Showing 60001 words to 63000 words out of 107296 words
aunty dede da second daya ba wai hankalinta ya gushe sam banjiba kuma banganiba,kusan ince tada husuma ne banaso tunda Allah yai hani da ita,amma Wlhy bakya bina bashin rantsuwa maganar nan daxan fada maki babu 'karya cikinta magajiya itace silar komi,dan lokacin da hakan tafaru bayan wasu kwanaki nida ke baffanku yamai damu gidansu aunty kafin al'amura su warware,bayan anyiyyi cigiya babu labari se aka aiko da rashin lapiar innarmu(mahaifiyarta)inda mama tace nakoma gidah nakula da mahifiyar tawa dawowar daban yiba kenan to bayan lokuta sunshu'de danaji babu labarin aunty senasa...."sekuma haule tai shiru tana girgixa kanta,
Damuwa 'karara ta bayyana a fuskar UMMI AISHA murya narawa take fa'din;
"Aunty haule kinsani cikin duhu dan Allah ki 'karasamin kinji"
"Ba wani abun bane UMMI AISHA kawaide ba bayan nakoma gidah shine nai aure kuma mijin dana aura aikin ganshi ma yaxo rannan,almajirine shine yai istikhara inda yaga magajiya itace tai silar barin aunty daga gidan nan,ta hanyar saka mata hauka amma Allah da ikonsa auntyn batai hakan ba setabar gidan de tunaninta ya'dauke,kamar yadda auntyn tafada wanine yaka'deta daga funtua shiya daukama sanadiyar hakanne tunaninta yatafi,se bayan yasa anmata ro'kon Allah ne aka gano kurciya akai mata aka gusar mata da tunaninta,mutumin ma yarasu Allah sarki mutanen kirki bashine auntyn takoma gidansu Hajja barira ba ashe ma gidan abokin baffan kune,to kinji yadda abun yake amma magajiya kam itace ta haddasa komi,Kuma Wallahy idan bata ro'ki gafarar aunty ba Wallahy Allah baxe yafemataba,dande ke yarinyace wasu abun baxeyiwu afada maki bane,danma aunty tanada kaifin addu'oi da abun yata'axxara"
"Allah xesaka mata Insha Allah,kuma aunty taya akai ammi tabar gidannan aranar?!"
"Baxan mantaba nide 'karshen magana ta da ita tacemin,na 'dakko mata jarkar nonon da aka kawo daga kaduna acikin freezer a kitchen"
"Kaduna Kuma?!,lokacin umman baby Kay na kadunan kenan ko tana nan??"
"Tananan lokacin Kuma itace ma taka....."haule bata 'karasaba hafsat tashigo parlor 'din rike da waya a hannunta tana magana,
"Uhm uhm mjay babu ruwana gaskia bari nabawa haulen kuyi magana da Ita,saboda Allah me gidanta naganin mutuncina"Sannan tacire wayar daga kunnenta ta mi'kawa haule,
"gashi Mjay ce xakuyi magana amma babu ruwana ciki"da axama haule takarba wayan tasa a kunnenta inda Mjay kece mata dan Allah koxata samu xuwa ranar asabar?!washegari kenan kan tanaso ta'dan xauna da ita tunda haihuwa xataxo Kuma babu Wanda ze xauna da Ita,tunda girma yaxowa maman,inda haulen ta amsa mata da xata shedawa maigidan nata tukun tinda yatafi tashi(Neman kudi wani garin),hirar da basu 'karasa ba kenan da UMMI AISHA tinda hafsat taxauna awajen se xancen haihuwar mjay din da akeyi,amma duk xancen da ake ba abinda UMMI AISHA ke tunani se maganar da sukayi da haule,
Aranar haule ta kira megidan nata inda ya amsa mata da babu komai taxauna awurin mjay din tunda bayanan Idan yadawo xekira ta tadawo Insha Allahu,kodakuwa yananan baxe iya hanawa ba saboda kunya da Kuma dattako dayake gani na hafsatun captain 'din,
Washegari da safe haule taiwa gidansu mjay asubanci dayake Mjay din 'karfe 10 na safe jirgin su xe sauka daga capetown xuwa nigeria kano state,maganar da basu samu damar 'karasata ba kenan amma UMMI AISHA ta ro'ki haulen kan ko yaushe suka ha'du dan Allah ta 'karasa mata,
_A ranar ne Kuma da misalin 'karfe tara na safe magajiya tatashi da matsanancin zazza'bi ko Ina najikinta ciwo yake se mur'kususu take tana juyin azaba akan gado,adole captain adam yatasata agaba sukaje asibiti,tashin farko dr NAUFAAL yai gwaje gwajensa inda yagano ai ancire mata mahaifarta,
"Mahaifarta fa kace?!"captain adam yafadi hakan yana me kallon magajiyan kallon tuhuma,
"Of course check for yourself"dr NAUFAAL din yafadi haka yana scrolling din scanner din dake scanning cikin magajiyan,
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"captain adam yakarashe maganar yana dafe kansa,itade magajiya dake gefe se tsuru tsuru take da ido alamar rashin gaskia,
"Kana nufin baka saniba?!"dr NAUFAAL Yatambayeshi yana me mamakin re action din captain adam 'din daya canxa Lokaci 'daya dama ana gane hakan ta inda kafcececiyar jijiya ke fitowa tundaga tsakiyar Kansa xuwa goshinsa Sannan idanuwansa sun ka'da sunyi jajir to inde hakan tafaru lalle tabbas ran captain adam yakai matuka wajen ba'ci......
•✨•
67
Da'kyar captain adam yaseseta kansa sannan yagyra xamansa kan kujerar dayake ka'kalo fake murmushi yai yanakallon dr NAUFAAL 'din Sannan yafara fadin;
"Bawai bansaniba,kagane shi...shi likitan tun a kaduna ne ai seda nace masa kada yacire mata mahaifa,yamata de wankin cikin,to naje abuja inaga da ciwon yataso shine takoma seya rufeta yacire mata mahaifartata"
yakarashe maganar yana girgixa kansa gefe daya Kuma yana ro'kon Allah kanya yafe masa abisa xancen dayai yanxu Yayi hakanne saboda shi mutum ne Wanda baisan wani yaji sirrin iyalinsa koda kuwa abun da sukayi ba hakan yakeba yagwanmace yamasu hukunci dagashi sesu,shiyasa yacewa dr NAUFAAL din hakan amma azahirin gaskia besan abinda magajiya taiba shibe masan ancire mata mahaifa abinda inxata fita unguwa bekai matsayin tatambayeshi ba sede yadawo yaga batanan koya tarar sundawo atare,badan tanacin arzikin gwaggo ba tatuni yarabu da ita,amma datayi lefi xatai saurin gayawa gwaggon Ita kuma xata hanashi abinda yai niyya,shikuma seya hakura amma tabbas hakuri yake da magajiyan amma yanzu kam takaishi 'karshen ma'kura dole ya'dau tsats'tsauron mataki akanta,
"Ayyah ai wasu doctors 'din basuda Imani,tohh Allah yasawwake,se akiyaye nan gaba"yace da captain adam din yanamewa magajiya kallon gar'gadi..
"Insha Allahu doctor,nagode"takarashe maganar tana kallon captain adam da kotakanta bebiba yadda Kasan ba'a haliccetaba awurin,
Bayan sungama abinda sukeyi,sallama yaiwa dr din Sannan suka fito waje suka shiga mota,gaban magajiya se dukan uku yake,musanman datasan yau kashinta ya bushe,dama hausawa sukace rana dubu ta 'barawa rana daya tak tame gidah,yaukam magajiya xata gane kurenta,se ayyana abinda xe mata take,addu'oi kuwa seyau tasan anayinsu se xabga addua take ciki harda taban da'ki kuwa,suna xuwa gidah yai parking yashiga ciki se binsa take a baya ahankali Kuma dama sati yaxagayo a 'bangarenta yake,suna shiga yashiga bandaki abinsa kotakanta bebiba yayo wankansa,yahada cornflakes yasha,sannan yakoma parlor yaxauna yana kallon channel 'din aljazeera ana news nakan yadda ake kashe musulmai yan'kasar Aleppo(pray for Aleppo pls)a 'darare taxo wucewa yai sauri yakirata
"Zo nan ke"yakira magajiyan cikin fushi da alama yau ran ba ha'dejan a bace yake,
Sumsum ta isa inda yake ta tsugunna,
"Wanene yabaki izinin xuwa acire maki mahaifa,Meyasa?!akan wane dalilin?!yaushe ne?!a'inane?!,kibani amsar tambayoyina yanzunnan dan insan wane hukunci xan 'dauka akanki,mutuniyar banxa wadda batasan ciwon kanta ba,Idan kika gayamin 'karya kikuka da kanki marar mutunci wadda batai halin gadon gidansu ba"yakarashe maganar yana huci,
Yawun tsoro magajiya tahadiye Wanda yatokare awuyanta yatsaya mata,idanuwanta suka kawo ruwa,dakyar ta iya magana murya narawa tafara fa'din;
"Kwanakin bayane lokacin Muna kaduna,naje asibitin saboda banajin da'din jikina??"
"Ina jinki se akai yaya?!kinga tundaga nan lefin ki yafara zuwa wani wurin batare da izinin mijinkiba kokinsan duk matar data fita batare da izinin mijinta ba hartaje tadawo a tsinuwar mala'ikun Allah take?!kamar bakije Islamiyya ba kodayake I doubt so,dakinje xakiji wata 'kissar matar da aka aiko mahaifinta dayai silar ta xuwa dunia bashida lapia dataje wajensa,matar nan batajeba saboda bata tambayi mijinta ba Kuma yafita karshede harseda mahaifin nan nata yamutu aranar batajeba seda mijinnnata yadawo take fada masa yace aida tasani taje tace a'a aibata tambayeshi ba tukun,amma ke Ina nidin wa xaki tambayeni unguwa aiban isaba,cigaba Ina jinki"yakarashe maganar yana 'tsareta da ido,
"To shine yace mahaifata tayi damage dole sede acireta"
"Me kikai da har mahaifar ki tai damage?!pills kikesha nasani ai ko kinxata bansaniba?!,a kadunan inbaki mantaba har'daukeshi nai naboye ranar nashigo daki bayan nadauke kiketa neman abu duk kin hau'tsana dakin nace mekike nema?!kikai 'Karya kikace medicated glass dinki kike nema,to ai Gashinan shan pills yamaki rana anrabaki da mahaifar ki"yakarashe maganarsa yaname karo volume din tv,
"Kayi hakuri dan Allah"
"Ina ruwana ni?!menene nawa aciki,ni aka cirewa?!kanki kikayiwa ai baniba,Toh ki bude kunnuwanki kiji abinda xance maki nayanke shawara Kuma Wallahy baxan fasaba badan albarkacin gwaggo ba datuni nada'de da rabuwa dake aikin sani,yanxu de kam kinkaini bango nasakeki saki..."
Dasauri magajiya ta rike hannun babbar rigarsa tana girgixa kanta tana hawaye murya narawa take ro'konsa
"Dan Allah yaya adam kayi hakuri Wallahy baxan sakeba natuba kamin gafara"
Wani ma'ko'kon bakin ciki yatsaya wa captain adam wannan shine adakeka Kuma ahanaka kuka,hannu yadaga da niyyar marinta sekuma yatuna babu kyau,hannun babbar rigarsa yadaga kamar yadda hadisi yakawo yadaddaketa dashi,Sannan ya mike tsaye yafara fadin;
"Nasakeki saki 'daya kixauna kigama iddarki anan kamar yadda musulunci yace Sannan kikoma gidanku xamana dake ya'kare hakanma kinci sa'ar 'diyar dake tsakaninmu badan Khadija ba da Wallahy kinda'deda barin gidannan"Sannan yafice ko takanta bebiba yanajiyo ta tana xunduma ihu girgixa Kansa yai alamar takaici sannan yashiga mota yai fitarsa..
Yana fita tajanyo waya tana tsiyayar hawaye takira muna_b tasheda mata abinda akeciki,inda tace mata tananan xuwa Kuma xataxo da dadda'dan labari akansu UMMI AISHA kamar yadda tace a baya lokacin yaxo kenan,
BAYAN SATI BIYU;
Abubuwa da dama sun faru ciki harda haihuwar da Mjay tai tasamu 'ya mace Wanda satin sama xa'ai suna,shirye shiryen jarabawa su UMMI AISHA suke shiysa kwata kwata batabi takan 'karshen xancen su da haule ba,Wanda ta'ajiye hakan se ranar suna inda rai da lapia,
Ta 'bangaren ASHRAF kuwa abubuwa sunyi masa xafi ciki harda rashin fa'dawa UMMI AISHA abinda ke cikin xuciyarsa dabayyi hakan ba,yayi meyiwuwa yafara yakice baby kay daga jikinsa a hankali tayadda abin baxeyi mata ciwo ba,shima ARFAAN yanxu yayi 'ko'karin cire UMMI AISHA daga xuciyarsa ashe tausayinta ne a xuciyarsa yayi yawa harya tsaida hakan amatsayin ko soyayya ce,xargin dayakewa MUS'AB kosuna soyayya da UMMI AISHA Ashe ba hakan take ba tsantsar sha'kuwa ce kawai tsakaninta da Mus'ab din da haryake ganin ko soyayyace...
•BAYERO UNIVERSITY KANO;
(SOCIOLOGY DEPT)
Da sauri driver 'dinsu ya ajiyeta a kofar dept 'din kasancewar UMMI AISHA ce kadai ke subside da course din Ita baby Kay mass communication tadauka,tana xuwa tai sauri tashiga cikin hall din saboda takusa makara,kasancewar saura Kwana biyu sunan mjay se shrye shrye ake jiyan batai bacci da wuri ba shysa tatashi late,tana shiga da ASHRAF idonta yafara tozali sosai ta lura yacanxa halinsa yanzu kullum yana rigata xuwa ga maida hankali dayakeyi dukkoda yanada 'ko'kari sosai,ba lefi Kuma yana updating notes 'dinsa,'dauke kai tayi tashiga taxauna a nesa dashi,gaba daya yaxuba mata ido bayako 'kiftawa,
Basu suka tashi ba seda akai 4-6 da sauri UMMI AISHA tafara hada littattafanta tasasu cikin jaka,sedata gama tsaf sannan takira driver dinsu yace mata yanakan hanya,da sauri tagyara xaman hijabinta tai hanyar futa ganin daga Ita se ASHRAF,a sukwane yai saurin rufe 'kofar theatre yanabinta da kallo,
"Meye haka?!"tace dashi tana binsa da kallon tuhuma,
Bebata amsa ba se sakala hannuwa dayai yatokareta ajikin bango yatsura mata ido yana taune pink lips 'dinsa,rasa yadda xatai tayi yahana fita,gashi yatsura mata Ido takasa jure salonsa adole tai kasa da kanta,murya 'kasa 'kasa yafara mata magana,
"When you know that someone in this world is thinking about you and wants to be with you and thinks the world of you and makes you fall in love with him over and over again"sekuma yai shiru sanadiyar mutsu mutsu da UMMI AISHA keyi takwaci kanta xata gudu yai saurin sa hannu ya ri'ko hannunta ahankali yake mata magana,
"Baxaki tafi ba sena gama,because you know that there is always that one person who will never leave your side and that person to you is ASHRAF KABEER KAMILU,
UMMI AISHA ta ware ido tana binsa da kallo,a hankali take girgixa kanta tana hawaye,murya narawa take magana da batasan ma tafa'daba
"Bad boy game xakai playing akaina?!"sekuma tai saurin rufe bakinta da alamaa batasan tafadi hakan ba,
•✨•
Gaisuwa mai tarin yawa gareku masoya littafin UMMI AISHA,a 'karamin hakuri pls...!
WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:58 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•
(THE MAGNIFICENT)
68
©®MISS XOXO
DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼
nanahafsat.wordpress.com
•✨•✨•✨•✨•✨•
Girgixa mata kai ASHRAF yai alamar abinda tafada ba hakan yakeba,dakyar ya iya fadin;
"Ba haka bane UMMI AISHA Wallahy kakki kawo hakan a xuciyarki,ke kadai ce acikin zuciyata,walla....."
Bekarasa ba UMMI AISHA tai saurin sunkuyawa ta 'kasa tafice da gudu tana hawaye,da sauri ASHRAF yabi bayanta yana kiranta
"UMMI AISHA,UMMI AISHA"amma Ina driver dinta yaxo a lokacin tai saurin bu'de murfin mota tashiga ta kulle,driver 'din yaja motar,she was panting and out of breath data tuno kalaman ASHRAF,kwata kwata takasa yadda dashi ta tsaida hakan ama'tsayin yaudara dakuma cin amana daxewa 'kanwarta wato baby Kay,
Kodah takoma gidama dakyar ta'iya cin abinci,dayake gidan cike yake da yan uwa anata hidimar shirya abinda xa'ayi ranar asabar sunan Mjay kenan,bayan tayo wankane taxura sau'kakkiyar doguwar rigarta marar nauyi tahau kan gadonta ta kwanta dayake ba sallah take ba,wayarta ta 'dakko ganin tunanin datake ya'kici ya'ki cinyewa,yasa tashiga tafara buga game din candy crush nanma duk a banxa bata denaba,tajanyo system dinta tafara ganin animation film din moana,nanma to no avail,hakura tai tadanna number aminiyarta wato Waliyya takirata,Sannan tasa a handsfree ganin kanta ciwo yake mata,ringing biyu Waliyya ta'dauka;
"Slm alykm bestie boo"UMMI AISHA tace da Waliyya,
"Wa'alykm salam,tawan yagari yakomi?!inataso nakiraki kin rigani"
"Dama kullum ni nake kiranki bestie ai yanzu kinyi dumping 'dina a dustbin kinsamu ha'dad'dun 'kawaye 'yan old site"
"Allah yakiyaye nai dumping my other half,ai ke tadabance tawan,wallahi inataso na kiraki naje kaduna fa amma yau xandawo Insha Allah yanxu haka ha'da shirgi na nake dama takalmana naje 'dakkowa"
"Kede fa'di gaskia autar mama,kice de kinyi missing mama xakije kiganta kidawo,ataho mana da tsarabar kd"
"Hahah,Allah shirgi na natafi kwasowa dama hakan kuma,Banda abinki ta'ina naxama autar nime 'kanne fal?!,Insha Allah xantaho maki da tsaraba karki damu ban da'de daga dawowa daga kasuwa ba kuwa"
"Kosu nawane kece yar auta tinda keka 'daice mace,Yawwa bestie godia nake xanxo na karba"
"Kinban daria tawan,ai xanxo gidan nakuma yaushe ne sunan aunty mjay ne?!"
"Jibi ne fa"
"Yawwa Allah yakymu xanxo ai Insha Allah,Ina ya MUHANNAD"
"Yummytreeats xakice,bahaka kika samaiba?!yananan qalau daxunnan muka gama waya dashi,dan Allah kizo yau bestie akwai maganar daxamuyi dake pls"
"Kibari jibin mana tawan,ko serous issue ne,'dn bani hint mana"
"Nide kixo kawai base kitafi jibin bama dan Allah bayan angama sunan seki tafi"
"Ban fa'dawa aunty ba('kanwar mahaifiyarta datake wajenta take karatu)
"Ai komai yaxo da sauki Aunty ta wajenace,xankirata"
"Shikenan tawan kirata kiji,karna cinye maki credits duk yadda kukai seki fa'damin"
"To shikenan bestie se nakira,barin kirata naji"
Sannan sukai sallama da juna inda UMMI AISHA tai saurin kiran auntyn waliyyan wadda take wurinta take karatu,babu wani bata Lokaci tafada mata yadda sukai da waliyyan inda auntyn tace babu komai Allah yakymu jibin tunda itama xataje sunan,dayake aminan junane kaf dangin junansu babu Wanda besan amintar UMMI AISHA da waliyyan ba sunxamto yan uwa tamkar jini da tsoka,(ya Allah kabarmu da masu sonmu ameen)
•LAMIDO CRESENT KANO;
ASHRAF dakyar ya iya driving yakai kansa gidah gaba daya yarasa meyake masa da'di a duniya,jin abinda UMMI AISHA tafa'da ahankali Yamaimaita abinda ta fada yana dafe da Kansa
"Bad boy game xakai playing akaina,ohh bullshit"yafadi hakan yana naushin steering motar tasa daya kasa fitowa daga ciki dukkoda yashigo har cikin parking space din,semagana yake shi ka'dai kamar mahaukaci,
"Me ta'dauka kenan?!kodan taga nayi pretending akan sister 'dinta,amma ai ba idea na bace,Meyasa take kuka does that meant....no no bahaka bane,duk lefin jay ne,I'm going to kill you jay"
yakarashe fadin hakan tareda fitowa daga motar ko rufeta baiba yashiga cikin gidah,Bala da sameer masu gadi dake gefe suka kalli juna,Bala ya mi'ke xe rufe motar,sameer yai saurin dakatar dashi yana fa'din;
"Inso Kuma kake karasa aikinka Kuma toh?!kobaka lura da Wanda yafito daga ciki bane?!"
"Naxata hakan yana nufin..."
"Nufin me?!rufawa kanka asiri kaji, ASHRAF nefa,yanzu kaje karufe wallahi baka bina bashin rantsuwa shan jar miyarka agidannan ta'kare se karkara kuma"
"Hakane Kuma,Toh Allah yarufa asiri ameen"
"Ameen,xomu shiga daga ciki muyi kamar ma bamu saniba"tashi sukai suka shige cikin 'dakin gadinsu dan kaf gidan yadda ake tsoran ASHRAF ko mai gidan ba'a shakkarsa haka,
ASHRAF nashiga cikin gidah kansa tsaye yai hanyar part 'dinsa,mama tahangoshi tai saurin kiransa ganin beci abincin safe ba gana rana ta ajiye masa Kuma taga alamar baci xeyiba
"ASHRAF"takirashi tana me 'dan daga murya,ganin takirashi yasashi dawowa yaxo inda take
"Gani mama"
"Nace abinci bakaci na safe ba ga na rana nan anyi an ajiye maka ko sekayi wanka xakaci?!"tafadi hakan tana kallonsa,
"Mama a'koshe nake"yace da Ita yana kauda kansa dan bayaso tagano tsantsar tashin hankalin dayake ciki,
"Shi kenan anjima kaci,jameelu(jay)ma yana ciki yaxo tun safe wallahi dashi sukaje banki ma suka ciro sa'kon da abbanku yaturo"takarashe maganar tana maida kallonta ga tv,don tagano tsantsar damuwa cikin idonsa,
"Toh"kawai ASHRAF yace Sannan yanufi sashensa yana shiga yatura kofar da 'karfi kwance jay yake male male akan gadon ASHRAF yana bacci abinsa,hannu ASHRAF yasa ya'dumamawa jay dundu abaya,da sauri jay yamike yana Shafa bayansa yana bin 'dakin da kallo ko gamo yai da aljanu suka sakarmai wawan dundu haka,
"Meye haka?!"jay yafadi hakan yana hararar ASHRAF dashi dinma hararsa yake,
"Screw you jay,you mess everything,?!"
"Relax relax dude,meya faru?!"
"UMMI AISHA nayi yadda xan iya a school yau a sociology lectures nai trapping dinta jikin bango nafada mata abinda ke cikin xuciana Wanda Wallahy nafi kwana nawa ina haddace sweet words dinnan just for her,amma Kasan me tace??"
"A'a"
"Wai bad boy game xanyi playing akanta,kenan gani take 'karya nake mata,da sister 'dnta nake soyayya,jay it's all ur fault you messed everything up,I'm going to kill you"yakarashe maganar yana jefa masa pillow,
"But nibanga abin damuwa ana ba dude,tunda harta buda baki tafa'da haka ai inaga itama tana sonka"
"Abinda yake damuna yanxu shine baxata yarda tai accepting 'dina ba shine kawai tunda Ita gani take har yanxu akwai abinda ke tsakanina da wannan sister 'din nata"
"Allah yakymu gobe muje gidan nixan fa'di laifi nane xan wankeka dude"
"U promise??"
"Insha Allah xanyi hakan"
"Ai dole kayima"
Da hakade abokan sukaita hirar yadda xasuyi goben insunje,Sannan suka shiga wata hirar davan,seda