Showing 1 words to 3000 words out of 107296 words

Chapter 1 - UMMI A'ISHA(THE MAGNIFICIENT) COMPLETE

22 Aug 2024

7688

[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: 20/12/2016. 4:00
•✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
1

STORY AND WRITTEN BY
MISS XOXO👄

Copyright©by miss xoxo
No part of this novel may be reproduced,stored in a retrieval system or transmitted in any form or by any means electronic,mechanical photocopying or otherwise without the prior permission of the writer(I)..akiyaye hakkinane basiratace duk Wanda yai hakan nabarshi da Allah!!

This book is dedicated with love and appreciation to my wonderful co writer UMMI_A'ISHA💕...

Bismillahir rahmanir Raheem.....✍

•✨•✨•✨•✨•✨•

Tasss ta bata wani kyakkyawan mari me tafiyar da mutum lokaci daya.. Sannan dayar wadda suke tare itama tasa hannu ta tunkudeta ta fadi akasan tiles din dake a parlor din dagudu Wata yar'madedeciyar mata tafuto daga kitchen da alama me aiki ce tana fadin"aunty lapia naji kara haka?!tana isowa parlor din taja tai turus ganin wa'enda suke a parlor din Se huci suke inda sabo sunsaba xuwa suyi haka wani lokacin har ita suke hadawa siwa lilis sosai tabo na a dukkan jikinta na dukan dasuke mata baxasu irguba ,"murya narawa ta tsugunna har kasa tana gaishesu ina wuninku addah surayya da addah sadeeya?!wacce takira da "addah surayya tana wani sunce mayafin datai damara dashi a kugu Sannan ta yafa akanta tana huci kamar tsohuwar karya tareda kada idonta Ta aikamata da wata muguwar harara tajefawa yar'aikin. dabamu wuniba xaki ganmu yar'aiki?! Nayi tunanin yauma xaki shisshigin dakika saba kice xakisaka wannan hannun naki dayasha kanta kice xaki rabiyar fadan wannan yar iskar tasa hannu Tana nuna matar dake kwance akan tiles da alama she's unconscious kila ta suma ma.wannan juyar (wadda bata haihuwa)dan kwa juya xance tunda bata aikin Komi sede taci Tasha tacika masai da kashi Allah ya isan wanmu daya auro Tama Wlhy kila kyanta da kalar datake dashi yarude shi dama mata sekace aljana Dan Kyau.. shekara kusan 20 ba haihuwa kullum jiya'i yau da ike angama dashi tawanke tabashi yasha ai yakasa Komi kullum cikin fadar basu cire rai... Bata karasa maganar ba wacce aka kira da "addah sadeeya tace enough surayya kina bata bakinki kina wa yar' aiki magana dallah xomu wuce mutafi dukan wani satin inya xagayo Ma seyafi wannan wallahi..Sannan suka fice ,itade yar'aikin bata tanka masu ba Se rufe kofar datai Sannan ta koma tana jijjiga matar dake kwance kan tiles din batako motsi"aunty,aunty..shiru kakeji bashiri tai kitchen tabude freedge tadakko ruwan gora me sanyi tabude ta yayyafa wa matar,,cikin ikon Allah kuwa matar tafara atishawa tana rike da kanta dan yadda yake sara mata kamar ze fado dan ciwo tarike kan tana salati Sannan tai addua tagoga akan.."dakyar tabude bakinta tace haule temakanni da pain killer cikin drawer jikin tv..da azama haule tamike tadakko takawo mata Sannan tace tadakko mata ruwa marar sanyi xatasha maganin dashi. Tasha maganin kenan tabude baki"tace haule temakanni nahau kan kujera Dan Allah .rufe bakinta keda wuya wani dattijon mutun yashigo ciki fari kyakkyawa yanada tsaho da jiki madedeci fuskarsa dauke da murmushi kamar kullum yashigo da dan trolley ahannunsa dakuma leda a dayan hannun "yadan daga murya Yana fadin Hajia Hafsat nadawo ai tafiyar nan baxata yiwuba yau..cak yatsaya da maganar lokacin da muryar haule me aiki ke reto akunnensa Tana fadin sannu da dawowa abba,ganin Hafsat dinsa kwance akujera goshinta yakumbura yayi suntum ga kuma parlor din yayi kaca_kaca da alama wani abu ya faru!

Bashiri yasaki trolley da ledan hannunsa akasa yanufi inda Hafsat din take Sannan yadagota yadora kanta a cinyarsa Yana duba goshin ga jikinta yadau zafi rau sosai daka ganta kasan batada lapia.."ahankali yace my Hafsat meya faru?! dakyar "tabude baki tace hayatee(rayuwata,my life)bakomi bigewa nai da...setai shiru Tana naxarin da mexatace tabige Sannan tace ruwane yadan xube kan tiles shine na zume nikuma nabige da tiles dinnan Sannan Ta sunkuyar da kanta kasa Dan bata taba fadawa mijin nata cin kashin da yan'uwansa suke mata ba Sannan tace haule Ma karta soma fada sosai sunfi shekara 15 suna ci mata mutunci amma dede da rana daya bata taba fadawa mijin nata abinda ke faruwa ba.. Sosai yaji tausayinta Sannan "yace toh sannu my Hafsat kiringa lura pls shisa nace akaro wata wadda xata dinga kula dake kinki ,banasan kina wahala my Hafsat .."Hajia Hafsat tai shiru azuciarta Tana yaba yadda mijin nata ke sonta baya san ganin bacin ran nata ko kadan yawanci idan tai masa maganar ya'ya yakance ita yakeso ya aura bawai danta haihu ya aureta ba,hakade yake yawan fada mata kyawawan kalamai masu sanyaya zuciya. " my hafsat kinyi shiru' "Hajia hafsat tace haule Ma kadai Ta Isa hayatee ,Sannan tadanyi murmushi Ina tafiyar kuma naga kadawo ?! Yai Daria da dimples dinsa suka lotsa Sannan yasa hannu Yana gyara mata gashin kanta "my hafsat wallahi wakili natura Dan wani bangare na zuciana Yana cemin Kai mijin hafsat kakoma gidah your Hafsat ba lapia kawai naji baxan iya tafiya nabarki ba shiysa nadawo ashe ashe dagaske ne bakida lapia wannan tiles din yazumeki,gobe xansa acireshi asa marbles ma..Hajia Hafsat tai Daria calm down hayatee baruwan tiles dinnan ruwane yaxube fa,haka kwanaki fa daga tv yajani seda kacanxa TV sets din duka uhm uhm hayatee nide kabarshi Allah Bakomi nawarke..sosai sukai Ta Hiran soyayyarsu kaman basu manyantaba ya Allah kabarmu damasu sonmu!ledan daya siyo yadakko kaji ne ciki soyayyu sekuma bracelet na azurfa mekyau dashi anrubuta*my hafsat *ajiki.sosai Hajia Hafsat tayiwa hayatee dinta godia danbaya gajiya da faranta mata rai.hugging dinshi tai tana hawaye "I so much love you hayatee Allah yabarmun captain adam dina amin...

WANENE CAPTAIN ADAM ABDULRASHEED?!

Shide asalin captain adam abdulrasheed Dan asalin garin hadeja ne,don dukkan iyayensa uwa da uban duk yan' cikin garinne.amma yanxu iyayen nasa suna garin kaduna,ko ince mahaifiyarsa na garin na kaduna Dan mahaifinsa Malam abdulrasheed yadade da rasuwa..suna zaune a unguwar dake kaduna wato Halliru dan toro dake malali GRA!
Itakuma mahaifiyarsa Hajia ateeka yar unguwar kasuwar kofa ce dake garin na hadeja ,aikine yakawo me gidan nata kaduna Wanda Allah yayi nanne wajen zamansu.

A nan garin kaduna suka haifi dukkannin ya'yan nasu sunada ya'ya guda 5 alhaji sameer shine babba Se Capt. Adam Wanda sailor ne se kuma kannensu mata wato addah surayya da addah sadeeya Se karamar su bilkisu.kafin rasuwar mahaifinsu yakasance business man ne Yana saro kaya Sannan sunada shagon saida laptops dakuma makaranta takoyarda computer ..babarsu itakadaice awajen babansu har Allah yakarba ransa.yakasance harkar da mahaifinsu keyi Ta computers ita babban Yaya wato alhaji sameer yakeyi ,Sannan kannensu mata duk sunyi aure inda dukkansu a Kano suke da xama Se karamar wadda akai bikinta bara Tana zaune kadunan ita.

Tunda captain Adam yagama karatunsa yanufi gidan abokin babansa dake kano ,anan yasamu scholarship yatafi karantar bangaren sailor a mariners university of birmingham dake England.bayan dawowarsa sosai yasami aiki awani qualified company dake abuja..bayan dawowarsa ne idanuwansa suka hadu Dana nana hafsat ya' ga kanin abokin babansa..nande soyayya dakuma shakuwa Ta tsanani tashiga junansu harde abu yafito fili tana kammala secondary school lokacin Tana shekara 18 aka hadasu aure da captain adam..sosai sundace da junansu Dan nana hafsat karshe ce akyau to shidinma captain Adam kyakkawanne,ashekarar yanema transfer daga Abuja xuwa kano ashekaranne kuma sukai aure suka tare a unguwar sardauna crescent dake badawa kano...shiru shiru nana HAFSAT na xuba Ido amma haihuwa shiru takanyi kuka tasa kanta cikin damuwa amma "captain Adam Yana kwantar mata da hankali tareda fadin da haihuwa da aure da mutuwa duk lokacine arubuce yake.tun yan'uwnsa naganin kamar xata haihu shiru kakeji wai maye yaci shirwa tuni suka fara jefa mata magana.. da lokaci ko ince shekaru suka shude abu seya canxa tuni raini yasake shiga tsakaninsu ganin bata tanka masu kuma da alama wannasu bashida masaniya akai ganin bata fada mai ba besaniba,Se duka kuma da gorin fadin juya ce bata haihuwa sede taci tai kashi takwnta tai barci!!!


•✨•
nanahafsat.wordpress.com Gamasu neman books Dina to albishirnku duka nasakasu cikin blog dina har Wanda muke yi yanxu DANNAN KIRJI..dakuma sabo kuma Wanda yasake xuwa da unique idea da yafi NAUFAAL ..wato UMMI_AISHA.(THE MAGNIFICENT)kada kubari abaku labari....!!!!


WRITTEN BY THE ELOQUENT WRITER;MISS XOXO👄
[4/18, 11:56 PM] Asy Khaleel: 21/12/2016. 3;30
•✨UMMI_A'ISHA✨•

(THE MAGNIFICENT)
2

©•MISS XOXO
👄

DEDICATED TO UMMI_A'ISHA👌🏼

•✨•✨•✨•✨•✨•

Kodah safe bayan Hajia Hafsat ta tashi sosai ta taya haule me aiki gyara gidan Sannan suka hau shirye shiryen kayan breakfast:soyayyen Kosai dayaji hanta da kwai sukai Se plantain da aka soya dakuma doya gefe daya kuma lafiyayyen kwai ne da yaji vegetables Se soup din Kayan ciki dakuma kunun shinkafa dayaji kayan kamshi..sosai suka jereshi a katon dinning table dinsu Wanda xeci babban family of 15.sannan haule tasaka turaren wutan gaf gaf daya hautsine ko'ina da kamshi kamar a company din alharamein ,daki tashiga sannan tawuce bandakin dake cikin dakin Sannan tafaffesa turaren wuta dakuma toilet perfume eu de toilete sosai kamshi yahau tashi.."bude curtains din dakin tayi Sannan tadan daddaki gefen gadon hayatee,hayatee katashi kashiga wanka nahada maka ruwan,gashi har rana tafara fitowa yau kam kasha bacci abinka ka more..

Da salati captain Adam yatashi Yana mika wai my Hafsat Nagode sosai danma Allah yaso natashi nayi asubah a masallaci aida yau bansan mexankira kainaba kaman Wanda tse tse fly yaciza, Hajia Hafsat tai daria to atashi ashiga bathroom nahada Komi inka fito kuma your favourite breakfast na jiranka kan dinning "Capt Adam yai murmushi your wish is my command my Hafsat sena fito Sannan yamike yashiga bathroom Yana yaba kamshin dakuma yadda Hafsat dinsa tagyara ko'ina tsaf dukda kullum haka takeyi amma tsafta irin Tata gaba takeyi abin nata Yana matukar birgeshi sosai yakejin sonta naratsa bargon jikinsa.

Kodah yafito daga wanka ,yadi fari kal a goge yagani kan gado dakuma hula da takalmi a goge shima tayi polishing dinshi agefe ga turaruka da mai samfarin Vaseline na kasar waje shima ajiye agefe ,murmushi yai ganin yadda Hafsat dinsa ke kula da tarairayar sa tun sanda sukai auren saurayi da budurwa gashi yanxu shakera 20 kenan kuma babu abinda yacanxa nadaga kulawar dasuke baiwa junansu haihuwa ce kadai Allah bebasuba kuma har yau basu fitar darai kan hakan ba.cikin shirinsa na dattijantaka yai sauri ya kammala sa kayan nasa Sannan yanufi dinning area dake parlor din,sosai kamshin aroma din abinci yafara masa sallama bashiri yakarasa cikin dining area din Yana my Hafsat your aroma is calling ,Hajia Hafsat ta durkusa tagaysheshi Sannan ta Kamo hannunsa suka xauna akan kujerun sosai tai serving mijinta cikin plates dakuma mugs atare suka xauna sukaci Komi suna feeding junansu abin gwanin ban sha'awa.

BAYAN sati daya ; captain Adam yai shirin xuwa headquarters dinsu dake abuja kamar yadda yasaba duk weekly,sosai Hajia Hafsat taji badadi Dan bakaramin kewar mijinta take ba in yatafi duk koda inyadade acan yai kwana 3 gashi tasan yan uwansa dole suxo su nada mata na jaki kamar yadda suka saba,adaki suke tare dukkansu da safe da alama alokacin xetafi Yana kallon mudubi Yana gyara karin hular Kansa sanann yadora akansa sosai yayi masifar Kyau kaikace saurayi ne dan shekara 30 baxaka taba cewa yawuce shekara 50 ba sosai yabi lungu da sako najikinsa Yana fesa turaruka, itakuma Hajia Hafsat Tana gefen drawer Tana shirya masa kaya cikin trolley dinsa,Yana gama sa links din hannun rigarsa yajuyo yakalleta yadda jikinta yayi sanyi ga idonta ya ciko taf da hawaye ,asanyaye yakara sa kusada ita yajiyo da ita amma taki kallon face dinsa danbatasan yaga damuwar dake face dinta dakuma hawayen dake kokarin zubowa a'idonta ahankali cikin sanyayyar murya yake fadin"my hafsat,Sannan yasa hannu yadago habarta tareda rungumota jikinsa ,"bansan kukanki please my hafsat kiyi hakuri kidanne zucianki karkiyi please idan kuma tafiyan ne bakiso inyi wallahy xaki mamakin kitashi da safe kiganni agarin kano,mexan samo acan abujan dayafi farin cikinki my Hafsat?!please kifadamin mekikeso?!dakyar Hajia hafsat tadedeta muryanta tareda kokarin maida hawayen nata cikin ido "hayatee bakomi,wani abune yadan shigarmin Ido kakka damu Allah yakaimun Kai lapia yadawo dakai lapia of course I'm gonna miss my hayatee but bayan haka bakomi.capt Adam yai murmushi yasa hannu ya gyara gashin kanta Yana Shafa bayanta it's okay my hafsat insha Allah baxan dadeba xandawo ko ina naje afadin Dunia kisani Ina tare dake,haka suka danyi hiran soyayyarsu Sannan tarakashi parking lodge din dake gidan driver yajashi Se airport xuwa federal capital territory!

Asanyaye tadawo cikin parlor din taxauna tana daily tunanin ta,hawaye ne suketa reto a fuskarta ahankali tashiga yin magana abin tausayi.."Allah kayayemana damuwar dake cikin zukatanmu/zuciyoyinmu!yanxu diyar amina hartakai shekara goma shabiyar,"ya rabbi kayafeni ubangijin Rahama kasa inadaga cikin Wanda xasu dace da kyautar ya'ya hakika ya'ya rahamane,"wannan cin mutunci da kannen mijina sukemin nagaji dashi Sannan tasa tissue Tana goge hawayen fuskarta "naga suma basu sukaba kansuba kuma bawai Allah yafi sansuba,amma sundau kyama sundoramin saboda banida ya'ya ,,"gashide ba inda bamu xaga a dunia ba ance banida Wata matsala hakama hayatee,Toh bayadda xanyi amma basa gani ,"ya rabbi kasakamin kadorani akansu fiye dayadda suka daukeni,Tana cikin maganan ta haule me aiki tashigo ciki ta tsugunna akasa "aunty mexa'a dora da rana?! Hajia hafsat tai shiru kamar menazari Sannan tai ajiyar zuciya "banajin xan iya cin komi haule ,kidafa maku kawai duk abinda kike ra'ayin ci keda hannafi da modu(guardsmen)"haule tai kalar tausayi hakika tasan abinda ke damin auntyn tata dama kuma damuwar bata karuwa harse Capt Adam yakoma wajen aiki,ga fargabar xuwan yan' uwansa kowanne sati da irin kalar rashin mutuncin dasuke xuwa suyi mata shi.shekara goma kenan da aikin haule agidan kuma duk sati yan'uwnsa kexuwa su badawa idonsu kasa a ido su zubamata bolar dasuka kwaso,amma dede da second daya Hajia Hafsat bata taba shedawa megidan nata abunda ke faruwa ba,sosai haule me aiki ke mamakin dama akwai saurin mata irin haka kamar Hajia Hafsat adunia?!to inma akwai su tabbas wasu tsirarine dabasu da yawa,da wannan tunanin da haule takeyi tamike bayan tace "Toh aunty Sannan takoma bakin aikinta a kitchen "yinin ranar haka Hajia Hafsat ta wuni batasa komi cikin taba Se ruwa,sefa aikin amsa kiran da hayatee dinta ke mata,har dare suna manne awaya Sannan bacci barawo yasaceta...washegari Ma abin da yafaru kenan dayake ba gwanar cin abinci bace dakyar haule ta roketa Sannan Hajia Hafsat Ta amince tace haule tamasu faten dankali da bushasshen kifi(smoke fish)! "Washe gari bayan tafiyan Capt Adam da kwana biyu ,Hajia Hafsat ce zaune akan darduma(praying mat)da alama sallah tai ta idar,gefe daya kuma littattafan zikirine da carbi,Se alqur'ani a hannunta Tana karantawa tana Kai aya tarufeshi sannan ta shafa a fuskarta tareda rufewa,Sannan tamaida komi inda yake ,jin kanta Yana ciwo yasa tadan mike akan gado nan take bacci yai awun gaba da ita..

"Addah surayya ce tai sallama tashiga parlor din gidan addah sadeeya dake unguwar Daurawa maiduguri road tarauni..."Tana shiga tadafe haba oh ni surayya,sadeeya kina nufin baki shirya ba wallahi kinfiya shininniki Allah de ya kyauta,.."sadeeya tai Daria Wlhy ni jikina ne yai sanyi karfa muje muga yaya Adam yadawo kinsan Wlhy da kashin mu ya bushe ranar,"surayya tai tsaki kede wannan yarinya da danbanxan tsoro kike kinmanta kwana uku yakeyi ne,kuma Se dare yake dawowa "Dan Allah tashi ki shirya kixo muje ni hannuna kaikayi yake gwara muje mu jibgi banza kinsan Allah nifa bawai danbata haihuwa kadai na tsaneta ba a'a ,"wallahi shegen kyawun datake dashi nakejin tsanarta araina wannan datana da ya'ya musamman ace diya mace wallahy dakinga layin zance agidannan to Se Allah yasan manufar jaki dabeyishi da kaho ba........

•✨•
3

"Addah sadeeya tai Daria kai safeeya lalle kinfini tsanar matarnan,ni abinda yafi damuna yadda Yaya Adam yadau son dunia yadora wa matarnan yadda kikasan itakadaice mace adunia,"addah safeeya tai tsaki kyaleshi can daya banzan,"yawwa nikwa yamaganar magajiyan inno Fanta??kinsan fa lokaci yanadada kurewa inbata aminceba munemo Wata kawai,"addah sadeeya tace ohh about that ?!well munyi maganr da ita takuma amince tace inde har ya aureta to filin kofar na'isa yaxama namu Sannan gidan kajin nan dake lamido terrace shima yaxama namu,addah safeeya tabata hannu suka tafa"tareda doriyar yawwa yar'gari yanxu naji zance Kice muma munada rabon namu arzikin ashe..

"Addah sadeeya tace kwarai kuwa yanxu de gwaggo kawai zamu samu mushawo kanta tayadda Yaya Adam xeyadda ya amince ya auri magajiyan inno,,kinsan dadina da gwaggo saurin daukar zancenmu tai amfani dashi,"addah safeeya tai Daria kwarai kuwa yanxu de isauri kishirya kixo mutafi Dan Allah .."suna gama shirinsu suka haye Dan sahu se unguwar sardauna crescent dake kano ,"suna xuwa addah sadeeya takalli modu megadi dajikinsa yadau rawa danbaxe taba mantawa da marin da ta sharara masa ba.. ranar daya hanasu shiga gidan sanin rashin mutuncin dasuke yiwa matar oga."ayatsine tace dashi kai megidan nacikine yadawo daga tafiyan?! Modu murya na karkarwa yake fadin a'a beda...bedawoba,,ko kallon inda yake basu karayiba suka sa Kai suka shiga ciki .

"Parlor suka shiga inda kamshin faten dankali dayaji kifi yafara dukan hancinsu,adakile addah sadeeya kefadin eh lalle munxo adede kenan,cikin kitchen din addah sadeeya tashiga tana kallon komi daya bayan daya ga tukunyar Akan gas tanata zabalbalar girki,haule

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login