kuma frozen lemonade ne dayasha madara,kan dinning suka jere abincin suka bulala turaren wuta,suka d'ebi nasu suka hau sama dashi tareda chu chu da ya hajja ta d'auketa suka hau saman donta kyale su ashraf suci abinci,da Ummi Aisha xatace dama ta kyaleta tunda baci xeyiba sekuma ta share kawai,
"Aroma is calling"jay yace hakan yana nufar kan dinning yana bud'e foodflask d'in yana baje hanci yana kallon ashraf
"Dude come and serve your self,kaji k'amshin abinci kuwa ?chai gaskia bayan sallah xanyi aure wai"
Daria ashraf yai yacigabada kallon jay dukkoda ransa biyawa yakeyi najin yadda k'amshin abincin ke tashi,
"Dakai nake fa dude"
"Nak'oshi jay"
"Meyasa dude??"
"Kawai saboda banacin abincinta"
"You gat to be kidding me right??"yace hakan yana ware ido
"I'm damn serious"
"Meyasa to??"jay yace hakan tareda cika bakinsa da jollof rice
"Idk kawai naga nima ina hakan,nayi nayi nakasa nakasa,itama kuma she's so afraid of me shysa ko nayi niyan cin abincin nake fasawa"
"To kana mata wannan banzan arrogant halin naka badole tadinga tsoranka ba ranar dinner d'inku harda karb'ar mike kai wani kneeling down kana wani she's the best woman on earth hardasu fad'in you will worship her,ai daka fad'i hakan thought danazo zanga Kai kake abincin tunda bauta mata kace xakai ashe k'aryarkace"yakarashe maganar yana daria had'e da sipping lemonade d'insa,
"Ni nadafawa mace abinci Allah ya kiyaye over my dead body"
"Yanzu de zoka d'iba abincin nan tunda naga kamar kunya kakeji karta ganka,kafita can waje kaje kaci"
Ashraf yadinga daria harda rik'e cikinsa,sannan ya mik'e tsaye yana girgixa kansa
"No i can't, i won't.Idan kagama cin abincin ina waje ina shan iska abina"sannan yafice waje abinsa,kunnensa sak'ale da earpiece...
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT........
[4/18, 11:59 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
89
©®MISS XOXO
👄
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
Baby Kay nacikin kukanta aka fara knocking k'ofar d'akin hotel d'in cikin sauri tagoge hawayenta duk axatonta bobon nata ne yadawo,
"Yass come in"tace hakan cikin muryar shagwab'a tana k'ara rufe jikinta da bedsheet...
Bud'e k'ofar keda wuya idanuwanta sukai toxali da room service ashe ba kamal bane ko ince tanimu ,sanye yake cikin suits irin tasu ta masu aikin hotels,
"Madam kinason wani abu ne?!"cewar room service d'in,
"No I'm okay,thank you"
"You r most welkm madam,sannan kud'in 5hrs mijinki yabayar yanxu kuma its 5hrs 30mins,gashi wasu sun biya kud'in d'akin.Madam kid'anyi sauri ki gyara ki settling bills d'inki a k'asa.
"T..Toh"cewar baby kay,gabanta se fad'uwa yake sisin kwabo batada shi yanzu yaxatai?!
"Thank you madam"yace hakan tareda bud'e k'ofar yafuta,
Kukanta tacigaba dayi seyanxu ta tabbatar kamal yaxeed mak'aryaci ne,tafara tariyo tarin k'arairakin dayake mata,kullum cikin fad'in iyayensa na Qatar nextweek xasu dawo kullum basu dawowa,gashi inyazo da mota yau to gobe watace daban,ashe ashe mak'aryacine,share hawayenta tai bayan ta tsine masa yafi ak'irga ta mik'e tashiga cikin band'aki cikin tafiyarta ta ta ta ta,dak'yar ta iya d'aurayo jikinta tafito ko wankan tsarki bataiba sallah kuwa dama ba damunta taiba sede muce Allah ya kyauta kawai... A hankali a hankali tamaida kayanta had'e da d'aukar jakarta tasauka k'asan wurin hotel service dake tsaye a wurin da aka tanadar masa yana cike wani littafi,k'arasawa tai tana k'ak'aro murmushin dole;
"Sannu ma'am"yace da ita,
"Yawwa sannu"tabashi amsa
"Ma'am mijinki yabiya kud'in 5hrs dede to kuma kunyi exhausting 5hrs d'in harda d'oriyar 30mins akai yanxude xaki ciko mana 15k cikon kud'in"
"Pardon??"baby Kay tace hakan tana binsa da ido
"Yass 15k xaki ciko ma'am"
"To nide yanzu banda kud'i gaskia sede idan xaka sa wani yabini gidah ya amsa"
"No bama haka anan,idan da akwai master card gurinki kibayar semu cira taciki"
Duba jakarta tayi babu,da alama tabarshi gidah Kuma kodah yanananma kud'in ciki baxasu kai 15k ba,
"Yana gidah"tabashi amsa a tak'aice...
Tuburewa yai kanse tabasu kud'insu magiya tashiga yimasa kamar ba ita ba kan yahad'ata da wani suje gidah tabashi tsoro take kada baffanta yadawo yaga batanan tasan kashinta ya bushe amma k'ememe mutumin yak'i yadda kan cewar dole inde taga tafita daga hotel d'in to lalle tayi settling bill d'in kanta,adole tasamu kujera awajen waiting area taxauna tana tunanin ina mafita?!...
•
Meanwhile alokacin da captain Adam da Hafsat suka isa asibitin Malam aminu kano dake kan titin xaria road , likitoci suka karb'i muna_b ganin taxama unconscious yasa suka shiga da ita emergency ward cikin sauri suka fara mata ceton gaggawa,aka saka mata oxygen tareda yi mata allurori likitan yasheda masu cewar xuwa safiya Insha Allah xata farfad'o jin haka yasanya su captain Adam komawa gidah,koda suka koma bayan sunci abinci sunyi sallah captain Adam yaje b'angaren magajiya don duba baby kay kamar yadda yasaba kullum amma wayam batanan sefa magajiya dake bacci akan kujera d'ankwalinta agefe babu gashi ko d'aya akanta,tsayawa yai yanabin sank'on kan nata da kallo ,gefenta kuma tulin kwalayen magunguna yagani na brain tumor da na Asperger's syndrome kamar wanda xece wani abin sekuma ya d'auke kansa yafita dede k'ofa yahad'u da lamunde me aikin magajiyan xata shiga cikin parlorn gaisheshi tai ya amsa yana tambayarta;
"Ina Khadija?!"yace da lamunde hakan
"Tafita tun d'axu da safe"da gayya lamunde tace hakan saboda baby kay ba k'aramin bata haushi takeba kullum cikin sata aiki take agidan,
Be ce komai ba yafuta daga parlorn,wayarsa yaxaro a aljihu yasoma kiran baby kay ringing biyu ta d'auka jikinta se k'yarma yake;
"Kina ina khadija?!"
"Baffaa"tace hakan atsorace
"Nace kina?!"yadaka mata tsawa
"Bristol palace"tafad'i hakan a tsorace da alama batasan ma tafad'a ba,
Katse wayar yai yafigi mota aguje be tsaya ko'ina ba se cikin bristol palace,kai tsaye yashiga ciki xuciyarsa se tafarfasa take,hango tayai atsaye duk ta firgice tana ware Ido,k'arasawa yai gurinta yanabinta da kallon tuhuma,
"Me kike a nan?!"yace da ita yana xare mata ido
"Baffa k'awata na ra,k'awata na rako"muryarta se rawa take,
Dajin yadda tai maganar yasan k'arya take,k'arasawa yai gurin hotel service had'e da xaro identity card d'insa ya nuna masa,ganin ID card din yasanya shi firgita tareda cin alwashi a xuciyarsa na kowacce tambayar xemasa xe bashi amsa kafin ya rasa aikinsa don yatsorata da captain Adam d'in k'warai matuk'a yamasa kwarjini..
"Waccan yarinyar koxan iya sanin da wa taxo wajen nan?kar Kuma ka kuskura kamin k'arya don xaka iya rasa aikinka"
Yawun tsoro mutumin ya had'iye jikinsa ya soma rawa don duk axatonsa yai xaton akan yace setayi settling bills d'intane dakyar jikinsa na mak'yark'yata yake fad'in;
"Sir,some hours back sukazo nan itada mai gidanta suka karb'i d'aki na 5hrs,to kuma har five hrs yawuce basu bar hotel d'innan ba sema sake k'arawa kansu bill sukai na 30mins,kuma tun d'axu mai gidan nata daxe fita mukace masa idan Lokaci yasake wucewa koda minti nawane sesun biya saboda haka constitution d'in hotel d'in yake seyace mana babu komai yabata kud'in,to kuma se wasu suka xo sunason single room kamar nasu kusan ince shine me sauk'in kud'ima na aika musa wanda co worker dinmu da yake incharge of d'akin kan yacemata tasakko k'asa tabiya bills d'inta anriga da ankama d'akin to kuma shine muketa de case d'in da ita tace ita batada kud'i master card d'inta yana gidah,nikuma nace mata baxeyiwu taje gidah batare da tayi settling debts d'inta ba"yak'arashe maganar yana saukar da kansa k'asa,
Shiru captain Adam yai yama rasa tacewa,gumi ne yafara keto masa,wato baby Kay halin data xab'a itama kenan?!wa'innan yaran duk tarbiyyar daya basu basa d'auka kenan?!neman kujera yai yaxauna yana dafe da kansa can ya mik'e sanin hotel ne yanufi wajen mutumin yabiya kud'in batare dayace mata komai ba yafuta wajen yashiga motarsa,cikin tafiyar ta ta ta baby kay tabi bayansa tafuto wajen itama,captain Adam yana hankalce da yadda take tafiya,girgixa kansa yai yana goge sirarin hawayen da suka xubomai,babu kunya tabud'e gidan gaba tashiga,bece mata komaiba yatashi motar suka tafi gidah suna xuwa gidah yai parking motar yabude yafita still bece mata cikanki ba,hantar cikinta se kad'awa take ahaka tashiga part d'insu cike da tsoro don tasan fushin baffansu daxe hanashi magana ba k'aramin abu bane.Yana shiga part d'insa ya xaune akan kujera hannunsa dafe da kansa yama rasa me xece waya yadakko yafara kiran yayansa sameer,ringing na farko yayan ya yad'auka;
"Assalamu alaykm"cewar captain Adam
"Wa'alykm salam Adam"
"Na'am yaya barka da dare"
"Yawwa barka kade Adam ya iyalin naka?!"
"Lapiar su qalau yaya,ya wajensu Aunty?!"
"Qalau suke Adam,lapia de ko?naji sautin muryarka wani iri"
"Eh to yaya wata yar matsala ce tataso kuma bansan yadda xan yanke hukuncin ba shine nakiraka"
"SubhanAllah wani abunne yafaru??"
"Babu komai yaya kawai neman shawarar ka nake"ya fadi hakan kasancewar bayason ya tadarwa yayan nasa hankali
"To shikenan babu komai xamu iya xancen ta wayane?!"
"Eh to,ku Kuma naxo kadunan ko?"
"A'a baka wahala ba ai,gobe dama nakeson shigowa xancen kwangilar nan kaga sena biyo tanan"
"Eh yaya hakn ma yayi"
"To to shikenan Allah ya rufamana asiri"
"Ameen yaya seda safe nagode a huta lapia"
"Allah yatashemu lapia agayda mutan gidan"
Haka sukai sallama kowanne yakashe wayarsa sannan captain Adam ya d'anji sauk'i aransa jin muryar yayan nasa dayai,band'aki ya shiga ya d'auro alwala yafara sallolin nafulfuli yana rok'on rabbus samawati daya k'ara shrya yaran nasa dana mutane baki daya kan tafarkin tsira!
____Ummi Aisha nasauka k'asa kitchen tashiga tafara had'a kayan baking d'inta su k'wai su full cream milk su icing sugar.Cikin k'ank'anin lokaci tahad'a komi tafara baking cake d'in nata,ba'akai 30mins ba cake yayi ta saka wiping cream d'inta harda masa design sannan tasaka shi acikin freedge yad'anyi sanyi saboda da xafin sa sannan tai hanxarin kad'a ice cream tamaidashi milk shake tasaka a freedge shima donyai cooling,hawa sama tayi don sake d'auraye jikinta saboda k'wai dayad'an fallatsa a rigarta gurin mixing.Band'aki ta fad'a tayo wankanta da bath khumra sannan taxura riga iya gwiwa tad'aure gashinta ciki tad'ora turban hula akai ganin dare yayi,sosai tai kyau kamar kasaceta ka gudu,k'asan tasakko tana tafe karatun theories of diplomacy da ka da alama haddarsa tayi,tana shiga kitchen sukai ido hud'u da Ashraf hannunsa rik'e da wuk'a gabansa kuwa tray ne da cake d'in ke kai da alama yanka xeyi don hardasu d'an plate da fork d'insa a jiye waje d'aya,
"Kan bala'in can"Ummi Aisha tace hakan tana k'arasa shiga cikin kitchen d'in,
Har inda yake taje tad'auke tray d'in ta rik'e a hannunta tana watsa masa kallo,shima kallonta yake amma nasa kallon na kyan dataine yadda rigan yakama saman k'irjinta da yadda tai flowing ta k'asa,muryar Ummi Aisha ce tasashi ya kauda kansa daga kallon nata da yake,
"haka kawai xaka d'aukarmin cake,nasha wahala nayi abin nawa kaikuma kaxo kad'auka kaci haba malam ai ba haka ake rayuwa ba"ta k'arshe maganar had'e da murgud'a masa d'an k'aramin bakinta,
Murmushi Ashraf yai yana taune da shegun pink lips d'insa mamakin sabuwar tsiwar Ummi Aisha yake Kuma gashi idan tanayi kamar ana k'ara masa wutar sonta axuciarsa haka yakeji.Ganin bawani abu xece ba yasanya Ummi Aisha juyawa abinta ta futa daga cikin kitchen d'in tabarshi nan tsaye bayan tad'au cup da robar milk shake d'inta,parlor ta nufa taxauna abinta tana kallon show d'in big brother naija,slicing cake d'in tai into 4pieces ta tsiyaya milk shake d'in a cup tafara yanka tanaci da wuk'a tana d'auka da fork tanaci,alokacin Ashraf yafuto daga cikin kitchen d'in kujerar datake yaje yaxauna don neman tsokana.ko cikanka bata ce masa ba tacigaba da kallon su efe tana murmushi ganin haka yasanya Ashraf d'aukar cake slice d'aya yafaraci,
"what the f..."tace hakan tana masa kallon meye haka?!cikin tsiwa tace;
"Malam banfa bakaba tunda bacanai kad'aukaba"
"Zoki danneni ki k'wata" Ashraf yace hakan.
"Aini ba y'ar iska bace"tace hakan tana murgud'a masa baki.
Tareda d'ukar cup d'in milkshake d'inta ta kwankwad'a tana ajiye cup d'in Ashraf yad'auka yashanye tass ,murmushi kawai tai ta d'auke kanta donta gane neman nayi yake,
"You smiled and i became obsessed with how good it looked on you" Ashraf yace da ita hakan yana sakar mata murmushi,
Murtuke fuska Ummi Aisha tai ta mik'e xata bar wajen Ashraf yai saurin rik'o hannunta yana murxawa a hankali cikin wata irin siga yake mata magana;
"Listen to me. I'm in love with you.Mad crazy in love with you. I'm not going anywhere. Ever. You can't get rid of me."
Fisge hannunta tai ta nufi sama da gudu tana shiga d'aki tafad'a kan gado tana muxurai;
"Sekace wani film kaxauna kana gayawa mutane maganar love kullum de magana d'aya"tak'arashe xancen tana sakin siririn tsakin takaici,
Mik'ewa tai tashiga band'aki tayo brush had'e da komawa cikin d'aki tad'akko pajamas d'inta tasaka tad'auro alwala tafito tana fitowa taga Ashraf male male akan gadonta hardasu hard'e k'afa yana danna iPad d'insa,tabud'e baki xatai magana ya rigata;
"Ummi Aisha Adam Abdulrasheed wayabaki izinin hawowa sama?!"yace da ita hakan batare da ya kalleta ba yacigabada danna iPad d'insa.
Bata kulashi ba ta d'auki wayarta akan mudubi tajona ajikin charger dake jikin gadon,
"Dake nake fa"yace da ita in a serious tone.
"Test xanyi shysa"tace hakan a tak'aice.
"Okay nikuma bayi xanyiba kenan ko?!"
Bata bashi amsa ba tacigaba da gyara xaman turarukan dake kan mudubinta a jere.
"Ba magana nake maki ba?!"
"Naxata kai kayi ai"tace hakan tana d'an dubansa.
Bece mata komi ba ya mik'e daga kan gadon yafuta waje,d'akinsa yanufa ya watsa ruwa yasaka kayan baccin shima yakoma d'akinta hannunsa d'auke da littafinsa takashe fitilun d'akin se side lamps don neman fitina ya kunna duka xaune yahangota akan gado tana karanta azkharul naum da alama bacci xatai,kallo tabishi dashi sekuma tad'auke kanta,gefen gadon yaxauna tareda janyo littafinsa yana karantawa,
"Bacci xanyi fa"tace dashi a shagwab'ance.
"To me kikeso namaki yanzu?!"yace hakan yana dubanta
"Naga ka kunna fitila kuma bana bacci da haske a kunne"
Tab'e bakinsa yai yacigaba da karatunsa,ganin baxe kashe ba yasanyata jan bargo tarufe kanta ta k'udundune kamar kayan wanki,gajiyar datai yasa batad'au lokaci da kwanciya ba daddad'an bacci yai awun gaba da ita,can cikin barci taji ana shafata,taxata mafarki take abu yak'i karewa sosai Ashraf yake romancing d'inta babu inda baya kissing ajikinta,da sauri takunna side lamp ta b'angarenta tareda sa hannu ta ture hannunsa ganin yadda ya yamutsa mata riga da gashin kanta data gyarashi ta taje yadda taga gashin yatashi kamar iroko tree hularta a jefe shiyasanta tunzura ta mik'e a wahalance don bak'aramin matsa tasha ba,tashi yai yabita har bakin k'ofar dataje yana mata magana