Showing 15001 words to 18000 words out of 107296 words
tambayar Ina kake ,tace wallhy kunya dukta kamata ,toh kasani ni kaba kunya bawani ba,dan ni nace mata xakaje kuma nace kafin kaje ma xaka kirata awaya kuma haka mukai dakai,da kujerun nan suna magana da sun bada amsa domin sune sheda se wannan yaron (Yaya sameer)...ashe ashe kunnen uwar shegu kai,kai fatali da maganata,ina mamakin sauyawarka lokaci daya 'dannan..nasanka da BIYAYYAR IYAYE amma yanxu duk karushe wannan tarbiyyar,
"Capt adam yagirgixa Kansa yana hawaye dan dede da second daya bayasan ganin fushin gwaggon nasa,dukkoda yasan har a zyciarta yasan batasan wannan abin datake masa,annamimanci ne da kuma munafurci irin na 'kannensa Wanda sun saba yimasa shi,har mamaki yake kome yasa oho?!"murya narawa yake fadin gwaggo dan Allah kiyi hakuri wallahy tallahy ba wai da niyya nai hakan ba,
"Naga niba yaro bane Ita ba yarinya ba,mexe sa ma tawani kaini wurin kawayenta su ganni?!,naga ba auren fari bane,amma insha Allah xanje gwaggo xami magana da ita."Rannan dinma Wlhy akasi aka samu dakuma halin mantuwa irin namu na'yan adam,gwaggo Allah ya huci zuciarki ,nasan nayi kuskure insha Allah baxan sake ba,
"Tsakanin uwa da 'da se Allah ,kankace me,murmushi har ya fada'da a fuskar gwaggo ,tuni ta yafe masa suka shiga hira na abinda xe wakana a bikin..dama gwaggon ba haka halinta yakeba mata ce me halin dattako da sanin yakamata,"gwaggo tace to lalle bayan magrib yahanzarta yaje su gaisa da magajiyan kada abin yaxama abin magana,
"Bayan sallar magrib kuwa,Capt adam yayo wankansa dukkoda bawai dan magajiyan yaiba,Yayi ne kawai saboda gajiyar tafiya dakuma yanayin hazo nagarin,
"Farin yadi yasa shara shara wanda ake iya hangar kyakkyawar farin shimin (singlet) dake jikinsa me 'dishi dishin baki,bakar hula yasa tareda takalmi baki se agogon hannunsa silver color na company din swatch,mild perfume yafesa,sosai yayi Kyau kamar wani matashi baxaka taba cewa yakai shekara hamsin ba,kodan yana samin gatane dakuma karatu na alqur'ani dayake akai akai?! Yayi Fresh dashi sosai gashin kansa yakara kwanciya luf, sannan yafita waje wurinsu yace jirgi yakaishi unguwar tudun wada dake kadunan inda nan gidansu magajiyan yake,
•✨•
14
DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼
•✨•✨•✨•✨•✨•
"Sosai sunsha wahala kafin su gane gidan ,dan rabansa daxuwa gidan tun mahaifiyar magajiyan na raye wato inno fanta,dede wani madedecin bungalow (gida marar bene/flat)sukai parking kamar yadda aka masu kwatance,
"Capt adam yaja iska ya fezar yana kallon gidan,dakyar yadan kauda kansa gefe murya adakile "yace jirgi samu yaro katura cikin gidan kace magajiya taxo inji adam din gwaggo yanxu,jirgi nafita Capt adam yaja tsaki bumbling idiot kawai ko uwar mexatamin oho,badan kaddara bama wallahil azim mekama da itama baxan kula ba ballanta in aureta,
"Maganar jirgi ce ta katse mai tunani,"jirgi ya leko ta fuskar mudubin mota yana magana'oga ga...ga ta tafito fa,
"Ko kallonsa capt adam beyiba seda yagama 'fadansa shikadai sannan yaja tsaki yabude kofar motar yafito,
"Bakar fuskar magajiya ce tafara masa sallama ,se washe baki take ,ga gatson bakinta ta sunturo waje,se wangale baki take tana wani rausaya gata shapeless da ita,
"Abinda take shi yabawa capt adam daria,se wani bankaro kirji take tana fari da ido,hamdalah yayi azuciarsa ganin hafsat dinsa tafita komi,muryartace takatse masa tunanin dayake Jiyai kamar buga drum ake dan sosai yafita sanyin murya,
"Yaya adam ina wuni anxo lapia nayi fushi seyau xakazo?!
"Capt adam yaja tsaki a fili sannan yai Allah ya isa azuciarsa naganin irin matar dasu surayya suka hadashi da ita,"a fusace yace lpy qalau ,to banda abinki auren nanfa dole akamin sanin kankine inada matata danakeso kuma takeso na,yanxu ma danaxo seki godewa Allah ko,kinje kina neman hadani da uwata ko,to burinki yacika gani nazo...
"Magajiya tai katsa da murya tanawani shagwaba,ni ni yaya adam bawai hadi bane ,'kawayena keta san ganinka shine fa nafadawa gwaggo hakan,
"Capt adam ya murtuke fuska ke dan gidanku nixakiwa shagwaba?!sa'an kineni,kokwa dan 'kaddarar aure tahadamu shine zaki renani?!sannan yasa yatsa yana nunata ni ba sa'an wasan kibane barganin kin saye bakinsu surayya,sannan inaso inja maki kunne wannan yaxama nafarko kuma nakarshe kada ki kuskura naji maganarnan agun gwaggo wallahy tallahy naji wannan tafito abakin gwaggo to kisani duk hukuncin dana dauka akanki kada kizargi kowa,
"Magajiya tai shiru tana sauraronsa sannan tace Toh seda safe,
"Harta juya tafara tafiya Capt adam yai tsaki nace kitafi ne?!sannan yasa hannu a aljihu yaciro bandir na dubu daya yamika mata ungo kyayi wata hidimar ta biki,
"magajiya tadan tsugunna tasa hannu biyu takarba sekace mutuniyar arziki,kaman gaske...tareda doriyar nagode yaya adam Allah yakara budi'.
"Bebi takanta ba ahankali yace ameen sannan yai tafiyarsa yashiga mota,jirgi yaja suka tafi...
"Suna tafiya magajiya tai Wata bazawar daria tana kallon kudin daya bata'ta yatsine fuska lokaci daya tacanxa yanayinta kamar bata taba fara'a ba,'adam kenan senayi maganinka da so called matar taka dakake ikrarin fadi,sena maidakai tafin hannuna muje zuwa,sannan takoma cikin gidah!
"Tunda Capt adam yazo kaduna gwaggo batabarshi yaje Kano ba,daurewa kawai yake amma Yayi missing Hafsat dinsa kwarai matuka'sede kullum suna manne awaya abinsu,
"Tun ranar juma'a da daddare Capt adam yake kuka sosai kaman ba babban mutum ba ..sosai hafsat take bashi hakuri ta waya,kukan dayai yafi Wanda yai sanda babansu ya mutu,dukde saboda bakin cikin auren magajiya da zeyi yadda kukasan shine kishiyar daxe xauna da ita,da baki da hafsat take bashi dakuma Wanda yaya sameer a kanwarsa bilkisu suke bashi yasamu salama a zuciarsa,
"Ranar asabar da safe karfe shadaya da rabi aka daura auren Capt adam abdulrasheed da magajiyan inno fanta akan sadaki naira dubu hamsin chif..karfe shabiyu Dede akai reception a farfajiyar gidansu,antaru ba lefi,dukkoda ka'karo murmushi kawai adam yakeyi yana gaisawa da mutane amma cikin zuciarsa tarin bakin cikine wanda baxe misaltuba,
"Ana gama hidimar walima capt adam yakoma sashen baki tareda dialing number Hafsat dinsa yana kira,sau uku yana kiranta bata dauka ,hankalinsa yakai matuka atashi,bashiri yaxiri mukullin mota kotakan jirgi driver bebiba yatafi kano,
"Itakwa Hafsat alokacin tana gidansu sunata shan hirarsu wayar tatakuma tana dakin mjay kanwarta sukuma suna parlor,.....
nanahafsat.wordpress.com
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
15
©•MISS XOXO
👄
DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼
•✨•✨•✨•✨•✨•
"Hafsat sunata shewa da yan'gidansu a parlor mama itace mahaifiyar tasu(koda yake mahaifiyarsu hajia amina tadade da rasuwa tinlokacin su hafsat din na kanana,se aka baiwa mahaifin nasu kanwarta 'Hajja Fareedah'wadda suke cewa mama,sosai take rike dasu kaman ya'yan data haifa,su biyu ne kawai wajen mahafiyarsu daga hafsat din se mjay,inda kanwar maman tasu kedah ya'ya 3 maza biyu wanda yan biyu ne habbab da hanbal,se mace kwara daya ihkhram wadda ke schooling a amsterdam!
"Mjay tadakko wayarta agefen kujeran datake xaune sannan tadago kai tana kallon Hafsat din,"Yaya hafsat anturo RUWAN KASHE GOBARA ki maxa kishiga duniyar makaranta yanzu,'se asannan Hafsat ta tuno tabar wayarta adaki,
"Mikewa tai tana aini shaf namanta wayar ma adakinki,xanso inga dillema din daxe faru tsakanin lamido da ihkas,"mjay tace hmm akwai ruguntsumi nan gaba,Hafsat tai hanyar dakin mjay,tana fadin kede bari ai akwai jan aiki,
"Tana shiga dakin mjay,tai sauri tai zipping jakarta tadakko wayar tata,Wanda 5 missed calls tagani,3 na
Hayatee dinta se 2 na wata kawarta 'nafeesat'
"Sauri tai tareda dialing number hayatee din seda ta kusa tsinkewa sannan yadaga,dasauri tai salllama tana fadin hayatee,aimin afuwa pls nabar wayar ne adaki nikuma ina parlor tareda su mama,"capt adam yace bawani abu my hafsat ina driving yanxu I wll call you back,"jiki sanyaye hafsat tace okay hayatee drive safe,sannan takatse wayan,
"Komawatai jikin bed site drawers tajingina ajiki tana tunanin ko Yayi fushi ne da'ita?!to driving din meya keyi yanxu ?!oh okay kila daga wurin daurin auren ne,
"Jiki sanyaye takoma parlor taxauna,mjay tace yanxu nasan andaura auren yaya adam ko?!tanayi tana kallon hafsat din,sekuma tai saurin sa hannu tarufe bakinta dn bakaramar katobara tai ba,
"Mama dake karatun magazine tai saurin ajiyewa agefe tace wane adam dinne xaiyi aure badai mijin hafsat ba?!!
"Itade mjay shiru tai dukta dubibice tai kasa da kanta,hafsat ta kakaro murmushi tana kallon mama, Sanyayyar ajiyar zuciya tai sannan tace "ehh adam ne zekara aure,amma tilasta mashi akai bawai yin kanshi bane,cousin dinsace aka hadashi da ita,kiyi hakuri mama dabamu sanar maki ba,
"Mama tace bakomi hafsat aiba magana me dadi bace dakin gayamin dinma,toh Allah yasa hakane mafi alkhairi ,yabaku xaman lapia yahada kawunanku,Ki saurareni dakyau nasanki da biyayya amma kikara wata akan wadda kikeyi,Sannan babu ruwanki da zazzafan kishi kinajina ,ansan duk macen dabata kishin mijinta batacika mace ba amma atleast kakki nuna kishinki akanta,tukunna ma wacce cousin din nashi aciki?!
"Hafsat tace magajiyan inno fanta wadda auren nan nata ya mutu,
"Mama tace ohh wannan ta kadunan ko,nide ince aiba wasu yammata ragowa inde ba mancewa naiba,akwai wasu addu'oi na tsari na kariya sunanan arubuce insha Allah inxaki tafi xandakko maki Allah yakareki daga sharrin masu sharri ,
"Hafsat tai kasa da kanta Tana fadin amin mama nagode,
"Sosai mama taxauna tana Bawa hafsat motherly advice tana dauka,harzancen kayan daya kawo mata sedata fada mata,mama ta ajiye kunya a gefe tabata shawarwari kan yadda xata kula da kanta dakuma mijinta,seda suka shafe awa daya da rabi suna magana,"alokacin kuma megadi yaleko yana fadin Capt adam yace amasa iso yana kofar gate,
"Hafsat taware Ido tana kallon megadin,"yana waje kokuma dan aike ya aiko?!
"Kafin yabada amsa mama tace jeka ilu kace gatanan fitowa,sannan tadaga kai takalla hafsat datai shiru kaman me tunani,"jeki yana waje kinsan dasanyi garin kishigo dashi ciki,Hafsat tace toh Sannan tadau mayafinta tayafa tafita wajen ....
16
•✨•✨•✨•✨•✨•✨•
"Da sauri takarasa inda yake tana aika masa da kyakkyawan murmushinta Wanda bakowa takeyiwa ba sefa adam bahadeje,shima sakon murmushin yamar mata Wanda kyakkyawar wushiryarsa ta bayyana,
"Ahankali takarasa inda yake,bayan sungaysa tace hayatee mushiga ciki bansan sanyinnan yatabaka,capt yaware ido yana fadin"inkin ganni lahira kaini akai my hafsat,kinsan nawa mama babban lefi bansan dawanne idon xankalleta ba,
"Hafsat tai murmushi tareda sa hannunta tarike hannunsa suka fara tafiya tana fadin"Bakomi ai hayatee nariga nafada mata duk yadda abin yake kakka damu kanka,
"Atare suka shiga cikin parlor din Wanda mama harta bar gurin..kujera yaxauna yana yan waige waigensa,"Hafsat tasa gefen mayafinta tana daria kasa kasa "hayatee kacika tsoro wallahy calm down mana,bata rufe bakiba mjay tafito daga daki da saurinta ta karaso wajensu tana magana,
"Yaya adam yau agari,sannan tagaysheshi,"capt adam ya amsa cikin fara'a 'mjay mutan capetown naga turare me dan karan kyau da tsada nagode Allah yasaka da alkhairi,
"Mjay tai daria 'Yaya kenan naga kamin godia a whatsapp kamin ta waya Sannan yanzuma kasake min godia ,nice xanyi godia hidimomin da kakemana Allah yasaka da alhairi,
"Capt adam yai murmushi kawai ,ina mama?!bamu gaysaba,mjay tamike tace barin kirata...
"Mintina kadan maman tafito sanye da dogon hijabi kamarsu daya da Hafsat din sede itama bakace kamar mjay,gaisawa sukai sosai da adam din cikin kamala da sanin yakamata,
"Murya na rawa capt adam yake bawa maman hakuri kan rashin sanar da ita dayai auren daxeyi,"mama tai murmushi "bawani abu kada kadamu kanka wallahi zance ya wuce,Allah yasanya alhairi yahada kanku,Allah yakauda fitina,
"Capt adam yace ameen,"mama talura a takure yake dan inde tana guri baya sakewa,mikewa tai tanafadin murja kawo masa abinci da drinks a kitchen,"ka gayda mutan gidan,
"Capt adam yatsiri Sosa keya yana dukar da kai,xasuji insha Allahu,
"Seda yaci dadda'dan abincin maman,tsaftaraccen dambun shinkafane dayaji carrots da green beans se yankakken hanta sliced aciki,tareda salad dayasha hadi,gefe daya kuma kunun aya ne dayasha madara se kamshi yake,seda yaci yakoshi dan rabonsa dayaci abinci haka sosai tun yana Kano kafin yaje kaduna,dan duk sanda yatuno magajiya ce xexauna da ita amatsayin matar aure seya ture abincin gefe guda haryadan fada,,sosai yaci yakoshi sannan yamasu sallama,suka fito shida Hafsat dinsa compound din gidan inda motarsa take,
"My hafsat muje gida ko?!hafsat ta bude idonta tana kallonsa hayatee muyime agidan ?!
"Capt adam yai murmushi tareda daga mata gira daya,yanzu dan miji yacewa da matarsa haka lefine?!
"Hafsat ta girgixa kanta bakai lefi ba hayatee sede naga bekamatabane,
"Capt adam yace ko?!to meyasa bekamataba inajinki?!
"Hafsat tai kasa da idonta danbaxata iya jure kallonsa ba,hayatee kasande yau akai daurin aurenka a kaduna ko,amma kakamo hanya kataho kano yanzu nasan su yayana(Yaya sameer)sunacan suna nemanka tawaya,kaduba kaga zancen nan..Dan Allah kayi hakuri wallahy bada wani abin nafada ba banasan abinda gwaggo xatai fushi dakai hayatee ,
"Capt adam yai ajiyar zuciya yana hura iska Yana fezarwa gabadaya mood dinsa yacanxa "da husky voice dinsa yakalleta bayan yabude mota yashiga shikenan my Hafsat nagane uzurinki amma kisani nifa magajiya bandauketa amatsayin matar aure ba,
"Hafsat tai saurin bude gaban mota tashiga'karkace haka hayatee abinnan fa haka Allah yarubuta seya faru saboda haka ka fawwala masa al'amuranka kawai,insha Allah xancigaba da tayaka addua ,"Capt Adam yace nagode Allah dayabani KE amatsayin matata,'Hafsat tai murmushi Sannan ta matsa kusadashi,
"Kiss tamai a kumatu tareda fadin Allah yakaimun Kai lapia hayatee,Capt adam yace uhm uhm my Hafsat ai ba anan kikeminba,Hafsat tai murmushi sannan tamai a inda yakeso Sannan sukai sallama tarufe masa kofa takoma ciki cikeda soyayyar mijinta,
"Hakan take awajen Capt Adam Dan dakyar yaja motar se kaduna ,yanatafe yana tunanin Hafsat dinsa da irin kyawawan kalamanta dasuke shiga jinin jikinsa suke kuma zaga kwakwalwar sa,murmushi yai yanafadin Allah kabarni da Hafsat dita har karshen rayuwarmu!
nanahafsat.wordpress.com
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
17
©•MISS XOXO
👄
DEDICATED TO
UMMI_A'ISHA👌🏼
•✨•✨•✨•✨•✨•
Seda Capt adam yashiga cikin kaduna sannan yakunna wayansa,dan tunlokacin daya amsa Kiran Hafsat dinsa yakejin alamar waya nashigowa shyasashi yakashe,sosai messages sukai ta shigowa na Allah yasanya alkhairi dakuma na yana ina abokai nata nemansa,bekarasa karanta message din imran abokinsaba dayake tsokanarsa wai 'mijin hafsat angon amar....kiran Yaya sameer ne yatsaidashi daga karanta messages din dayake,dasauri yadaga tareda sawa a handsfree,
"Slm alykm yaya....bekarasaba 'Yaya sameer yafara fadin,
"Kana ina haka adam?!yan uwa da abokanan arziki se nemanka suke saboda Allah tunda aka gama reception kaxargawa karenka igiya ina kaje oho,kabar masu daukar hoto da video coverage dukma bawannan ba saboda Allah kasa gwaggo se fada takemin,kana Ina yanzu haka?!
Capt adam yai shiru yana sauraron yayan nasa wanda yasan wannan fadan dayake haka tabbas ransa abace yake,kila gwaggo ce tadora masa lefi,"yaya ina cikin kaduna yanxu xankaraso nadan fitane,
Yaya sameer yai ajiyar zuciya "to kai sauri ka karaso gidah yanxu dan mutan hadeja kai suke jira xasu juya gida yanxu,
Capt adam yai saurin kada Kansa kamar yaya sameer din nawajen dan sosai yake bashi girmansa dukkoda bawani girmansa yai can ba,"ganinan yaya insha Allahu yanzu xan karaso da yardar Allah ,abasu hakuri..Sannan sukai sallama da juna,
Reverse yai yafigi motar aguje yai gidansu malali ,dayake dama yakusa karasawa tafiyar bayawa,musamman dayaba motar wuta...
Yana xuwa yai parking motar yafito,aikwa sauran abokai dabasu tafiba sukayo kansa akafara gaisawa,Sannan daukar hotuna yabiyo baya,dakyar yasaci jiki yashiga cikin gidah,zaune yasamu gwaggo da yan'uwa birjik a parlor din hira akesha ga abinci nan varieties ajere a kasan carpet da drinks ,gwaggo ma tayi Kyau ba lefi cikin atamfar super sheraton Wanda tayi kyanta dede gwrgwado,suma su surayya sunci ado kamar bikinsu ake sosai sukai shiga cikin wani lace blue and silver,
Bilkisu kanwarsa yar autarsu ita tafara ganinsa tataso tana fadin"yaya ,tundaxu naxo bangankaba barkada rana an wuni lapia?!
Capt yai fada'da murmushinsa ganin bilkisu kanwarsa duk cikin kannensa bawanda yakeso kaman ita,batada hayaniya kuma abin dunia beda metaba,"lapia qalau bilkisu yagida ya ya atiku?!(mijinta)kodayake mungaysa dashi awaje ma,"lapia qlau yaya...
Karasawa yai cikin parlor din inda suka gaysa da yan 'uwa da abokan arziki,sosai sukaita tsokanarsa shide murmushi kawai yake dan Capt adam bade kunya ba,sosai yaxauna suka sha hira da mutan hadeja inda yamasu goma ta arziki lokacin dasuka tashi tafiya,sosai akaci akasha sannan aka watse ,
Bayan magriba aka kawo amarya magajiya gaysuwa gurin uwar miji wato gwaggo, gwaggo tamata fada irin yadda aka gada daga kaka da kakanni,sannan tabata kudi dakuma turamen atamfofi da turaruka,kai tsaye akai convoy a motoci aka nufi gidan amarya magajiya dake unguwar kawo,gidane tanfatsetsen gaske Wanda ya amsa sunansa ,sama da 'kasa dakuna birjik da faluka,harda sashen baki..yan uwa se yaba kyawun gidan suke tareda saka albarka dakuma kawo kazantar daki',
Kodah capt adam yaga anwatse sashen baki yanufa nagidan su yashiga yayo wanka tareda daukar Waya yakira hafsat suka sha hirar soyayyarsu yana cikin wayar surayya tashigo 'kerere ta tsaya akansa,Capt adam yadago kai yakalleta Sannan yacigaba da wayarsa seda aka kusan daukar minti ashirin sannan sukai sallama da hafsat dinsa badan yaso ba yakatse wayan,kotakan ta bebiba yacigaba da harkar gabansa bayan yadakko laptop yana dannawa,surayya tagaji dan kanta sannan tace"kaje gwaggo nanemanka,tajuya tai tafiyarta!
Capt adam yaja tsaki yana karkada kansa,rigarsa daya aje agefe yadauka yazura ajikinsa dan singlet ce jikinsa se dogon wandon rigan tunda yai wanka yake ahaka sunata faman waya da hafsat dinsa,dakin yarufe tareda nufa sashen gwaggo,yana xuwa yai sallama yashiga Ita kadaice a parlor din tanajan tasbaha fuskarnan a murtuke ba'alamar annuri,karasawa yai gabanta yaxauna tareda sunkuyar da Kansa kasa ahankali yake fadin
"Gwaggo barka da dare,
Gwaggo takauda kanta gefe sedata dau lokaci sannan tace"'dan'nan mekakeyi haka bayan kasan kaidin yanxu kanada Iyali yanzu anan garin?!sanin kanka ne layin dagidanka yake babu mutane sosai,gashi hardare yaja haka ashe kana sashen baki kome kake oho,maxa maxa yanxunnan katashi katafi kafin raina yaba'ci..
Capt adam yasake sunkuyar da Kansa yana fadin"shikenan gwaggo bari inje Allah ya huci zuciarki insha Allah haka baxata sake faruwa ba,
Sannan yamike tsaye yana fadin"seda safe gwaggo nina tafi,
"Toh Allah yatashemu lapia,
Fita yai yakoma sashen bakin yai saurin hada kayansa cikin yar karamar trolley din dayaxo da Ita kadunan sannan yahau motarsa yatafi unguwar kawo inda gidan nasa yake,yana tafe yana magana shi kadai harya wuce wani tukubar me nama yai reverse yakoma baya yana fadin"nasan halin kalatacciyar matarnan yanxu inban siya mata namannan ba sarai seta kira gwaggo tafada mata