Showing 63001 words to 66000 words out of 107296 words

Chapter 22 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7698

jay ya tabbar ASHRAF hankalinsa ya kwanta Sannan yamai sallama yatafi gidah,kan cewar se goben Kuma in Allah yayi xasuje,Se ASHRAF yaga yadedeta sannan yatashi yatafi dinning area yaxuba abincinsa yaci tareda korawa da sanyayyan ruwan sanyi daxe sanyaya masa xuciya,









•✨•
69





•SARDAUNA CRESCENT KANO;

"Are you sure abinda yafaru kenan?!"Waliyya ce ke tambayar UMMI AISHA hakan xaune suke dukkansu akan gado tareda plate dake cike da yankakkun fruits da toothpick daxasu dinga ci dasu,

"Allah abinda yafaru kenan,bakiji yadda xuciyana yake hurting ba bestie,gani nake bad boy game kawai xeyi playing akaina ko?!"

"Ba haka bane tawan,nidama nafa'da maki lokacin damukaje flavours da MUHANNAD dinki nake ce maki anya kuwa wannan soyayyar ta ASHRAF da baby Kay ba akwai wani abin a kasa ba kikacemin Wai nacika sa'ido"

"To ke yanzu mekike gani Akan hakan?!"

"Ni anawa hangen nesan bawai son Kai ba senace maki gaskia ASHRAF yana sonki tsakani da Allah,Kuma wani abu dake tsakaninsu da baby Kay keep that aside bamusan manufarsu tayin hakn ba"

"Ni abin ya'dauremin kai,ko kinsan kwanaki nan tashigo tana waya ashe shine yana wani cemata soulmate ita Kuma tana cemasa baby boo dan Allah idan basonta yakeba meyasa xasu dinga yin hakan??"

"To menene aciki dan sunkira junansu hakan,ko kinsan kodan kiji haushi ma ta iya fadin hakan,to tayaya ma kikasan yanace mata hakan?!"

"Yakirasa sunanta setasa wayan a kunnenta nikuma naji sanda yace mata soulmate sa'a handsfree"

"Mtscewww"Waliyya tasaki tsaki hade dasa toothpick taciro gwanda tasa abakinta seda taune tahadiye sannan tacigaba
"To kodan wani manufar tasa yasa yafadi hakan,manufar kowa Bakomai bane face dakon soyayyar dayake maki"

"Wannan arrogant 'din?!"

"Komaya halinsa yake,nikam naruga nagano inda komai yadosa"

"Sekitayi ai danasani ban fadamaki ba naga alama backing 'dinsa kike,abar xancen"

"Gaskiane kinsan Kuma duk inda gaskia take sena fa'deta dama ance ai gaskia 'dacine da ita,anbar xancen Juliet ta romeo idan ta ru'ba maji,ya labarin MUHANNAD shima naga kamar sonki yake"

"Shikenan nikuma naxama ta maxa kowa ni kenan,to bemuyi haka dashi ba,shi wannan aikinsa xebarshi yayi xancen soyayya ne,nanyake wuni kullum anjima ma xakiji anan gidan"

"Ba wani symptoms daya nuna maki?!"

"Ni ina xansani kullum de seya cemin wai Ina saurayinki?!kokuma yace bani labarin saurayinki,kullum de maganar 'dayace,senace masa yananan qalau"

"To kinjiba aikwa shima soyake ya furta maki kenan"

"Hahaha,Allah ya kyauta Toh ,kowane juji da ya yi Kuma se akwaso ace seni"

"Waye jujin da ya yin?!ai duk samarinki babu nabanxa dukkansu responsible mutanene"

"To ai ni baxanyi aure yanzu ba shine kawai,kuma de ya MUHANNAD inde bayau xece UMMI AISHA inasonki ba be ta'ba fa'daba"

"Xe fa'dane lokacine yananan xuwa"

"Mubar xancn asako xancen wani abin Kuma nagaji,yaya danbo kuwa ?!Allah sarki aunty rebecca kotananan kuwa?!"takarashe maganar tana daria,
dahaka suka koma wani sabon shafin hirar ta daban,basu suka kwanta bacci ba se gaf da asubah sunata hira kamar cin 'Kwan makauniya...,
____Washegari da safe bayan su Waliyya da UMMI AISHA sun karya,suntaya an tsaftace gidan,ammi ta aikesu kan suje kasuwar rimi da kurmi su siyo abinda aka manta ha'de da extra packs na snacks Wanda xa'asa a sunan gobe na mjay data haifa 'diyarta mace santaleliya da Ita Kuma mu'ayyad mijin Mjay 'din shida mjay sunyi shawara Kuma sun a minced sun tsaida sunan jariryar da 'Hafsat' sunan hafsat taci matar captain adam inda xa'a dinga ce mata 'nana',



"Yanxu abinda kika fada yasakeki dagaske?amma dr nmandi bekyauta makiba gaskia, nagaya maki ni wallahi bahaka yaminba lokacin danaje"Muna_b 'kawar magajiya itace ke fa'din haka suna magana da magajiyan a 'dakinta,

"Wallahi abinda yafaru kenan,yasakeni Kuma Idan nagama iddata yace intattara inbar masa gidnsa xamana dashi ya 'kare"

"Allah ya kiyaye haka baxata faru bama,sede ku tattara kubar masa gidansa dagake har wadda tasiye zuciyar tasa"

"Oho masa 'canta matse masa nifa nafara gajiya,"

"Hakuri xakicigaba dayi,har mugama abinda xamuyi amma kema da lefinki seda nace maki pills 'dinnan sau 'daya akesha a sati ko sau biyu a wata amma bakijiba kika sashi agaba kikai tasha aigashinan da bakiji bariba aiyanxu kinji ho ho,nande lefin kine 'kawata"

"Nasani ai,amma Kuma hukuncin daya 'dauka Yayi tsauri 'kawata"

"Hakane,nikuwa ya labarin sadeeya da surayya banajin 'duriyarsu"

"'Karshen xuwana kaduna gwaggo kecemin yaya sameer yatattarasu yamayar dasu hadejia suda ya'yansu yabasu kudi su ja jari anhanasu yawo kwata kwata"

"To ai gwara haka"

"Sosai"

"Nace naxo fa da shirinmu kan UMMI AISHA"

"Bar wannan xancen 'kawata nagaji wallahi"

"Sobada kinacikin wannan yanayin xaki fa'di haka?!to wallahi a'a kudina baxasu tafi abanxa da wofi ba,ban 'kiba daga wanann Shikenan baxa'a sake komai ba sefa a karkato maki da hankalin mijinki wurinki"

"Shikenan 'kawata ya abin yake?!"

"akan Wanda yake yawon zuwa gidan nan akansa xa'ayi Kuma cikin abincinsa xa'a xuba saboda haka dole baby kay tashiga cikin mission 'din"

"Kema kinsan ca xatai Ita a'a"

"Kiramin ita"muna_b tafadi hakan tana ware ido,

Magajiya tashiga 'daki takira baby kay data fito tana zum'burar baki kamar shirwa,tanemi waje akan kujera taxauna,

"Gani"tafadi hakan tana hararar muna_b don ta tsani tana bacci atasheta,

"Magana xamuyi dake"

"Ni bacci nake gaskia Kuma ban gama abunaba"

"Yanzu xamu gama ki koma fa"

"Inajinki"tabude baki tana hamma da alama baccin be gama sakintaba,

Nande muna_b taxauna tadinga shararawa baby kay 'karya dukdande ta yadda da abinda xatace mata tayi,hardasu sakin da baffan nata yaima ummanta seda magajiyan tafa'da Kuma bata nuna magajiyan ce me lefi ba ta 'boye maganar pills tace wai asiri hafsat din kewa umman nata,Sannan takawo xancen MUHANNAD 'din ciki dayadda baby Kay xatai da garin maganin,

"Gaskia baxan iyaba"shine abinda baby Kay tace Sannan ta mi'ke tashiga 'daki,


Su UMMI AISHA nadawowa daga kasuwa suka shiga cikin gidah ganin wata ha'daddiyar jeep dasuka gani sunxata yan taron sunane suka fara xuwa dukkoda Se gobe,suna shiga hancinta yafara sha'ko mata dadda'dan kamshin turaren da baxata ta'ba manta kamshin ba Wanda yahanata sukuni tun ranar farko data fara toxali da Wanda yafesashi,dukkoda ita'dinma ma'abociyar turarece wannan kamshin tabbas yafita daban,sallama suka doka cikin parlor 'din itada Waliyya atake kwayar idonta tasauka kan kwayar idon ASHRAF wannan karon ba coffee brown color din idonsa suka xama ba,grey suka koma Yayi tsaf dashi cikin manyan kaya yana taune Pink lips 'dinsa se Mayen kallo yake jefar ta dashi dayake neman tarwatsa mata lissafi,ita kuwa hafsat se hira suke abinsu da jay dama shi akwaishi da hira Idan yasamu waje,

"Har kundawo?!sannunku da xuwa"Hafsat ke fadin haka tana kallonsu Waliyya da UMMI AISHA,

"Mundawo ammi ga kayan can akitchen"Waliyya tafadi hakan,

"Barinje indubako?,gasu ASHRAF nan sunjima anan munata hirarmu dama nace masu yanzu xaku dawo ashe kuwa kuna hanya"Sannan ta mi'ke tashiga kitchen tabasu waje,

Waliyya Ita kadaice tagayda su ASHRAF,Banda UMMI AISHA dake cika tana batsewa,dakyar ta iya gayda jay sannan ta kauda kanta gefe ita adole batasan dashi awajen ba,jay shine yai gyaran murya yafa'di duk yadda komai yake,Sannan ASHRAF yafadi komai yadda yake,Waliyya takalli UMMI AISHA kallon tunin maganar dasukai jiya hakan take,ahankali Waliyya ke fadawa UMMI AISHA;
"Kintuno maganar da mukai jiya gashi hakan take kaman yadda nace"

"No I don't want to remember and I can't remember"UMMI AISHA tace da Waliyya hakan,

ASHRAF yai rau rau da idonsa yana kallon UMMI AISHA datai kasa da idonta don batasan kallon mayun idonsa masu sanya mutum shiga wani hali na daban,har cikin 'kwanyar kanta ta jiyo muryar ASHRAF yana mata magana,Lokaci 'daya yasakko daga 'kasa yasa gwiwoyinsa akasa ahankali yake mata magana;

"Dan Allah Kiyi hakuri UMMI AISHAAA ,banyi hakaba don intoxartaki kodan wani abu Wallahy duk abinda yafaru tskanina da baby Kay duk plan ne ba reality nake hakan ba"yadda yaja aaaa 'din tawani siga setaji duk duniya babu Wanda ya iya kiran sunanta kamar hakan,haka yadinga bata hakuri jay yanasa baki,hakama Waliyya dake gefe itama sa bakitayi suna bawa UMMI AISHA hakuri,adole UMMI AISHA ta hakura tamaida makamen ya'kin amma haryanzu fuskarta a kumbure take,sannan ta mi'ke tashiga da'ki abinta.. ASHRAF yamaida dubansa ga Waliyya dake magana da jay,

"'Sister 'kawarki na bani tough time fa,dontaga inasonta tana gasani son ranta to ni najanye maganar soyayya ko 'kawance ma muyi"yakarashe maganar yana daria hade daxama kan kujera daga dur'kushen dayai,

"Ai a boy and a girl can never be friends,dole se soyayya tashiga tsakaninku amma inka yadda da 'kawancen se muyi registering 'dinka a friends club"

"Wasa nake fa,ita kadaice cikin kundin zuciyata"

"Tohh nidai ince,tunda 'kawata akwai white blood yanzu semu maye wani a gurbinka"

Haka sukaita hirarsu Banda UMMI AISHA datunda tashiga 'daki bata fitoba,Sannan sukai sallama da ammi suka fito parking space xasu tafi,iya Waliyya ce kadai tarakasu sekace itace budurwar,itama jay se rawar jiki yake da'ita da alama shima xeyi register a club dinsu ASHRAF,dede lokacin da xasu shiga mota dede da futowar baby Kay daga apartment 'dinsu,ido taxaro waje tana 'Kara kallonsu sune kokuwa?!"tabbas sune"tabawa xuciyarta amsa,cikin part dinsu takoma da gudu tana xunduma ihu kamar Wanda aka aikowa da sa'kon mutuwa,

"Menene baby Kay?!"muna_b ce ketambayarta hakan itada magajiya dasuka tsaya akanta suna jira tagama kukan tagaya masu menene?!


••✨••

PerfectStrangers#May be a life can change them😊



WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT....,..
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
70

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

Seda baby kay tai kukanta me isarta kafin tada'go idanuwanta dasuka kada sukai jajir kamar jan gauta ta azasu akansu muna_b da magajiya dake faman jiranta tagama kukan tagaya masu menene yasata kuka batajima da futa ba tace zata neighbor 'dinsu wajen 'kawarta?!murya narawa saboda tsabar kukan dataci take fa'din,

"Aunty muna_b ASHRAF naganifa awaje yafuto daga site dinsu UMMI AISHA"takarashe maganar tana goge hawayen daya xubo mata,

"Wanene Kuma ASHRAF?!menene ala'kar ki dashi??"muna_b taxayyano wannan tambayoyi Lokaci daya tana me kallon magajiya dake gefe tana sauraronsu,

"ASHRAF,sau..sau..rayinane Kuma naganshi wurin UMMI AISHA dama tun kwanaki yafara canxamin ashe wurinta xekoma"tafashe da kuka,

Da'di kashe muna_b najin abinda baby Kay tace yanxu dole tayadda da abinda suka ce tayi kenan,muna_b tai shiru tana tunanin me xatacewa baby can dabara ta fa'do mata,tai sauri taiwa magajiya signal da gira sannan tasoma fa'din

"Wannan maganar be kamata ayi ta anan ba mukoma cikin daki se asan abinda xa'ayi akai"

Kamar yadda tace 'din kuwa hakan akai suka koma cikin daki ana tattauna batin yadda xa'ai muna_b tai gyaran murya kmar gaske

"Yanxu de baby Kay idan kinasan komai yadedeta kamar yadda kuke da da ASHRAF dole sekin bamu ha'din kai kinyi abinda mukace kiyi tunda kingade ba xamu ta'ba cutar dake ba kusan ince duk dan saboda ke nema hakan tafaru,amma yanzu idan kika yadda komai yawuce Shikenan fa ko yaya kikace??"

"Aunty to nimexanyi akai kenan?!"

"Kamar yadda nafa'da de xamusan yadda xamuyi MUHANNAD sunan na'cac'can yaron nan ko dayake zuwa kusan kullum?!"

"Ehh sunanshi kenan"magajiya tafadi hakan tana daria ahankali

"Yawwa tohh MUHANNAD 'din xamusan yadda xa'ayi yayi raping UMMI AISHA,inyaso idan hakan tafaru akwai abinda xamuyi tinda bacikin hankalinsa bane xece shi bashi yai hakan ba,Kinga ASHRAF baxe yarda ya aureta ba kenan kafinnan ma magana ta kara'de duniya Kinga sunanta ya'baci kenan,Kinga anyi biyu babu kenan babu MUHANNAD 'din babu ASHRAF,Kinga ASHRAF xedawo wajenki tinda dama nakine tun farko"

"To aunty yaxanyi hakan tafaru wane role xanyi playing??"

"Yawwa 'yar gari yanzu kikayi magana,kinajina yanxu abinda xaki kicire maganar jealously kakki nuna ko sau 'daya a idonki,nuna kaman kin ha'kura dashi,kidinga shiga jikin UMMI AISHA kuxama very close karki ta'ba nuna mata kinajin haushin hakan,sannan kisan yadda xaki ku sha'ku da MUHANNAD 'din tahakane xamu cinma burinmu akansa"

"Wai 'dan'kari ma'kari,yarinyar nan xata iya kuwa?!"cewar magajiya data cire tagumin data xabga

"Haba 'kawata kamar bamu muka haifeta ba,ai abin a jini yake xata iya kinsani nasani"

"Zan iya mana aunty"

"Nasan zaki'iya 'diyar arziki kodan musha biki da ASHRAF,Ita Kuma UMMI AISHA nasan baxe wuce a ha'data da danginsu na hadeja ba,tunda sefa su'din nanwa xe aura yarinyar data ba'ta rayuwarta?!"

"Aunty kikace Kuma MUHANNAD 'din...."bata karasaba muna_b ta amshe

"Ke yarinyace baxaki ganeba kibari komai ya wakana se amaki bayani,ai MUHANNAD 'din akwai abinda xa'ai xece shibashi yai hakn ba,Kinga idon hakan tafaru waye xexo wurinta acikin samarinta?!kowa jabaya xeyi kar ace shine"

"Oh okay nagane"

"Yawwa yanzu kidena kuka kitashi ki wanko fuskarki kije part 'dinsu UMMI AISHAn kuyi hira dasu kar kinuna alama koda a fuska ne,kinuna babu komai cikin ranki sonake su saki jiki dake kafin komai ya wakana"

"Toh aunty baby kay"

tace hakan tana mi'kewa daga kan gadon,
Suma wata hirar suka shiga bayan tafiyar baby din site dinsu UMMI AISHA,se gaf da magriba muna_b tatafi kan cewar xata dawo sati me kamawa ko kafin sati dukde yanda tayiwu afa'dama aranar zata zo don komai ya wakana gaban idonsu,

•LAMIDO CRESCENT;

Kodah ASHRAF yakoma gidah gaba 'daya yakasa samun nutsuwa duk kusurwar daya juya baya ganin komai sai kyakkyawar fuskar UMMI AISHA,fuskarta,shigarta,kyakyawan murmushinta kai komai nata ma burgeshi yake,gashi yakasa bacci gaba 'daya hotan UMMI AISHA yamai kanai kanai azuciya da sauron gab'ban jikinsa,dayaga kwanciyar bata 'kare bace wayarsa yajanyo yanata Allah,Allah yasa begoge number 'din taba begoge taba kuwa gashinan a rubuce 'baro 'baro yarubuta 'mus'ab's cousin'goge sunan yai yana naxarin me zesata mata shikadai kmar zararre se magana yake,

"Soulmate?!no naga baby Kay ma soulmate nace mata even though that was then,how about le boo?!no no too local,baby?!no baby yayi yawa kowa baby sekace doll"can yai shiru yana tunanin mexe mata saving akan sunanta,shi kadai kuma yai murmushi da alama ya samo sunan daxece,

"LIFE PARTNER,yasss life partner yayi sosai saboda ta'can'canta"

saving yai ahakan Sannan yadanna kira yakirata Se addua yake Allah yasa ta'dauka kowa yasamu yayi bacci,sau takwas yana kira ba'adaukaba kmar yai hauka yaji kodayake yayi 'karamin haukan tunda yature cd handles ya'bare akasa duk cikin haushinne,dakyar yai bacci yanayi yana kallon wayar yaga kozata kira back dakyar ya hakura sarai yasan tana sane bata 'daukaba don tabbas lokacin UMMI AISHA hira sukesha da waliyya tasan xa'arina shiyasa tun yamma tamaida wayar tata silent mode,

WASHEGARI;
____ ASHRAF da wuri ya shirya cikin shadda getzner coffee anmata aiki brown yasha takalmi agogo hula duk brown,abin se Wanda yagani,Sannan yafesa turarukansa masu da'din kamshi yafito parlor yana tafe yana shafa chapette balm a pink lips 'dinsa,yayi kyau kamar ba gobe,kan dinning yanufa yana bu'de foodflask 'din cooler 'din Farko tuwane na masara ya lailayu kuwa se 'kyallin mai yake,da sauri yasa hannu yarufe cooler 'din,cooler ta biyu kuwa yana sa hannu yana budewa yai saurin zaro handkerchief yana rufe hancinsa ganin miyar kuka dayai shar da ita se nama dataji tana tashin kamshin tafarnuwa gefe 'daya kuma man shanu ne,dede lokacin da Ayush da mama suka fito kenan da alama fita xasuyi,

"Mama barkada rana" ASHRAF yace da Ita yana rufe cooler 'din sosai,

"Barka kade ASHRAF"

"Ya akai haka mama?!"yace da Ita yaname nuni da coolers 'din

"Kasan jia aka kawomin sabuwar me aiki Wallahy wainace ta share kitchen tayi wanke wanke da sauran aiki,Wai Ita taxata sauran aikin danace har girki nake nufi shine tatashi tai tuwo,amma xeyi amfani ai,kainede don bakacin tuwon nibansan me tuwo yamaka a dunia ba katsaneshi haka,gashi fita xamuyi amma akwai sauran irish potato a freezer ragowan na jiya da soup Kai sauri kai reheating 'dinshi sekaci kafin nasa tagirka maka wani abin tunda kasan ba sani tai ba"

"No it's okay naci acan"

"'Can Ina kenan?!"

"Ba gidan suna xakuba?!"

Mama ta ware ido tanabin ASHRAF da kallo don tunda take arayuwarta bata ta'ba jin ko ganin ASHRAF ya fa'di hakan ba sekuma ta lura da shigarsa da alama dama yanada niyyar xuwa kenan don matuka tayi mamaki weekends ASHRAF bai tashi da wuri,

"Allah dagaske nake mama"yakara fadin hakan a karo na biyu

"First time in history" Ayush tafadi hakan tana daria

"Inna baki mari xakisan first time in history"

"Shikenan muje amma Kai xakayi driving kenan?!"Maman tafa'di hakn

"Ehh xanyi mama"
yafadi hakan atakaice

Hakan kuwa akai har gidansu hafsat yakaisu,acan yaci lapiyayyar jollof rice da soup na cowleg ha'de da sanyayyan kunun aya,duk inda UMMI AISHA tai idonsa nakanta sanye take cikin doguwar rigar codelace blue seta 'daura rawsik baby pink tayi Kyau kamar ba gobe,har akatashi daga suna besamu yayi magana da Ita ba tana sane tagudu bata kosu su ha'da Ido da wannan mayun idanuwannasa,suna yayi armashi mai jego Mjay tayi Kyau abinta hakama baby nana hafsat ansa mata Kaya pink 'yar caras da ita,ansha pics ankuma raba savouniers kamar ba gobe,

•BAYERO UNIVERSITY KANO;

Duk wani gudu da UMMI AISHA takewa ASHRAF sedata hakura,yana ce ya yi ro'kon da magiyar sedata ha'kura tagaji suna magana ba laifi ba kamar da ba,kullum seya tsarar mata sit a hall ko theatre,ko baya subside da course 'din seyaje lectures 'din duk dande yai tozali da sanyin idaniyar tasa,kamar kullum yauma da safe ko abinci bata ciba tai sauri tatafi lectures 'din masscm da sukeyi karfe takwas xuwa goma,taso ta makara da sauri ta karasa cikin class 'din taxauna alokacin malamin yaxo Wanda yake 'daukarsu 'media history' tana zuwa ASHRAF na mata nuni da sit close to him daya aje mata,bata shareshiba wannan karon don tasaba share shin,zamatai tana xaro note 'dinta hade da biro tafara rubuta topic 'din da malamin ya rubuta Akan board wato 'penny press'

"Morning beautiful" UMMI AISHA ta tsinkayo muryar ASHRAF acikin 'kololuwar kanta yasa hannu yana gyara mata note 'dinta daya lankwashe,

"Morning"tace dashi tana janye littafin nata

"How was your night?!"

Ta bu'de baki zatace ya kyaleta kenan muryar lecturer 'din ta tsaida ita

"Check out,both of you,I'm lecturing and you guys are busy making noise,no not in my class"

UMMI AISHA ta'ki tashi kaman ba da Ita yake ba don ba'a ta'ba mata haka ba'a makarantar duk wannan ASHRAF 'dinne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login