Showing 99001 words to 102000 words out of 107296 words

Chapter 34 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7706

sukai taduba kallo d'aya tagano muna_b ce k'awar magajiya,sosai tausayinta yakamata,da magiya da komi na hafsat captain adam ya yadda aka kirawo ambulance tad'au muna_b suka d'au hanyar asibitin koyarwa na aminu Kano wato(Aminu Kano teaching hospital).


Zaune Ummi Aisha take akan kujera sanye cikin sleeveless riga pink,tayi packing gashinta da ribbon blue tanabin tsala tsalan frames d'in da jay yabata da kallo d'ayar ledar kuma kwalayane na pounding cake da kuma wipping cream duk na strawberries, ashraf ne yashigo cikin parlorn da sallamarsa amsawa tai tad'auke kanta,

"Ummi Aisha adam Abdulrasheed"yace da ita yanabinta da kallo don bak'aramin kyau tayi masa ba sekace wata baby doll.

"Na'am Ashraf kabeer kamil"tafad'i hakan taname cigaba da karanta instruction na jikin kwalin cake d'in,

Murmushi yai wanda ke k'ara masa kyau yatashi yadawo gefenta dayake akan kujera me 3 sitter take,ko gezau batai ba tacigaba da aikin gabanta kamar batasan da mutum awajen ba unlike before da kafin yaxo wajen tafara rawar jiki tana bashi hak'uri,

"Ummi Aisha Adam Abdulrasheed lets play a game mana"yace da ita yana bin gashin kanta dake lilo xuwa bayanta da kallo,

"I'm kinda busy may be some other time"tace hakan a tak'aice,

Murmushi yai yana taune pink lips d'insa ganin sabon tsurfar data taso dashi kuma .Donshi xuwa yai da niyar yabata hak'uri seya tarar da wani sabon salon datafito kuma dashi.

"Okay then practice makes perfect say i love you ashraf"

"Lol yau kuma tanan kabiyo kenan kaje kawai da wasu love quotes d'inka ni karatun test ma xanyi pls"

"Ko?to muyi karatun tare mana,inyee kinyi kyau just like elsa ta frozen,i love you"yace hakan tareda d'an matsawa ya bata cheek kiss!

Sa hannu tai tagoge wajen tacigaba da abinda take,

"Su love manya"tace hakan tana k'arkad'a k'afa sekace wanda sukai switching habits d'in juna a moment d'in,

"I love you ,that means I'm not just here for the pretty parts.i'm here no matter what, I had choices but I chose you...and it was always you."yak'arashe maganar tareda mik'ewa yasa hannunsa cikin aljihu yashiga d'akinsa tareda rufo k'ofar.

Siririn tsaki Ummi Aisha tai tanabin k'ofar d'akin da kallo sekuma yabata tausayi can ta girgixa kanta ta had'e rai tafara magana ita kad'ai;

"Ai ba lefina bane,lefinsa ne tun farko bashi yake min haka ba?yanda yaita gasani wlhy nima sena rama,yanxu ma nafara ramawa kam"tafad'i hakan tareda mik'ewa ta d'auki kwalayen cake ta sauka k'asa abinta da alama cake d'in da jay yakawo xatai baking.......!


•✨•

"Wannan shafin nakune y'an ;HOME OF NOVELS,XOXO'S PALACE, TAREDA CUTE XARAH NOVELS 1 DA MJAY NOVELS...DA DUK MA MASOYA MAKARANTA LITTAFIN UMMI AISHA NAGAISHEKU GAISUWA MAI K'IMA.
Team#UATM☘




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:59 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
90....

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

EPISODE FINALE(K'ARSHE)...


"Ummi Aisha!"itace kalmar da bakin muhannad ya sake furtawa.

Ware ido Hajia Sakeena tai tana kallon muhannad jin sunan wadda ya ambata,

"Mafarkinta kayi?!"tace dashi hakan a tak'aice,

Kasa bata amsa yai illa cigaba da fad'in sunan Ummi Aishan dayake tayi kaman zaucacce,dakyar Hajia Sakeena tasamu ta lallab'ashi yai alwala yai sallah yai addua ya kwanta ta masa seda safe takoma d'akinta.

WASHEGARI:

Kwance captain Adam yake akan doguwar kujerar parlorn sa idanuwansa sun kad'a sunyi jajir dasu,daka ganshi kasan besamu wani ishashshen bacci ba hannunshi na dama rik'e da carbi yanaja,k'ara wayarsa tafarayi alamar kira dake shigowa,ganin sunan wanda ke kira yasashi hanxarin d'auka cikeda girmamawa yasa a handsfree saboda ciwon kunnen fungal infection dayake fama dashi yakanyi hakan duk sanda xeyi doguwar amsa waya;

"Assalamu alaykm yaya"

"Wa'alaykm salama Adam"

"Yaya barka da safiya antashi lapia?!"

"Barka kade Adam,lapia qalau Alhamdlh."sekuma yai shiru,

"Yaya kataho ne?!"cewar captain Adam,

"Wallahi Adam bansan ma mexance ba kaga yanxunnan Ambassador Abubkhar yakirani kancewar lalle yanasan aikinnan na maiduguri 'damboa' cikin satinnan kaganni yanxu narasa mexanyi wallahi"yafad'i hakan cikeda rashin jin dad'i

"Yaya ai babu komai anan,abune da anrigada an yishi,ni inaganin kaje maidugurin kawai in kadawo se ai solving wannan issue d'in Allah yatema kemu yasa asamu nasarar aikin Amiin"

"Ameen Adam nagode k'warai,dukma yadda ake ciki xamuyi waya Insha Allahu inyaso senai squeezing time nazo kanon"

"To shikenan Yaya Allah yakymu Amiin"

Sukai sallama kowannensu ya kashe wayar,yana ajiyewa hafsat tashigo cikin parlorn sanye cikin doguwar rigar atamfa da hijabi yawuce gwiwa tayi kyau abinta,a k'asa taxauna gefensa tasa hannu tana masa tausa

"Har kin shirya my Hafsat?!"captain Adam yace hakan yana kallonta cikeda k'auna,

"Na shrya hayatee tun d'axu,harma nad'an yiwa marar lapiar abu me d'an ruwa ruwa,sannan naje wajen magajiya namata maganar xuwa asibitin batace min komai ba na hak'ura nadawo"

Murmushi yai cikeda so da k'aunar Hafsat d'in tasa,

"Dakyau my hafsat,Allah ya maki albarka,nagode da tausa barin watsa ruwa semuje asibitin ko?Allah yasama ta farka Amiin,Ita Kuma kyaleta ai k'awar tace taje daga baya"yace hakan had'e da mik'ewa tsaye donshiga bathroom,

"Amiin hayatee"tafad'i hakan tareda mik'ewa tashiga band'akin don had'a mashi ruwan wankan.

A TAK'AICE;

Captain Adam nagama wankan Hafsat tatemaka masa ya shrya suka tafi asibiti wajen muna_b suna xuwa wani likita dake dubata yayo wajensu yana fad'in;

"Yawwa Alhamdlh gwara da kukazo gatacan tana fad'an wasu maganganu barkatai kode tanada tab'in hankaline?!"

Kallon juna sukai shida Hafsat sannan suka garxaya ciki d'akin da muna_b take se faman haure haure take tana maganganu ciki harda fad'in su sukaiwa hafsat asiri da maganganu de barkatai marassa kan gado,Ita kanta Hafsat sosai maganganun muna_b ke ratsa ta seyanxu tasake tabbatarwa tabbas magajiya itace silar kurciyar da akai mata tashiga dunia,muna_b tabud'e baki xata fara wasu maganganun wani likita yai hanxarin yi mata allurar bacci cikin mintina k'alilan bacci yad'auketa Bawa nurses d'in abincin sukai kancewar idan tatashi su temaka su bata,suka koma gidah kowannensu yana xancen zuci kan abinda muna_b keta fad'a d'axu,
_____Tun sanda romantic moment yashiga tsakanin Ummi Aisha da Ashraf suka fara wasan b'uya a tsakaninsu,tak'i yadda su k'ara xama kodah waje d'aya ne,kullum idan xasu school xata saka hijabinta har k'asa ta gaisheshi daganan magana baxata sake had'a suba se washegari,tun Ashraf naganin kamar hakan having fun ne harya fara ayyanawa axuciarsa lalle Ummi Aisha batasansane shysa take axabtardashi tahanyar k'in kulashi datake don harya d'an rame ba kad'an ba.Kamar kullum sundawo daga makaranta tana xaune a kujerar nesa dashi tasaka wani American film 'never been kissed'tana kalla tayi crossing leg sekace itace mijin,lokaci lokaci takanyi murmushi idan annuno abin daria,duk abinda take Ashraf dake gefe yaxuba mata idanuwa yana kallonta kamar xe cinyeta,wani abin daria akai sosai Ummi Aisha tadinga daria harda hawaye, ahankali Ashraf yadawo inda take yasa hannunsa kan nata yana murxawa ahankali yana kallon kwayar idonta dataki had'a ido dashi cikin wata irin murya yake mata magana;

"The theory of entrainment in physics states that some specific sounds increase the rate of your heartbeat.For me,ummi Aisha ,that specific sounds has always been your laughter"

Zare hannunta tai ahankali tana dubansa kafin daga bisani tace;

"Dan Allah ka k'yaleni pls"

Sake narkar mata da sexy idanuwansa yai yanabinta da kallo

"I don't think you understand how important it is for me to hear the sound of your voice everyday my heart is yours Ummi Aisha I'll never leave you"yak'arashe fad'in hakan tareda mata light kiss akan lips d'inta yahaura sama abinsa.

Days passed;
Abun Ashraf da Ummi Aisha k'ara ci gaba yakeyi saboda Allah yana namiji me lapia hankalinsa akwance meyasa baxe buk'aci matar saba?amma ita sam takasa ganewa,ba komai yasanya ta hakan ba se RAMUWAR GAYYAR datace itama setayi akansa,xaune take akan gado tana karanta wata jarida akan case d'in julian assange na extradition law,Ashraf yaturo k'ofar yashigo se k'amshi yakeyi,murgud'a masa baki Ummi Aisha tai;

"Malam mekazoyi a d'akina?"tace hakan tana masa duban ya akai?

"Nazo ne na karb'i hakk'ina"yace hakan yana nufar inda take,

Matsawa Ummi Aisha tai baya yasake binta har k'arshen gadon suka kai cikin tsiwa tace;

"Ko ka manta abinda yafaru tsakanina da muhannad"

Dafe kansa yai alamun rashin jin dad'in kalmar data fad'a,

"The fucking thought of you with somebody else,I don't like that Ummi Aisha"yace da ita hakan tareda sa hannunsa yana tab'a nude lips d'inta,

Shiru tai daga haka bata sake cewa komai ba,janyota Ashraf yai jikinsa yana shak'ar k'amshin khumran dake tashi daga jikinta,ahankali yasa bakinsa kan nata yana kissing d'inta romantically tareda sa hannunsa d'aya cikin rigarta yana yawo dashi,tahaka yasamu yarabata da rigar jikinta da xafi xafi yafara aika mata da sak'onnin da tunda aka haifeta bata tab'a jin yanayinba sefa a moment d'in,ahankali taxame jikinta daga nasa xata sauka daga gadon yai saurin rik'o hannunta yana girgixa mata kai cikin dakushewar murya yake fad'in;

"I just want you to know that when i picture my self happy it's with you,Ummi Aisha pls lets frgt about the past duk wani abu da yafaru a da mu ajiyeshi a matsayin history bawai don haka ta faru dakeba na tausaya maki, no not at all inasonki ina k'aunarki shiyasa na aureki and you will always be perfect to me nothing will ever change that kigane hakan"

Itade Ummi Aisha batace komai ba sema k'ok'arin k'wace hannunta datake,ganin tana b'ata masa lokaci gashi he's badly in need kawai yajanyota ya'ajiyeta atsakiyar gadon batare dawani b'ata lokaci ba yafara aika mata da sak'onni gadan gadan,ko'ina najikinta babu inda baya kissing ga hannunsa d'aya yana karakaina ajikinta,ta haka yasamu yai fatali da pajamas d'inta yafara neman hanyarsa ta k'asan ta alokacin Ummi Aisha tayi shab'e shab'e da hawaye tana rusar kuka don yad'au lokaci yana wasa da ita,mexe gani abinda yake shirin gani ba hakan bane,axatonsa xesameta amtsayin ba virgin ba seganin hagun yayi,sake dubawa yai dukkoda ba sanin kan abin yai ba amma tabbas Ummi Aisha cikakkiyar budurwa ce wadda namiji be tab'a shigartaba.Fasa abinda yai niyyar yi yai ganin inde yace xeyi xe'iya wahalar da ita don a matse take sosai,rungumeta yai tsam ajikinsa yana maida numfashi yana kuma godiya ga Allah bisaga wannan babban abu da yafaru,ita d'inma maida numfashin take tana kuma mamakin abinda yahanashi aikata abinda yayi niyyar yi,sa harshensa yai kan fuskarta yana lashe hawayen dake gangarowa daga fuskarta ,to meyasa tace wani abu yafaru tsakaninta da muhannad?!ganin ba yanxu yakamata yai mata wannan tambayarba yasashi xameta daga jikinsa ahankali yai addua yatofa mata sannan ya mik'e yafuta bayan yakashe mata fitilun d'akin,d'akinsa ya nufa yai alwala yafara sallolin nafulfuli yana kuma rok'on Allah daya nuna gaskiar yadda al'amarin yake,yana fita Ummi Aisha tamik'e tashiga band'aki tayo wankan tsarki takwanta akan gado cikeda courage d'in lalle lokaci yayi daxata fad'awa Ashraf gaskiar lamari......



"Uhum ina jinka muhannad kasande sarai inada abinyi muba k'ananan yara bane daxaka tara mu anan kayi shiru kana sunkuyar dakai kamar wani sabon ango"mahaifin muhannad shike fad'in hakan ganin yadda muhannad d'in yahad'asu da Allah yanasan magana dasu kuma yai shiru!

"Magana fa mahaifinka yake maka muhannad ko dama bakasan mexaka ce ba?"Hajia Sakeena ke tambayar muhannad hakan dake gefensu a ts'akure.

"Abba akan mafarkin danake kullum ne"muhannad yace hakan with full confidence,

"Se akai yaya da mafarkin da kake?!"

"Abba nasan it's high time dayakamata ace nafad'a maku wannan maganar amma kafin nace komai inaso kuyafemin Wlhy abba ba lefina bane kuma ba lefin yarinya bane nasan ba abinda yashiga tsakaninmu but at least i betrayed her trust"

"Mtscewww"mahaifin Ashraf yaja tsaki had'e da mik'ewa tsaye yana gyara malum malum d'in jikinsa,

"Alhaji Yaya haka?!"cewar Hajia Sakeena

"Sakeenatu meyasa xan tsaya inajin sakarcinsa,koba kiji me yake fad'a bane?!to badaniba idan ke xakiji xaki iya xama kiji inkun gama kidafomin shayin na'a na'a kikawomin parlor na"

"Alhaji baxa'ai haka ba,dan Allah katsaya kaji me xece badan niba don Allah"

Bayadda mahaifin muhannad jinta had'ashi da babban bango haka yaja babbar rigarsa yaxauna yana muxurai,hakan yabaiwa muhannad damar fayyacewa iyayen nasa bindi da wutsiya na abinda yafaru tsakaninsu da Ummi Aisha tunfarkon had'uwarsu tareda d'oriyar ba ahayyacinsa yai hakan ba kuma babu abinda yashiga tsakaninsu sede kokawa dayai doncin galaba akanta amma dukda hakan ba'abinda yashiga tsakaninsu.Cikin kuka yak'arasa fad'in duk mafarkin dayake kwanannan akanta yake yana ganinta tana kuka tana fad'in yarabata da MARTABARTA,yakuma sake rok'on iyayen nasa dasu temaka masa wajen tayashi rok'on gafarar UMMI_A'ISHA,fafur mahaifinsa yak'i yarda,da magiya da komi da suka dinga had'ashi da ita ya hak'ura yashafawa kansa lapia,yakuma yarda xe wuce gaba domin neman yafiyar UMMI_A'ISHA dakuma iyayenta,sannan suka sake jawa muhannad kunne tareda masa fad'a meshiga jiki,shima basu hak'uri yai yakuma yi alk'awarin canxa halayyar sa dukkoda yanada BIYAYYAR IYAYE amma rashin maida hankali wajen neman tsira ga ubangijinsa shike neman jefashi cikin halin MATSALAR RAYUWA...



Washegari;Ranar asabar kenan su Ummi Aisha basuda lectures tana xaune kan dinning table tanashan quaker oats Ashraf yasakko daga sama sanye cikin shigar manyan kaya kansa babu hula yataje sumar nan ta kwanta luf kamar ta jarirai yaja kujera d'aya ta dining d'in yaxauna yana facing d'inta,gaisheshi tai ta kauda kanta gefe tana cigaba da shan oats d'inta

"Ummi Aisha"yakirata cikin husky voice d'insa,

"Na'am"tace hakan tana d'an dubansa ta gefen ido,

"Inaso kigayamin gaskiar al'amarin daya faru tsakaninki da muhannad"yace hakan tareda sa hannu yagyara mata napkin d'in wuyanta,

Shiru tai tana kallon gefen inda yake kamar me tunani,kallonta yake cike da so da shak'uwarta axuciyarsa,

"Please"yace da ita hakan,

Nannauyar ajiyar zuciya tasaki;

"Tsakani da Allah muhannad be rabani da MARTABATA ba,yade yi yunk'urin hakan amma Allah be bashi sa'a ba"

Shiru yai yana kallonta wani b'angare na xuciyarsa na gasgata abinda tace,

"Amma meyasa xuwana na k'arshe gidanku kafin muyi aure kikacemin muhannad yayi raping d'inki?!"

"koda nace maka beyi ba baxaka tab'a yarda ba saboda kowa ya yadda yayimun d'in"

Nande taxauna tabashi labarin komai yadda tafara sanin muhannad sukai sabo haka,dayadda yai yunk'urin raping d'inta da yadda Allah yatemaketa ya k'ubutar da ita daga hannun muhannad d'in tareda d'oriyar Allah yatemaketa period pain take alokacin sekuma mummunar buguwar datai a agararta tafashe sakamakon flower vase daya doka mata,se kuma tabashi labarin video d'innan da batasan wanda yai ba yakaiwa baffansu,jinin period din datake shine yaxuba ya b'ata kan gado,na agararta kuma shine wanda ke tsiyaya yab'ata har k'ofar d'akin hotel d'in saboda yadda tadinga jan k'afar,ta k'arashe da cewar to ganin wannan video d'in da akai dakuma yadda wajen kokawa dashi ya turemata d'ankwali gashinta yatashi sama da yadda rigarta ta tsage sakamakon k'ofa dataja shine kowa ya yarje kan lalle yayi raping d'inta tak'arasa gaya masa tana hawaye.Kyakkyawar runguma ashraf yai mata tareda fad'a mata dad'ad'an kalamai masu dad'i yasa harshensa yana lashe mata hawayen dake xuba daga idanuwanta ,alokacin suka yafi junansu,yakuma ce mata lalle yau xasuje gidah su fad'awa su amminta gaskiyar lamari don wannan ba abinda ya kamata ai shiru bane,Ummi Aisha tanuna ita gaskia abar xancen tunda komai ya wuce dakyar Ashraf yashawo kanta tayadda tareda rad'a mata kyawawan kalamai masu dad'i akunnenta;

"I will always be here for you. I will always listen. I give you till the end of time.With me,you will never be alone,you are the smile to my face and the beat to my heart"yak'arashe maganar yana bata warming kisses akan bakinta...!

Suka kuma tsaida bayan sallar la'asar da yamma amatsayin lokacin daxasuje wajen su amminta sugaya masu abinda ake ciki.




Yaya Sameer na isowa kano kamar yadda yafad'a bayan yaje wajen kwangilar yasauka daga jirgin maiduguri xuwa na kano yabiyo ta gidan captain Adam d'in,tarbar arziki hafsat tayi masa alokacin Adam din yashiga wanka,sund'an tab'a hira kafin Adam d'in yafuto bayan yafuto kuma ta mik'e tashiga kitchen tabasu waje don xantawa shida d'an uwansa,bayan sungaysa ne captain Adam ya dawo k'asa kusada d'an uwan nasa yaxauna yana fad'in;

"Yaya dama hukunci nake son ka yanke,domin banmasan wane mataki yakamata nad'aukaba"yafad'i hakan yana girgixa kansa,

"Ina jinka Adam menene yafaru?!"

"Yaya yaran nan sunfi k'arfina banson ina sukekai tarbiyyar da aka ginata akansu ba,sunsa k'afa sunyi fatali da duk wasu sharudd'a danake gindaya masu"

"To Allah yarufa asiri,wani abin Ummi Aisha tasakeyi??"

"Yaya yanxu kuma ba ita bace dama ance abinda nasama dakai yakeyi shina k'asa dakai xeyi idan yataso"

"Dukma ba wannan ba shin menene yafaru Adam?!"

"Yaya abinda Ummi Aisha tai shi khadija k'anwar ta tai,wanda Ummi Aisha ma iyacewa tsautsayine dakuma sakaci da yadda da sukai da shi yaron dayake xuwa. Wannan kuwa yaya bristol palace wani sabon hotel da aka bud'e a titin farm center nan khadija taje take xubar da mutuncinta har hotel service d'in nacemin itada mijinta sukaxo sukai hiring d'aki na awa biyar,kuma har suka xarta da minti 30 saboda haka dole su k'ara dubu goma 15.atak'aice de yaya seni nine nabiya 15k d'in da akebinsu saboda yaron yagudu ya barta ita kuma sun hanata tafiya kansetayi settling bills d'in kansu tukunna"

"Innalillahi wa'inna ilahirr raji'un"shine abinda Yaya sameer keta maimaitawa,yana dafe da kansa hannu bi bibiyu yana girgixa kansa a wata irin murya me cikeda tausayi yace;

"Yanzu ina ita khadijan?!yaya kukai da ita sanda hakan tafaru?!tukunnama Adam kana ina akai wannan d'anyan aikin?nide iya sanina dakai baka sakaci akan iyalinka"

"Yaya banida tacewa,gaba d'aya narasa mexan yanke wlhy,kasan a ranar ai a kaduna muka wuni da Hafsat har akan hanyar dawowar munema wallahi mukaga wata aminiyar magajiya dake yawon xuwa wajenta yan vigilants grp sunmata dukan kawo wuk'a semu muka kaita asibiti yanzu haka tana b'angaren magajiyan saboda likitoci sunce baxasu iya ba tana hauka sun tattara sun sallamota.To kafin kafin ai haka lokacin da muka dawo daga kadunan ne nashiga b'angaren magajiyan neman khadija kamar kullum inda natarar da ita magajiyan tana bacci da tulin magunguna.."bek'arasaba Yaya sameer ya amsa;

"Batada lapia itama?!"yace hakan yana kallon captain Adam d'in.

"Yaya ina kaika, yaya ace ina cikin gidan nan magajiya batada lapia baxata sanarmin ba?idan ba xaman aure a tsakaninmu ai y'ar uwatace ta jini komade a iddarta take ai lapiarta akaina take tunda xaman idda take,wallahi Yaya magungunane na brain cancer harda wata cuta ni wallahy banma santaba wai Asperger's syndrome boldly gashinan a rubuce kanta ya saisaye babu gashi,nafita xantafi naga mai aikin magajiyan nake tambayarta ina khadija?!tacemin tun safe ta fice daga gidan,yanxu Yaya ashe abinda ke faruwa kenan cikin gidan nan bansaniba,rayuwar da magajiya taxab'ar wa kanta kenan itada y'arta,?yaya atak'aice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login