Showing 54001 words to 57000 words out of 107296 words

Chapter 19 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7702

ba'a xuwane ko yaya?!"

"To baxance ba'a xuwa ba amma gaskiya marassa shi ke xuwa,Kuma saboda Allah ka aurar da 'dane inda baxeji 'da din xama ba?!"

"Gaskiane yanzu auren 'KWARYA TABI 'KWARYA akeyi,nikaina nafison tashiga inda xamuci abinci mai yana gangarowa har gwiwar hannunmu inda xamuci naira mu taka naira mu hau naira mu kwanta mu watsa dollars,duk inda mukaje asandamu,ko yaya kikace??"(Allah yarabamu da SHARRIN 'KAWA amiin,kabarmu da 'kawayenmu nagari)

"Hakane 'kawata,Allah yasa haka"

"Ameen,kede bari kawai xuwa anjima kadan xangaya maki abinda nataho dashi Ina Kuma fatan xaki bani hadin kai"

"Tohh 'kawata"

"Ina Kuma baby kay nitunda naxo ban sata a ido naba"

"Wallahy bansaniba tunda natashi nima bangantaba nakira wayarta kuma ashe tabarta anan gida"

"Ko taje school ne"

"Anya kuwa?!amma bansaniba"
(Allah yakyauta Dan Allah mudinga sanya Ido akan ya'ya'yanmu musan dawa suke hul'da/mu'amala,musan inda xasu da Kuma inda suke,ya'yaye mata ba abin sanya Ido bane kabarsu su sangarce,hakan xe iya janyo masu gur'bacewar tarbiyarsu,xaka iya baiwa danka/yarka tarbiyya shekara da shekaru lokaci daya rana tsaka baka fargaba ba xakaga an rushe wannan ginin daka da'de kanayi masu na tarbiyya,hadisi ne ingantacce yaxo cewar kowannenku Allah yabaku kiyo Kuma seya tambayeku abisa abinda yabaku kiwo ciki harda 'ya'yayenku'Allah yasa muda ce ameen)
____Ta bangaren hafsatun captain kuwa suna xuwa suka shiga da sallamarsu haule dataxo kwana biyu tana dan kakakkabe jerin tum tum din dake parlor tagaishesu cikin girmamawa Sannan tashiga 'daki kiran auntyn tata,ba'awani jimaba hafsatun tafito sanye cikin material purple and white dayasha dinki cikin doguwar rigar A shape ya amsheta se babban mayafin kashkha fari data nanna'de kanta dashi,bayan sungaysa ne hafsatun ta umarci haule data kawo masu kayan kwalam da makulashe da aka tanadar masu,da sauran abubuwan Wanda akai dukdande saboda su,Hafsat ta rufe baki tana kallon Hajia sakeena dake shan home lemonade din da aka hada masu,

"Karde kicemin handsome boy dinnanne yaxama haka bade MUHANNAD bane kai halipha ne"

Hajia sakeena tai daria tana kallon MUHANNAD dake murmushi

"Shine Wallahy MUHANNAD ne ai shiyasa nasako shi agaba kiganshi karku hadu awaje watarana kikasa ganeshi,shi'ai halipha bekai MUHANNAD hasken Fata ba"

"Aiko kinkyauta tab lalle girman 'dan mutum ba wuya,Wallahy naxata halipha ne"

"Ina UMMI AISHA kuwa ko tana makaranta?!"

"Wanka takeyi ai xata futo tagaysheku bata da'de dashiga ba"

"Oh okay naxata tana school"

"A'a,da yau'din de da lectures din to Wai malamin daxe masu bashida lapia se akai masu fixing wani lokacin"

"Ayyah,Allah sarki,Allah de yatemaka anata karatu diploma take ko degree?!"

"Degree take level 100 harsunci semester daya ma,tana bsc.international relations"

"Allah sarki Allah yabada sa'a diplomat xa'ai kenan"

Daria Hajia hafsat tayi"Insha Allah,Allah de yaxaba abinda yafi alhairi"Sannan tadan daga murya"haule duba daki kiga idan UMMI AISHA tafuto kice taxo tagayda su aunty sakeenan sunxo"

"Yanzu kundawo nan kenan?!"hafsatun tafadi hakan tana jera foodflask din da haule takawo akan center table

"Wallahy mundawo Kano,bakiji dadin dana ke jiba ko'ina kajuya yan uwa ne gasunan birjik amma can kuwa waka sani banda Wanda katarar dashi,ai shi wanann sakaren yafison Abujan dakyar yabiyomu muka dawo"

Hafsat tai daria tana kallon MUHANNAD dake kallon tv

"Abujan xata 'dan fimasa dadi musanman dayake Kinga basabawa sukai daxaman nan 'dinba,cankuma Kinga peaceful environment ne babu ruwan wani dakai kowa rayuwarsa yake babu gulma babu gutsiri tsoma"

"Hakane,amma gwarade kanon,bamuda nisa ma daku Muna lamido cresent fa"

"Ashe ma banisa,munsamu wajen xiyara akusa kenan"

"Sosai ma kuwa"

Suna cikin hira UMMI AISHA tafito sanye cikin Riga da skirt na atamfa tasaka hijabi har kasa baki ja kalar kayan,babu wani makeup a fuskarta tayi Kyau abinta,fuskarta dauke da murmushi tashigo parlor din tana sallama har kasa ta tsugunna saitin hajia sakeena tana gaisheta,tunda UMMI AISHA tashigo MUHANNAD yakasa dauke idonsa akanta gaba daya yakasa koda motsi yaxuba mata idanuwansa yana kallonta tundaga sama har kasa sosai tayi masa kyau yashagala da kallonta kenan muryar mahaifiyarsa ta tsaida shi daga tunanin dayai xurfi cikinsa,

"MUHANNAD tana gaisheka fa tunanin mekakeyine?!"

Firgigit ya kauda idonsa daga UMMI AISHA yana Sosa 'keya baki narawa yake fadin

"Ba..ba.komai mama na dantafi day dreaming ne kan..."

Bekarasa ba UMMI AISHA tasake fadin
"Ina wuni?!"tana kallon gefe don taji ajikinta kallonta yake

"Lapia qalau,ya karatu?!"

"Alhamdulillah"tabashi amsa a ta'kaice

Haka suka nufa dinning Hafsat tai serving kowa abinci,se karar chokula ce ke tashi,itade UMMI AISHA tsakura kawai take tana ci don duk sanda tadaga kanta setaga idon MUHANNAD akanta,haka sukaci abincin suka koshi Sannan suka koma parlor MUHANNAD yatsinci kansa da san hira da UMMI AISHA,tunyana mata tambayoyi tana bashi amsa atakaice harde tagaji tasaki jiki dashi sukai ta hira kamar Wanda sukai shekaru da sanin junansu,ya lura batada hayaniya shidinma haka sede yadan fita hira don inde tabashi amsa setai shiru harse yasake sako wata tambayar daban,

•LAMIDO CRESCENT KANO

"Wai meye matsalarka dude ?!gaba daya ka shareni Baka magana abeg free it"

wani saurayi baxe wuce sa'an ASHRAF dinba yake fadin hakan dake xaune akan couch din dake dakin ASHRAF din,

"Nafada maka babu komai jay,kawai kaina ke ciwo"ASHRAF yabashi amsa a ta'kaice

"plss dude kafadamin menene matslar,plss just a piece of advice xe warware koma menene"

"Okay fine !ba wani abin bane akan wannan yarinyar nan ne"

"Wannan Wadda naganku tare a school"

ASHRAF ya wurga masa harara"what the fu..wannan yarinyar xaka hadani da ita?!Allah yakiyaye,sister dinta ce oh boy baxaka ganeba,I tried my best to stuff down the feelings akanta nakasa"

"Goddamnit,dama Akan hakan kake wannan abin,kawai kasameta kafada mata mana"

"Kullum nai approaching dinta daniyan nafada mata sena kasa,gashi sister din nata kullum taita takuramin niba sonta nakeba amma takasa ganewa Ita kuma THE MAGNIFICENT din bata ko kulani"

"Sunanta kenan THE MAGNIFICENT?!"

ASHRAF yai murmushi a hankali"well shima sunanta kenan,but sunanta UMMI AISHA'THE MAGNIFICENT'kuma award title din tane da aka bata,baxaka ganeba jay but..,"sekuma yai shiru yai kasa da kansa

"Dude yau kaine kake xancen mace?!so amazing atlast kasamu wadda kakeso"

"Idan ina gidah bana ganin komai se Ita,whenever naje school koda ba akusa nakeda Ita ba,sena dingajin wani mood atare dani me da'di,could this be love or like?!"

Jay(Jameel)yai daria"wanann yawuce like,dude wannan sign of love ne love dinma babban kamu kayi Allah yabada sa'a"

"Yaxanyi?!shunning dina take fa,bansan yaxanyi ba"

"Why not kayi dating sister din nata Ita baby Kay din"

"What the fu..,no noo baxa'ai haka ba baxan iya ba"

"No bawai dagaske ba,kagane kayi pretending like kanasan baby Kay din,duk inda Kasan UMMI AISHA nagurin kaje wurin kadinga pretending da baby Kay din kanuna mata so,everywhere ko a lectures ne"

ASHRAF yai fake smiling"gross,completely gross wannan taboo ne kaima Kasan baxanyi ba"

"Yass wannan shine kadai solution ta haka xakaga tanuna bataji dadiba or something like that de wannan girly jealously din nasu na mata xaka tadawo tana sonka"

ASHRAF yadinga Daria harda rike ciki"Wallahy jay idan nai haka wani Matsala yafaru duk abinda nai maka kayadda??"

"Yass na yadda"jay yafadi hakan with full confidence

"Well xanyi 'kokari nayi Allah yasa na 'iya"

"Xaka iya bad boy game kawai xakai playing,a karshe Kuma xakai wining heart din UMMI AISHA trust me"
Haka jay yaita influencing ASHRAF harde ya yarda xeyi kamar yadda yace...




•✨•
61


•SARDAUNA CRESCENT KANO;


Har waje su hafsat da UMMI AISHA suka rako su MUHANNAD,har wajen motarsu,MUHANNAD da UMMI AISHA dasuke baya suna hira ahankali MUHANNAD yasa hannunsa aljihu yaxaro wayarsa 'kirar iPhone6s+ yamika mata,ahnkali kamar me rada yake cemata:

"Can I have your digits pls?!"

Batai magana ba illa wayan data karba tasa masa number din nata,Sannan sukai sallama suka ja mota suka tafi bemaso suka tafi ba,yaso yaxauna har forever yana kallon UMMI AISHA dayakejin tana ratsa magudanar jininsa da 'bargonsa,
Muna_b da magajiya dake lekensu ta window se da sukaja mota suka tafi Sannan suka janye labulen suka koma suka xauna

"Kinga yakarba number ta ko?!"muna_b tafadi hakan tana tabe baki

"Nagani to mexanyi akai?!"

"Akwai kuwa yadda xaki,kina bani mamaki dakike bari opportunities dinki suke wucewa arayuwa idanfa baki tsayawa baby Kay ba tokwa xatai kwantai a layi"

"Wallahy ni abubuwannan sun isheni kawata,ga xubar gashinan kalli kaina yadda yadawo kalli yadda narame narasa meyake damuna,nifa ko asibiti nakasa xuwa Wallahy"

Takarahe maganar tana cire 'dan kwalin kanta babu komai akanta Se gashi tsilla tsilla kamar wadda tai gobara akanta gashin dukya saisaye se 'kuda 'kuda kamar gashin hammata,

"Tohh Allah yabaki lapia asibiti xakije dole,amma wannan xance kuwa tashi tsaye xamuyi akai bamuga taxama ba"

"To yaya xamuyi kenan?!"

"Best solution din dayafi yanzu 'kwaya dayane kinga de hafsatun mukasa mata hauka shekara goma sha hudu tabar gidah batasan inda takeba badan ma wannan yan iskan sungantaba sunsama mata lapia tahanyar rokon Allah aida babu labarinta sede me irin sunanta,kalli duk abubuwan da mukai akan cikinnan nata Kuma sedata haife ta gashinan yarinya taxama budurwa ma yanzu abinda yafi kawai shine musa'ayiwa Ita 'yartata raping Kinga haka xesa a 'kyama ceta kowa baxeso ya aureta ba"

Magajiya ta dafe 'kirji tana ware idanuwanta"rufamin asiri kawata uhm uhm badaniba gaskiya Ina xan iya wannan 'danyan aikin"

"Bawai muxamu samo ai mata ba bakuma yanzu nake nufi ba,acikin masu son nata xamu samu 'daya musan duk yadda xamuyi koda tahanyar gusar masa da hankali ne Yayi mata ta karfi dayaji,kamar misalin Wanda yakarba number din nan nata,yai mata hakan bayan angusar masa da hankalin yakuma dawo yatubure yace shi bashi bane Kinga baxe aureta ba kenan,Kuma sauran samarin nata xasu gujeta"

Magajiya tasaki ajiyar zuciya"banfahimce kiba kawata"

"Da Hausa fa nake magana,Tohh abin nufi shine fyade xamusa ayimata a LALATA rayuwarta,Kinga yadda captain yakeson yarinyar hakan xe ragu a xuciyarsa xekuma nisanta gatan dayake mata tunda naga YAR GATA CE,Kuma hakan bakaramin tashin hankali xesa hafsatun ciki ba,Kinga captain xega kamar bata bata tarbiyyar kirki bane ko Yaya kikace?!"

"To idan Kuma besaniba fa,ma'ana idan basu sanar dashiba suka boye hakan fa?!"

"Wannan maganar baxata 'boyuba baxamu barta ta 'boyuba,maganace wadda babba da yaro kowa seyaji ta cikin danginnan rankataf gaba da bayansa"

Magajiya ta girgixa kanta tana gyara 'daurin 'dankwalinta Sannan tafara fadin,

"Gaskiya 'kawata...........!"



•✨•

"Thank you for how well this story has already done,I'm kind of mind blown bisa ga warming comments dinku dake 'karfafa min gwiwa,it barely even started#😂😂😂love y'll,a Kuma 'karamin hakuri makaranta ta aureni sosai se addua kawai,Allah yabamu sa'a Amiin.....!"



WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.......
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
62

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

"Gaskiya 'kawata ban ta'ba sanin kinada wannan babbar idea haka ba,shekara da shekaru aida tuntuni kika fa'di haka da munsa angama mata aiki"takarashe maganar tanabawa muna_b hannu suka tafa,

"Banda abinki Idan da'din nafadi hakan ke seki yarda da hakan?!ai da da'din akai hakan datuni yanzu tadawo ta ha'de ba lalle agane ba tunda an'dau tsawon shekaru kuma karki manta inde hakan tafaru babu wanda xa'a xarga fyace ke,tunda awajenki take..xa'aga wani sakaci ne haka daxesa ba'ayiwa diyarki ba setata tunda kusan sa'annine,yanxu kuwa babu Wanda xece kece tunda yarinya ri'konta yakoma wajen mahaifiyarta"

"Gaskia 'kawata kinada kaifin basira,Allah de yabarmu tare"

"Ameen 'kawata,ai kafin ka aikata abu kayi naxari akai tukun,nada'de ina kawo wannan araina Idan baki mance ba nata'ba ce maki inde akan UMMI AISHA ne kibarni ni nasan mexan aikata akanta,to bakomai bane fyace wannan maganar dana kawo yanxu"

"Natuno kuwa tabbas hakan take"

Suna cikin magana baby kay tashigo tana tafiya sharaf sharaf da alama agajiye take li'kis,xama tai Akan kujera tana maida numfashi,

"Ke Kuma menene haka kamar wadda tai gudun famfa la'ki?!"Muna_b tafadi hakan tana kallon baby kay

"Aunty muna_b ina yini?!nagaji ne wallahy bacci ma nakeson yi"

"Daga ina kike school?!"

"No,munje la_sultana ne nida wasu frnds na,frnd dinmu xatai bday awajen"

"Ohh okay"

"Yeah"
baby Kay tafadi hakan ata'kaice Sannan ta mi'ke tashiga daki kotakan magajiyan bata biba,
Haka magajiya da muna_b sukaci gaba da hirarsu se da yamma takusa Sannan muna_b tabar gidan takama hanyar kaduna!
___Bayan wani 'dan lokaci,sha'kuwa ce sosai tashiga tsakanin MUHANNAD da UMMI AISHA kusan kullum yana gidansu UMMI AISHA,safe rana dare yana gidan bacci ne kawai ke maidashi gida,Ita kanta UMMI AISHA sosai tayi mamakin saurin sha'kuwar su da MUHANNAD din kodayake shi ba arrogant bane kamar ASHRAF,he's very friendly Kuma ya'dauketa kamar 'kanwarsa,bata 'boye masa abunda ke damunta komai ma fa'da masa take,Kuma yana bata shawara dede gwargwado,ta'bangaren ARFAAN kuwa duniya tamasa xafi musanman dayalura akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin UMMI AISHA da MUHANNAD din,

Kamar kullum ranar asabar da rana ARFAAN yashiga part dinsu UMMI AISHA bayan yadawo daga jogging din dayake,yana shiga bakinsa dauke da Sallama yaxauna akan kujera me biyu dake facing Wanda UMMI AISHA take kai,tayiwa kanta matashi da trowpillow dake kan kujerar tana danna waya se murmushi take,ajiye wayan tai agefe tana murmushi,
"Ya ARFAAN kadawo?!"

"Uhm nadawo"yace da Ita yana kauda kansa gefe,

"Wai dagaske yau ya MUS'AB xexo?!"

"Gashi kuma kin fa'da"

"Thought ko wasa yake daya gayamin yanxu,Kasan sungama exam din final dinsu se project dasuke"

"Ina Aunty?!"yace da'ita be bata amsar data tambayeshi ba danbayason Kara sako xancen MUS'AB,ya lura UMMI AISHA tafi sabawa dakowa akansa

"Ammi tana kitchen,barin kirata"

"A'a kyaleta ai ina nan harta fito"

"Tohh"UMMI AISHA tafadi hakan Sannan takoma tai kwanciyarta tana cigaba da danna wayarta,sanye take cikin doguwar rigar material blue tasaka babban hijabinta yellow akai,Dan Ammi tace mata tadinga sa hijabi akai inde safiya tai saboda su ARFAAN dake shigowa tunda ba muharramanta bane,ga kyakkyawar sura da Allah Yayi mata me 'daukar hankalin duk Wanda yakalleta shiyasa ammin tasanya mata dokar hakan

Ba'awani jimaba hafsat tafito tana goge hannunta da hand sanitizer,ganin ARFAAN xaune yana kallon jarida yasata xama kan kujera tana dubansa,shi hankalinsa ma baya kanta
"ARFAAN yaushe kashigo?!"

"Ban wani jimaba dashigo waba"

"Aida katurata ta kirani"

"Eh tace kina kitchen bari takiraki,nace a'a tabarshi tunda aiki kike xanjiraki"

"'Dan wake nake sakawa,MUHANNAD ne yace yanaso nace barinyi mana duka,aikaima kanaso ko?!sede Kai da mangyada kafiso"

"Eh am..."bekarasa ba MUHANNAD yai sallama yashigo cikin parlor din sanye yake cikin 'kananan Kayan dasuka amshi jikinsa se kamshi yakeyi,
Hannu yabawa ARFAAN din kansuyi sallama seda ARFAAN din yajima kafin yabashi hannun,Sannan ya mi'ke tsaye,
"Aunty barin koma da'ki"

"Baxaka bari agama 'dan waken ba ARFAAN?!"

"A 'koshe nakene Aunty may be xuwa anjima xanci"

"Shikenan ARFAAN"Hafsat tafadi hakan tana kallon ARFAAN din dayafuce fuskarsa a 'daure Lokaci daya yanayinsa yacanxa,shiru tai tana naxarin ARFAAN din kwana biyu,kamar Akwai wani abu tskaninsa da UMMI AISHA,amma koma meye xata tambayi UMMI AISHA Idan MUHANNAD yatafi,musanman yadda taga suka gaysa da MUHANNAD din dakyar yabashi hannu,

Sosai MUHANNAD yajima agidan sunata hira da UMMI AISHA,harta dakko note dinsu na international law yakoya mata under'vienna convention of treaties'tunda shi xasuyi ranar Monday dayake MUHANNAD din yayi professional masters akan international law 'din yanxu haka form yasiya na Ph.D. xefara,Kuma yana aiki a 'national biotechnology development agency,dayake cikin 'bio resources development center,kano a makarantar bayero university Kano,babban admin ne cikin administrative site dake wurin',bayan tafiyar MUHANNAD kenan hafsat takira UMMI AISHA karamin parlor din dake 'dakinta,

"UMMI AISHA"Hafsat tace da ita tana kallon tilon 'diyar tata tana Kuma jin sonta yana ratsa jijiyoyin jikinta,

"Na'am Ammi"

"Magana xanyi dake kibani hankalinki nan kina jina?!"

"Ina jinki ammi"UMMI AISHA tabata amsa kanta asunkuye

"Kinga kede yanxu kin wuce lokacin da baxakice bakison so ba,kifa'damin gaksia amatsayina na mahaifiyarki tunkafin maganar nan taje wajen baffanku,tsakaninki da Allah cikinsu wanene kuke soyayya dashi?!"

UMMI AISHA ta ware Ido tana kallon mahaifiyar tata,suwaye haka?!tatambayi xuciyarta,
"Ammi suwaye?!"

"ARFAAN KO MUS'AB?! Cikinsu wakike soyayya dashi bansan sakarci kifadamin gaksia"hafsat takarashe maganar cikin tattausar magana,

"YA ARFAAN KO YA MUS'AB?!"UMMI AISHA tamaimata hakan a fili,da alama maganar xuciyarta ce tafuto fili'to Ita kuwa babu Wanda yataba furta mata koda kalmar so cikinsu,ko nunawa babu Wanda yai cikinsu sede brotherly advice dasuke bata insun ha'du kowannensu,

"Ehh inajinki"

"Ammi Wallahy Allah babu"

"Babu me?!"

"Allah kuwan babu wani cikinsu damuke soyayya dashi Allah ammi kiyadda babu,babu kowa ma basuba Allah,ni karatu nakeso ammi"takarashe xancen muryarta na rawa,

"Shikenan tashi kibani waje"
hafsatun tafadi haka tinda tagano hakan tunma ba'a abinda tafadi ba,kodaga idonta ka kalla xaka gane,musanman dayake UMMI AISHA bata boyewa mata komai nata,yanxunma tatambayeta danta gano gaskiyar al'amarin Kuma tagane basu fada Matan ba amma da alamar suna son yarinyar,daga hannu tai sama tana adduar Allah yaxa'bawa yarinyar abinda yafi alkhari,yabata miji nagari wanda xasu xauna tare har karshen rayuwarsu,






•✨•
63




•LAMIDO CRESCENT KANO;
WASHEGARI:

"Kabuga mata nace dude bakajin magana wallahy"
Jay ne kefadin hakan yana kallon ASHRAF dake dafe da Kansa,

Dago idanuwansa yai coffee brown dasu wani lokacin Kuma xakaga sunkoma kamar grey color haka Allah Yayi masa su,Lokaci daya sunkada sunyi jawur dasu,

"Wai tsaya idan Kuma yarinyar nan taxata dagske nake fa,Allah yakamani da hakkinta kenan?!"

"Dude,fear not okay,kagane pretending xakai bawai harga Allah kake nufi ba,Idan Kuma baxakaiba kaxauna so yakasheka,nixan tafi tunda baxa'a Baka advice kadauka ba"
Jay ya'karashe maganar yana mikewa tsaye,

"Ina xakaje yanxu?!"

"Ina ruwanka?!"

"I'm serous Ina xakaje?!"

"Akwai wani clubbing daxa'ayi a la_sultana shine xanje"

"Barinxo muje,"ASHRAF yafadi hakan yana duba Kaya a closet dinsa kasancewar singlet ce kawai ajikinsa

"Ina mota"

"Okay"

Bayan ASHRAF yasaka kayan nasa shirt yadora blue darubutu da black color a rubuce'bad boy'seyasaka black skinny jeans dinsa da pcap,yafesa turarensa sannan yafuto wajen inda jay yai parking motar tasa,Sannan yabude gaba yashiga,kafin jay yatada motar yaduba ASHRAF
"Dude yaushe aka tare a wannan gidan?!"yasa hannu yana pointing wani duplex gidah me fentin blue da silver,

"Ohh,wasu ne suka dawo daga wani gari ne saboda matar gidan tashigo gidan mu kwanaki wajen mama"

"Ohh okay,ai gwara da kuka samu neighbors,amma da duk fadin layin nan kukadaine sewani gidah a bayanku se station na police"yakarashe maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login