Showing 78001 words to 81000 words out of 107296 words

Chapter 27 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7715

dan anko semunyishi kala kala senayi 'kara'i xan ajiye nana inkwaso shoki"

Hafsat da Ummi Aisha suka dinga daria ganin yadda Mjay tai da hannu xata kwaso shokin,

"Ai banajin xa'ai wani bidi'a daga 'daurin aure se wuni"

Mjay ta ware ido,
"Haba Yaya hafsat,sekace bikin baxawara yo ko bikin baxawara aiba'ayi haka ba ballantana,yaxa'ai bikin fari kuma babbar 'ya acikin gidan kice baxa'ai wani shagalin biki ba to kwa inde lami xakuyi baxanxo ba count me out"takarashe maganar tana girgixa kanta

"Bikin 'yar kune Kuyi abinda kukaga dama mjay nina isa nahana?!"tafa'di hakan tana daria,

"Yawwa yanxu naji xance ai duk wani ha'dad'dan event da akeyi abikin 'yangayu muma semunyi bikin first niece 'din nawa,tundaga kan bridal tea party har cocktail dinner semunyi da izinin Allah"

"To Allah yakaymu darai da lapia"

"Ameen"

"Kuma su magajiya sun sani?!"

"Ai ba sarasa ji ba ko?!"

"To Allah yashiga tsakanin nagari da mugu"

"Amiin de"

Hira suka shiga yi ta yan uwa suna Kuma bawa Ummi Aisha motherly advice tana 'dauka,



"Ummah wai magungunan me kike tashane?!"cewar baby kay

"Nace maki banajin da'dine"magajiya tafadi hakan tana share gumin dayake tsattsagowa daga kanta,

"Gumi fa kike ummah ga Kuma ac tanayi"

"Dan Allah khadija ki kyaleni kaina ciwo yake"

Hannu baby Kay tasa tadauki ledar maganin me tambarin well care pharmacy,ware Ido baby Kay tayi ganin magungunan dakuma abinda suka 'kunsa da sauri magajiya ta wafce ledar amma ina baby Kay tagama gani,

"Brain cancer ummah"baby Kay tafadi hakan tana rufe baki,

"Eh itace dani khadija nima se shekaran jiya nakeji awajen likita amma dan Allah karki fadawa baffanku"takarashe maganar tana rufe san'kwan kanta da dankwalinta,

"Dole naje asibiti ayimin checkup nasani ko nima nayi inheriting daga gurinki"

"Guduna kike khadija?!"tafadi hakan tana ware Ido

"Ba wani gudunki ai gaskiyace ummah dole naje nai confirming"tana rufe baki kenan captain adam yai sallama yashigo ciki dayake kullum yana shiga daman yabasu ku'din cefane kamar yadda aka fada cewar inde mace xatai iddah gidan mijinta to cinta,shanta yarataya awuyan mijin har iddarta ta 'kare,bayan sungaysa ne captain adam ke kallon khadija yana tambayarta;

"Akwai abinda kuke bu'kata ne?!"

"Akwai abinci baffa sede handouts ce tafito na wannan week 'din shine nakeson insiya"takarashe maganar kamar gaske bayan babu wani handouts ku'di de kawai takeso,

"Nawane??"

"Sunada yawa Kuma kowannesu daga 500 yake kamawa sauran manyan kwara uku Kuma dubu 'dai 'dai ne"

Ciro ku'di yai da yawa xasi dubu goma ya mi'ka mata,godia tai sannan yai hanyar 'kofa xefuta sekuma yadawo yana kallon gefen da magajiya take,

"Ankawo ku'din Ummi Aisha 'daxu seku sanyata cikin addua"Sannan yasakai yafice

"To"kawai magajiya tace atakaice,

"Ummah kinji meyace?!"

"Naji kila wani 'dan abokin nasa ne kowani a hadejia suka hadashi da Ita"takarashe maganar irin ko ajikin nan nata

"May be"baby Kay tace hakan sannan ta mi'ke tashiga cikin 'daki..dan duk axatonsu wani ne davan basu ta'ba kawowa ashraf bane,

Ta 'bangaren ashraf kuwa Mama ce tasashi agaba kanlalle yakira Ummi Aisha yatambayi size 'dinta na Kaya da takalmi da inner wears tunda lokaci akure yake gwara aikomai agama,gashi ba waya suke ba rasa yadda xeyi yayi adole yashiga 'daki maman sunata tsokanrsa shikwa shiga 'dakin dayai akan danbada Ita xeyi wayar bane shiysa,ringing biyu waliya ta'dauka dayake Ummi Aisha Tafada mata komai,nan yatambayeta komai tace xata mashi text suna gama wayar kuwa ba'ajimaba text dinta yashigo harma da abinda yamanta dukta rubuto harda favourite colors 'din Ummi Aisha da irin kayan datakeso kaf waliyya sedatamai text 'dinsu,








•✨•
80






Kafin sati biyu tacika gidansu ashraf sun ha'da lefe yan gaske babbar yayarsu ashraf 'din itada hajia aysha su suka tafi dubai suka ha'do Kayan lefen babu ce kawai babu aciki akwatuna guda talatin da takwas(38) yan gaske customized akayosu daga designer company 'din dkny(donna Karan new york)mama takira Hafsat tace mata xasu kawo lefe ranar asabar nanda kwana uku kenan,atake a gurin Hafsat takira yan uwa da abokanan arziki harda ma'kota tashisshiga Tafada masu da kanta,rankataf 'yan uwansu na uwa da na uba sedata fadawa both site,har yan borno sedata fadawa dayake asalin mahaifiyarta kanurin yerwa ne,yan uwan mahaifinta kuma asalinsu 'yan yola ne fulanin yola shysa hafsatun take Kama da jinsin larabawa saboda ruwa biyu ta ha'da,kaf yan hadejia duksunji su sadeeya da safeeya duk xasuxo har gwaggo data tsufa tukuf itama tace da'ita xa'ayi,

Ranar asabar 'karfe 3;30 shine lokacin da aka saka xa'a karbi lefin gidan yacika ma'kil babu masaka tsinke,kowa yanaso yakashe tsutsar idonsa yakuma sanya albarka ga tilon 'diyar hafsatun,muna_b ma taxo amma su 'yan ganin 'kwa'kwaf ne se tuntsururun dariya suke aganinsu lefan jigari jigari xa'ayo mata irin ha'din 'dambatta suke fatan gani,sosai akai ordering abinci da snacks agurin meena,da leda da akayota musanman idan mutane xasu tafi se'abasu cike take da Kayan 'kwalam da ma'kulashe,,Ummi Aisha da sauran 'kawayenta na part 'din baffansu itakam gatanan gatananne don haryanxu ashraf be kirataba tayi mamaki kwarai dataji bestienta tace Ita yanakiranta,bu'dewar gate 'din gidanne yatabbatarwa Ummi Aisha da 'kawayenta 'yan kawo lefi sunxo,aguje suka fice suka barta ganin haka yasa tatashi tashiga ban'daki tadauro alwala tafara sallar godia ga ubangiji da ya azurtata da wannan babbar baiwa yakumasa takeda rabon aure a doron duniya....
_____Motoci ne da suka amsa sunan motoci sukai ta shigowa kala kala wasuma basu samu wajen parking ba dukkoda katon parking space din dake gidan wasu motocin awaje aka barsu,kayan su shinkafa da su masara buhu buhu akaita shigowa dasu harda Kayan tea cartons cartons da carpets kwara uku manya sekuma akwatuna suka biyo baya haka aka dinga shigowa dasu kala kala pink,amber orange dakuma purple,red sauran ba'ka'kene har guda talatin da takwas,kallo seya koma kan akwatunan da mutanen dake shigo dasu,gasu 'yan gayu,magajiya da muna_b da baby Kay xuba na mujiya sukai suna kallo baki bu'de hassada ta nuna 'karara a fuskarsu kowa yagane ba'kin ciki suke,bayan anyi addua aka fara bu'de akawatuna kamar yadda al'ada ta tanadar,aunty fareelah auntyn ashraf itace takalli akwatunan kamar an manto wani abu waigawa tai tana kallon ayush 'kanwar ashraf,

"Ina basket 'din yake?!"

"Laa yana motar jay bari na 'dakko"tafadi hakan tana mikewa,suka fita itada wata kansu 'daya

Ba'ajimaba suka shigo da katon basket 'katoton gaske dakyar suka ajiye suna maida numfashi cike yake da sacks kanana na henna/lalle/nalle da goro da alawoyi da chewing gums kwali kwali harda sabulai kala kala da slippers dayawa dakuma perfumes da incense(turaren wuta)da humra fal cikin basket 'din se 'kamshi ke tashi,se kallo Kuma yakoma kan basket din da aka ajiye agefe,sosai aka shiga ciro Kayan akwatin 'daya bayan 'daya kamar yadda 'yan sa'ido suke,kowa idonsa yayo waje don basu ta'ba tsammanin hakan ba,sosai baby Kay dasu magajiya sunyi mamakin ganin lefen wani babban tashin hankalin Kuma ashraf ne mijin ashe abinda sukai yatashi abanxa kenan?! akwatin gold ma daban yake 'dan babban kit dashi design har uku da dubai,Saudi dakuma english gold harda awawwaraye daban suma dakuma zobuna,banda fashions kala kala 'yan gaske kowa na gurin was deeply suprised ganin kayan, komi naciki sabon fitowa ne na watan Kuma yawanci ma customized ne.

Laces ma abin kallo ne Kaya de kam baxasu 'kirguba,takalma da jakankuna kaf designers ne daga su dkny,yvsl,giogio armani harda designer dinsu kardashians wanda bakasafai ake sakosuba sefa ya'yan who is who.Da mayafai kala kala harda design 'din basma k,turarukama ba'a magana,na 'karkare maku xance de lefen Ummi Aisha was beyond your expectations duk wani yadda xaka kawo lefen azuciyarka to yawuce haka,ku'din 'dinki ma abin kallo ne to cut it shot lefen THE MAGNIFICENT yayi babu 'karya ko hasidin iza hasada baxe kusheba babu itace kawai babu aciki,bayan angama kalla tsaf aunty fareelah tajanyo babban basket 'din dakyar ta ajiye atsakiyar parlorn,

"munji ance rabin amaryarmu kanurin borno ce kanurin ma Kuma yerwa ko?!"

Nanfa kanuri's dangin hafsat na uwa suka fara gu'da suna yarawa suna maganar wannan haka yake,

"To wannan Kayan amaryar mune don munsanta tanasan 'kamshi itada aunties 'dinta na uwa, humran ciki Kuma abawa aunties 'dinta na uba(bawaa)"

Sosai sukaji da'di both dangin Ummi Aishan kanurin 'bangaren hafsat dasu sadeeya aunties 'dinta na uba da irin wannan karramawa da aka masu,kanurin 'bangaren hafsat sune suka fa'di yadda al'adar take Kayan basket 'din da aka kawo suka suka rarraba tsakaninsu sannan suma suka basu nasu tukwicin kamar yadda akeyi,wasa suka dingayi tsakanin Fulani da kanuri kamar yadda akeyi ada suna tsokanar junansu kowanne yana kare yarensa,sannan aka kai dangin ashraf babban parlor din gidan da abinci da aka jere musu na buffets/serve ur self,,,Se 'karar cokula kakaje(nima miss xoxo special kujera naja naxauna naci nai nak tattass na lashe kwano na!No shame!)bayan dangin ashraf sunci sunsha suka Fara haramar tafiya nansuma gidan su Ummi Aisha sukai tasu bajintar ku'din tukwici sosai suka bayar me tsoka da lots and lots and lots of cartons na drinks,huge coolers na abinci shi akasaka kaji se manyan trays aka saka snacks harda gasassun kifi,mjay Kuma tata tarbar gashashshen rago taiwa dangin ashraf suka tafi dashi,godia both dangin couples din sukai wa junansu anyi raha kamar sundau shekaru da sanin juna,Hafsat dake 'daki Banda sallolin nafila babu abinda takeyi na Allah yasa yadda aka kawo lefen nan a sa'a yasa agama komi a sa'a yamaida kowa gidansa lapia yakuma ka'de fitina amiin,

Kafin kace me magajiya,muna_b da baby Kay sunbar wurin suntafi bangarensu ba'kin ciki karara a fuskarsu sede Allah ya kyauta kawai,kowa yayi murna ciki harda su sadeeya kannen captain adam,lefe yasha 'dauka a hoto yakuma sha posting a social media,,mutane sunyi addua Kuma sun kashe tsutsar idonsu,duk maitar mutum sede ya hakura base yaga 'karshen Kayan lefen nanba don yawon Kayan maidasuma aikine,sede muce Allah yasanya alkhairinsa ciki amiin,an tsaida date 'din biki wata 'daya cif on 28 of janaury shine ranar da aka tsayar na 'daurin aure,

Da dare captain adam yaga lefen yakuma sanya albarka,Hafsat ma haka dayake atare suka gani,Ummi Aisha kuwa se washegari da safe suka sake gani itada Waliyya,sosai tayi mamakin wannan Kayan haka kamar wani mini mall ace duk natane??lalle Allah shine abin godia me azurta wanda yaso aduk lokacin dayaga dama,a washegarin Mjay tafara bawa hudayya order na Kayan events din Ummi Aisha Wanda amaryar xatasa,akuma ranar suka shiga kasuwa fitar da anko na events kamar yadda Mjay da Waliyya suka tsara,xa'ai bridal tea party,kamu,elegants eve,yini,royal ball,dinner da kuma wushe wushe night ,gala night, duk haka suka tsara danda captain adam beyardaba Mjay ta nace da magiya da komi sedaya shafawa kansa lapia ya yarda,amma duk wannan abin da ake ko sau 'daya ashraf tun rabuwarshi da Ummi Aisha besake kiranta ba,har aka kawo lefen ake Kuma shirye shryen biki tun tana damuwa harta ha'kura se addua datasa agaba kawai...



"Gaisuwa mai 'dimbin yawa tareda fatan alkhairi xuwa ga masoya makaranta littafin
UMMI_A'ISHA
(THE MAGNIFICENT)
Kunjini shiru famanai da kumburin ido, naga messages 'dinku na fatan Allah yabani lapia,Alhmdlh Allah yabani lapia ngd sosai da addu'oinku*i love y'll beyond words*
Team#UATM🎊




WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;NANA HAFSAT.....
[4/18, 11:59 PM] Asy Khaleel: •✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
81

©®MISS XOXO
👄

DEDICATED TO;
UMMI_A'ISHA👌🏼

nanahafsat.wordpress.com

•✨•✨•✨•✨•✨•

Shirin biki ake ranga ranga from both site na couples 'din bikine Wanda kowa yake lale marhabun dashi,kasancewar ashraf shine namiji babba agidansu Kuma shine auren farko daxa'ayi na babban 'da namiji agidan,to ta 'bangaren amarya Ummi Aisha ma hakan take shiri ne aketata yinsa bikin fari Kuma bikin babbar 'diya agidan....Ankon dasu Waliyya suka fitar yayi Kyau ba 'karya kafin kace me ya 'kare ansake ordering wasu,kowanne event da ankonsa sede ba a tsawwala ba iya nagida-nagidah ne kawai xasuyi amma saboda halin karamci da dattako irin na hafst shiyasa har ma'kota wasu sukai dashin xubin 'daukar farko dukde akan suma su samu suyi ankon Ummi Aishan.

Sosai hafsat da 'yan uwanta suka shiga gyaran Ummi Aisha,gyara ne akeyi matashi wanda yakama daga gyaran jiki ciki da wajensa,harwani 'kamshi ne yake tashi na musanman inde taje waje koda kuwa giftawa tai,yakaka kala itace wadda ke mata gyaran jikin,yanxu kam babu laifi Ummi Aisha tafara maida jikinta duk 'kasusuwan wuyanta dasuka futo kamar sar'ka sunkoma ciki ta'kara fari hasken fatarta ta bayyana sosai,jikinta kuwa harwani luwai luwai fatarta tayi kamar na jarirai,sosai akayo iv cards kala kala na events 'din Wanda 'kwara uku daga ciki na gidansu ashraf ne xasuyi;bu'dan kai,barbecue day da kuma dinner se katin 'daurin aure na musamman da aka bugoshi,sosai akabi dangi da abokanan arziki aka raba masu katinan gayyatar,tun biki na rage sati 'daya gidan ya cika taf da yan uwa na maiduguri,jimetan yola,hadejia da Kuma 'yan kaduna angyare gidan tsaf har fenti aka sakeyi,sosai captain adam yabada ishashshen ku'di aiwa Ummi Aisha komai dakansa kuma tun sanda aka kawo lefe yatafi dubai yai mata siyayyar kayan gadaje da kujeru da komai ma daxa'a sanya agidan na kitchen ne kawai yabada ku'din asiya mata anan,ranaku suxo su wuce harde bikin Ummi Aisha ya rage saura kwana uku Kuma haryanxu ashraf baya kiranta awaya ba Kuma yaxuwa gidan koda ta kirashi baya 'dauka,

Washegari;

Xaune Ummi Aisha take ta kifa kanta tana rera kuka ahankali acikin 'dakinta,knocking 'kofar 'dakin akai da sauri ta mi'ke tana goge hawayen nata gudun kar agano kuka take kuma bataso ta tada hankalin ammin nata,itakam batasan me ashraf yake nufi da hakan ba,bu'de kofar tayi Waliyya ce tashigo janye da akwatinta da alama taxo kenan har agama biki,rungume juna sukai kowanne da murmushi a fuskarsa sun 'danyi hira kafin waliyya tace;

"Tawan meyafaru?!"

"Me kika gani bestie?!"Ummi Aisha tace hakan tana 'ko'karin 'ka'kalo murmushi,

"Haba tawan,ai baxaki 'boyemin damuwar kiba shekarar mu nawa tare?!kinsan halina nasan halinki wallahi kuka kikai Kuma akwai abinda ke damunki dan Allah menene?!"

"Bakomi bestie"

"Allah fa nace"

Hawayen datake 'boyewane ya xubo,tai saurin sa hannunta tana gogewa,

"Bestie bansan me ashraf yake nufi ba bansan meya 'boye cikin zuciyarsa ba,bakya ganin wannan auren da mukai akwai wani wani 'boyayyen lamari cikinsa?!nifa inaganin yasa ankawo lefen nanne kawai saboda wani abu daya 'kudurta azuciyarsa banso ingayawa ammi ne kada tasa damuwa aranta"

"To ke ki kirashi mana tawan"

Ummi Aisha tasa hannu ta'dakko wayarta agefen kujera ta mi'kawa waliyya,

"Duba kigani"

Kar'bar wayar Waliyya tai tagani sau 22 Ummi Aisha tana kiran ashraf be 'daukaba ga texts 'din datai masa nan ba'adadi,Ita kanta bataji da'diba bakuma taso ta nuna mata kada ta'kara tayar matada hankali,

"Babu komai tawan kicigaba da addua kawai kinsan dama dole ya'danyi fushi na wani 'dan lokaci amma I assure u komai xedawo yadda yake da yardar Allah,aida bedamu dake ba kotakaina baxe biba amma muna waya dashi muna shirya duk yarda xa'ai komai yacemin ma xasuje bridal tea party 'din shida abokanansa amma baxasu da'deba"

"Allah ya kaymu"tace ata'kaice,

"Yaya batin rigunan da xa'asa ranar bridal tea party 'din"

"Aikinsan yau mukace xamu kar'bo,jia ma hudayya fadoul ta aiko da kayana duka suna gurin aunt Mjay ta ajiye"

"To makeup artist 'dinfa wacece xatai meenah 'dince?!"

"A'a beejay ce xatamin sannan mekyaj fandy ma xatamin ,na ranar bridal tea party kuma monavee ce xatamin kinsan 'kawar aunty mjay ce tace xatamin kyauta"

"Allah yakymu tawan aizamu matso kyau"

Daria kawai Ummi Aisha tai,sannan suka cigaba da hirarsu ta yadda bikin xe kasance,

Rana bata 'karya sede uwar 'diya taji kunya yau take 23 ga watan January 2017 ranar farko da xa'afara hidimar bikin Ummi Aisha,bridal tea party shine event 'din xa'a fara dashi Wanda iya couples 'dinne kawai xasuje da Kuma frnds dinsu wanda xa'a yishi a royal tropicana,'karfe 7;30 shine lokacin daxa'a fara event 'din tun safe su waliyya ke shirin event 'din 'kawayen Ummi Aisha kaf sunxo dayake hardasu xa'aje wajen make up din kowacce tace xa'a mata casual makeup ko Allah xesa suma su samu nasu mijin acan, rigunan su suketa gwadawa wanda bayan rigan ke arubuce boldly daga sama da btp (bridal tea party) se tsakiyan of se 'kasan Kuma ansa#UMASH017(bridal tea party of Ummi Aisha and ashraf 2017)tun magrib su ummi Aisha suka tafi wajen kwalliya bayan sunyi sallah,suna xuwa can tasa rigarta aka fara mata kwalliyan,sanye take cikin doguwar rigan 'floral cape dress'amma iya gwiwa ce rigan se wando irin me ha'de da 'kafarnan,rigar blue ce wandon kuma yellow ne,ammata curly gyaran gashi ya kananna'de wuri 'daya harda crown tasa,takalminta da accessories 'dinta duk blue ne,tayi Kyau beyond beautiful she looked super adorable,kamar ba Ita ba,'kawayen nata ma sunyi kyau kamar ba gobe,sanye suke da rigar shirt ce dama se wasunsu sukasa leggings wasu Kuma jeggings sukasa wasu ma skirt sukasa but they looked beautiful dayake shirt 'din yellow ne da rubutun blue ajiki,duka monavee tai blending masu kyansu sosai suka futo cass dasu,su waliyya kyau kamar ba gobe,baby kay ma tayi kyau dukkoda ba'kin ciki ne fal ranta musanman dayake saura wata 'daya da kwana goma magajiyan iddarta ta 'kare sunrasa madafa kullum cikin sabon ciwo take gashi sun kasa dena nuna hassada akan auren,'kawayen amarya tundaga kaduna wasu sukaxo sauran Kuma yawanci duk course mates 'dintane yan buk,7;40 dot suka fara tafiya royal tropicana donyin event 'din,hall 'din cike yake da springy flowers yasha decorations blue and yellow,ga abinci kala kala na buffet dogon dinning table akai me cin mutane 50cike yake da Kayan da'di dasu desserts harda su ice creams different flavours ga cups na tea tunda bridal tea party ne kowanne cup 'dauke yake da #umash017 ajiki,'kawayen amarya su suka fara gaba yarage daga waliyya sai Ummi Aisha dake jiran jay yaxo 'daukarsu suna jiransa wurin kwalliyan dake titin lamido cresent,se gurin 7;50 dede jay yakira waliyya kansu fito yaxo,

"Kinyi Kyau tawan"Waliyya tace da Ita lokacin da suke sakkowa daga stairs na makeup studio 'din da aka masu kwaliiya

"Allah bestie?!nikam bakiji yadda nakejiba kamr na fasa xuwa gabana fa'duwa yake"

"kinsan farko dama haka akeji sekisaki jikinki tunda yaune farko akwai many more events agaba wanda mostly da rana ne ma"

Daria suka kyal'kyale atare sannan suka 'karasa sauka daga kan stairs 'din hango jay sukai tsaye ajikin motarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login